Showing 117001 words to 120000 words out of 182919 words
da har zai sota ita data kasance jinin talakawa ,me yasa zai sota?"kai wanan ma ba abune mai yuwu ba, akwai dai abinda yake nema a wajenta wanda ba sai ta tsaya wahalar da kanta ba tuni tasan me yake so atare daita gara ta kama mutuncin kanta zai fiyye mata alkhairi kuma har abada bazata yarda ta banzatar da budurcinta ba duk wuya duk runtsi tana tare da abunta .”cike da natsuwa ta shiga ta zauna bangaren daya bud’e mata tana mai ra'be jikinta tare da kamkame kayan jiknta tana kallon bangaren da take zaune tana jinsa ya shigo ya zauna a kusa daita bai ra’beta ba sai dai taji idanunshi ajikinta suna yawo wanda ke qara saka zuciyarta tsinkewa tare da mummunar bugu .”
ahkl mota biyu suka fara fita sai motar da suke ciki tabi bayansu sai kuma mota biyu dake biye dasu a natse direba ke jansu, motar tayi shiru yadda bai ce mata qalla ba itama bata waigo inda yake ba bare ma ita bata da abinda zata ce masa ,dan kusan shi ke takalota da magana har suka isa titin Liverpool bai ce uffan ba , anan taga motocin gabansu sun d’auki wata hanya haka ma motocin bayansu yayinda motarsu ta sauka zuwa kasan bridge din Liverpool ahankali direban ke jansu ,tukinsa bai yi slow ba hakazalika ba mugun gudu yake shararawa ba a haka har suka shigo unguwarsu still babu wanda ya cewa danuwansa wani abu ,a ruwa yayi parking a inda yayi jiya yana cewa “ranka ya dade mun qaraso mr ata bai ce masa qala ba illa ya rankwafo zuwa jikinta yana qoqarin bud'e mata murfin motar daga cikin “ya rabbi ta furta tana saisaita numfashinta sakamakon abinda taji ya tsarga mata ai yana barin jikinta tayi wuf ta fito daga mota adaidai lokacin daake kiran sallahr isha'i kafin tayi tattaki ta tsallaka ta karya kwanar da zata shigar daita dogon layinsu taga ya fito bata tsaya ba ta soma tafiya.”
ahankali ya biyo bayanta, idanuwanshi na kanta haka ya dinga binta yana bin duk wani takunta da kwayar idanunshi tamkar wacce ke rangaji haka take ajiye takunta a nutse duk ilahirin jikinta na juyawa ,duk jin kan maryam daya sani da nuna ita wa tace wajen iya gayu da sanyin murya tare da iya tafiya bai ta'ba ganin tayi irin salon maryama ba kai bai ma san mata nada irin wannan salon ba ko don bai kallon mata ne sai maryam din data zame masa dole kuma da ita kad’ai ya zauna bai sani ba , dan shi bai san komai da ya shafi shirgin mata ba tsakaninshi dasu a wajen aiki ne kuma tsakani da Allah shi baya kallon tafiyarsu ."
"Wait" ! Kunnuwanta suka jiyo mata muryarsa mafi soyuwar sauti domin dai ko tana so ko bata só zuciyarta ta aminta yana da sanyin murya mai dadi da shiga jiki ,ta tsaya cak ta kasa juyowa zuwa garesa sakamakon abinda ke nukurkusan zuciyarta da ganganr jikinta a natse ya qaraso zuwa gareta ya tsaya a gefenta yana had'a kafad'anta danashi "ta d'an matsa kad’an aranta tace "matsalarsa kenan son jikin matseefa”.
ya motsa lip's dinsa ahankali "karki mata tambayar da nayi miki d'azu a office ,tana jinsa amman tayi shiru "zan baki lokacin nan da qarshen watan nan ina son ki natsu kiyi tunani akaina, bana son idan na tambayeki ki tsaya min inda inda ko kice baki fahimci komai ba ,ko kuma kizo min da wannan banzar kukan naki I can't take it "yana gama fad'ar haka yace zaki iya wucewa zuciyarta na bugawa da matsanancin qarfi ta soma d'aga qafafuwanta wanda take jin sun mata nauyi kamar yadda maganarsa suka mata nauyi acikin kwakwaluwarta ,tana tafiya amman still tana jin idanunshi na biye daita a duk inda tasa qafarta sai dai ta kasa juyowa taga halin da yake ciki a haka ta shige gidansu bazata iya cewa ga adadin lokacin daya d'auka a kofar gidansu ba ."kai tsaye bangaren umma ta shiga kamar koda yaushe Sai dai duk jikinta yayi wani iri umma ta hango zaune ita kad’ai a parlour’n hannunta rike da casbaha da alamun idar da sallarta kenan .”
assalamu alaikum “ta furta tana mai qoqarin qarasawa inda take, umma ta amsa mata tana kallonta da kulawa “maryama kin dawo ?”na dawo umma sannu da gida .”yauwa !”ta amsa tana dubanta maryama tayi shiru tana jingina bayanta ajikin kujera har lokacin zuciyarta taki daina bugawa inda ita kuma so take ta saisaita ta dawo normal .”
“Lafiya kuwa maryama naga duk kinyi wani iri “?hawaye ya d’an gangaro a gefen idanunta amman tayi dabarar gogesa “haka fa jiya kika shigo min nayita tambayarki abinda ya samu hannunki kika
yi ta wasa da hankalina batare da kin fad’a min ba yau ma gashi kin shigo min wani iri anya kuwa maryama kina son kwanciyar hankalina “?nafi kowa son kwanciyar hankalinki ,babu komai ne yasa yau na gaji ne sannan jiya yankewa nayi yasa kika ganni wani iri “naji kin gaji ne yau shi yanka garin yaya ne ta faru ?”maryama taso sheida mata komai amman dai tayi tunanin ta bari har mr ata yagama mata binciken da yace zai yi mata ta gyara zamanta tana duban umma “ki kwantar da hankalinki babu komai kawai dai sausayi ne numfashi umma ta sauke tace “naji sausauyi ne amman fa kisan bayanshi akwai abinda ke damunki menene shi ?”maryama tayi shiru suna kallon juna da umma tasani dole umma zata damu sakamakon jiya bata runtsa ba zariyar data dinga yi daga dakin zuwa parlour ma kad’ai ya isa ta gane tana da damuwa wacce baa akan kowa bane sai akan mr ata .”
”ina jinki fad’a kinji maryamata baki da wacce tafini nima kuma haka damuwarki damuwata ce haka kuma farinciki farincikina ne .”maryama kam data rasa me zatace wa umma kawai ta fashe mata da kuka “subhallah maryama me ye abun kuka ?”ta fad’a tana riko hannunta maryama ta share hawayeta haka nan ta tsinci kanta da cewa “gaskiya umma na gaji da wannan shegen aikin akwai abinda nake jira da zarar na gama zan daina zuwa wannan dan iskan aikin na huta “nunfashi umma
Ta sauke cikin rarrashi tace “haba maryama ki dena
iskanta aikin da muke cin abinci dashi kiyi hakuri wata rana sai labari yanzu fad’a me ya faru ?”Umma dan kana cin abunci a k'ark'ashin mutum sai ya dinga wulak'antaka, shima fa Allah ne ya bashi ba wayansa ko dabarar sa ba."hakane maryama amma wasu basa fahimtar hakan, yanzu fad’a min mai kuma mai kamfanin creation yayi miki dan nasan shi ne kawai yake baki matsala ?”shiru maryama tai dan bazata iya fad’awa umma cewar mr ata yana ta’ba mata jiki ba “kawai dai wulakancinsa ne yayi yawa “in dai akan wannan ne ke meye damuwarki
in sha Allah wata rana zaizo ya daina “babu rana kullum abubuwansa gaba suke ta fad’a tare da mikewa ta nufi dakinta umma tai murmushi kawai tana cewa “Allah ya kyauta shi kuma Allah yayaye masa .”
Mr ata bai shigo babban parlour'n mami ba sai bayan qarfe goma kai tsaye samansa ya nufa yayi sallar isha' bayan yayi wanka, ya sanya fara riga hamles da gajeren wondo ash iya gwiwa ya sauko ya shiga parlour'n mami na biyu bai ganta ba ya zarce d'akinta bakinsa d'auke da sallama inda ya iske mami zaune tana yiwa mai aikinta bayanin abinda take bukata kasamcewa gobe da sassafe zataje mata kasuwar matuwaf ganinsa yasa mami ta dakata da abinda yake ta amsa masa sallama tana dubansa da kulawa har ya qaraso ya zauna kusa daita "sweet heart barka da dare?"barka adamcy nan yaushe ka shigo ?"ta tambayesa tana sallamar tabawa inda ta mike da sauri ta gaishesa ta bar d'akin adaidai lokacin ya motsa labbansa "ban wani jima da dawowa ba sweetheart cikina qugi yake ".okay tashi muje dan ta fahimci yunwa yake ji atare suka mike suka fito zuwa babban parlour'n ya samu waje ya zauna a saman dining,yayinda mami ta shige kitchen. ya zauna shiru yana tunanin muradin ransa "ko a wani hali take yanzu ?"ko me taci a daren nan ?"allah yasa dai tasanyawa cikin wani abu dan ya fahimci bata son cin abinci fitowa mami tayi daga kitchen rike da cup a hannunta ta mika masa "fara shan ruwan zafi ".
Yasa hannu ya kar'ba yana cewa "na gode sweetheart "bata ce komai ba ta soma qoqarin zuba masa abinci shi kuma ya kai cup bakinsa ya kurbi kadan yace "ina ashraf?"yana tare da mamansa da babansa ?"yayi shiru kafin ahankali yace "yaushe ne zasu tattara su koma gidansu?"mami tayi murmushi tace har ka gaji da baban naka?"no sweetheart ina matukar qaunar yaron ko dan shi bazan so su koma ba amman dai ya kamata su komai din dan nasan hisham zai fi buqatarsu atare dashi "wannan kuma haka ne ta ajiye masa plet din abinci a gabansa ta zauna saman dining ta zuba masa idanu shima idanu ya zuba mata yana kallonta,tace "in sha allahu next week zasu yi arbain kwana uku kawai zasu qara su koma”
a natse yake cin abinci suna hira da mami har ya tashi da plet din abinci "gaskiya yau kaji yunwa ?"
“sosai sweetheart baa magana” me yasa kake barin cikinka babu abinci ?"ka dinga qoqarin cin wani abu "in sha allahu zan kiyayye dake yau din ne ban zauna ba numfasawa tayi kana ta cigaba da magana "zuwa yaushe ne zaka bar AGC kamar yadda kayi min alqawari?"sweetheart ina kan shirin barinsa at anytime zan barshi me zai zaunar dani bayan nayi miki alqawarin barinsa ?"yauwa adamcy na Allah ya yi maka albarka yace ameen tare da mikewa yana cewa "ni zanje na dan yi wani aiki sai da safe allah tashemu lafiya ya juya tabi bayansa da kallo har sai data ga ba cewarsa ."
*******
Zaune mr ata yake bisa carpet a babban parlon mami kasancewar week end ne ba aiki, k'afarshi d'aya a miq'e d'ayar kuma ya lank'washeta ya d'ora system kan cinyarshi yana operating d'inta.sanye yake cikin fari sol d'in dogon wando da red d'in riga mai k'aramin hannu, sai farar facing cap daya d'ora akansa, duk da cewa kayan shan iskane na gida hakan bai hana kayan suyi masa kyau ainun ba Gefenshi kuma mami ce akan kujera sanye idanunta cikin medical glasses tana kallon labarai , can gefe kuma nana hauwa’u ce kwance bisa doguwar kujera ta maida hankalinta gaba d'aya kan waya saboda charting d'in da take da maryam da kuma wasu friends d'inta Parlon shiru kowa da abinda yake.
Bayan kamar mintuna goma mami ta mike ta shiga kitchen inda nana hauwa’u ta katse shirun dake tsakaninta da mr ata ta hanyar cewa “dan Allah yaya ko zan iya tambayarka bai dago ba yace “uhm !”wanda hakan ke nuna alamun tayi “nace yarinyar nan da kukayi presentation daita last week tayi kama matukar da yarinyar mafarkinka “yana jin amman yaki d’agowa ya cigaba da aikinsa “ko ..”ko dai itace ka ganota amman baka fad’a mana ba ?”tayi maganar muryarta cike da tsoro “bata bace !”ya fad’a ataikaice still bai dago kanshi ba “okay may be kama ce dan gsky sunyi kama sosai “ba ita bace kuma babu wani kamar da sukai .”
Nana hauwa’u ta sauke numfashi tana dubansa a tsanake kafin ahankali tace “to yaushe ne zaka sake kawo mana mu gaisa ina son na sake ganinta ".
A fusace ya d'ago tare da galla mata wata uwar harara yace. get out tun kafin inxo in tattakaki anan wajen nak'i in kawota d'in munafukar banza kawai ni zaki kawo salon munafurci ?”yaya …”shhiiii maza ka gabanki na sake jin ki sake min maganarta wata yarinyar sai kinga yadda zanyi dake nonsense kawai
Tashi tayi ta shuri takalmanta tana qoqarin barin parlon mami ta fito tana cewa “lafiya ku dana barku lafiya me kuma ya kawo batun nonsense?”nana hauwa’u bata tsaya ba ta wuce tana k'unk'uniaiko ya qara mata da "Very stupid". Yace yana rakata da harara, dan bayason abinda zai taso da maganar maryama a gidan yanzu sai ya gama komai da kanshi zai fito da maganar mami dake tsaye tana jinsa ta ajiye plet din hannunta tare da zare glass d'in idanunta.kallonshi tayi ta b'ata rai tare da fad'in.
"Wai adamcy sai yaushe zaka can zane?, uhm yaran nan fa basu da wani d'an uwa daya wuceka idan basuyi hira dakai ba dawa zasuyi?kullum tsakaninka dasu hantara ne ko wulakanci to banason haka kaji na fad'a maka".
"Toh sweetheart ". yace yana rufe computer tare da sauketa k'asa,"Kuma fa maganar nana hauwa’u nakan hanya ya kamata ka kawo mana ita yarinyar kamar yadda mukayi da kai mu gaisa ko".ya jiyo muryar mami na fad'a."Kai sweetheart wai dan Allah ya zaki biyewa shirmen yarinyar nan".idan na kawota kuce mata me ?”yarinyar nan babu komai tsakaninmu ku jira mana har na fara sonta ,”
Murmushi mami tayi tace “ ba wani shirme ya kamata ka kawota mu ita mu gaisa in ganta kafin tazo a matsayin matarka". Kan dole ya amsa mata saboda bai son yin musu da ita.system d'inshi ya d'auka ya nufi side d'inshi yana tunanin ta inda zai kawo maryama gidansu yasan ma yana mata maganar kai tsaye zata fassara shi .”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 34
Zaune hajiya rahma take a gefen katifarta hannunta rike da hotuna wanda a 'yan shekarun nan a duk sanda zata ke'bance kanta to wad'an nan hototunan sune abun kallo agareta, wani lokaci yasata zubar da hawaye ,wani lokacin kuma tayi murmushi tare da nadamar zartar da hukuncinta akanta ,tayi shiru cikin tsananin tunanin wacce ke cikin hotunan kamar yadda ta saba ,ta dade zaune tana kallon hotunan tana sake zurfafa tunaninta da nadamar abinda ta aikata kafin ahankali ta fara zance a fili "Allah sarki bilkisu baiwar Allah mai tsananin hakuri da son mutane, mai tsananin kawaici ,Allah sarki diyata duk inda akaje sai anyi jimamin rashinki bilkisu mai tsananin son yan'u wanta har da ma wad'an da ba yan’uwanta ba ,bilkisu mai tausayi da amana ,nayi rashinki diyata Allah ka juyo min da hankalinta zuwa gareni.."nan kuka mai qarfi yaci karfinta "ai ko ta soma kuka sosai tana duban hotunanta "yau tsawon shekaru nawa kenan tana fama da abu d'aya?"kusan shekaru ashirin da wani abu kenan ,lokacin da abun yana sabo sabo bai dameta ba amman sai daga baya ta fahimci kusku renta,a kullum idan ta tuna sai ta tuna maganar hajiya safiyya aminiyarta,ta kance kiyi hakuri rahma ki rungumi qaddarar diyarki wata rana komai zai wuce .haka kullum take fad'a mata ,kuma baa wata shida bata kirata ba,tai ta rarrashinta tana bata baki amman duk tasa qafa ta shure maganarta .ta tuna shekaru goma da suka wuce mijinta alhaji rafi'u giwa tun yana jin zai iya hakura da lamarin bilkisu har yazo ya kasa yazo yana nuna a zahiri bazai iya rashin bilkisu ba ,har ma yace zai je ya nemi inda take amman tace masa a'a yayi hakuri ya d'aure yayi zamansa kar yaje zata dawo da qafafuwanta domin matsawar sukaje gareta tayi nasara akansu kuma taci bulus akan kuskurenta gara a barta idan ta sha wahala da kanta zata dawo ."
alokacin sai Allah yazo ya dora ma alhaji rafi'u giwa wani irin hakuri akan bilkisu ya cigaba tsabgoginsa da harkar kasuwancinsa da muamula da sauran ya'yansa ."sai gashi ita daga baya ta kasa hakuri tayi ta zuba ido yaushe ne bilkisunta zata zo ?"yaushe ne zata dawo garesu a tun shekarun goman nan gashi har an haura shekara ashirin bilkisu shiru tun tana ganin abun kamar film har sai da'aka d'auki wannan shekarun babu ita babu labarinta tasan cewar lallai bilkisu tayi fushi mai tsanani dasu kuma babu tabbas din zata dawo domin duk inda take a yanzu ta tsaya bisa qafafuwanta kuka take sosai," wannan ciwon na rashin bilkisu ciwo ne da kullum yake cin zuciyarta wanda take jin bazai ta'ba warkewa ba har qarshen rayuwarta ,tunda zuciyarta tayi nisa daita ta rasa wani bangaren na rayuwarta ."tana zaune tana kuka yaya mahmud ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama ,ganin halin da take ciki ya bita da wani irin kallo kafin ahankali ya qaraso gareta jikinsa na d'aukar rawa ya durkusa agabanta ya kamo hannun ta cikin nashi babu abinda ya tsana kamar ganin hawayen iyayensa balle mahaifiyarsa da bai da kamarta a duniya kukanta har cikin zuciyarsa yake ji "mum kiyi hakuri ki daina kuka nan ki fad'a min damuwarki kafin tace wani abu tuni hotunan bilkisu guda uku dake rike a hannunta suka zubo."
yabi hotunan da kallon mamaki yana jin wani iri acikin zuciyarsa dama gangar jikinsa nan take jikinsa yayi mugun sanyi domin kuwa ko bata fad'a masa damuwarta ba yasan kukan rashinta take yi nan take yaji da akwai yadda za'ayi ya dawo mata da bilkisunta da zai yi amman sun rigada sun ma kansu alqawari muddin ba itace ta dawo da qafafuwanta babu wanda zai taka zuwa gareta ,ya matso sosai kusa daita yasa kanshi akan cinyarta yana jin yadda zuciyarsa take ta fasa yana jin kamar sune silar kukan mahaifiyarsu ,yana jin duk laifinsu ne da