Showing 30001 words to 33000 words out of 182919 words

Chapter 11 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

348

."


shiru yana zaune yana sake sake can yaja tsaki tare da sake mikewa yana zagaye office din "bai ka mata nã bar maryama haka ba dole ne na nuna mata kalata domin na lura yarinyar bata da tsoro shirunsa da qarfafan idanunshi basa firgitata ya kamata na shigar da tsorona cikin zuciyarta kai da kake bukatar ta soka idan ka shigar da tsoronka sai ya kenan ."?mr ata yayi shiru a tsaye kamar gunki  yana nazari da tunanin abinda zai yi sai ga d'aya daga cikin wayoyinsa ya d'auki sauti a natse ya juya  yasa hannu ya d'auki wayar dake ringing ya soma magana cikin had'addden turancinsa "No it  will be possible zuwa gobe zaku samu  ok ba damuwa."  yana gama fad'ar haka kashe wayar ya  ajiye wayar ya cigaba da tunanin maryama ."yanzu me zai faru idan yarinyar nan batayi aikin nan gobe ba ?"yayiwa kanshi tmbyr hannu ya kai goshinsa yana murzawa ahankali "adamcy ka natsu ka bar yarinyar nan tayi aikinta kai ma abinda kayi baka kyauta ba sam sam bai dace ba ,dole ka tunzura zuciyar maryama ya dace ka barta tayi aikinta ."numfashi ya sauke yayi taku biyu ya zube akan kujera yana kallon saman office din wani  murmushi dole ya bayyana akan fuskarsa yana cewa zuciyarsa "duk duniya ke kad'ai ce macen da zata kawowa adam rainin hankali ya barta ta kwana lafiya ."


A matukar gajiye maryama ta qarasa gida , ga tarin gajiya ga 'bacin ran mr ata  bata iske umma a parlour'n ba sai dai taji  alamu  tana kitchen dan haka kai tsaye d'akinta na bangaren  umma ta shiga ta ajiye jakar aikinta tana sauke numfashi sannan ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah la'asar byn ta idar ta fito zuwa parlour inda ta iske umma zaune tana gyara efo,ta samu guri ta  zauna acikin daya daga cikin kujerun parlour'n tare da yi mata sannu da gida "umma ta amsa cike da kulawa maryama ta  yi  shiru gbdy ta kasa yin komai hatta aikin da ta kan taya umma idan tana gida  bata yi yunkurin yi ba bare wani aikin mr ata wanda take jin a yanzu bata da lokacinsa." umma ta kalleta a tsanake tana nazarinta sai dai bata ce mata komai ba yayinda  maryama  ke kukan zuci  zuciyarta na mata zafi da qunci. gashi bata da damar nunawa saboda yanzu ne umma zata fita shiga tashin hankali shiyasa tayita danne quncinta ita kad'ai."


ganin idan ta cigaba da zaman falon umma zata fahimci damuwarta dan har ta fara tambayarta da kwayar idanunta yasa ta mike ta koma d'aki ta kwanta  tana danne damuwarta batayi cikakken minti goma ba umma ta kirata ta fito jikinta a sanyaye ta tsaya tmkr wata mara lafiya  "lafiyarki kuwa tunda kika dawo na ganki wani iri meke faruwa dake ?"ahankali maryama ta nuna wa umma bata  da damuwar komai yanayin aiki ne "amman shine zaki shige d'aki ki zauna   ke kad'ai ga "? ba zama nayi ba na d'an kwanta ne ,"kwanciya adaidai wannna lokacin da magriba ta karato ?shiru maryama tayi dan yanzu kam bata da abun cewa ba umma ta tsura mata ido kafin ta cigaba da magana "ni nasan kina da damuwa yau kina dai son boye min ne ."


"Allah umma babu wata damuwa kawai dai yanayin aiki ne babu dadi ta fad'a tana zama kusa daita umma ta mike ta shige kitchen batare da tace mata komai ba dan tasan lallai akwai abinda ke damunta maryama umma ta fito rike da wata roba ta cigaba da aikinta yayinda maryama ta dan saki ranta kad'an tasa hannu suka cigaba da aikin tare da umma tun umma na saka mata ido domin son sanin damuwar maryama har ta sake domin dai ta fahimci babu komai din yanayin aikin ne kamar yadda ta furta abinda umma batasani ba shine kowace second da dare ke karatowa tashin hankali ga maryama domin kuwa damuwarta qaruwa sukeyi duk lokacin data tuna yanayin data  baro mr ata da yanayin tashin hankalin some ta biyo dashi sai taji zuciyarta ta buga da qarfi .sai hawaye ya cika idanunta da sauri take dannesu ."


Hannunta ta cire ta kwantar da kanta kan hannun kujera ta shiga duniyar tunani had'uwarta da mr ata gobe shi yafi komai gigitata matukar tsoronsa take ji bata san yaake take samun kwarin gwiawar musayar yawu dashi ba,anya kuwa zaki aiki gobe ?"tayiwa kanta tmbyr "no bazan je aiki gobe ba gara nayi zamana   "to me ke nan kikayi ?ai kin sake qarawa kanki sabon laifi kiyi qoqarin ki qarasa masa aikinsa idan Allah ya taimakeki kafin gobe zai  huce kai maryama karki je wannan mutumin bashi da kirki sai ya wulakantaki " zuciyarta ta gargadeta mikewa tayi tsam ta shiga d'akinta ta shig toilet ta kunnawa kanta ruwa tana qoqarin jan numfashi da karfafa zuciyarta karta yankewa hukunci kin zuwa aiki gobe dole itace qarama kuma dole itace zatayi hakuri da duk wani abinda zai yi domin ta samu damar cigaba da aikinta cikin salama ."



Karfe shida daidai  ya mike ya soma tattara abubuwan amfaninsa ya fito domin wucewa gida
Bayan sallar isha' i bayan yayi wanka ya  sanya gajeren wondo da farar riga ya kwashi  wayoyin kasuwancinsa guda biyu ya  fito zuwa parlour qasa qafafunsa sanye cikin wasu  hadadden silipas farare sol ga qamshin turarensa red na tashi ta koina a sansar ajikinsa kai tsaye dinnig ya nufa ya ja kujera baya kad'an ya zauna yana  daddana wayarsa  daya . yana  zaune saman dining dayar wayarsa  ta soma ringing ya d'auka ya duba yaga mai kiran  mutanen da suka bashi aiki ne dan hk  ya manna wayar a kunnensa tare da yin shiru yana sauraran mai magana "."ai nace maka it will be possible tomorrow zuwa 11 am haka I think komai yayi ready okay yana gama fad'ar haka yayi discounting din kiran ya soma neman  layin maryama kira biyu yayi mata bata d'aga ba har zai hakura dan bai saba 'bata lokacinsa akan kira ba da zarar yayi kira d'aya baa d'auka ba shikenan zai hakura sai dai a biyasa ."


Amman wannan karon sai ya tsinci kanshi da kasa hakuri ya cigaba da kiranta ai a karo  na hud'u ne ta dauka batare da sanin ko shine mai kiran ba"Slm alaikum ta furta cikin sanyayyar muryarta mai matukar sanyi da ratsa sansar jiki "shiru yayi yana jin yadda sautin muryarta ke saka bugun zuciyarsa na qaruwa fiyye da kaida yayinda kowace jijiya dake  jikinsa ta natsu tana amsar sakonni daga muryarta wani irin shauki soyayyarta ne ke fizgarshi  bai san sanda ya kai hannusansa daya daidai saitin qirjinsa ya fara shafawa ba daga can bangarenta ya sake jiyo sautin muryarta "hello wake magana  ?ta sake furta muryarta cike da rauni hannunsa daya ya cire daga qirjinsa ya kai daidai tsakankanin dogon hanshinsa zuwa goshinsa sai da ta sake maimaita hello sannna ya fixgo magana da kyar yace "hello !sai kuma yayi shiru yana jin wani irin mummunar faduwar gaba ".


"An kira mutun kuma anyi shiru dan Allah wake magana ina son na kwanta  bacci ." sauri ware idanunshi yayi sosai tamkar tana gabanshi "wato ma ba aikinsa bane agabanta bacci zatayi? ahankali ya kalli agogon wayarsa yanzu tara zata buga "idan mutun bazai yi magana ba ni gsky zan kashe wayata."  ya lumshe idanunshi yana furzar da iska mai zafi yayinda sonta ke sake huda zuciyarsa dama gangar jikinsa  tana cikin haka sai ga umma tace "ke kuma da waye ?"wallahi umma kirana akayi  tun dazu na d'auki kiran amamn tun daga hello basake cewa komai ba" muga number ko irin daya ce da wacce ake kirana ayi shiru."


maryama ta sauke wayar a kunnenta tare da katse kiran yayinda umma ta qarasa inda wayarta take ta dauko ta dawo kusa daita ta mika mata  wayar "umma ba number daya bace ."to Allah ya kyauta amman babu dadi a dinga kiran mutun ayi shiru ni yanzu ma yanke shawarar bazan sake daukar kiran layin ba koma Kiyi min blooking din layin na huta inji cewar ummah "uhm umma ki barshi kawai idan mai shi ya gaji ya daina kiranki tana rufe baki wani kiran ya sake shigowa wayar maryama  the same number daaka kirata ,da kamar bazata dauka ba sai kuma tayi tunanin ta dauka idan baa yi magana ba ta kashe wayar gabad'aya dan haka ta dauka tare da sallama sannan tace hello wai wake magana ne ?"


A zafafe yace "zakice baki gane mai magana ba ?"ni  gsky ban gane mai magana ba hassalima ban san number ba bare muryar mai magana "okay kina magana da mr ata "what !? ta fad'a tare da zaro ido waje jikinta na d'aukar rawa  daga haka bata sake cewa komai ba ta katse kiran jikinta na wani irin rawa "tabbas muryarsa ne" shikenan na rasa aikina inna lillahi wa inna ilaihi rajiun  umma ta matso kusa daita ta zauna akan hannun kujerar da take zaune  tana tambayarta "wani aikin zaki rasa ?cikin kuka ta girgiza mata kai tana saka hannu ta rufe bakinta saboda wani kukan da yake sake kufce mata.


"Ashe  maryama  akwai damuwar da zaki kasa fad'a min ?tayi shiru tana kuka kafin ahankali taji shigowar sako wayarta nan jikinta ya sake daukar rawa ta sake tabbatarwa kanta sakon dakatarwa ce "shikenan na rasa aikina ".shine kawai abinda ta dinga  maimatawa a fili cikin kankanin sakanni idanunta suka kada suka koma jazur ta dinga fidda huci " wani bala'in tausayin maryama din ya mamaye umma , "me kikayi  har aka dakatar dake aiki ?shiru maryama ba magana sai kuka "ni daman tun da kika dawo na fahimci kina tattare da damuwa amman kikace babu komai kinfi son kiyita boye  damuwa a zuciyarki tana cutar dake kina tunanin  boye damuwar shi zai miki maganin halin da kike cikine?"



cikin  murayar kuka ta shiga fad'awa umma abinda ya faru shiru umma tayi tana sauraronta har ta dasa aya umma  tace "maryama baki kyuata ba ya dace kisan yadda zaki masa magana duk da nasan kureki yayi ."wallahi umma kureni yayi sam mr ata bai da mutunci ni bansan sanda yana fad'a ina fad'a ba "amamn tunda a qarqashin ikonsa kike dole sai kinbi dokarsa sannan zaki zauna lafiya nan dai umma tayi mata fada sosai tare da kwantar mata da hankali dan bata son tana  yawan shiga damuwa da tunani saboda ba wai ta gama dawowa normal bane  da kyar ta  samu maryama tayi shiru ta share hawayenta  tace ta bata wayar ta duba taga sakon daaka turo  mata."


"A'a umma karki bude kawai ni nasan babu abinda zai saka mr ata kirana adaidai wannan lokacin ko ganin sakon madam some sai dan dakatar dani "ni umma miko min charbinki kawai na fara ja  ko
tunani  da damuwa zasu barni  ta qarasa mgnr tana sake furta kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihir raji un, tana hadawa da salatin Annabi da istigifar "maryama ki natsu  in sha allahu ba abinda kike tunani bane Allah yana sane dake kuma zai kawo miki dauki bani wayar na duba jiki a sanyaye ta mikawa umma wayar  ta amsa ta shiga inbox dinta  umma ta fara karanta sokon a fili  "ki tabbatar da kin zo da aikin da muka baki Gobe karfe tara daidai wani irin juyowa maryama tayi ta fuskanci umma hawaye na bin kuncinta ."



Kallon kallo suka shiga yiwa juna "kingani ba duk da abinda kikayi masa amman har yanzu suna bukatarki a ma'aikatan su lumshe seyx eyes dinta tayi tana godewa allah da ba dakatar daita sukayi ba sako na farko umma ta karanta "ki dauki kiran mr ata magana ce akan desing's din daaka baki aiki shine sakon some dayafi komai daga mata hankali naunayen ajiyar zuciya ta sauke " yanzu sai ki tashi kije ki fara abinda ake bukata daga gareki "wallahi ni yanzu duk jikina a sanyayye yake akan aikin baa wa mr ata gwaninta komai kayi baka iya ba komai bai masa ba wallahi umma bansan ta ina zan fara ba ."


" haka zaki karfafa zuciyarki ki tashi kije ki fara sosai umma ta dinga karfafa mata gwiwa har  ta samu natsuwa da jin zata iya masa fiyye da abinda yake bukata daga gareta ."ahankali ta mike ta shiga dakinta taja kujera ta zauan ta fito da kayan aikinta d'auki farar takardar data fara zanen tana duba zanen da yace bai masa ba zanen yayi kyau sosai tana cikin tunanin yadda zata kawo wani sauyi akan zanen ya sake  kiranta  jiki a sanyaye ta d'aga cike da sanyi muryar tace " barka da dare sir ?you are very stupid dake da  gaisuwarki".shiru tayi hankalinta na sake tashi "ni zaki katsewa kira ?muryata nã rawa ta soma bashi hakuri ai kuwa hakan ya bawa mr ata damar zuba  mata ruwan matseefa."


Aiko  hanakalinta yay mugun mugun   tashi gabanta ya dinga  dukan tara tara cike da jin tashin hankali tace "nifa sir bana son fad'a kabi komai ahankali tunda kace tara ka bari taran gobe tayi mana idan banyi abinda kake bukata ba sai ka dauki mataki akai ".daga can inda yake zaune ya gyara zama tare da motsa bakinsa da niyyar sake mata wani sabon rashin mutunci  tunin maryama  ta kashe wayarta gabad'aya ta zuba tagumi da hannuwanta duka  tana mai runtse idanunta wayar ya cire a kunnensa yaga dip alamun ta kashe ya sake kira yaji swichoff
Tsaki yaja yasan zata rina ga rashin kunya ga tsoro wanda shine abinda yafi bukata tagani atattare daita
Ata nã zaune  yana tunanin had'uwarsu da maryama Gobe kamar ance ya d'ago kwayar idashin kawai yaga fitowar mutun daga kitchen ."


Tsumammun idanunshi ya ware akanta maryam ce da  ritsetsen cikinta da  yayi  girma sosai tana d'aga kafafuwanta da kyar yayi mugun tsura mata ido yana    kallota  nan take  yaji qirjinsa na wani irin  bugawa da qarfi  "duk da  cikin jikinta yayi girma sosai sai dai cikin bai  sa  tayi wata kiba ba sai uban fari data qara da gajarcewa yayinda hannunta ke rike da plet wanda bai san ko meye aciki ba ,ahankali ta cigaba da tafiya da kyar irin tafiyar masu ciki ta samu waje opposite dinsa ta zauna  tana danne damuwarta dan ita kad'ai tasan irin damuwar da zuciyarta take ciki akanshi ,dan ta  dauka kiyayyar da yake mata zata tsaya ne a iya kanta a she har da cikin jikinta kiyayyar  zata shafa ta sunkuyar da kanta kasa tana danne hawayen daya cika kwarnin idanunta ta soma cin d'anwake  wanda shi har lokacin bai san ko meye acikin plet din ba  sakamakon tazarar dake tsakaninsu tsumammun idanunshi kawai ya zuba mata yana kallonta da cikin jikinta ."


Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 9

Yadda mr ata ya tsurawa maryam kwayar idanunshi yana kallonta zaka d’auka zuciyarsa ta d’an saduda ne akanta ,sai dai azahirin gaskiya ba haka bane kawai tsabar mamaki ne cunkushe a zuciyarsa” wai d’ansa ko ‘yarsa ne kwance acikin matar da yake jin duk duniya bashi da abinda ya tsana sama daita tunda ta bar rayuwarsa ya d’an samu natsuwa da kwanciyar Allah a yanzu idan yace yaji dadin ganin fuskarta yayiwa Allah karya haka zalika ganin girman cikinta bai saka zuciyarsa jin komai aransa ba ko jin digon tausayinta ba sai ma jin haushi da bakinciki ganinta ne ke nunkuwa a kasan zuciyarsa yayinda zuciyarsa ke zafi da suya.” dogon tsaki yaja wanda yasa maryam tabar cin abinci da take ta d’ago kanta ta zuba masa ido dan ko bai fad’a ba tasan saboda ita yaja tsaki .”shiru tayi kawai tana faman sauke ajiyar zuciya .”fuskarshi babu walwala ya sauke kwayar idanunshi akanta alokacin da kiran gaggawa ya shigo wayarsa ya kai dubansa ga wayar ,d’aya daga cikin abokan kasuwan cinsa ne daga haka ya mike tsaye, a natse ya nufi hanyar fita waje dan gara tun wuri ya qara gaba kafin sweet heart tazo masa da batun yarinyar dan yasan dole zata masa maganarta wanda shi kuma abinda yafi tsana kenan .”


Mikewarsa ya daidai da sake jefa zuciyar maryam cikin gagarumin tashin hankali juyawa tayi tabi bayansa da ido tana kallon yadda yake d’aga qafafunsa tamkar baya son taka qasa .” kallo d’aya zaka mata ka tabbatar da cewar bata cikin natsuwa da walwala da kwanciyar hankalinta dan tunda ta sauka hankalinta da natsuwar da kwayar idanunta babu abinda suke da muradin gani tamkarsa so take taga yadda reactions dinsa zai yi idan ya ganta d’auke da cikinsa ,sai dai kash a ganin farko yayi buris daita da cikin jikinta tamkar bai gansu ba ,ita kuwa burinta ta ganshi hakazalika babynsu taji dumin jikin mahaifinta duk da tasan abu ne mai matukar wahala ya basu wannan damar .” bata san tsananin qaunar da take masa ya zarta dukkanin tunaninta ba sai data d’aura kwayar idanunta akanshi yanzu .


“ tunda taganshi taji komai ya dawo mata sabo ji tayi tamkar ada can bata ta’ba són shi ba a yanzu ne take son shi . numfashinta ya shiga sauka da sauri sauri sai ga hawaye sharr sun shiga turereniyar zubowa daga cikin kwarnin idanunta saboda rashin kulawar daya nuna mata ita da cikinsa ,gabad’aya taji gwaiwarta tayi sanyi wanda hakan ya sake tabbatar mata babu abinda zai canzasa daga ra’aayinsa ita da babynsa baza su ta’ba samun kulawa da soyayyarsa ba “me yasa bazata ciresa aranta ba tunda har qiyayyar ta kai haka ?”me yasa take son shi haka ?meye laifinta dan taso shi fiyye da komai a duniya ?”babban tashin hankalinta yanzu cikin jikinta wanda likitanta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login