Showing 168001 words to 171000 words out of 194715 words

Chapter 57 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

991

sannan kuma ya tashi ya bar wajen ba, dole ya jira sai Romeo ya sallame sa.

Miƙewa Romeo yayi ya nufi saman bene, zaro brown eyes nasa waje yayi a ɗan tsorace yace "Lion what happened to your hands naga jini na zuba ne" tamkar Romeo bai ji me Michael ya faɗa ba, ya wuce ya nufi part nasa ba tare da ya sake cewa Michael uppan ba.

Ganin ya tafi bai masa magana ba yasa Michael kara turo baki ya miƙe da sauri yabi bayan sa.

Dai dai zai shiga part ɗin Romeo, shi kuma Romeo har ya shiga yana fitowa, ɗan ja baya Michael yayi ya ba shi hanya, wucewa Romeo yayi jikin sa na sanye da puffer Jacket ya sanya hular jacket ɗin a kan sa, sannan ya sanya face mask, binsa da ido Michael yayi har ya fice daga palon kasa, shiru Michael yayi yana tunanin anya yau lafiya kuwa, me ya faru? Ina kuma lion zai je da irin wannan shiga haka? Ina James? Me ya samu lion a hannun sa yake jini? Sai jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su yake, daya ga tambayoyin suna neman su tarwatsa masa tunanin sa, sai ya hakura ya nufi hanyar part nasu, riƙe da agogon da Romeo ya bashi a hannun sa.

Ko da yaje wajen shiga part nasu, kasan cewar part ɗin sa dana James a gere suke waje guda, gajiya tasa ya shige part ɗin James a mai maikon nasa part ɗin

Yana zuwa yasa ruwa ya wanke jinin dake jikin watch ɗin ya kwance wanda president ya bashi, ya ɗaura wanda Romeo ya bashi yanzu,

Yana ɗaurawa ya haye saman gadon James ya kwanta, dan jikin sa duk a mace ji yake kamar bashi da lafiya, ba zai iya yin komai ba, sai ya kwanta kawai yana mai da numfashi, yana kwanciya watch nasa dake aljihun jacket ɗin jikin sa ta faɗo saman gadon, shi kuwa ya lumshe ido alamar barci yazo, ba jimawa barci yayi awon gaba da shi, ga watch ɗin dukka biyu suna jere waje guda, dan hannun sa dake ɗaure da watch ɗin yana kusa da asalin watch nasa da ya faɗo daga aljihun sa, shi kuwa yayi barci bai gani ba.


🏞️Dajin Colorado🏞️

Cikin karkashin kasa, wani ɗaki ne mai girma gaske a karkashin kasan, matasa ne masu jini a jika wadda a kalla zasu kai su 10 a cikin ɗakin, ga wasu manya manyan disturb computers dake cikin ɗakin, gaba ɗaya ginin ɗakin ba da block akayi shi ba, da dutse a kayi shi, komai na cikin wannan ɗakin da dutse akayi su hatta tables ɗin da wayan nan disturb computers ɗin suke kai, da dutse akayi tables ɗin, kowani matashin aikin dake gaban sa kawai yake, sun dukufa suna aiki tukuru, kallo ɗaya zaka musu kasan sun samu horarwa mai kyau, dukkan su fuskar su babu alamar annuri a ɗaure take tamau.

Daga wani keɓaɓen waje a cikin wannan ɗakin wutane yake ci awajen a gefe guda, gaba ɗaya cikin ɗakin ya kaure da ɗumi mai daɗin gaske

Kyawawan matasan turawa ne wadda ba za su wuci saanin James da Michael ba, su uku ne tsaye kan James dake kwance saman wata lafiyayyiyar bed mai kyau da tsada, kallo ɗaya zaka yiwa matasannan kasan sun samu horo damin kowanne su jikin sa a murɗe yake kamar dai na James, sai aiki suke cikin kwarewa suna kokarin yiwa James dressing in da bullet ya ɗan kuskure sa, ba wani babban waje bane, kasan cewar bullet ɗin kuskuran sa tayi ta wuce.

10mins suka ɗauka suna wanke masa wajen da hydrogen, kafin nan su sanya masa bandeji su ɗaure wajen, duk da cewa sun sanya chemical da ya tsotse jinin wajen gaba ɗaya amma dai sun kara masa da bandeji saboda tsaro

Kamar jira yake su kammala, suna gamawa ya miƙe tare da ɗaukan wani yar gora kusa da shi ya nufi wata yar hanya dake ɗan gefen su.

Har ya ɗan yi nisa, sai kuma yaji karan wayar sa, da gudu ɗaya daga cikin matasan nan ya biyo bayan sa da wayar a hannun sa yazo ya miƙa masa.

Karɓan wayar yayi tare da bin screen ɗin wayar da kallo, guntun tsaki yaja tare da mai da wayar aljihun sa ya ci-gaba da tafiyar sa, har cikin ransa yake jin raɗaɗin azaban zafin wajen da bullet nan ta kuskure sa, daurewa kawai yake yana tafiya.

Wani waje ya shiga mai kamar ɗaki, wajen wani dutse mai kama da table ya nufa, yana zuwa ya cire wayar sa daga aljihun sa ya ajiye a gefen sa, sannan ya fara haɗa wasu chemicals masu bala'i karfi

Wani gari ya ɗebo ya zuba cikin goran da ya ɗauko, sannan ya ɗauko wani kwalba dake ɗauke da wani ruwa kamar ruwan acid, cikin wannan garin ya zuba wannan ruwan kwalbar, shi da kan sa sai da ya ja baya lokacin da ya zuba wannna ruwan cikin garin, saboda karfin chemicals ɗin

Yana zuba ruwan wani kara garin yayi kamar an zubawa tafasasshen mai ruwan sanyi,

Zubawa chemicals ɗin ido yayi yana kallon yadda suke canza kamanni,

After some minutes ya kara matsowa ya jawo wata yar akwati dake wajen ya buɗe ya ɗan yi dube duben sa dan ya tabbatar komai na ciki

Ganin komai na ciki ne yasa ya rufe akwatin ya ɗauka tare da wannan chemical da ya haɗa ya juya ya nufi wasu maza guda biyu da suke sanye da kakin soja daya ɗaure su ɗaurin goro a wajen.

Tun bai kariso wajen su ba, suke girgiza masa kai alamar suna son yin magana domin ya rufe musu baki, ko kallon arziki basu samu daga wajen saba bare kuma su sa ran zai iya tausaya musu.

Wata yar kujera ya jawo ya zauna a gaban su tare da ajiye akwatin dake hannun sa da kuma chemical ɗin,

Akwatin ya fara buɗe wa, ya ciro wasu manya manyan almakashi guda biyu, a hankali ya fara datsewa sojojin nan yatsun kafar su da wannan almakashi, ga azaba amma babu halin yin ihu dan ya rufe musu baki, sai mutsu mutsu suke alamar suna jin azaba.

Yayin da James ke azabtar da wayan nan sojoji shi kuma Romeo yana can ɗakin hora masu laifi dake cikin gidan su, ya ɗaure manya maza su biyu, kana ganin su kaga marasa gaskiya, da alama yana son yi musu tambayoyi ne.

Ɗakin horar war nasu ɗaki ne mai cike da manya manyan makamai da injuna na azabtar da ɗan Adam mai laifi, ga masuna kala kala na hukunta mutun, sannan akoi chemicals iri daban daban har da su acid da sauran mugayen abubuwa, kamar ɗakin yaki, sannan ɗakin yana da girma sosai ga jibga jibgan sojoji masu jini a jika kewaye da ɗakin ta waje saboda tsaro

Gidan William jacop kenan gida ce hukumance mai zaman kanta, babu abun da ba zaka samu a cikin gidan ba, sai kotu, lawyer ma akoi alkalin ma suna da shi kotun ne kawai basu gina a cikin gidan, amma suna da asibitin su, suna da ɗakin horo, ɗakin doka, ɗakin karatu, duk wani abu mai mahimmanci suna da shi.

Gaban wayan nan mazan Romeo ya zauna saman kujera suna fiskantar juna, yayin da ya ɗaure su saman a nasu kujeran, shima ya rufe musu baki ba damar suyi magana.

Zubawa tattoo jikin su ido yayi yana kallon abun da suka zana A,N,D,L,R,C shine abun da suka rubuta ta ko'ina a jikin nasu, shiru yayi yana tunanin aina ya taɓa kallon wannan tambari, sosai ƙwaƙwalwar sa ke faɗa masa kamar a bedroom ɗin James ya taɓa gani, amma sai ƙaryata ƙwaƙwalwar nasa yake, dan baya son zargin yan uwan sa.

Amma da yaga duk wani tunani da zai yi sunan James tunanin yake bashi sai ya fara wasu tunani, ya akayi James ya iya harbi da bindiga ranan? Ya akayi ya iya tsere da doki? Ina James yake yawan zuwa? Idan suka tambaye sa sai yace party yaje, yanzu ma gashi yace musu ya tafi party a New York, anya gaskiyane New York ya tafi kuwa? Wayan nan abubuwa suna kamanceceniya da juna, wani tunani ne ya sake faɗo masa, anya wannan watch ɗin na Michael ne kuwa? Nan take zuciyar sa ta fara bugawa da sauri sauri, cikin sauri ya ciro wayar sa ya fara bin hotonan wayan nan criminals ɗin yana kallo.

Daga farko har karshe ya kalli hotonan, amma babu na James a ciki, da karfi da yaji ya tilasta wa zuciyar sa a kan James ba criminal bane dan haka ta dai na zargin sa, har wani yar firgice wa yayi lokaci guda dan zuciyar sa ta fara zargin James, kwakwalwan sa ba zata iya ɗaukan James a matsayin criminal ba, cikin sauri yayi kokarin ya kawar da wannan zargi da tunain banzan.

Gently ya dawo da kallon sa kan wayan nan maza daya ɗaure, hannun sa ya sanya ya zame musu short ɗin jikin su gaba ɗaya, suka zauna tsirara ba komai ajikin su, dan dama already ya cire musu rigan jikin su kam, buɗe a kwatin dake gefen sa yayi ya ciro wani katon almakashi irin wanda James ya fitar yana yanke yatsun kafan sojijin can.

Ajiye almakashi yayi a gefen sa, ya sanya hannu ya cire musu abun da ya rufe musu baki da shi, kamar jira suke ya cire musu suka fara magana, hannu ya ɗaga musu alamar baya son wani magana, shiru sukayi suna zazzare ido kamar an tare ɓera a tarko.

Gently cikin harshen Chinese ya fara tambayar su, abun da yake bukatan sani daga gare su.

Sai faman zare ido suke cike da tsoro suka fara bashi amsa, muryan su sai kerman tsoro yake, har wani haɗiyar wahalallen yawo suke, suna ta haɗa zufa, kai da gani kasan sun gama tsorata over.

Almost 20 mins suna yiwa lion bayani, nan take face na shi ta sauya idon sa sukayi jawur, a hankali ya furta "Josephine why?" A fusace ya ɗago hannun sa ya mai da musu bakin nasu ya rufe ya ɗauko wanna almakashin da ya ajiye a gefe.

Babu alamar tausayi ko kaɗan a face nashi dan ya fusata, da karfi ya sanya almakashin ya datsewa ɗayan gaban sa, saboda azaban zafi wanda aka datsewa gaban nasa bai san lokacin da yayi baya baya da kujeran ya faɗi kasa ba, sai Allah kaɗai yasan me ye sukayi wa lion, babu ko tausayi ya datsewa ɗayan ma gaban sa, gashi ya rufe musu baki babu ta yadda zasu yi ihu sai mutsu mutsu suke kamar zusu mutu, ga hawaye wani na bin wani.

Shi kuwa lion zuciyar sa sai tafasa yake masa kamar zata fasa kirjin sa ta fito waje, rai a ɓace ya ɗauko wani mashin ɗan karami mai tsini kamar kifiya ya saita saitin cinyar ɗaya daga cikin su, ya kunna mashin ɗin

Yana kunnawa wannan tsinin jikin mashin ɗin ya fara fasa namar jikin mutumin yana ratsa cikin gashin sa

A takaice wanna mashin ɗin har kashin cinyar wannan mutumin ta fasa ya fito ta kasa, gashi babu damar yin ihu ya rufe musu baki sai zafafan hawaye kawai suke fitar wa, gwanin ban tausayi, amma shi lion ko kaɗan babu alamar tausayi a fiskar sa

Haka yayiwa ɗayan ma, ya fashe masu cinyoyin su har kashi, gashi ya yanke musu gaban su wato bananan su

Sai da ya musu raga raga da cinyoyin su sannan ya miƙe rai a matukar ɓace ya fice daga wajen ya nufi cikin gida, ya bar su awajen suna zubar da jini, suna hawayen azaba.

A ɓangaren James kuwa, tas ya datsewa sojojin nan yatsun kafafun su dana hannayen su, sannan ya ɗauko wannan chemical daya haɗa ya fara bin wajen da ya cire yatsun nasu yana zuba musu, ga kuma jinin dake zuba daga wajen, sai mutsu mutsu suke bala'i azaba suke ji, sun rasa ina zasu sanya ran su su ji sauki.

Face ɗin James ta sauya tamkar ba shi ba, idon nan nasa sun yi jawur kamar jini asalin kamannin sa ya bayyana sai faman furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, alamar yana cikin matsanancin ɓacin rai.

Bayan ya gama zuba musu chemical ɗin ne ya miƙe ya je ya ɗauki wayar sa ya fice ya barsu a wajen, nan take namar wajen da aka cire musu yatsun nasu ya fara dagargajewa saboda karfin chemical ɗin, sai zaro ido waje suke ga idon nasu yayi jawur Allah sarki bayin Allah abun tausayi, ko wai'wayan su James bai yi ba, ya wuce ya bar wajen.

Sai da ya fito gaba ɗaya daga wajen ne ya ɗago hannun sa da niyar bari ya duba time a watch nasa, sai yaga babu watch ɗin, zaro idon sa waje yayi cike da tashin hankali ya fara taɓa aljihun sa, walam babu komai, da sauri ya juya ya koma cikin wajen nasu, ya koma in da ya kwanta aka masa treatment na hannun sa.

A hargitse ya fara duba ko ina a wajen amma wayam babu, duk matasan dake wajen ya tambaye su, cikin girmamawa suka ce masa basu gani ba, sosai ya shiga damuwan ya zai yi da rayuwar sa, wannan watch ɗin tamkar rayuwar sa take, dan duk in da zai je idan yana tare da watch ɗin ji yake tamkar yana tare da Triplets nasa, babban damuwar sa ma idan Romeo ya tambaye sa ina watch ɗin me zai ce masa, tunani cike fal ransa, jikin sa ba kwari ya bar wajen ya nufi hotel ɗin da ya kama dan yace wa Romeo ya tafi party a New York sai gobe zai dawo shiyasa ya kama hotel.

Yana shiga hotel ɗin wayar sa ta fara ringing, ko da ya ciro wayar sai yaga My lion ne ke kiran sa, cikin sauri ya saita nitsuwar tare da yin picking call ɗin, a nitse yace "Hello lion" daga ɗayan ɓangaren Romeo yace "Duk abun da kake ka bari ka dawo gida ina son ganin ka yanzu" kara zaro idon sa waje yayi ya ɗan juyo ya kalli ciwon hannun sa, a hankali yace "Okey give me 30mins" ɗiff Romeo ya katse kiran ba tare da ya sake magana ba.

Wurgi da wayar James yayi a saman bed ɗin dakin hotel ɗin ya nufi toilet da sauri, Allah ma yasa ba wani ciwo sosai yaji ba, sauri sauri ya sakarwa kan sa shawa, ya fara wanka.

Yana wanka yana tunanin yadda akayi watch na sa ya fita hannun sa, ya san dai lokacin da sojoji suka zo wajen taron nasu suka fara harbin bindiga yayi kokarin guduwa ya bar wajen, kasan cewar daman yasan da zuwan sojojin shiyasa ya shirya ta yadda zai gudu idan suka zo, sai dai an samu akasi dayayi yunkurin gudu wasu sojoji uku sunbi bayan sa, sai da ya tsaya yayi faɗa da su, ya kashe ɗaya ya kama biyu ya ɗaure su ya tafi da su, sune yaje yana azabtar dasu a wa can ɗakin,

To abun da ya faru shine a wajen faɗan da yayi da sojojin ne watch nasa ta fita daga hannun sa ba tare da ya sani ba, kasan cewar ya jiwa sojan da ya kashe ciwo hakan yasa jikin watch nasa ta ɓaci da jini, wannan shine ta yadda akayi ya rabu da agogon kuma ta yadda aka samu jini a jikin agogon.

Sosai James ya rinƙa tunanin ai na ya yasar da watch nasa, da kuma amsar da zai bawa Romeo idan ya tambaye sa ina agogon sa.

Har ya gama wanka ya shirya abun da yake tunani kenan, High neck sleeve shirt ya sanya a jikin sa tare da Ripped Jeans sai ya ɗaura jacket ɗin su ta sukafi kauna wato puffer Jacket, sannan yasa Booth a kafar sa, ya canza kamar ba shi ba, ya fito sauri sauri ya shiga motar sa, da gudun gaske ya bar hotel ɗin ya nufi gida.

A ɓangaren Romeo kuwa yana fita daga wannan ɗakin nasu na hora masu laifi kai tsaye bedroom na dad ya nufa ransa a matukar ɓace.

Dad na kwance jikin sa duk yayi weak saboda maganin sa da Tga ya bashi, gefen sa Romeo yazo ya zauna, cike da ɓacin rai yace "Dad I want to talk to you" miƙewa zaune dad yayi har lokacin jikin sa na kerma dama haka ciwon nasa ke masa.

Cikin harshen turanci sukayi magana mai ɗan tsawo da dad sannan ya kira James a waya yace yazo gida yana son ganin sa, daga haka sukayi sallma da dad ya fito ya wuce part nasa.

After some minutes.

Kamar wani mara gaskiya haka James ya shigo gidan, ko da yake dama ba gaskiyan gare shi ba, yasha mamakin ganin an canza komai na palon, ran sa cike da tunani kala kala ya haura sama.

Kamar zai wuce part ɗin Romeo sai kuma yace bari ya shiga part ɗin sa ya sanya hulan sanyi a kan sa, dan kar Romeo ya masa faɗa, akan ya fita cikin sanyin nan babu hula a kan sa, da sauri ya shiga part ɗin sa, nan ya isko Michael yana ta zuba barcin sa hankali kwance

Kai tsaye dressing room nasa ya nufa ya ɗauko hula ya fito ya tsaya gaban mirror dan ya duba jikin sa ko akoi wani abun da zai sa a gano sa, sai ya gyara

Ganin babu wani abun da ya bayyana a jikin sa na rashin gaskiya ne yasa ya sanya hulan a kan sa yana kallon face ɗin sa, kamar a mafarki ta cikin mirror ya hango watch guda biyu a gere saman bed nasa, dana hannun Michael da kuma wadda ya faɗo daga aljihun Micheal ɗin.

A sukwane ya juyo dan ya tabbatar wa idon sa abun da yake gani, ganin da gaske ne yasa ya karisa wajen da sauri ya sanya hannu ya ɗauki asalin na Michael wadda ta faɗo daga aljihun sa yana mamakin ya akayi watch ɗin sa ya dawo gida, to ko dai daman bai tafi da shi bane? Ya jefawa kan sa tambayar da bashi da amsar ta, tuna cewa Romeo na kiran sane yasa yayi saurin ɗaukan watch ɗin ya fice zuwa part ɗin Romeo.

Yana tafiya a hanya ya ɗaura watch ɗin a hannun sa.
A nitse yayiwa Romeo excuse sannan yashiga ɗakin, Romeo yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login