Showing 30001 words to 33000 words out of 194715 words

Chapter 11 - Triplets Book 1 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

956

sa, cikin girmamawa director ya miƙawa daddy hannu yana faɗin "Barka da zuwa gaskiya munji daɗi da amsa gayyatar mu da kayi muna alfahari da hakan" murmushi daddy ya saki har sai da dimple na shi ta lotsa yace "Ai dole nazo ko dan siha ta" ya kai karshen maganar tare da shafa kan Rimsha cool murmushi ta saki har sai da dimple nata ya lotsa siririn open teeth dake tsakanin fafaren hakoran ta ya bayyana hakoranta fafare tas da su kamar gonan audiga, manya manyan Alhazawan dake wajen dukkan su Rimsha ta matikar burge su sosai. Malamar su Rimsha ce ta ƙaraso ta gaida daddy cikin girmamawa ta kama hannun Rimsha tana faɗin "let's go and get ready" a hankali ta lumshe sleeping eyes nata ta sake buɗe wa kafin tace "Bye daddy see you in the Hall" ta kai ƙarshe maganar tana yi masa bye bye da hannunta shima bye bye ɗin ya mata ita dai Jehan tun saukowar su ba ta jira kowa ba ta wuce wajen friends nata,
Director ne yace "sir please let's go in"
Kallon Gwaggo daddy yayi yace "Anty A'isha muje Koh"

a tare suka ranƙaya zuwa cikin katafaren hall ɗin dake cikin School ɗin a nan za'ayi taron ƴan jarida sunzo ɗaukar new gidan TV kala kala gaba ɗaya student na ciki kowa na zaune saman kujera an kawata hall ɗin sosai da kalar makarantar Dark blue da light blue an rubuta Sunan Makarantar da ballons dark blue da light blue idan nace zan tsaya zayyana muku haɗuwar da hall ɗin nan yayi to zamu kwana mu wuni bamu kammala ba kawai ku kawata shi a ran ku, hall ne mai girman gaske an cike sa da kujeru da student suka zazzauna, ta gaba kuma inda aka tanadar na ɗaliban da sukayi graduation ɗine, daga saman staircase wani ya opposite ɗin students ɗin, a ka shirya wasu haɗaɗu kujeru masu kyau sun kawatu iya kawatuwa ga wata doguwar table a gaban kujerun an jera drinks a sama da ruwan faro masu sanyi wadda daga ka gani kasan wajen baki na musamman ne daga tsakiyar kuren a kwai wata haɗaɗiyar kujera golden color an mata kwalliya sosai kamar kujerar sarauta daga gani kasan mutun na musamman a ka tana dawa,

manya manyan alhazawa da sarakuna ne zazzaune saman sauran kujerun da a ka jera layi sai wan nan ɗayan mai kama dana sarakuna shi da na kusa da shi ne babu kowa a kai, saman sa daddyn su Jehan yaje ya zauna ita kuma gwaggo ta zauna a kujerar kusa da na shi, nan take student suka miƙe suka fara kwasan gaisuwa daddy na amsa musu da fara'a a face na sa, duk school nan ba wanda bai san shi ba sai dai in new comer amma student ɗin school ɗin sun san shi dan mutun ne shi mai fara'a da kyauta gashi da son yara duk kuɗin da yake da shi, shi da kan sa yake kawo su Jehan school kuma ya dawo ya ɗauke su dan gani yake kamar idan ya bari driver ya kai su ba zai kula masa da su sosai ba, shi yasa ko abu suke so yake ɗaukan su suje shopping tare da shi komai aikin da yake zai ajiye yazo yayi attended nasu, yana bala'i kaunar su sosai,

Bayan sun gama kwasan gaisuwa ne suka koma suka zauna.
Mike director ya ɗauko ya sanya a saitin bakin sa ya fara magana cikin harshen turanci "Ina mai farincikin zuwan wan nan rana mai albarka Jehan Nawazudden Salman kizo ki buɗe mana taro da Addu'a" shiru hall ɗin yayi, gaba ɗaya manya manyan bakin da suka halakci taron sun zubawa Jehan ido wadda ta taso tana tafiya a nitse, a hankali ta tattaka saman staircase ɗin ta hauro sama taje ta tsaya kusa da director, miƙa mata mike ɗin director yayi ta ansa cikin kyakkyawa turancin ta da zazzakar voice nata mai sanyi da daɗi ta fara da yi musu sallama san nan ta fara jero addu'a "We take refuge with Allah, The Supreme and with His Noble Face, and His eternal authority from the accursed devil In the name of Allah, and prayers and peace be upon the Messenger of Allah O Allah, open the gates of Your mercy for us Amin" ta kai karshen Addu'ar tare da rufewa da Ayatul kursiyyu, sosai jama'a suka yi ta kabbara ciki hadda daddy da gwaggo sosai daddy yaji daɗi, ji yayi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha,

bayan Jehan ta sauka ta koma mazaunin ta ne director yace a shigo da ɗaliban da sukayi graduation ɗin, a cikin layin suka shigo cikin tsarin suna sanye Cikin graduation gown kalar uniform ɗin makarantar daga bayansu kuma malaman sune kowa fuskarsa cikin annashiwa da tsantsar farin ciki, kai tsaye inda aka tanadar domin su suka karasa sannan sukayi Anthem ɗin makarantar aka basu iznin zama
Director ne fara kiran graduates ɗin ɗaya bayan ɗaya sukazo su gabatar da kan su san nan suyi jawabi tare da nuna farincikin su sai suyi karatun al Qur'ani mai girma,

ba laifi yaran sun iya kira'a daddy ya kosa a kira Rimsha ɗin sa haka ita ma gwaggo ta kosa taji karatun Rimsha, duk yarinyar da tazo a kace ta karanta Al Qur'ani mai girma bata wuce karanta sura daga nasi zuwa amma ko sabbi,

Rimsha itace yarinya ta goma da a ka kira cikin nitsuwa ta taso tana tafiya a nitse ta hauro saman wajen ta ansa mike ɗin da zazzakar voice nata ta fara da bilmillah san nan ta karanta suratul fatiha daddy yaji ba daɗi a tunanin sa a suratul fatiha zata tsaya sai yaji ta sake wata Bismillah ta fara karanta Suratul Baƙara,
shiru hall ɗin yayi ba abun da ke tashi sai zazzakar voice ɗin Rimsha dake tashi, gaba ɗaya kowa ya nitsu tsit suna sauraron baiwar da Allah ya mata farincikin a wajen daddy da gwaggo ba'a magana,

hawaye Rimsha ta fara yi tana karatu ko da tazo In da Allah ke magana a kan itaciyar da ya hana Annabi Adam ci Annabi Adam yaci ta sanadiyar haka Allah ya fito da shi daga aljanna, sau uku tana mai mai ta ayoyin san nan ta ci gaba tana karatu tana kuka, tun muryan ta na fita sosai har ya fara sarkewa saboda kuka da take idan ta tuna girman Allah ta tuna mutuwa kwanciyar kabari gadar siraɗi hisabi sai ta kara fashe wa da kuka shi kan sa daddy sai da kwalla ta cika masa ido duk wani mai imani a wajen sai da idon sa ta kawo kwalla dan kukan da Rimsha ke yi tana rero kira'ar nan, masu saurin kuka kam ma tuni sun fara rera nasu kukan cikin harda Jehan,

da kyar Rimsha ta iya kai karshen suratul bakara tana kokarin durkushewa kasa a wajen daddy da ya kasa hakuri ya taso da sauri yazo ya rungume ta yana faɗin "It's okey my siha" cikin kuka tace "Daddy me mutun zaiyi a dunuyyar nan da ya wuce bautan Allah daddy mutuwa gaskiya ce kwanciyar kabari gaskiya ce gadar siraɗi gaskiya ce hisabi gaskiya ce haka zalika wuta da aljanna gaskiya ce daddy, duk wani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa daddy, duk lokacin da na kalli kwayar idon ɗan Adam daddy ina kara jin tsoron Allah da ganin girman Allah a rayuwata dan idon ɗan adam ma kawai ya isa yasa bawa mai hankali ya kara jin tsoro Allah, duk lokacin da na tuna da mutuwa hisabi kwanciyar kabari gadar siraɗi wutar jahannama daddy ina shiga tashin hankali sai in ji gaba ɗaya duniya ta fitamin a rai na daddy, me ya rage bawa yake so bayan yayi bautar Allah dan ya samu ya tsira ranar gobe kiyama, daddy ban taɓa kwaciya barci na sawa rai na zan farka a duniya ba, ban taɓa lissafin me zai faru gobe na ba kullu lissafi na iya yau nake dan bana sawa rai na zan kai goben mutuwa gaskiya ce kuma tana ɗauka duk lokacin da kwanan mutun ya kare ba ruwan ta da abun da kake ko in da kake zata ɗauke kane kawai, daddy duk wani musulmi kamata yayi ya sawa ransa iya yau kaɗai garesa ba zai kai gobe ba dan ya samu damar aikata aikin Allah, daddy duk lokacin da na samu dama har tsawon kwana na ya kai nayi sallar issha, ji nake tamkar an sauke min wani katon dutse a kai na dan kullun ina cikin fargabar kada na mutu gab da wata sallar ko azahar ko la'asar kuma a ce ban samu damar yin wan nan sallar ba" ganin maganar da Rimsha take babban magana ne yasa director ya kawo mata mike ɗin sai tin bakin ta dan kowa yaji maganar nata, sosai hall ɗin gaba ɗaya suka ɗauka da kuka babban magana miƙewa manya manyan sarakuna irin su sarkin Zazzau Sarkin kano Gombe Bauci da dai sauransu suka yi, ba karamin tashin hankali magangun Rimsha ta jefasu ba yariya yar karama kamar wan nan amma tana da karfin imani har haka shi kan shi daddy yayi shocked da jin maganar Rimsha yasan dai tafi Jehan ilimin addini dan ita kullun tana tare da mum tana koya mata karatun addini ban da Jehan da a iya islamiyya kawai take ɗauka bai taɓa tunanin girman ilimin Rimsha ya kai haka ba, ba wanda bai yi mamaki da jinjinawa Rimsha ba ta girgiza gaba ɗaya hall ɗin ta karawa mutane da dama imani a ran su dayawa daga cikin wayan da suka halakci wajen sun kudurci niyar gyara ɗabiun su marasa kyau ta dalilin maganganun Rimsha, sosai suka shiga tashin hankali duk wanda ya manta da lahira yau sai da Rimsha ta tuna masa wani ma ji yayi kamar yaje ya sadakar da dukiyar sa dukka ya koma ga Allah yayi ta ibada,

da gudu Jehan ta miƙe ta hauro saman wajen ta rungumi Rimsha tana kuka tana faɗin "Kinyi gaskiya yar uwata duk abun da kika faɗa gaskiya ne amma jama'a da dama sun shagala da duniya sun manta da mutuwa da kwantatciyar kabari sun manta duhun kabari da siraɗi da hisabi idan ka dace ka shiga aljanna idan baka dace ba ka wuce wutar jahannama bayan ka gama ansan azabar kabari dana siraɗi ga tsayuwa kafin hisabi tsayuwar shekara ɗai ɗai har shekara dubu saba'in ga kuma rana a dai dai sai tin kan ku babu dare babu inuwa sai wan da yayi aikin Allah ne kaɗai zai shiga inuwar al'arshin Ubangiji Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah mun tuba mun tuba ya Allah" sosai jama'a suka ciro wayoyin su suka rinƙa yi musu video ciki har da director.

Da kyar daddy ya iya rarrashin Rimsha sai da tayi shiru san nan ya riƙo hannun ta suka miƙe ya dubi director yace "Mu zamu wuce gida ba zamu iya jira a gama taro ba dan jikin siha ya fara zafi saboda kukan da tayi" ya kai karshen maganar tare da kallon gwaggo dake zaune saman nata kujerar tana goge kwallan dake idon ta yace "Aunty A'isha muje ko?" Da kyar gwaggo ta iya miƙewa dan gaba ɗaya Rimsha ta kashe mata jiki, gaba ɗaya manya manyan baki da sarakunan dake wajen suka miƙe dan raka su daddy zuwa wajen mota, sunyi sunyi a kan daddy ya bari suyi hoto da Rimsha amma yaki haka suka hakura ba dan sun so ba suka bar su Rimsha suka tafi ba tare da sun yi hoton ba, da haka taron ya watse dan dukkan su sun kasa gudanar da komai jikin su ya mutu da har da kayan kiɗa suka kawo amma jin zancen Rimsha yasa suka manta da wani kayan kiɗa da suka kawo, kowa ya wuce gida taro ya watse

💞💞💞💞💞💞💞💞

KANO

Zaune jelly take saman mirror chair daddy na tsaye a kan ta yana ɗaure mata gashin kan ta da roba irin na kitson yara kasan cewar gashin nata yayi tsantsi sosai baya kitsowa sai dai a ɗadɗaure mata shi da roba, sai murmushi take fararen hakwaranta masu kyau suna jere kanana da su sai kyalli suke, shi ma daddy sai murmushi yake yace "My baby kinyi kyau over" kara murmushi tayi sosai a wan nan karon har fararen hakoran ta suka kara bayyana sosai "Daddy amma dai yaya Imran zai zo school na mu ko?" Tayi maganar cikin shagwaɓa "Eh my baby yace min zai zo In Sha Allah" tana kokarin sake yin magana daddy yace "Sauko na gama kuma surutun nan ya isa dan 07:00 am tayi yanzu taso na sanya miki uniform dan karmuyi late" make masa kafaɗa tayi cikin shagwaɓa tace "Daddy kai fa ka ɗaurani saman chair ɗin yanzu kuma kace na sauko da kai na ni ban iya ba" girgiza kai kawai yayi ya sanya hannu ya ɗagota cak suka nufi wajen gado dan bai son biye mata idan ya biye mata ba zasu wuce school da wuri ba,
saman gado ya ɗaura ta san nan ya wuce ya ɗauko mata uniform nata riga fari da wando blue sai ɗan hijabi fari ya dawo ya sanya mata sharp sharp san nan ya ɗauko perfume ya feshe ta da shi nan take ta fara zuba kamshi wuce wa yayi ya ɗauki suit nasa da zai sanya ya shige toilet,

tana zaune har ya fito shirye cikin bakin suit da ya ɗauka ya dube ta yace "Let's go my baby" shiru ta masa kamar bata ji me yace ba, sake mai mai ta maganar yayi dai dai lokacin da yake ɗauko jakar computer sa nan ma sake masa shiru tayi kamar bata san da mutun a ɗakin ba, da sauri ya juyo dan yaga wai ko barci tayi ne ganin idon ta kar a kan sa ta turo baki kamar biro ne yasa ya dafe kan sa da hannun sa yana faɗin "Yanzu kuma menene? haba my baby zamu makarafa" kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "Ni daddy yanzu ka dai na sona baka ɗauka na sai kace na tafi da kafata" "Haba my baby yanzu fa 11 years kike da shi gaskiya kin min katuwa ba zan iya ɗaukan ki ba" sauka kasa tayi daga saman gadon ta kwanta a kasa ta fara birgima tana masa kuka girgiza kai yayi ya ratiyo jakar computer sa ya kariso wajen tare da sanya hannu ya ɗauke ta cak kamar yar baby suka nufi waje, ganin ya ɗauke ta yasa tayi shiru kamar an kashe gen.

Ko da suka fito palo su Zuwaira sun kammala shirya musu breakfast ga kuma basket na school ɗin Jelly sun shirya mata abincin ta a ciki roban cool Yoghurt ne mai ɗan girma da snacks a cikin wata kyakkyawar transparent roba sai pepper chicken a cikin foodflask, daddy bai tsaya yin breakfast ba dan time ya tafi basket na lunch nata kawai ya ɗauka mata suka nufi waje lokacin 7:45 am yayi.

Suna fita harabar gidan wata dankareriyar mota kirar Mercedes-Benz ta danno hanci cikin gidan ihu jelly ta fasa mai rikita ƙwaƙwalwa tana faɗin "Daddy ka sauƙe Ni" ba musu ya sauƙe ta da gudu ta nufi motar zata runguma ba ruwan ta da tafi motar yake, saura kaɗan yabi ta kan ta dan irin shigar da tayiwa motar, a sukwane mamallakin motar ya taka birki, ba karamin tsorata daddy yayi ba ganin saura kaɗan motar ya take ta, ita ko, ko a jikin ta bata ma san me tayi ba da gudu ta karisa wajen marfin motar tana faɗin "Yaya Imran nayi kewar ka" gently a ka buɗe kofar motar a hankali ya zuro kyawawan kafafun sa dake sanye cikin cover shoe baƙi waje kafin ya fito gaba ɗaya, cikakken namiji ne chocolate color yana da dogon hanci da dara daran idon ga kyakkyawan saje kwance a face na shi kaman sa ɗaya da daddyn Jelly sai dai shi chocolate color ne sosai, yana sanye cikin dakakkiyar shadda fara tas da hula baki sai cover baki a kafar sa kyakkyawa ne a jin farko, da sauri Jelly ta faɗa jikin sa tare da sakin kukan shagwaɓa, ɗagata sama yayi yana faɗin "Rabin rai na nima ai nayi kewar ki yanzu dai a dai na min kukan haka ya isa kin san ban son kukan ki ko?" kwantar da kan ta tayi saman kafaɗar sa tana yar dariya kamar ba ita ke kuka yanzu ba, wucewa Imran yayi ɗauke da ita a jikin sa ya nufi daddy dake tsaye sai murmushi yake bakin sa yaki rufuwa yana bala'i kaunar Imran sosai,

Risinawa kasa Imran yayi ya gaida daddy, da fara'a daddy ya amsa yana murna "Daddy muje ko lokacin ya tafi" cewar Imran yayi maganar tare da ansan basket ɗin Jelly dake hannun daddy,
a tare suka ranƙaya zuwa wajen motar Imran,
daddy ya shiga gidan gaba tare da ansan Jelly shi kuma Imran ya koma mazaunin driver ya zauna tare da yiwa motar key yana satar kallon face ɗin Jelly yaja motar suka bar gidan suka nufi School ɗin su Jelly

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞

*💞The beginning💞*



STAR 🌟 LADY..✍️



Episode 8

*KADUNA*

Zaune Abbi yake saman sofa a cikin palon sa ya buga uban tagumi yayi shiru, kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin matsanancinyar damuwa, duk da sanyin Ac dake cikin palon hakan bai hana shi zufa ba, jikin sa sanye da jallabiya baki gaba ɗaya a hargitse yake,

da sallama Irfan ya shigo cikin palon, Abbi yayi nisa cikin tunani bai ji sallamar da Irfan ɗin yayi ba,

````Irfan````

Cikakken namiji ne yana da tsawo dai dai san nan yana da ɗan kiba kaɗan yana da faffaɗar kirjin ga hancin sa dogo har baka idon sa dai dai ne basu da girma sosai kuma ba kanana bane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login