Showing 177001 words to 180000 words out of 194715 words

Chapter 60 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

999

gudu, Allah sarki Hajiya Turai gata da ƙiba sosai haka Jelly tasa baiwar Allah nan ta rinƙa tikan gudu kamar mahauniya sai haki take tana mumfashi sama sama.

A wannan yanayin na yar tsere da suke da Jelly Nawid ya shigo cikin gidan same su, dan yana ta horn ba wanda ya buɗe masa gate, dan mai gadin ma dayake mara hankali ne irin kauyawan nane wai sai ya ɗauko sanda yana bin Jelly zai make ta, idan kuma ta juyo ta kalle sa, sai ya fasa ihu ya shige bayan flowers.

Nawid dai yaga tashin hankali dan kuwa ya rasa me ma zai yi, tsayuwa kawai yayi yana kallon yadda iyayen nasa da kannen sa har ma da yayyun sa mata ke gudu suna ihu, tun shigowar sa kallo ɗaya yayiwa Jelly ya gane ita ɗin ce, abun da bai ganeba shine gudun me iyayen nasa keyi, dan shi bai ga abun da suke wa gudun ba, saboda yaga Jelly ɗin na binsu ita ma tana gudun, gashi dukkan su sai ihu suke har da ita Jelly, shine abun ya kulle masa kai ya rasa me suke wa wannan gudu da ihun

Afnan uwar rashin kunya yau tayi gudu ne har ta godewa Allah, gashi kuma sai addu'a suke aljananan wato Jelly taki ɓace wa, sai gudu suke daga masu kiran, ya Allah ka kawo mana ɗauki sai masu faɗin, Ya Rahman bayin ka suna cikin halin a ula'e, addu'a kala kala yau sun zuba shi, wasu ma basu san me suke faɗe ba kwata kwata saboda tashin hankali, duk abun da yazo bakin su suke faɗe.

Shiru Nawid ya tsaya, sai da ya ga Hajiyar sa na kokarin zubewa kasa saboda gajiya sannan ya karisa wajen da sauri, cikin tsawa yace "Wai me hakan ne? Meke faruwa ne?" Ya kai karshen maganar tare da riƙo Hajiya Turai, sai faman nuna masa Jelly Hajiya Turai take da hannun ta ta kasa magana, kallo Jelly yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Hajiya "Ummi me babyn kuma tayi yau kike gudun ta? Ko dan tayi wannan kwalliyar ne" sai lokacin Hajiya Turai ta waro idon ta da kyau ta kalli Jelly da kyau, daman su sauran yan gidan basu san Jelly ba bare su gane ta, dan bata taɓa zuwa part ɗin kowa ba, kullu tana tare da Hajiya

Ganin Jelly ce da gaske yasa Hajiya Turai ta sake jikin ta tana faɗin "Ruwa a taimaka min da Ruwa" ba ita ka ɗai ba masu bukatar ruwan suna dayawa a wajen, mafi yawancin su sun baje a kasa suna a basu ruwa, girgiza kai Nawid yayi ya riƙo hannun Hajiya, da kyar da kyar take ɗaga kafar ta, suka wuce ciki, har sun ɗan yi nisa, ya juyo ya kalli Jelly dake tsaye, da hannu ya mata alama da tazo su tafi, da yar gudun ta ta kariso wajen sa suka shige cikin palo tare, su kuwa sauran sun baje a kasa suna ta neman agajin ruwa, mai gadi ma ya fito daga maɓoyar sa wato bayan flowers ya koma bakin gate yana faɗin "Amma wannan abu bai min daɗi ba, naso na make shagiya ta mutu, amma ba komai akoi gobe ma ai sai na make ta ta mutu ɗin" sai surutan sa yake shi kaɗai kamar wani zararre.

Hajiya Turai suna shiga palon su, ta haye saman sofa mai zaman mutun 3 ta kwanta tana mai da numfashi, ruwa Nawid ya ɗauko mata mai sanyi a fridge ya bata tasha sannan ya wuce bedroom nasa, kusa da ita Jelly ta zauna tana kallo a Tv ko a jikin ta, Hajiya kuwa ta lumshe ido tana sauke mumfashi wahala, dan yau ta wahala fiye da tunain mai tunani, kun dai san yadda gudun mai ƙiba yake to hakane.

Kun dai ji halin da Jelly ke ciki na saka mutanen gida motsa jiki, yanzu dai muje mu leƙo Washington DC mu dawo kafin nan kila Hajiya tayi barci ta huta, sai ta tashi tayiwa Jelly ɗin ku wanka...


💞WASHINGTON DC💞


James yana fita wajen Romeo kai tsaye word room ya nufa, zaune ya isko Musharraf, abun ku da na'urori na zamani sha yanzu magani yanzu, idan kana da kuɗi ba abubuwan da ba za'a maka ba, saboda kayan aiki na zamani da Dr William jacop yake da shi hakan yasa kafar Musharraf yayi saurin samun sauki, sai dai baya iya tafiya sosai kaɗan kaɗan yake ɗingisa kafar, amma yana iya tashi da kan sa ya zauna, kuma yana samu kulawa sosai a wajen dad da James, su kaɗai ke kula shi a gidan, shima dad dan bai san Musharraf Musulmi bane da ba zai kula shi ba.

Gefen Musharraf ɗin James yazo ya zauna yana faɗin "Uncle are you feeling?" Murmushi Musharraf yayi kafin yace "My son I'm getting better" "what do you want to eat today uncle?" Sosai Musharraf yaji daɗi cike da matikar kaunar James yace "Gaskiya ina son cin miyar steew da akayi da kifi, da kuma shinkafa" okey James yace lafin ya miƙe ya ɗauko wa Musharraf kujeran tura mara sa lafiya wayan da ke da matsalar kafa

Kamar baby haka James ya ɗaga Musharraf ya ɗaura sa saman kujerar yana faɗin "Muje ka ga gida, yau dai ka ɗan fita waje" sai murmushi Musharraf yake yaji daɗi sosai dan dama ya gaji da zama a ɗakin.

James da kan sa ya turo Musharraf suka fito, kai tsaye palon kasa ya nufa, su dad gaba ɗayan su suna palon kasa suna zaune suna hira har da Michael mai barci ma ya taso yayi joined nasu.

Suna ganin Musharraf suka ɗaure fuska, musamman uncle Herry da Tga da John, Jay ne yace "Kai James who is this man?" Dan su Jay kwata kwata basu san da zaman Musharraf a gidan ba, atakaice James ya faɗa musu waye Musharraf da kuma zaman me yake a gidan, nan fa suka ce basu yarda ba dole Musharraf ya bar gidan nan yau, a kai shi hospital ayi jinyar sa a can ba dai a gidan nan ba, kallo Michael James yayi kafin yace "Kana tare da su Michael? Kana son uncle ya bar gidan na?" James ya tambayi Michael ne dan yasan idan Michael yace baya son Musharraf ya zauna a gidan tofa ko zai mutu sai Musharraf ya bar gidan, dan lion ba zai yarda da zaman Musharraf ba muddin Michael baya so, amma idan Michael yana so to ya samu daman da zai tinkari Romeo ya neman wa Musharraf takardan izinin zama a gidan.

Romeo yana da wata ka ida, ko wani irin mutun ne yazo gidan zai zana to fa ba zai yiwu ya zauna ba sai da takarda izinin zama gidan, misali yanzu idan daddy ya kawo abokin sa yace to ga abokin sa zai ɗan zauna da su a gidan, tofa sai ya sa hannu a takarda dan gidan su tana da takardan zama a cikin ta, ma'anar takardan nan kuwa, shine, misali bari ayi gwari gwari, idan bako yazo zai zauna dasu, Romeo zai tambaye sa zaman shekara nawa zai yi, idan yace shekara ɗaya, to Romeo zai rubuta a takardan sa, shekara ɗaya mutunmin zai yi, sai ya baka ka sa hannu, kana sanya hannu to ka dawo karkashin kulawar Romeo ko fita zakayi sai da izinin sa, dan shi baya yarda da mutane shiyasa, ba zai bari ka rinƙa fita da shiga gidan ba, sannan kuma baka isa kace zaka tafi wannan shekara ɗayan bata cika ba, baka isa ba, kome zai faru sai wannan shekaran ta cika, amma babban abun daɗin shine in dai ka samu takardan zama a gidan tofa kana cikin tsaro, dan Romeo zai kula da rayuwar ka duk in da zaka je zai iya sanya sojiji su raka, dan ka sanya hannu a takarda kamar ka zama ɗan gida ne, sai dai fa samun takardan izinin zama a gidan nasu ne, babban tashin hankali dan basu ma son bako, bare har ya samu wannan takarda, amma in ka samu lafiya Lou.

Shiru palon yayi suna jiran amsar Michael, ya amince Musharraf ya zauna ne ko kuma bai amin ce ba, hannu Michael ya miƙa wa Musharraf yana faɗin "James is my blood, i love him more than everything in my life, duk abun da James yake so ina son shi dan haka uncle ɗin James kayi zaman ka tare da James ɗin ka" nan fa Tga ya bugi kirji yace uban kuturu yayi kaɗan bare na makawo, ba zai taɓa yarda ba dole Musharraf ya bar gidan.

Miƙa hannu Musharraf yayi sukayi shaking hand da Michael, shi kuma James ya wuce ya haura sama ya bar Michael da Musharraf suna hira, su kuma su Tga suna surfa bala'i dole Musharraf ya bar gidan, kamar gidan su.

Part ɗin Romeo James ya nufa dan yaje ya nemawa Musharraf takardan izinin zama a gidan, ko da ya shiga bedroom ɗin Romeo sai yaga kamar Romeo na barci, ganin haka yasa sai ya juya a hankali zai fita, kamar daga sama yaji sexy voice ɗin Romeo yace "James" da sauri ya juyo still idon Romeo a lumshe sai dai ba barci take ba

Da sauri James ya koma kusa da shi ya zauna yana faɗin "Please my lion wata alfarma nazo nema" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, ci-gaba da magana James yayi dan yasan Romeo na jin sa sarai "Ina son ka bawa uncle na wadda na buge da mota takardan izinin zama a gidan nan dan su Uncle T da uncle Herry sun takura masa wai sai ya bargidan nan, ni kuma bana so ya tafi yanzu dan ya faɗa min bai da kowa" sai lokacin Romeo ya waro dara daran fararen idon sa tal kamar audiga masu ɗauke da kwayar ido blue, shiru ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma gently yace "Ba dai kai da Michael kuna son zaman shi a tare da ku ba?" Da sauri ya gyaɗa kai yana faɗin "Of course numa so" da hannu yayiwa James nuni da cikin drawer mirror sa, akan ya ɗauko takardan, cike da zumuɗi James yaje ya ɗauko takardun ya dawo ya miƙa masa, karɓa yayi ya ciri guda ɗaya ya miƙawa James ɗin yana faɗin "Ka kai masa ya karanta doka idan yayi agree fine ya sa hannu ka kawo min nima na sa hannu" da sauri James ya karɓa ya nufi waje.

Har lokacin sai surutu su Tga suke a kan lallai Musharraf ba zai zauna a gidan ba, ganin James ya dawo riƙe da takardan izinin zama a gida ne yasa sukayi tsit kamar babu kowa a palon, dan sun san lion ya amince kenan basu da wani bakin magana kuma, James kan ko a jikin sa yazo ya miƙawa Musharraf takardan yana faɗin "include we need your signature here" karɓan yar takardan Musharraf yayi ya fara karanta dokokin kamar haka, shekara nawa zaka zauna, hannu Musharraf ya miƙawa James a kan ya bashi bairo, ba musu James ya ciro bairo daga gaban rigan Tga ya miƙa masa, haushi kamar Tga ya shaƙe su daga James ɗin har Musharraf ɗin duk su mutu.

Wajen da aka rubuta shekara kawa zakayi, haka kawai Musharraf ya tsinci kan sa da rubuta 4 years bai yi tunain me zai je yazo ba, kawai ya damɓara shekara huɗu, doka ta biyu, idan ka sa hannun rayuwar ka ta zama a karkashin kulawar lion kuma sai abun da yace zakayi, Musharraf ya damɓara yes ba wani tunani, na uku, babu fita daga gidan nan babu zuwa ko ina sai da izinin lion, nan ma ya damɓara yes ya yarda kenan, na huɗu, baka isa kace zaka bar cikkin familyn William jacop ba har sai wannan shekaru da kace zakayi sun cika, nan ma ya damɓara yes, daga karshe ya sanya signature wato sa hannun sa, ya miƙa wa James, sai daɗi James yake ji ya wuce ya mayarwa Romeo takardan ya karɓa ya sa hannu sannan ya bawa James ɗin ya mayar in da ya ɗauko,

Su uncle ba karamin haushi sukaji ba wannan ma basu san cewa Musharraf musulmi bane wata kila idan sun sani sai kisa kawai zasu masa, dan haushi.

James na dawowa Palon ya wuce kitchen yaje ya sanar da sojojin dake musu girki a kan suyi miya da kifi yau, sun sha mamakin jin abun da James yace, amma basu da wani zaɓi abun da yan gida keso shi suke girka musu.

Sosai James yayi yawo da Musharraf a cikin gidan, nan yake sanar masa anjuma da daddare zai yi tafiya, amma baya son kowa ya sani, har lion shiyasa ma zai yi tafiyar dare, shima Musharraf ɗin ya faɗa masa ne dan yasan ba zai faɗawa kowa ba, sosai Musharraf ya masa fatan alkhari da fatan nasara, haka suka ci-gaba da yawata cikin gidan suna hira.

After some hours

Gaba ɗaya family'n daddy sun haɗu a table dan cin abinci amma banda oga lion, sai kuma James da ya tafi kai wa Musharraf abincin sa, daga kaiwa Musharraf ɗin abinci sai ya zauna suka ɓige da hira, haka kawai yake bala'i kaunar Musharraf har cikin ran sa.

Bodyguards dake serving nasu abinci ne suka fara zuba musu abincin

Jin kalan kamshin da abincin keyi yasa gaba ɗayan su suka ɗago idon su a sukwane suna kallon kallo wa junan su, mamaki ya hana su magana, yau shinkafa da miyar steew kuma har da kifi da basa ci a gidan su, nan take ran kowannen su ya ɓaci, Michael yafi kowa shiga ɓacin rai dan saboda shine ma ba'a girka kifi a gidan, kwata kwata baya son kifi bai son ganin kifi, saboda shi Romeo ya kafa dokar kada a kuskura a girka kifi a gidan, ba'a taɓa girki da kifi ba, shiyasa sauran ma basu saba cin kifin ba, kuma suke kyamar kifin sosai, dan suna ganin kamar wani kazanta ne tun da lion ya hana girkawa, shi kuma James lokacin da yaje ya sanar da masu girkin su dafa miya da kifi, bawan Allah ya manta bai cewa sojojin iya abincin Musharraf kawai zasu girka da kifi ba, shi dai kawai yace suyi girki da kifi bai rabe musu ya zasu yi ba, shiyasa sukuma suka labta kifin wa gaba ɗaya jama'ar gidan.

Jin warin kifin yasa Michael miƙewa da gudu ya haura sama, ya shiga part nasa, yaje toilet ya rinƙa kwara amai kamar zai amayar da hanjin cikin sa, gaba ɗaya bodyguards dake wajen sai da hantar cikin su ya kaɗa, saboda tsoron hukuncin da zasu fiskanta duk da basu sukayi girkin ba.

A tare gaba ɗaya family dake saman table ɗin suka tashi da gudu sukabi bayan Michael dan sun san bawan Allah amai yake, tun yana yaro baya son ko kallon kifi da ido

Shi kuwa James yana can yana zuba hirar sa da Musharraf, Musharraf na ba shi labarin tarihin rayuwar sa, sai dariya James yake kamar ba shi ba, can kuma ga Michael na tikar amai kamar zai amayar da ƴaƴan hanjin sa.

Sosai family suka tausayawa Michael dan yayi amai ne har ya galabaita kamar zai amayar da kayan cikin sa duka, da kyar da ma kyarkyata ya samu amai ɗin ya dakata, rai a matukar ɓace ya fito ba tare da yayiwa su daddy magana ba, kai tsaye ɗakin ajiye makaman su ya wuce, babu kalan makamin da babu a ɗakin sai na kare dangi

Wata iriyar wuƙa mai bala'i kaifin gaske wadda ke aiki da wata yar inji a jikin ta wadda akewa charji, idan aka kunna injin wannan wuka zata iya zaba ɗan adam gida biyu saboda kaifin balai da take da shi, wannan wukar Michael ya ɗauko ya nufi waje.

Kai tsaye palon kasa ya koma su daddy suna biye da shi, cikin tsawa ya kira sojojin dake musu girki, sai wani huci yake kamar ɗan zaki, cikin sauri sojojin suka fito daga cikin Kitchen ɗin, kallon sa dad yayi kafin yace "Michael what are you going to do with this AK" sunan wukar kenan AK, "that I want to cut their hand"

Tashin hankali kasa sojojin suka zube sunji Michael zai yanke musu hannu, ɗaya daga cikin su kam ma kuka ya fara yi dan yasan yaran William jacop basa maganan da ba zasu aikata ba, hakuri dad ya shiga bawa Michael yana lallaɓa sa akan ya kyale sojojin yayi hakuri ya tsaya suji dalilin da ya sa suka saka musu kifi a abinci, ina Michael yayi nisa baya jin kira ya dage sai ya yanke musu hannayen su, da sauri daddy yace da su jay su rike Michael kar su bari ya yanke wa sojojin nan hannu,

Kin rike Michael ɗin su Jay sukayi dan mugunta sai ma kara ingiza shi suke, jikokin mugaye, su Jay akoi su da mugun ta zuciyar kafurci babu ɗigon imani, shi kuwa James da ya haddasa wannan bala'i yana can suna hira da Musharraf hankali kwance sai dariya yake bai san meke fatuwa ba, sai dai shima yaki cin abinci ko da Musharraf yace yaci, sai yace a'a basa cin kifi, basu saba ba, shi a tunanin sa iya Musharraf kawai akayiwa girki da kifi.

Sojojin dake girkin kuwa sai kuka suke bayin Allah basu jiba basu gani ba za'a yanke musu hannun suna ji suna gani, ɗayan kam har da majina ya haɗe hawaye sharɓa sharɓa a fuskokin su, Tga har da cewa idan Michael ba zai yanke musu hannu ba ya bashi wukar bari shi ya yanke musu, mugun kafuri zuciya ba imani ba tawakkali, shekara wajen 8 sojojin nan suna yi musu girki ba'a taɓa samun matsala ba sai yau, yau ɗin ma matsalar daga wajen James aka samu shine bai musu bayani yadda ya kamata ba, amma su Tga sun murje ido sunce dole su yankewa sojojin nan hannun su, daga saman wajen hammatan su zasu yanke gaba ɗaya.

A ɓangaren Romeo kuwa, tsaye yake gaban mirror ɗaure da towel mai laushi fari tas a kugun sa, soft skin na sa kaɗai abun kallo ne, yaji hutu sosai yana kwance lif sai sheki yake ga tsantsi kamar fatar jariri, kasan cewar babu riga a jikin sa, hakan ya bayyanar da kakkarfar suran jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login