Showing 27001 words to 30000 words out of 182919 words
ta gaisheta”ina kwana ummah ?kin tashi lafiya maryama ?alhamd umma “har kin shirya zuwa aiki ?eh umma na shirya sannu da aikin “yauwa maryama .mai yasa baki tasheni nayi ba ? ta fad’a tana tsura mata ido “numfashi umma ta sauke tana dubanta itama “ lafiya umma ko shigata batayi bane naje na canza ?Aa shigarki tayi kinyi min kyau né sosai fiyye da lokutan baya “murmushi maryama tayi tace “na gode sosai umma zauna kici abinci atare suka zauna umma ta zuba mata abinci ta fara ci a natse tana duba lokacj bayan ta gama ci tayi mata sallama ta fita gurin aunty ta shiga ta gaisheta tace “aunty zan fita aiki aunty tace daita “tô pricess sai kin dawo allah ya tsare.” ta fito tana ma aunty bye bye itama aunty daga mata hannu tayi cike da farinciki.”
Ahankali take d’aga qafafuwanta hannunta rike da file ta nufi office din ATA hankali take tafiya tana tuna maganganunsa na jiya “idan zakizo aiki karki zo min da wannan package din Kiyi shiri kamar kowani ma’aikaci ta furzar da numfashi tana rausayar da kwayar idanunta saboda sanin cewar ba irin shiri su tayi ba ta dai sauya daga nata shirin dan gsky bazata iya shigar suit da wondo ba da wannan tunanin ta qarasa jikin glass door tayi knowking tare da neman izinin shiga daga can bangaren aka bata umarnin shiga .”cike da sanyin jiki ta tura kofar ta shiga yana zaune akan kujera ta tsaya a gabansa tana kallon kasa ya bar abinda yake ya d’ago tsumammun idanunshi ya tsura mata yana kallonta cike da tsantsar qauna ,shigar tayi masa kyau sosai dan daman shi yana mugun son yaga doguwar mace cikin shigar dogayen kaya but yanayin aikinsu kowa shigar suit yake kusan minti shabiyar yana kallonta kafin a hankali ya d’auke kwayar idanushi .”
Muryarta a hankali ta fito “good morning sir ! bai amsa ba ya nuna mata wurin zama “ki zauna jiki a sanyaye taja kujerar dake fuskarsa baya kad’an ta zauna a hankali tamkar kazar da Kwai ya fashewa aciki yayinda zuciyarta ke wani irin rawa shi kuwa gabadaya hankalinsa da natsuwarsa suna kanta amman bazaka ta’ba iya ganewa ba stil kuma idanunshi na Kan file din hannunsa .itama haka nan ta tsinci kanta da kallonsa kyakkyawan gaske ne kuma fari ne tas tmkr balarabe yana da idanu masu dan girma da dogon hanci mr ATA iyakar haduwa ya gama haduwa sosai ajin farko yana da tsayi da fadin qirji yana da saje zuwa rabin fuskarsa sai gashin bakinshi daya zagaye gemunshi gashi dogo mara kiba sai dai ya dan fita tsayi da kad’an ”.
Shiru har tsawon mintuna ashirin bata ce uffan ba “ko zamu iya yin maganar aiki dan a tunani shi ya kawoki ba wai tsayawa kallona ba ? tai saurin d’auke idanunta akansa ta sunkuyar kasa saboda tsananin kunyar data mamayeta ahankali ta kamo yatsun hannunta tana wasa dashi “zamuyi aiki ne akan wani project kuma ina son kece zakiyi .”yayi mgnr yana dago kwayar idanunshi ya zuba mata adaidai lokacin da itama ta d’ago nata kwayar idanun nan take idanunsu ya tsarke cikin juna wani abu suka ji ya tsarga masu alokacin daya yana bin jijiyoyin jikinsu barin ma ata wanda taji tamkar ana fizgar ransa ne .”
A natse ta gyada masa kanta alamun ta gamsu cigaba da kallonta yayi tare da yi mata bayanin yadda yake son aikin ya kasance still kwayar idanu shi na cikin nata dole so yake ya dasa qaunarsa cikn zuciyarta domin ta hakan ne kawai zai samu saukin fahimtar daita sirrin dake ransa .”ya mike tsaye daga Kan kujerarsa ya d’auki system dinsa ya zagayo zuwa inda take zaune , ya zagayeta da hannunwansa duka yana nuna mata irin aikin da yake bukata yana nuna mata yana shakar numfashinta yayinda kamshi turarensa ya dinga sakata jin mummunar fad’uwar gaba mai karfi .” ya dauki tsawon lokaci suna haka kafin daga bisani ya ajiye system a gabanta ya zuba hannuwansa ciki aljihu “ina fatan kin fahimci abinda nake bukata ?In sha allahu zanyi aiki mai kyau zan kwantar da hankali nayi maka abinda kake bukata” da kyau ya fad’a ya dauki file yana dubawa muryarta na rawa tace “sir ko zan iya tafiya ?da hannunsa yayi mata alamar zata wucewa ta mike tsaye da kyar ta wuce tana mamakin hali irin nasa tunda take bata ganin mutun irinsa ba mai jin kai ,mulki da nuna isa ko da yake shi din mai tarin kudi ne kudi kuma babu abinda basa saka mutu .”
Jiki a sanyaye ta koma office ta soma aikin da sectary ta bata bata wani dauki lokaci ba ta kammala ta kai mata ta dawo office byn Kmr minti goma ata yasa aka kira ta shigo da sallama ta tsaya cike da girmamawa tace “sir gani ! “set !ya fada yana kokarin bude system sannan ya fara magana ina bukatar fresh design na kamfanin wanda yafi AGC kuma ana bukatarsa ne cikin kwana daya kacal d’an haka sai ki shirya aikinsa daga yanzu “amman sir ko zai zama kwana biyu saboda na samu natsuwar yinsa akan tsari ?”no ! ya fad’a tare da tashi tsaye ya fice daga office din ya barta zaune .” ta juya da sauri tana bin bayansa da kallo yana tafiya a natse hannunsa daya cikin aljihunsa ,goshinta ta dafe “wannan wani irin mutun ne sam baya tsayawa yaji raayin mutun babu yadda ta iya haka ta mike ta fito ta koma office ta fara shirin aiki.”
Tana zaune a office tayi concentrate sosai akan aikinta ya shigo ya tsaya akanta yana qare mata kallo kamshin daddan turarensa ne yasa ta d’ago kwayar idanunta ganishi tayi tsaye rungume da hannunwansa duka a qirji yana kallonta da tsumammun idanunshi shiru tai tana mamakin irin kallon da yake mata, fahimta yayi zata iya fassara kallonsa gareta yasa cike da sanyin jiki ya soma magana “har zuwa wani lokaci zaki kammala da wannna aikin? shiru tayi kawai tana dubansa na second biyu sannan tace “sir ina Kan kokarin yi”Kinsan dai na fad’a miki akwana daya ake bukata daga yanzu zuwa gobe da safe kenan “na sani sir zanyi qoqari in sha allahu na kammala yanzu haka ma nayi nisa so..” bai tsaya jin mai zatace ba ya fita ya barta bude da baki .”byn Kmr awa daya ya sake shigowa ya kai hannu ya d’auki makeken takadar zanenta yana dubawa ta dan kallesa ta dauke kanta tana rausayar da kwayar idanunta Kan zanen da take ji yayi kamar ya zube ajikinta ya rungumeta tsam ajikinsa yana mugun qaunar kallonta . can ya ajiye takardar ya maida kansa ga kallonta idanunta na Kan takadar zane har guda biyu “wannan zanen bai min ba gasky .” ya fad’a a tsawa ce.”
ta dago daga abinda take tare da mikewa tsaye tana kallon farar takardar dake Kan table “a haka ne kike cika baki kin iya har da zaa yi alfahari dake this is totally nonsense “ ya fad’a yana jan tsaki .”sir a naka ganin zaka iya ganin kamar bai yi ba, amman mai zai hana ka bari na kammala tukun sai kasan matsayin da zaka bashi “nace abu bai min ba kina agurment dani ?yayi mgnr adaidai lokacin da sectary dinsa ta qaraso ta tsaya a bakin kofa cikin tsananin tashin hankali.”sir wannan ai ba argument bane bayani nayi maka sai magana ta gaba ai sai daka tabbatar da kwarewata kafin kasa a nemo ni kuma ina tabbatar maka babu kamfanin da zaa kai zanena su kushe suce bai yi ba ,duk wanda kaga ya kushe zanena to hassada ce .” ta fad’a tana kallon cikin kwayar idanunshi kallo daya zaka mata ka fahimci ranta a ‘bace yake “ taya na kwantar da hankalina domin nayi maka abinda ya dace amman tun ban kammala ba ka fara zariya kana kushe min aiki amman idan kana ganin akwai wanda zai maka fiyye da nawa a kamfanin nan kana iya bashi yayi maka
ko da yake babu wanda zai iya shiyasa ka..”hussein maryama! taji an kira sunanta bata juya ba dan tasan ko wacece “how dare you argument with sir ?
“No ma ba argument bane ina dai fad’a masa abinda ya zamo gaskiya ne kawai taya tun ban qare aiki ba yazo ya tsaya min yace bai yi masa kyau ba this is totally nonsense .” ta fad’a tana hura masa hanci qirjinsa ne yayi wani irin bugawa da karfin gaske ya dinga jin kamar ana tsira masa allura a duk wata jijiya dake sansar jikinsa “tunda ya kafa mata tsumammun idanunshi bai dauke ba har sanda ta dasa aya gabadaya tsoro tattare da matsanancin firgici ya kama sectary dan bata ta’ba ganin wanda yayiwa sir haka ba yana magana ana maida masa cikin fad’a wannan shine karo na farko “kallo biyu ma baka isa kayi masa ba bare jayayya ta magana dashi .office din ya dauki shiru baka jin motsin komai sai na bugun zuciyar mutun uku mr ata , some da maryama “shikenan ki cigaba zanga karshenki ya fad’a yana kokarin juyawa tace “sir ina ganin ma zan wuce gida yanzu dan akwai abinda zanyi .”da sauri ya juyo yana dubanta a tsanake Kmr zai cinyeta,in sha allahu zan kammala zuwa gobe, sannan ka rike min takardata ko zan iya kar’ba? shiru ne ya biyo baya, ganin hk yasa maryama ta kwace takadarta daya rike yake kokarin fita dashi ta saka cikin jaka ta ra’ba ta gefensa ta kama gabanta ta barshi tsaye da mamakinta har ta kai bakin kofar fita ta tsaya batare data juyo ba “karka damu sir I wil make sure a submit the design tomorrow by 7 dot .”ta wuce ta barshi tsaye yabi bayanta da kallo yana jin wani irin quna lallai akwai aiki agabansa ya fad’a acikin zuciyarsa sectary ta matso kusa dashi “sir kayi hakuri I will talk to her zata canja lumshe idanu kawai yayi ya koma zuwa office dinsa wani zufa na karyo masa
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 8
Mutuwar tsaye mr ata yayi a wajen yana cigaba da kallon hanyar da maryama tabi ,duk yadda yaso ya kai ga son motsa sansar jikinsa ko ya bar office din zuwa nasa ko ya tsaidaita amman ya kasa saboda tsananin firgicin abinda tayi masa . "hakika ya yarda ya kuma amince wa zuciyrasa ya sadaukar wani mummunar abu na shirin faruwa dashi ,ko kuma yace alqadarinsa yazo qarshe akan maryama ." soyayyarta da yake tason boye mata take son lallai sai ya fito daita sarari kowa acikin ma'aikatar ya san da zamanta wanda shi sam babu tsarin haka a ra'ayinsa yafi son sai ya shigar da soyayyarsa cikin zuciyarta ta yadda itama zata kamu da tsananin soyayyarsa sannan ma duk abinda zai faru ya faru ."
ji yake kamar yayi kukan abinda tayi masa a yanzu a gaban some. sosai zuciyrasa ke masa zafi da qunci gashi baya son tozartata sannan baya son ta janyo masa raini a wajen sauran ma'aikatansa ."kusa dashi some ta matso kad'an tace "sir kayi hakuri dan Allah "wani zazzafan numfashi ya sauke tare da naunayen ajiyar zuciya sannan muryarsa a tsarke ta fito tamkar mai koyon magana yace "karki bari maryama ta wuce gida kiyi maza ki tsaidaita lallai ki dawo tare daita ". some tayi matukar jin mamakin abinda ya fito daga bakinsa dan a tunaninta kalmar dakatarwa ce zata fito daga bakinsa amman sai taji sa'banin haka ,dan haka bata tsaya cigaba da jin mamakinsa ba cike da hanzari ta furta "okay sir sannan ta fice da sauri tamkar zata hantsila yayinda maryama tuni ta sauka qasan ma'aikata tana d'aga qafafunta a natse sai dai kallo d'aya zaka mata ka fahimci ranta a matukar 'bace yake dan wani irin tafasa zuciyarta ke yi."
ahankali tasa kai ta shiga cikin ma'aikatan dake qoqarin fita daga cikin ma'aikatar sai ga some ta sauko tana ihun kiran sunanta "maryma! mryma !! sarai maryama ta jita amman tayi mata banza taki juyowa bare ma tayi tunanin zata tsaya ta saurareta kanta a kasa ta qarasa ficewa "securities karku bari yarinyar ce mai doguwar riga ta fita ku tsaidaita min ku tsaidaita !!sai dai ina tuni koda suka je tsaidaita tuni maryama ta tsaida mai adaidaita ta shige tana bashi umarnin su wuce ."
cikin tsanani tashin hankali some ta rike kugunta tana kallon bayan motar da maryama ta shiga yayinda hankalinta na qara tashi dan bata san yadda zata fuskanci mr ata ba ."tsabar mamakin maryama yaki barin zuciyarta bata san rashin mutuncinta har ya kai haka ba ,mr ata din zata dinga sa'insa dashi."? "Mai take taka dashi ?shiru tayi na second biyu kafin daga bisani ta girgiza kai ta fara tana zance zuci "anya ma kuwa babu wata a qasa ?sosai ta dinga tariyo irin kallon da mr ata din yake bin maryama din dashi a d'an tsakankanin wannan lokacin saurin kawar da tunaninta tayi domin tana jin hakan ba mai yuwa bane mr ata bazai ta'ba kamuwa da son maryama ba, wasu irin mata ne bai gani ba a rayuwarsa, bai kamu da soyayarsu ba sai wata maryama ."
bangaren mr ata kuwa cikin tsantsar 'bacin rai ya nufi office dinsa gabdaya duniya ta chakud'e masa waje d'aya jira kawai yake some ta dawo masa da maryama ya samu yayi mata ko mari d'aya ne ya d'an huce abinda tayi masa zai d'auki komai amman ban da raini . ahankali ya fara zariya acikin office din kwakwaluwarsa na sake tariyo masa magan ganun mryma sosai zuciyrsa ta dinga motsawa ."
da sauri some ta biyo bayansa zuwa office dinsa kamar wacce aka jefo haka ta shiga office din cikin tsananin tashin hankali ta kame nisa kad'an dashi tana had'e hannuwanta waje d'aya yayinda zuciyarta ke cike da matsanancin tsoro da fargaba ,magana take son yi amman ta rasa ta inda zata fara dan tasan shi kamar yunwar cikinta kad'an daga halinsa sai ya huce akanta."
"ina ma hakan zai faru da zai fiyye mata sauki akan action din da zai iya d'auka dan tasan ita kanta ba tsira zatayi ba tunda fushinsa ba iya kan wanda yayi laifi kad'ai yake tsayawa ba ."zariya ya cigaba da yi tamkar wanda yayiwa sarki karya yana sake aunawa kwakwaluwarsa maganr mryama .daga kalmominta ya gane komai fa ya sauya agaresa yanzu ne zai gane shi din ba komai bane dan bai isa ya dakatar daita aiki ba kamar yadda ya saba yiwa sauran worker's dinsa sai daí bazai barta haka batare daya hukuntata ba dan dole ma ya ganar daita kurenta ko dan gaba anya kuwa adam zaka iya d'aukar mataki akan maryama "?yayiwa kanshi tamabyar yana mai juyowa."
cak ya tsaya sakamakon ganin some tsaye a bayansa dan bai san da shigowarta ba aikuwa ya kafeta da tsumammun idanunshi tamkar itace tayi masa laifi , haka nan taji gabanta yayi wani irin mummunar fad'uwa da sauri ta soma magana cike da in inna "sir.."!sir !! kayi hakuri ban samu damar tsaidaita ba amman ka barta dani hakika zan bari tayi datasani abinda tayi maka , ina ganin ma wannan shine karonta na qarshe da zata tako cikin ma'aikatan nan da sunan aiki ,dan ko zamu d'auki komai bazamu d'auki wulakancinta ba we can't take it any more cikin tashin hankali da tsoro take magana ." wani banzan kallo yayi mata mai tattare da jin tashin hankali mara misaltuwa wanda yasa take some tayi shiru cike da girmamawa tana dubansa ".
da sanyin jiki yake qarasowa inda take tsaye hannuwansa duka ya zura cikin aljihunsa wondonsa yana qare mata kallo atsanake wanda shi a zahiri ba ita yake kallo ba fuskar maryama ce ke masa yawo acikin kwayar idanunshi ."kusan minti goma ya d'auka yana kallonta sannan yaja wani dogon tsaki lokacin daya fahimci halin daya shiga ya koma mazauninsa ya zauna yana sauke wani wahallalen numfashi sannan a natse ya d'auki wani file ya rike kawai ba dan yin aiki akansa ba, gabad'aya ya rasa me zai yi ya huce "sir kayi hakuri zan rubuta mata takardar dakatarwa? ta fad'a tare da juyawa ta nufi kofar fita da sauri "wa ya baki damar aikata hakan ?."ta jiyo sautin muryarsa cikin tsananin fushi .cak ta tsaya tare da juyowa ta zuba masa idanunta tana mamakin jin abinda ya fito daga bakinsa ,sai dai idanunshi na kan kallon file din dake rike a hannunsa ,sam bazakace shine mutumin da yayi maganar ba ".
ta qara taku biyu ta tsaya gabansa cike da girmamawa tace "amman sir kana ganin ya dace abarta ta cigaba da aiki damu alhalin bata cancata ba ".?oh yanzu ne kikasan bata cancata ba ?yayi mata tambayar a wulakance tare da d'ago kanshi ya tsura mata ido "só .."sorry sir bansan mugun halinta ya kai haka bane shi yasa na .." "enough !ya furta a tsawace yana d'aga mata hannu "ke kinfi kowa sanin ko ni waye ba'a sani haka zalika ba hanani idan nayi niyyar dakatar daita ba sai kince ba ". yana gama fad'ar haka yace "leave my office! da sauri ta juya tana cewa "okay sir. " sorry sir !ta fice."wani dogon tsaki ya sake ja tare da ajiye file din hannunsa ya kai hannunsa daidai habarsa ya rike yana ciza lip's dinsa da karfi