Showing 24001 words to 27000 words out of 182919 words

Chapter 9 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

346

masa kyau sosai dan daman shi yana mugun son yaga doguwar mace cikin shigar dogayen kaya but yanayin aikinsu kowa shigar suit yake kusan minti shabiyar yana kallonta kafin a hankali ya d’auke kwayar idanushi .”


Muryarta a hankali ta fito “good morning sir ! bai amsa ba ya nuna mata wurin zama “ki zauna jiki a sanyaye taja kujerar dake fuskarsa baya kad’an ta zauna a hankali tamkar kazar da Kwai ya fashewa aciki yayinda zuciyarta ke wani irin rawa shi kuwa gabadaya hankalinsa da natsuwarsa suna kanta amman bazaka ta’ba iya ganewa ba stil kuma idanunshi na Kan file din hannunsa .itama haka nan ta tsinci kanta da kallonsa kyakkyawan gaske ne kuma fari ne tas tmkr balarabe yana da idanu masu dan girma da dogon hanci mr ATA iyakar haduwa ya gama haduwa sosai ajin farko yana da tsayi da fadin qirji yana da saje zuwa rabin fuskarsa sai gashin bakinshi daya zagaye gemunshi gashi dogo mara kiba sai dai ya dan fita tsayi da kad’an ”.
Shiru har tsawon mintuna ashirin bata ce uffan ba “ko zamu iya yin maganar aiki dan a tunani shi ya kawoki ba wai tsayawa kallona ba ? tai saurin d’auke idanunta akansa ta sunkuyar kasa saboda tsananin kunyar data mamayeta ahankali ta kamo yatsun hannunta tana wasa dashi “zamuyi aiki ne akan wani project kuma ina son kece zakiyi .”yayi mgnr yana dago kwayar idanunshi ya zuba mata adaidai lokacin da itama ta d’ago nata kwayar idanun nan take idanunsu ya tsarke cikin juna wani abu suka ji ya tsarga masu alokacin daya yana bin jijiyoyin jikinsu barin ma ata wanda taji tamkar ana fizgar ransa ne .”



A natse ta gyada masa kanta alamun ta gamsu cigaba da kallonta yayi tare da yi mata bayanin yadda yake son aikin ya kasance still kwayar idanu shi na cikin nata dole so yake ya dasa qaunarsa cikn zuciyarta domin ta hakan ne kawai zai samu saukin fahimtar daita sirrin dake ransa .”ya mike tsaye daga Kan kujerarsa ya d’auki system dinsa ya zagayo zuwa inda take zaune , ya zagayeta da hannunwansa duka yana nuna mata irin aikin da yake bukata yana nuna mata yana shakar numfashinta yayinda kamshi turarensa ya dinga sakata jin mummunar fad’uwar gaba mai karfi .” ya dauki tsawon lokaci suna haka kafin daga bisani ya ajiye system a gabanta ya zuba hannuwansa ciki aljihu “ina fatan kin fahimci abinda nake bukata ?In sha allahu zanyi aiki mai kyau zan kwantar da hankali nayi maka abinda kake bukata” da kyau ya fad’a ya dauki file yana dubawa muryarta na rawa tace “sir ko zan iya tafiya ?da hannunsa yayi mata alamar zata wucewa ta mike tsaye da kyar ta wuce tana mamakin hali irin nasa tunda take bata ganin mutun irinsa ba mai jin kai ,mulki da nuna isa ko da yake shi din mai tarin kudi ne kudi kuma babu abinda basa saka mutu .”


Jiki a sanyaye ta koma office ta soma aikin da sectary ta bata bata wani dauki lokaci ba ta kammala ta kai mata ta dawo office byn Kmr minti goma ata yasa aka kira ta shigo da sallama ta tsaya cike da girmamawa tace “sir gani ! “set !ya fada yana kokarin bude system sannan ya fara magana ina bukatar fresh design na kamfanin wanda yafi AGC kuma ana bukatarsa ne cikin kwana daya kacal d’an haka sai ki shirya aikinsa daga yanzu “amman sir ko zai zama kwana biyu saboda na samu natsuwar yinsa akan tsari ?”no ! ya fad’a tare da tashi tsaye ya fice daga office din ya barta zaune .” ta juya da sauri tana bin bayansa da kallo yana tafiya a natse hannunsa daya cikin aljihunsa ,goshinta ta dafe “wannan wani irin mutun ne sam baya tsayawa yaji raayin mutun babu yadda ta iya haka ta mike ta fito ta koma office ta fara shirin aiki.”



Tana zaune a office tayi concentrate sosai akan aikinta ya shigo ya tsaya akanta yana qare mata kallo kamshin daddan turarensa ne yasa ta d’ago kwayar idanunta ganishi tayi tsaye rungume da hannunwansa duka a qirji yana kallonta da tsumammun idanunshi shiru tai tana mamakin irin kallon da yake mata, fahimta yayi zata iya fassara kallonsa gareta yasa cike da sanyin jiki ya soma magana “har zuwa wani lokaci zaki kammala da wannna aikin? shiru tayi kawai tana dubansa na second biyu sannan tace “sir ina Kan kokarin yi”Kinsan dai na fad’a miki akwana daya ake bukata daga yanzu zuwa gobe da safe kenan “na sani sir zanyi qoqari in sha allahu na kammala yanzu haka ma nayi nisa so..” bai tsaya jin mai zatace ba ya fita ya barta bude da baki .”byn Kmr awa daya ya sake shigowa ya kai hannu ya d’auki makeken takadar zanenta yana dubawa ta dan kallesa ta dauke kanta tana rausayar da kwayar idanunta Kan zanen da take ji yayi kamar ya zube ajikinta ya rungumeta tsam ajikinsa yana mugun qaunar kallonta . can ya ajiye takardar ya maida kansa ga kallonta idanunta na Kan takadar zane har guda biyu “wannan zanen bai min ba gasky .” ya fad’a a tsawa ce.”


ta dago daga abinda take tare da mikewa tsaye tana kallon farar takardar dake Kan table “a haka ne kike cika baki kin iya har da zaa yi alfahari dake this is totally nonsense “ ya fad’a yana jan tsaki .”sir a naka ganin zaka iya ganin kamar bai yi ba, amman mai zai hana ka bari na kammala tukun sai kasan matsayin da zaka bashi “nace abu bai min ba kina agurment dani ?yayi mgnr adaidai lokacin da sectary dinsa ta qaraso ta tsaya a bakin kofa cikin tsananin tashin hankali.”sir wannan ai ba argument bane bayani nayi maka sai magana ta gaba ai sai daka tabbatar da kwarewata kafin kasa a nemo ni kuma ina tabbatar maka babu kamfanin da zaa kai zanena su kushe suce bai yi ba ,duk wanda kaga ya kushe zanena to hassada ce .” ta fad’a tana kallon cikin kwayar idanunshi kallo daya zaka mata ka fahimci ranta a ‘bace yake “ taya na kwantar da hankalina domin nayi maka abinda ya dace amman tun ban kammala ba ka fara zariya kana kushe min aiki amman idan kana ganin akwai wanda zai maka fiyye da nawa a kamfanin nan kana iya bashi yayi maka
ko da yake babu wanda zai iya shiyasa ka..”hussein maryama! taji an kira sunanta bata juya ba dan tasan ko wacece “how dare you argument with sir ?


“No ma ba argument bane ina dai fad’a masa abinda ya zamo gaskiya ne kawai taya tun ban qare aiki ba yazo ya tsaya min yace bai yi masa kyau ba this is totally nonsense .” ta fad’a tana hura masa hanci qirjinsa ne yayi wani irin bugawa da karfin gaske ya dinga jin kamar ana tsira masa allura a duk wata jijiya dake sansar jikinsa “tunda ya kafa mata tsumammun idanunshi bai dauke ba har sanda ta dasa aya gabadaya tsoro tattare da matsanancin firgici ya kama sectary dan bata ta’ba ganin wanda yayiwa sir haka ba yana magana ana maida masa cikin fad’a wannan shine karo na farko “kallo biyu ma baka isa kayi masa ba bare jayayya ta magana dashi .office din ya dauki shiru baka jin motsin komai sai na bugun zuciyar mutun uku mr ata , some da maryama “shikenan ki cigaba zanga karshenki ya fad’a yana kokarin juyawa tace “sir ina ganin ma zan wuce gida yanzu dan akwai abinda zanyi .”da sauri ya juyo yana dubanta a tsanake Kmr zai cinyeta,in sha allahu zan kammala zuwa gobe, sannan ka rike min takardata ko zan iya kar’ba? shiru ne ya biyo baya, ganin hk yasa maryama ta kwace takadarta daya rike yake kokarin fita dashi ta saka cikin jaka ta ra’ba ta gefensa ta kama gabanta ta barshi tsaye da mamakinta har ta kai bakin kofar fita ta tsaya batare data juyo ba “karka damu sir I wil make sure a submit the design tomorrow by 7 dot .”ta wuce ta barshi tsaye yabi bayanta da kallo yana jin wani irin quna lallai akwai aiki agabansa ya fad’a acikin zuciyarsa sectary ta matso kusa dashi “sir kayi hakuri I will talk to her zata canja lumshe idanu kawai yayi ya koma zuwa office dinsa wani zufa na karyo masa a gbdy ilahirin jikinsa “.


Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 7


Fita ata yayi daga gidan gabad’aya zuwa gidan mb sai dai har yaje gidan abinda baba qaramin yayi masa nata damunsa acikin rai , mb bai fahimci yana cikin ‘bacin rai ba dan yasan halinsa kullum cikin had’e rai da kamewa yake shiyasa ma ya fara da yi masa maganar maryam “adamcy baka ga ya kamata ka waiwayi yarinyar nan maryam da cikin jikinta ba ?shiru ata yayi tare da sake had’e fuska sosai , mb ya dawo kusa dashi tare da tsura masa ido yana dubansa “mai yasa kana girma amman har yanzu baka da wayo ?” yanzu d’an ko ‘yar da zaka fara samu a duniya zaka wulakanta?kallonsa kawai ata yake ko kifta ido ba yayi sai ma wani kalar kallon banza da yake masa .ahankali mb ya sauke numfashi “ka zauna ka natsu adamcy duk ‘yanuwanka sun kawo ido sun zuba maka saboda gudun fushinka “me zanyi mb ?”yayi maganar a zafafe yana jan tsaki “nifa yarinyar nan gabad’aya na manta daita arayuwata idan har ba maganrta akayi ba sam sam bana tunata“.


“ba ace ka dinga tunawa daita ba tunda ansan baka sonta ,abinda take d’auke dashi ake son ka waiwaya kasani ko iya rabonka kenan a duniya ?take ata yaji wani sabon damuwa ya masa mummunar kamu . sosai yaji zuciyarsa na bugawa da sauri sauri
“Ka natsu sosai ka duba maganata “.cike da jin haushi ya fesar da iskar bakinsa mai zafi yace “ka daina min mugun baki mana “ba mugun baki bane adamcy misali nayi maka domin kasan kuskure kake yi “to bana son wannan musalin please.”ya fad’a cikin tsnanin fushi “kayi hakuri adamcy ba baki bane bamusan menene a rubuce a cikin kundin littafinmu ba dan haka kayi wani abu ko sau d’aya ne kaje ka ganta “I can’t !”ya fad’a a zafafe .”zaro ido mb yayi “what do you mean adamcy ?kana da hankali kuwa? “ I don’t know ko ina dashi ko bani dashi but I don’t fell to go. “ what’s wrong with you?are you trying to say that you are not going to see her and your baby ?”exactly !”


“Please adamcy don’t do that kaje saboda babynka ba saboda ita ba “I don’t fell like zanje “okay ka kirata ko ta waya ne kaji lafiyarta data baby “dan girman allah mb banason damuwa bana jin zanje koina ,ko nace tayiwa kanta ciki ne ?ko lokacin daakayi cikin nasani bare yanzu kazo ka dameni da banza banzar magana ?ya hau mb da fad’a yana huci yana gama fad’ar haka ya d’aura kansa akan hannun kujerar da yake zaune sake matsowa kusa dashi mb yayi zai masa magan yace “enough !ya fad’a a tsawace tare da d’aga masa hannu alamun ya kyalesa “mb banason sake jin komai akan yarinyar nan .yarinyar data cuceni ta cuci rayuwata bazan ta’ba yafe mata ba tayi adduar ta rigani mutuwa domin idan nine na rigata mutuwa na barta da nauyi domin bazan yafe abinda tayi min ba .”


“zaro ido mb ya sake yi yana cewa”haba haba !!adamcy mai yayi zafi haka ?meye acikin abinda tayi bayan hakinta ne “shine akace tayi min fyade ?”dan allah ka daina fad’ar haka “na gaji mb abar maganar nan hk dan danasan dashi zaka tareni wallahi da bazan zo ba haka mutun yazo da damuwa ka sake qara masa wata damuwa ya fad’a tare da point dinsa da hannunsa “kyalesa mb yayi ba dan yaso ba sai dan sanin halinsa da yayi mutun da idan ya kafe akan abu to zai yi wuya a tankwarasa.” a natse ya mike tsaye yana jan tsaki ya fito zuwa haraban gidan inda motocinsa da masu tsaronsa ke zaman jiran fitowarsa ahankali mb ke take masa baya har suka qaraso inda motar da zai shiga yake aka bud’e masa “adamcy karkace na dameka amamn dan Allah kasamu lokaci ka duba maganata ,ka mika lamarinka zuwa ga allah ka tsarkake zuciyarka dominsa tun kafin haki ya kamaka ka tausayawa yarinyar nan wallahi ina tausayawa yanayin da take ciki ga tarin damuwa ga soyayyarka ga cikin jikinta.”


ata bai ce masa uffan ba sai ma d’aga tsumammun idanunshi yayi ya sauke aka wrist watch din dake d’aure a hannunsa ganin lokaci ya tafi yasashi jan tsaki sannan ya shiga bayan mota ya zauna aka jashi inda zuciyarsa ke wani irin bugawa da qarfin gaske kamar kar mb yayi masa maganarta haka nan kuma sai yaji abun na damunsa har ya dawo gida yana jin maganr na yawo cikin kwakwaluwarsa mai yasa ma naje wajensa?yayiwa kanshi tamabyar yana jan tsaki .” yana hawa sama bedroom dinshi ya nufa ya tsaya a bakin window dakinsa yayi shiru yana tunanin maganar mb gabadaya sai yaji duniya ta tsaya masa waje daya cak bai taba sani dan anyi masa maganar cikin jikinta abun zai tsaya masa arai har ya damesa ba ,wani irin tashin hankalin ya shiga qirjinsa na wani irin bugu “bai sonta amman abinda tayi masa yafi rashin son da baya mata ciwo "ya dauka zafi da ciwon rashin so da baya mata zai tsaya ne iya kanta kawai ashe ba iya kanta kadai zai tsaya ba har da dan cikinta “nonsense girl kawai yadda kikayi cikinki haka zaki raini abunki ki haifa I don’t care .”


Yana tsaye yana tunani mami ta turo kofar bedroom dinsa ta shigo hannunta rike da cup din shayi da d’an qaramin tray yayinda idanunta ke kansa bai san ta shigo ba sakamakon zurfin da yayi cikin tunani “ta qarasa ta ajiye tray din hannunta akan table ta sake dawowa wajensa ta tsaya tana kiran sunansa “adamcy nah ! firgigib ya dawo haiyacinsa yana sauke wani zazzafan numfashi ya tsura mata ido itama idanunta yana kanshi tana nazarinsa “lafiya tunanin me kakeyi haka ?numfashi ya sauke da karfi yana tura hannuwansa duka cikin aljihunsa sannan ya girgiza mata kai yana yamutsa fuska alamun babu komai “okay ga shayi nan na kawo maka ka dauka ka sha “ahankali yaja qafafunsa ya isa inda ta ajiye tray ya d’auki cup din ya rike yana dubanta “sweetheart ina kikaje ne tun safe banji motsinki ba kuma na kira wayoyinki duk suna shiga bakya d’auka ?”yayi maganar kwayar idanunshi na kanta “ naje hospital”da sauri ya motso kuda daita yana kallonta a d’an tsorace “lafiya ina Ke miki ciwo ?mai yasa kike je ke kad’ai baki tasheni ba ?yayi mata tmbyr ajere cike da shiga tashin hankali “lafiya ta lau adamcy naje wajen auta ne ta sauka lafiya ta samu d’a namiji “wani naunayen ajiyar zuciya ya sauke “na tsaya ne sai da’ aka gyara bby da mamansa sannna na dawo .”


Numfashi ya sauke fuskarsa yana bayyanar da wani sihirtaccen farinciki take maryam tazo ransa da sauri ya kawar daita yana cewa “masha allah auta ta zama uwa “sosai kuwa sauran kai ma ka zama uba dan nan kusa maryam zata haihu gefen bakinsa ya kamo yana cizawa ahankali ahankali batare da yace mata komai ba “Allah ya rabata da cikin lafiya !”shiru yayi yaki cewa komai ta riko hannunsa ta zaunar dashi akan gado itama ta zauna a gefensa tana dubansa kamar zatai kuka “adamcy na rokeka ka yafewa maryam wallahi rayuwarta na bani tausayi duban mami yayi yana kankance ido “wato shi ba abun tausayi bane data cucesa sai itace abar tausayi ? yayi maganar acikin ransa “ni mahaifiyarka ce ina neman alfarma ko sau d’aya ne ka yiwa maryam addaur sauka lafiya wallahi tana cikin wani hali likitoci ma sunce da kyar zata iya haihuwa da kanka runtse idanunshi yayi kawai batare da yace komai ba kusan mintuna shabiyar tana jiran yayi magana amman yaki cewa uffan “shikenan tunda baza kace komai ba ni zan koma hospital “.ta mike ta nufi kofar fita “bari nazo muje tare bata juyo ba haka zalika bata kulasa ba sakamakon nauyin da zuciyarta tayi .”


Washegari

Ahankali maryama ta tashi tana mika da salati tare da rufe bakinta sakamakon hammar data kamata kai tsare bayi ta fad’a tayi wanka ta fito tasa kaya zuwa wani had’ad’den doguwar riga blue da ratsin yellow tayi rolling kanta da qaramin mayafi yellow ta shafa powder kawai da white lips duk da ba wani kwaliya tayi ba amman she look attractive tayi kyau sosai ta feshe ilahirin jikinta da turare ta qarasa inda takalmanta suke ta sanya flat haif shoe ta fito inda ta iske umma a falo tana ajiye kular abincin akan qaramin table da alamun duk ita tayi aikin gidan dan ga koina nan fess ta qarasa inda take ta durkusa har kasa cike da girmamawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login