Showing 18001 words to 21000 words out of 182919 words
ya dinga fitowa daga cikin bakinta tana maimaitawa nan take jikinta yayi sanyi." "ungu nan ki karanta, emvelop ya mika mata tasa hannu ta karba jikinta na cigaba da rawa a firgice ta dinga bin rubutun sako ne daga AGC compaing wani sabon tashin hankali ta sake shiga mai tsanani tana dafe goshinta ."
"ki karanta a fili so that kowa da kowa yaji babu yadda ta iya ta soma karanta sakon a fili jikinta na wani rawa gabadayansu shiru sukai suna sauraronta zufa ne ya karyo mata sakamakon anyi cancelling sabon aikin data samu sakamakon AGC compaing na bukatarta sai kuma kamfanin gidan burodi wanda yake mallakin umma shima zai tashi domin zaa hana duk wani kamfani dake sarrafa flour bashi kaya jikinta ya cigaba da rawa kafafunta suka kasa daukarta ta sauke takadar tana furta "umma ki rikeni "! da sauri duk suka yi kanta banda mutun biyu baba gali da Aunty hasana "kasancewarki a AGC compaing shi zai sa kasuwancinmu ya cigaba da tafiya akasin haka kuwa kema kinsani sai dai a rufe kanfani mu zauna haka ya qarasa mgnr yana karbar takarda da ya bata ya kalli umma ya kamata kiyi wa wannna yarinyar magana idan ba haka ba zamu rasa komai ."
"Ai wannna galaliyar zataso haka ni ban ta'ba ganin mai kashin tsiya ba irin maryama daga wannan bala'i sai wannnan Ke dai ina ganin babu kashin arziki ajinin jikinki ni wallahi da ma aikin kika rasa gabadaya muka tsira da kafaninmu da zai fi min dadi yar bantar uba mai kashin tsiya ta daga hannu zata kai mata duka.."dakata hasana karki fara cak ta tsaya ."wai bana ce miki karki kara sa bakinki acikin maganr maryama ba muddin dai ba alkhairi zaki fad'a ba cewar granny , duk wani abu da zaa samu kasuwancinmu mutuncin zamu duba wannna kamfanin da suka mata wulakanci ko bashi bane duk suka gyada mata kai "to bazatai aiki dashi ba gara ta sake fita neman wani aiki sanyayye ajiyar zuciya ta sauke ta rarafo ta rike kafafuwan granny tana zubar da hawaye aunty ma kuka take dan baba gali ne ya kirata banci haka da bazata zo taga bacin rai ba "na gode granny dan allah ki taimakeni bana qaunar wannnna kamfanin ."hajiya wai me kke fad'a ne haka da babu dadin ji kin kuwa san adadin amfanin da wannna kamfanin yake mana ?gabdaya idan aka rufeshi to zamu dawo bara ne a bakin titi tayi aiki da AGC compaing mu kuma mu cigaba da kasuwancinmu ".
"Gali kayi hakuri da hukunci hjy ai rayuwar kunci ko da wannna kafanin ko babu idan allah ya ga dama sai yajefa rayuwarka ciki ,amman maryama bata sake komawa wannna kamfanin daaka wulakantata ba ,"maryama ta tsurawa umma idanunta daga ganin yadda take magana kawai dauriya ce da sadaukar da farincikta saboda nata farinciki zamu iya cigaba da rayuwa haka amman wulakanci bazamu dauka ba maryama maza tashi ki koma daki bama zakije koina ba ,"karki damu kinji " baba gali ya bita da kallo."maza taso diyata ta d'agata da kyar tana goge mata hawaye "kama hanya ki koma daki kina zaune wani aiki zaizo ai ke mai saa ce in sha allahu zaki samu wani ."Ahankali ta dinga daga kafafunta ta nufi kofar dakin d umma sai dai ta tsaya jiki a matukar sanyaye ta kasa cigaba da tafiya tana tunanin abinda yake faruwa daita daki daki komai yake dawo mata qirjinta ya buga lokacin data tuna maganr grany da umma hawaye masu zafi suka zubo mata "ni yanzu me ya ka mata nayi hakika idan nayiwa umma haka ban kyuata mata ba na zama silar rabata da abinda ta dogara dashi da kuwa na tabbata mai kashin tsiya idan ma akwai abinda yafishi zaa iya kiranta dashi dan dole nasan abun amman bazai yuwu nayi silar rugujewar kamfanin umma ba ko babu komai umma ta wuce haka a wurina."can kuma maganrsu sectry dinsa ce ta shiga yawo acikin brain dinta ta sake runtse idanunta babu abinda bata tuna ba amman karshe taji bazata iyawa umma haka ba ko ranta tace tana so zata bata bare yin aiki da AGC compaing babu abinda ya kamata tayi daya wuce tai joing din AGC compaing.
Dawowa tayi ta durkusa gaban umma "kiyi hakuri umma ki amince min zanyi aiki da AGC " wani sanyayyar ajiyar zuciya aunty ta sauke tana hamdala acikin ranta "ko kefa maryama sai yau nasan kinsan meye hallici kuma tabbas ke yar halace,karki bari mu rasa kamfaninmu da mukai tsawon shekaru muna amfana dashi "to baba na amince ka fad'a masu zanyi aiki dasu "a'a maryama bafa zan yarda a dinga tozarta min Ke ba dan haka kiyi zamanki da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko da kamfani ko babu zamu rayu "dan allah umma wallahi zan jure koma menene ni dai kawai Kiyi min addua umma tayi shiru ta rarrafa ta koma gaban grany "dan allah kiyiwa umma magana ta amince min tunda su suka nemi ne nasan bazasu tozartani ba kai ni akan martabar gidanmu babu abinda bazanyi ba idan yau mr ata rayuwata yake bukata zan iya bashi akan mu rasa kamfaninmu tana gama fad'ar haka ta sake dawowa gaban umma tana kuka tana rokonta amman umma tayi shiru tare da had'e rai "dan allah aunty kisa baki umma ta amince da kyar granny da aunty sukasa umma ta amince tare da mata fatan alkhairi."
Ahankali ata yake tafiya cikin shiga ta black suit hannusa daya cikin wondonsa yayinda James Ke biye dashi abaya rike da bakar jaka james yayi saurin shan gabansa ya bude masa glass door alokacin marayama na tsaye a office tare da sectary some suna magana akan yadda tautaunawarsu ta kasance akan waya a wancan rabar tare da neman afuwarta yana shigowa sectary tayi saurin gaishesa tana cewa "ga maryama hussein nan sir ."ya tsya cak tare da dan waigowa ya kalleta wani sanyi dadi yaji ya ziyarci jijiya da gangar jikinsa a natse ya juyo gabadayansa ya tsura mata ido itama a natse ta dago fararen idanunta ta tsura masa babu wani alamun tsoronsa atattare daita sai dai take taji qirjinta yayi wani irin bugawa da matsanancin karfi kallon juna suke ido cikin ido tana tuna haduwarsu ta farko duk da lokacin idanunta a rufe suke cikin nikaf shima rayuwar da sukayi a mafarki ne ya shiga dawo masa daki daki ,wanka da yake mata lokacin tana yarinya, wasa daita har zuwa girmanta da komai ya gama bayyana ajikjta da yanayin da yake ta'ba komai na jikinta tare da amincewarta yadda take sarrafa shi duk wani abinda Ke faruwa a tsakninsa daita acikin mafarkinsa babu wanda bai zo masa ba alokacin ."
a natse komai ya cigaba dawo masa boyayyayen ajiyar zuciya ya sauke sam ya manta james da sectary da suke tsaye sun kasa dauke idanu daga kallon juna ko kifta idanu basayi yaji kamar ya janyota jikinsa ya rungumeta yaji dumin jikinta na zahiri amman isa da jin kai bazai barsa ya aikata hakan ba ita kallon mamaki take masa mai ma yasa ya nace lallai sai tayi aiki à karkashinsa byn shine da kansa yasa aka koreta ? "shi kuwa kallon so yake mata yarinyar daya dade yana mutuwar so yarinyar daya dade yana marmarin haduwa daita ,yarinyar da yake muradin ta zamo mallakinsa itace tsaye agabansa a zahiri yana kallonta ba a mafarki ba ."
Bai ce dasu komai ba yana nufi glass door na biyu wanda Ke tsakninsa da sectary dinsa .yana shiga office dinsa ya kasa zama ya daura duka hannayensa akan kujera yana jiran shigowarsu da sauri sectry tayi gaba maryama tabiyota abaya cike da sanyi jiki some tace "kiyi knowking kafin ki shiga batai mata mutsu ba dan gabadaya ta sadaukar da rayuwarta gara kawai tai hakuri tayi aiki karta zauna haka babu aiki sannan kuma babu aure dan bata ga mai qararren kwanan da zai aureta ba bugu da gari kamfanin su."
a hankali tai knowking tana cewa "ko zan iya shigowa ?"Yes ! ya fad'a idanunshi na kan kofar shigowa tun daga kasa ya dauki kallon halittar dayafi qauna akan komai "mamanki ta iya haihuwa maryama ya fad'a acikin ransa tsayawa tayi ta rungume hannuwanta abaya tana hura masa hanci dan kallon da yake mata ya fara damunta sauke hannuwansa yayi ya zuba cikin aljihunsa yana cigaba da tsareta da tsumammun idanubshi masu bugar da zuciya da gangar jiki .Ita kuwa hade rai tayi sosai dan ranta ya soma baci tare da aiyanata wani sabon salon wulakanci zai mata shi kuwa fuskarsa wani annurin murmushi ne kwance amman idan ba mugun kallon kayi masa ba bazaka fahimta ba ya hade rai sosai yana cewa "me kikyi anan ? tayi matukar mamakin jin tambayarsa sai data maimaita kalmar sannan tace "mr ATA ne ya bukacini"ta fad'a har lokacin fuskata a hade ."
Sai data hura masa hancinta sannan ta cigaba da magana "sunana maryama hussein bagoro wannan sabuwar ma'aikaciyar da kuka d'auaka na rana daya sannna kukayi out daita, yanzu kuma kuka sake dawo daita ku kace tazo tayi aiki daku bayan kunsa anyi cancelling aikin data samu tare da barazanar zaa dakatar da kamfaninmu ."ta qarasa maganr tana sake hura masa hanci kamar yadda take masa a mafarkinsa."gabadaya ya mamayeta da tsumammun idanushi yana kallon kyakkyawan lip's dinta da siririn dogon hancinta komai na jikinta daidai ya dan lumshe mata idanunshi saboda dadin muryarta kamr ya fashe da dariya dan ya fahimci ya mugun bata haushi korar da yayi mata amman da yake shin din asalin miskili ne wuceta yayi da sauri ya zauan Kan kujera yasa hannunsa daya yana shafa sajen fuskarsa, can ya dauki wani file yana dubawa batare daya ce mata komai ba har tsawon mintuna shabiyar sannan ya ce "zaki iya tafiya yanzu nayi busy ."ta sake Shaka matuka mutumin nan fa mugun dan rainin hankali ne amman wallahi babu inda zata sai ta amayar da duk abinda Ke ranta ta sake gyara tsayuwa "nasan saboda kwarewata yasa kuka sake nemana domin dai bazaku ta'ba samu wacce zata baku abinda kuke buqa....."shhii karki wani cika wa mutane baki anan dan har yanzu baki da wannan matakin kwarewar , idan kika ga na wasu zaki sha mamaki da kanki zaki kira kanki da miss zero ".
"oh !
"gaskiya ne kam shiysa naga kun bukaci na dawo nayi aiki anan ? ya rufe file din hannusa da sauri yana kallon qaramin bakinta da magan Ke fitowa ta ciki ,kwata kwata babu wani alamar tsoro ko fargaba irin wanda yake hangowa a fuskar mutane dake aiki akarkashinsa idan suna tare dashi ."ni wallahi da an sani an barni alico insurance dina nayi aikina dan ma yafi kwanta min arai ."tayi mgnr tana rausayar masa da kwayar idanunta ."tsaki yaja yana motsa lip's dinsa "kisani duk inda zakije da sunan Kiyi aiki bazai ta'ba kai nan ba saboda aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ..."kayi kuskuren fad'ar hk sir ." ya ware tsumammun idanunshi sosai yana dubanta da mamaki kwamce a fuskarsa "eh haka na fad'a kayi kuskure sir kawai da dai da kun barni acan kawai batare da kun nuna karfin iko ba bare kace me ?mema kace ? "aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ."?"to a wurin wasu kenan yake abun alfahari amman ni dai abinda nayi imani dashi ko wani kamfanin na samu aiki zanji dadinsa sannna zanyi alfahari dashi kuma zanyi masu aiki mai kyau ." kun tursasa mutun yazo yayi aiki daku yanzu kuma kazo kace kayi busy dawa kenan kayi busy kai kai waye ma kai tukun ?ta fad'a a fusace .."
Mmn sudais
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 6
sai da gabansa yayi wani mummunar fad'uwa, zuciyarsa ke qoqarin motsawa amman ya dinga kwantar daita dan idan ya bari maganganunta sukai tasiri zai yi daya sani dan haka yayi shiru kawai ya cigaba da kallonta ba dan ya rasa abun yi ba she's the most beautiful girl I have ever seen in my life ya fad'a acikin zuciyarsa yayinda fuskar maryama ke cikin wani yanayi na fushi sai dai kuma kwayar idanunta na kanshi ta tsura masa idanunta kamar yadda yayi mata muryarta a sanyaye ta cigaba da motsa lip's dinta "kana tunanin dan zanyi aiki daku zan d'auki wannan wulakanci ne ?no I can't take it any more ta fad'a tare da zaro masa fararen idanunta ,da wani irin sauri ya tashi daga kan kujerarsa yana cewa" yana da matukar mahimanci kisan wani abu , yana da kyau kisan cewa kinyi mistake arayuwarki ba wai wulakanci bane kmr yadda kika d'auka, har sau biyu kina samu aiki damu kina rejecting wacece ke da zakiyi rejecting din aiki alokacin da kika só sannan ki so aiki alokacin da
kika so "yayi mgnr yana kallon cikin kwayar idanunta ."
Ahankali ta kawar da kanta zuwa gefe tana hura hanci tace "to kuma saboda banyi joining aiki daku ba alokacin da kuka so sai ya zama matsala ? wani irin kallo yayi mata mai tattare da gargadi sannna yasa hannusa d'aya cikin aljihunsa yana kallonta yana jin wani azababben qaunarta na bin jinin jikinsa ahankali ya dinga sauke numfashi kamar wanda yayi gudun tsare sannan yaja tsaki ya kai hannu sumar kanshi ya shiga ya mutsawa yana ciza gefen lips dinsa da d'an karfi "ya Allah karka sa yarinyar nan ta bani matsala "yayi mgnr a kasan ransa still yana cigaba da kallonta ." kusan mintuna goma ya d'auka yana kallonta sannna ya koma ya zauna yana sauke numfashi ya sake d'aukar wani file ya cigaba dubawa sakamakon rashin abunyi "kawai kuce kun nemi na dawo ne saboda kunsan ina da baiwar fikira da zaku amfana dashi well shikenan kawai sai ku rubuta ku ajiye ya zama tarihi ga AGC compaing ,sun ga maryam hussein na da baiwar fikira sun dawo daita aiki byn sun koreta a ranar farko ."yana jinta amman yayi mata banza yayi tamkar bai ji abinda ta fad'a ba haka kuma bai d'ago ya kalleta ba ya cigaba da abinda yake yana satar kallonta ta kasan ido yana danne bugun zuciyarsa dan wani irin sabon yanayi ya dinga jin yana shigarsa."
yayinda maryama tayita fad'ar maganganu son ranta wannan karon kam a matukar zuciye ya ajiye file din da yake rike dashi ya sake tashi ya tsaya cak a gabanta yana sauke numfashi har suna iya shakar numfashi juna da jin bugun zuciyoyinsu "Keep your mouth shut ki kama kanki kisan irin maganar da zakiyi anan dan ba'a kawo min raini , ba'a sakani kuma ba'a hanani and no body question me okay ."ya fad'a a matukar tsawace yana sanya kwayar idanunshi cikin nata, shi aiki da mahimanci ake d'aukarsa kamar yadda shi mai kasuwanci yake d'aukar kasuwancinsa ,ban dawo dake dan kizo kina min haukan banza anan ba, na koreki ne saboda na nuna miki kuskurenki, sannna na dawo dake ne saboda tausayawa domin na fahimci kin shiga tashin hankali mai tsanani a wancan ranar dana koreki idan zaki iya aiki damu kiyi idan kuma bazaki ba "leave!ya nuna mata hanyar waje da d'an yatsansa yana fesar da huci mai zafi daga bakinsa yayinda zuciyarsa ke cike da matsanancin fargaba dan yasan kad'an da aikinta zata iya juyawa ta kama gabanta ."
adduar ya shiga yi domin neman taimakon Allah" ya Allah kada kasa zantuttukana suyi tasiri a zuciyarta Allah kasani ina matukar son yarinyar nan da d'aukacin rayuwata ta shiga zuciyata dayawa ta sace zuciyata,ya Allah kasa na shiga cikin rayuwarta kamar yadda ka shigo daita cikin rayuwata domin ta zamo abokiyar rayuwata ta har abada ina matukar qaunar wannan halitta taka ya Allah ka jarabeta da soyayyata tun kafin na kai ga furta mata soyayyarta dake raina domin na azabtu akanta ,na sha wahala akanta ,ya Allah ka tausaya min ."Ita kuwa maryama shiru tayi na second goma tana dubansa batare da tace masa komai ba har ya gama maganarsa sai dai maganarsa tasa zuciyarta tayi sanyi daga zafin datayi tare da tunani ,duk da ya jefeta da kalmar hauka amman kuma ta wani bangaren sai taji kamar ya fita gsky domin kuwa a wannan zamani aiki wahala yake, idan ba kana da hanyar samunsa ba ko wata baiwa ba sai dai ka mutu haka babu aiki amman da kwalinka da karatunka sai su zama banza bazasu maka amfani ba ."dan haka Ke maryama kiyi maza maza ki shiga taitayinki ki dawo cikin hankalinki karki yarda Kiyi kuskuren da zaki sake rasa aikin nan dan haka muryarta a sanyaye tace "shikenan zanyi aiki da amana da gasky kuma in sha allahu kamfaninku zatai alfahari da ... "da kyau go back to work ." yayi sauri katseta ta hanyar fad'ar hk batare daya kalleta ba duk da kallon nata yake da bukata dan baya gajiya da kallonta amman ya kasa sai ma boyayyayen ajiyar zuciya ya sauke dan maganrta ba qaramin dadi sukai masa ba ."
"Yanzu ko zan iya sanin da me zan fara ?meet sectary "ya fad'a a dake ,ta juya jikin a sanyaye har ta kama handle zata bud'e kofa ya tsaidaita ta hanyar cewa "ke .." ta tsaya cak batare data juyo ba sai dai qirjinta na wani irin bugawa da sauri sauri "idan zaki zo aiki gobe karki kuskure kizo min da wannan package din, kizo cikin tsari shigar aiki Kmr kowani ma'aikaci ."da sauri ta juyo tana masa kallon tsana zuciyarta cike da mamaki to mai ya samu kayanta ?ta jefawa kanta tambaya tana dubansa bai kalleta ba sai dai ta kasan idanunshi yake d'aukar kallonta tana kallonsa ya janyo system gabansa ya cigaba da aiki ta bud'e kofa ta mayar da karfi ji