Showing 63001 words to 66000 words out of 194715 words

Chapter 22 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

970

bata san ka ba da bazata zo kusa da kai ba please she's pregnant kuma ina bala'i son cikin nata sosai" shiru Michael yayi kamar bai san da mutun a wajen ba, shi kuwa Copper tun da ya riga ya ansa umarni sai ya daka haushi mai razanar da kwakwalwa wadda yasa matan fasa ihu suka watsa a guje, kamar jira Copper yake yabi bayan su, yana gudu yana girgiza jikin sa, kuka sosai Dest ya fara ya ci-gaba da rokan Michael a kan ya dakatar da Copper kar cikin jikin matar sa ya zube, shi kuwa John da gudu yabi bayan su Copper duk da yasan ba zai iya dakatar da Copper ɗin ba, dan ba wanda ya isa ya dakatar da shi sai Michael ɗin da ya haɗa su da shi,

shima Test duƙawa yayi suka haɗu suna rokan Michael dake zaune yana latsa wayar sa hankalin sa kwance.


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo


*💞The beginning💞*


*Episode 15*


_____gudu sosai yan matan suke kamar zasu yi hauka suna kurma ihu, shi kuma Copper yana biye da su, haka suka bazama cikin school ɗin basu san in da suka nufa bama.

Suna gudu suna waigowa su kalla ko Copper ya kusa kamo su, matar Dest bata an karaba ta juya tana kallon Copper sai ji tayi ta bugu da mutun, baya baya tayi ta faɗi kasa, tare da fasa ihu,

ba shiri ɗayar yarinyar ta ja birki da gudun da take ta waigo dan ganin ko dai Copper ne ya kama matar Dest ɗin yasa take ihu, a guje Copper yayi kan ta da niyar cizon ta, a guje ta miƙe dan ta gudu bata lura da mutumin da tayi karo da shi ɗa zun ɗin ba, still yana tsaye a wajen tana kallon su, tana kokarin gudu ta sake yin karo da shi tayi baya zata faɗi, da sauri yasa hannu ya riƙo hannun ta tare da janta tayi ta bayan sa, daka sufa Copper yayi yayi kansu, a fusace James ya kai masa bugu a kai sai da yayi baya ya faɗi kasa,

a sukwane ya miƙe tare da daka haushi mai karfi yayi kan James ɗin yana buɗe baki kamar mayin wacin zaki, duƙawa kasa James yayi ya damko makogoran Copper ɗin tare da zaro manya manyan light ash eyes ɗin sa, cikin tsawa yace "put your eyes into my own!!"

Ganin James ne yasa Copper daka haushi mai tashin kai kana ya dukar da kan sa kasa, sakin makogoran nasa James yayi tare da miƙewa tsaye, cikin tsawa yace da Copper "Muje in da ka fito" juyawa Copper yayi ya wuce ya mufi *community garden*
ba tare da James ya yiwa su matar Dest magana ba ya wuce yabi bayan Copper, cikin sauri suma su matar Dest ɗin suka bi bayan sa.

Michael na zaune sai rokan sa Dest da Test suke amma bai kula su ba, da suka dame sa sai ya miƙe a fusace ya fara jibgan Dest kamar an aiko sa, fuskar nan tasa kamar hadari, gaba ɗaya student dake wajen sun tsorata dan basu taɓa ganin Michael ya daki Dest ba, yanzu tsawon shekara 5 kenan suna tare basu taɓa ganin wani abu makamancin haka a tsakanin su ba.

Dest kuwa ganin Michael zai iya yi masa illa ne yasa ya miƙe da gudu ya nufi hanyar fita daga community garden ɗin, da sauri Michael ya damko kafar sa ya jawo sa, ya sanya kafa ya take masa wuya ga kafar nasa sanye suke cikin Booth na yan kwallo masu karfin nan, haka ya takewa Dest wuya ya zaro belt ɗin wandon sa ya fara zabgawa Dest ta ko ina a jikin sa, sai zaro ido waje Dest yake dan numfashin sa na gab da ɗauke wa baya mumfashi da kyau saboda take masa wuya da Michael yayi, da gudu Test yazo ya duƙa ya riƙe kafar Michael ɗin yana kuka yana bashi hakuri karya kashe masa ɗan uwa, ina Michael yayi nisa baya jin Test, kawai saukewa Dest belt nashi yake ta ko ina a jiki kamar wani zararre ga belt ɗin na shin da tauri sosai, duk ya fashewa Dest jiki, duk da hakan kuma bai kyalesa ba gashi kuma ya take masa wuya

gaba ɗaya student dake wajen sun tsorata sosai sun san halin Michael da zuciya amma basu taɓa ganin sa cikin ɓacin rai har haka ba, su kansu Lucky da Winston sai haushi suke suna goga kan su a jikin Michael ɗin kamar suna dannan sa yayi hakuri.

A wan nan halin James ya iso ya same su, cikin nitsuwa ta baya ya anshe belt ɗin da Michael ke zane Dest da shi, a fusace Michael ya juyo dan ganin wani isasshene ya anshe belt, yana juyowa karaf idon sa ya sauka kan James dake tsaye fuskar sa babu alamar wasa ko kaɗan, ganin haka yasa Michael cire kafar sa daga wuyar Dest ya koma saman sofa ya zauna yana huci kamar wani zaki, kallon jama'ar dake wajen James yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Micheal "John Take him to *(HUHS) Harvard University Health Services*" yayi maganar tare da muna Dest dake ta kokarin bawa kan shi mumfashi, ma'ana yana kokarin jawo mumfashi sa ya saitata, da sauri John da Test suka ɗauki Dest ɗin suka wuce da shi HUHS, da sauri matar Dest da kawar ta suka bi bayan su

kallon tsab James ya yiwa Michael kafin yace "did he offend you?" Shiru Michael yayi sai huci yake kamar mayin wacin zaki "am I not talking to you?" James ya sake jefo masa tambaya, yayi maganar yana karasowa wajen sa, cikin fushi da tsawa Micheal yace "Why zai kawo min wancan banzan abun na shi a nan?" "Which Abu?" James ya tambaya da mamaki a face na shi "Matar sa mana" Michael ya bashi amsa, girgiza kai James yayi kafin yace "Wajen ka matar tazo?" Miƙe wa tsaye Michael yayi cikin fushi ya fara magana "Ba waje na tazo ba kuma bata isa tazo waje na ba amma ai yasan bana son hakan, bana son wayan nan azzaluman su raɓeni" zuba masa ido James yayi har sai da ya kai karshen maganar tasa san nan yace "Why kake haɗe mata dukka kace basu da kirki This is not good, ya kamata ka sani mummy daban suma sauran daban kamar dai yadda muke ɗin nan", gigitatchiyar tsawa Micheal ya daga masa a fusace yace "Stop James, stop talking about that human hare, she's not my mother at all, i came this world true my dad only, i hate that human i hate her more than your expectations, i don't have any mother in my life!!!"

Kasa da murya James yayi cikin muryan rarrashi ya fara magana "I knew it Michael, i know you hate mum and I, and i hate her because she had done bad thing to us, but this is not the reason, da zaka ce you hate all ladies in this world" dogon tsaki Michael yaja tare da komawa ya zauna yana faɗin "I hate all ladies I don't want to see tham close to me" shiru James ya ɗan yi kafin yace "Okey I agreed, know let's go back home i want to see you there, I want us to be discuss something" yayi maganar cikin sanyin murya

Tsaki Michael yaja kafin ya miƙe ya fice daga wajen rai a matuƙar ɓace, bayan sa James yabi yana mai matukar jin tsanar mum na su a ransa na karuwa.

Da sauri Copper Winston Lucky suka bi bayan su, sai mamaki student dake wajen suke

Kowa motar sa ya shige, kamar yadda suka saba haka lucky ya shiga gidan gaba Copper da Winston suka shiga gidan baya na motar Micheal, James na tsaye sai da yaga motar Micheal ta miƙi shinfiɗaɗiyar titin fita daga School ɗin san nan, shi ma ya tada motar sa yabi bayan Michael ɗin.

________________________________

*KADUNA*

Unguwar Malali

Kwance Umaisha take saman gadon su dake bedroom na su, tayi nisa cikin tunanin a kan Akil, while ita kuma Aafia tana ta fama da shirya kayan ta cikin drawer sanya kayan su, wayar Umaisha dake gefen ta ya fara kara alamar shigowar kira, sai da gaban ta ya bada dukan uku uku, tun ma bata ga mai kiran na taba,

cikin sauri jikin ta har kerma yake ta ɗauko wayar, My pleasure shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin, mamaki ne ya kamata wato shi Akil har suna ya zaɓawa kansa yayi saving number sa da shi, dan tana da tabbacin shine duk da bai taɓa kiran taba sai yau ɗin, ta san shi ɗin ne dan bayan shi bawan da ya taɓa mata waya, ko Aafia taki ɗaukar wayar dan tsoron Akil ɗin,

My pleasure ta mai mai ta sunan, cike da fargaba ta ɗauki kiran tare da manna wayar a kunnen ta, cikin sanyi murya tace "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Waalaikumussalam" "In wuni yaya Akil" tayi maganar cikin girmamawa "Me ya same ki?" Ya tambaya da ɗan tsawa, murya na kerma tace "Babu komai" "zaki faɗa min me ya same ki ne kosai na tashi na ɗauki mota nazo na same ki" kallon time tayi 11 na dare kuma ta san halin sa zai aikata, hakan yasa tace "Kayi hakuri zan faɗa maka" shiru yayi yana sauraron ta "Daman a kan School ne naji kace kar na sake fita ko ina kuma wlh ina bala'i son nayi karatu" ta kai karshen maganar kamar za tayi kuka "Ni kin ji nace kar kiyi karatu ne?" Cikin sauri ta girgiza kai kamar tana gaban sa, "A'a yaya Akil" "Kin iya mota?" da sauri tace "A'a ban iya ba" "Wan can dirty brother ɗin naki fa ya iya ne?" Gyaɗa masa kai tayi kamar a gaban sa tana faɗin "Eh ya iya" "Good zan sanya a kawo muku mota guda biyu ke ɗaya sister ki ɗaya sai ya koya muku ko?" Kasa ta kara yi da murya a nitse cikin fargabar abun da zai je yazo tace "Yaya Akil ka bar shi mun gode" wani gigitatchiyar tsawa ya daka mata wadda ya sa har wayar hannun ta ya kusa faɗuwa "Ke har kin isa in ce abu kuma kice na bari? To gobe da safe ina zuwa gidan, kai yanzu ma gani nan zuwa sai ki kalli cikin ido na ki faɗa min ko?"

Kallon Aafia dake tsaye ta Zuba mata ido Umaisha tayi, kamar zata yi kuka tace "I'm sorry yaya Akil ba zan sake ba, sai ka kawo motar muna godiya Allah ya kara arziki" dogon tsaki yaja tare da kashe kiran sa, ajiye wayar Umaisha tayi tare da sakin kuka mai tsuma rai,

haurowa saman gadon Aafia tayi tana faɗin "Ya isa haka Umaisha kiyi shiru" rungume Aafia tayi cikin kuka tace "Aunty Aafia wai shi kam wani irin mutun ne yaya Akil ɗin nan? Kullun cikin masifa da faɗa bashi da hakuri ga zafin rai" Aafia na kokarin magana wayar Umaisha ta kuma yin kara, a kule ta furta "Wai har da wani sawa number sa my pleasure, to yana sanin farincikin ne?" Ta kai karshen maganar tare da ɗaukan kiran ta kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Daman nasan kuka kike ai shi yasa na sake kira, bana hana ki kuka ba? Me yasa bakyaji ne? Tun yanzu kike yin abubuwan da na hana ki ko? Kina son ki ɓata min rai kenan ko?" Mamakin sa ne ya kara kama Umaisha wai shi wan nan wani irin mutun ne, ji yadda yake wani Magana kamar ba shi ya sanya ni kukan ba,

"Ba dake nake magana bane?" Cikin sauri tace "Kayi hakuri" "Aikin ku kenan sai kun yiwa mutun abu ku rinƙa bashi hakuri kuna cutar sa, to dai ki shirya gobe za'a kawo muku motocin guda biyu discussion continue and continue continue, ki ɗauki karamin ki barwa sister ki babban ku rinƙa zuwa school, zuwa gaba zan canza muku motar kina jina?" Da sauri tace "Eh muna godiya sosai da sosai" "Idan kinje School babu ruwan ki da kowa, karatu kawai nace kije kiyi, idan kika kuskura nasami labarin kina kula wani ba sai nayi magana ba kin san me zai biyo baya, san nan ina son ki mai da hankalin ga karatun sosai dan ni ina son wayayyiyar mace wadda tayi karatu sosai Allah ya ba da Sa'a" yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar taba ya katse kiran

Wurgi tayi da wayar gefen ta kamar zata yi kuka tace "Wai wan nan wace irinyar musifa ce" gyara zama Aafia tayi cikin nitsuwa ta fara magana "Umaisha kar ki ɓoye min ki faɗa min gaskiya kina son yaya Akil?" Ɗago ido Umaisha tayi tana kallon Aafia kafin tace "Eh ina son shi, amma bana son abubuwan da yake min, shi fa ba ruwan sa da wani soyayya umarni kawai ya iya bayarwa, sai shegen masifa da izzan na banza" dariya Aafia ta kwashe da shi har da riƙe ciki, a kule Umaisha tace "Me abun dariya kuma?" Cikin dariya Aafia tace "No wonder shi yasa mana kike bin umarnin nasa kuma kika nitsu ashe dan kina son shi ne, hhhhh lallai Umaisha nayi mamakin yadda kike masa biyayya kike biye masa ashe ashe, to zan baki shawara tun da har kina son shi so mai tsanani, dan wan nan so mai tsanani kike masa wadda yake sanya ki jure duk wani haukar da zai miki, to shawarar dai a nan shi ne a hankali ki rinƙa shi gar masa da kalaman soyayya a kan sa ki dai na zama shiru idan kuna waya ki rinƙa yi masa shagwaɓa In Sha Allah zai zo ya fara biye miki yana mayar miki da martani" shiru Umaisha ta ɗan yi kamar mai tunani

Can kuma ta ɗauko wayar ta cikin hanzari tana faɗin "Bari na gwada wani abu mu gani ko zatayi aiki" zuba mata ido Aafia tayi tana kallon ta, layin Akil ta kira, amma bai ɗauka ba sai ya katse kiran nata ya kirata, yana kira ta ɗauka cikin zumuɗi tare da shagwaɓe murya tace "Hello" "Lafiya kika sake kirana?" Ya jefo mata tambaya still dai da wan nan voice na shi mai kamar faɗan, kara shagwaɓe murya tayi kamar wata yar baby tace "Kai yaya Akil to na kira ne naji muryan ka, naji ina kewar kane" da sauri yace "Ke me kuma ya samu voice naki ban fa son munafurci ki ware murya ki min magana hai" zaro ido waje tayi tana kallon Aafia da ta zuba mata ido tana jiran taji ko zasu yi nasara ta ɓangaren shagwaɓa, tunani Umaisha ta shiga yi "wai shi yaya Akil shagwaɓar ma bai sani bane shi dai ko mai da karfi karfi ya sani innalillahi wa inna ilaihir rajiun" tayi nisa cikin tunani ya daka mata tsawa "Ke zaki faɗa min me yasa kika kirani ne ko kuma na kashe waya ta dan ina da abun yi!!" Haɗe rai tayi ciki ciki tace "Sai da safe" bai jira ta karisa ba yace "Idan kika sake kirana babu wani dalili sai ran ki ya ɓaci, dan ba aikin ki nake ba, da zaki rinƙa kirana babu dali kina ɓatamin lokaci bayan ina da abun yi!!" Ya kai karshen maganar tare da katse kiran, ɗaura wayar tayi saman bedside drawer ta kwanta kamar zata yi kuka, tun da Aafia ta ga yanayin face nata tasan basu dace ba dan haka ba sai ta tambaye taba ta kwanta a gefen ta kawai, suka jawa kan su bargo suka lukkuɓu, ba jimawa barci ya ɗauki Aafia ita kuma Umaisha ta jima tana tunanin Akil kafin daga baya barci ya ɗauke ta, asuba ta gari.

________________________________

*KANO*

Kamar dai kullun zaune Jelly take saman mirror chair daddy na gyara mata gashin kan ta, ya mata make up a fuskarta, ba laifi wan nan karon kam make up ɗin ya ɗan yi kyau, dan ya fara iya make up ɗin yanzu, sai murmushi take shi kuma daddy kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin matsanancinyar damuwa da tashin hankali duk ya rame ya sauya kamar ba shi ba, ya shiga tunani da damuwa, abubuwa biyu sun haɗu masa waje guda, abu farko contract da ya samu dole baban Muneer yace ya ajiye, Abu na biyu kuma baban Muneer yace dole duk abun da yake so shi za'a gudanar a filman na daddy, ma'ana company daddy, sosai daddy ya shiga damuwa a kan hakan dan yasan shi kenan time na rushewar company sa yazo, tun jiya ya rubutawa gomnati takarda a kan ba yason contract ɗin nan amma har yau babu reply, yana kuka yana rubuta later, duk ya rame yayi duhu kamar ba shi ba, babban abun da yafi damun sa ya ja masa raman nan, shi ne zina da a ka sashi yayi, wa iya zubilla san nan kuma har da video a ka ɗauke sa jama'a suna girmama shi suna kallon sa da mutunci, Allah ya sani shi mutumin kirki ne bana banza ba, yanzu idan video nan ta fita yake nan, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wan nan tunanin yasa shi yake ramewa ya shiga damuwa over.

"Daddy what are you thinking?" Jelly ta tambaya tana kallon hotuna a wayar sa dake hannun ta, kakalo murmushi dole yayi wadda yafi kuka ciwo yace "My Jelly ina tunanin kalar kitso da zan miki gobe ne" dariya tayi zata sake magana idon ta ya sauka kan hoton wani kyakkyawan puppy dog dake wayar daddy fari kal da shi, yar kara ta saki tare da furta "wow daddy I love this puppy dog please will you buy for me?" Kallo hoton daddy yayi kafin ya dawo da kallon sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login