Showing 69001 words to 72000 words out of 182919 words
hau Kan gadonta ta kwanta “.bayn fitar umma da kusan awa uku amman maryama ta kasa bacci sai faman juyi take kwance ta mike zaune ta duba wayarta taga lokaci ya wuce sosai dan d’aya ta kusa jin idanuwanta basa jin bacci ta janyo jakar aikinta ta cigaba da aikinta ahankali ahankali ta dinga jin kamar motsin shigowar mutun tayi tsam da ranta tare da dakatar da aikin da take na wani lokaci ta kasa cigaba aikinta ta kasa kunneta sosai ko zata ji takun tafiyar mutun sai dai bataji komai ba har tsawon wasu mintuna dan haka ta maida hankalinta kan takardar gabanta ta cigaba da aikinta .sai dai haka nan ta dinga jin zuciyarta na tsinkewa tare da jin mummunar faduwar gaba .”
domin ta samarwar zuciyarta natsuwa ta ajiye takardar dake Kan pillow ta yunkura ta tashi ta sauko daga Kan gado ta soma tafiya a hankali cikin sand'a har ta fito zuwa babban falon gidan ta tsaya shiru tana kallon koina ta cikin hasken da bai gama haskaka falon ba, ta kai idanunta ga kofar shigowa taga kofar a kulle take dan haka ta sauke numfashi ta koma ta cigaba da aikinta bayan wasu lokaci ta soma jin bacci dan da kyar take iya bude idanunta tashi tayi tana hamma tare da cewa " gashi ina tsananin jin bacci gashi banga ma aikin dake gabana ba ."
ta fito zuwa falo ta nufi kitchen ta dauko dan qaramin prepand mai zurfi ta zuba ruwa kadan dan tea take bukata ta daura akan gas ta kunna ta tsaya har sai da ruwan yayi zafi ta hada tea ta zuba a cup ta fito tana sha a ahankali ..qarar faduwar abu taji ta daidai bangaren d’akin yaya sadam ta tsaya cak tason ta qara ji amman shiru .”
sai dai batayi tunanin komawa dakinta ba ta fara tafiya a hankali zata dakin inda taji motsin qarar faduwar abu har tayi taku biyu sai kafarta tayi tuntube da takalmin aunty hassna ta sauke numfashi sannan ta tsuguna ta dauka tana cewa "bansa sai yaushe aunty hasana zata daina shigowa da takalmi har parlour' ba, idan ya zama dole ai akwai takalmin yawo a parlour ba irin wannan ba da zai cire maka farce , takalmi Kmr katako gashi abun haushin ma sai tazo da takalmi amman idan ta tashi wucewa ta sai ta barshi ta kama gabanta haka .ta qarasa inda suke ajiye takalma ta ajiye nan ya kamata da irin wadan takalmar wannan abu ya dauki hankalinta yasa bata shiga dakin ba ta koma dakinta ta zauna ta tankwashe kafafaunta ta dauki takarda wayarta taji ta dauki qara ta lalubo wayar ta manna a kunnenta"okay yusura nima ina Kan aiki bazan kwanata ba sai na kammala byn ta kammala ta ajiye wayar wani kiran ya shigo taja tsaki waye kuma adaidai wannnan lokacin ? ta lalubo ta dauka tana duba number bata san number ba kamar bazata dauka amman sai tayi tunanin ko emergency call ne ta dauka tana cewa "hello !
Daga can bangaren taji ance "maryama hussein ce maaikaciyar AGC company “yes sir okay gobe muna bukatar ganinki a kamfanin da misalin karfe bakwai daidai ana gama fadar haka akayi discounting din kiran tayi shiru tana tunanin wanda ya kirata wannan dai ba muryar mr ATA bane ta lumshe idanunta tana cewa babu mamaki ko cikin yan'uwansa ne wani Ke bukatar yin aiki daita dan haka bata sake yunkurin tashi ba gara ta qarasa kafin wani aiki ya shigo mata gobe tana hamma tana aiki har ta qarasa ta kwanta da zumar tayi bacci amman ta kasa runtsawa har aka kira sallah ko byn daaka idar ma bata iya komawa ba dan haka ta yi wanka tayi shirin zuwa aiki ."Karfe bakwai daidai a AGC company tayi mata koda ta shigo ma'aikatan babu wasu mutane sai tsirarrun mutane dake kai kawo da securities da masu share maaikata ta kama hanya zuwa sama nan ma dai bbu kowa koina shiru kai tsaye office dinsu ta shiga tana sauke numfashi ta cire jakar kafadarta ta ajiye akan table ta ciro takardun zanenta tana dubawa ta sake duba agogon hannuta .”
“gsky yau nazo da wuri sosai ko da yake na huta da complain din madam some kullum sai tayi complain akaina to gashi itama bata zo ba tukun.” ta fad'a tana sauke numfashi tare da tuna yadda take mata idan tazo late "Mis maryama hussein why are you always late ?ta fada da irin muryarta ?tana lumshe idanunta tare da saka hannunta cikin aljihun doguwar rigar dake jikinta yayinda hannunta daya ke tokare da table din gabanta exactly yadda mr ata shi kuma yake yi har da qara taku biyu ta tsaya Kmr yadda yake yi .murmushi ya bayyana akan fuskarta sakamakon tuno mr ata datayi tana jin wani iri ajiknta shi kuma matsalarsa always complain “baki daukar aikinki da mahimanci a tunaninki ke din professional ce bana bukatar mutane da basa daukar aikinsu da daraja kullum bakya son zuwa aiki da wuri , kullum da excuse din da kike kawao wata rana zan dakatar dake aiki ta fada a fili .kamar ance ta juya bayanta tana juyo kawai taga mutun tsaye ya jingina jikinsa da kofar shigowa idanunsa kyam akanta sanye cikin kanana kaya irin shigar jiya sak yayi sai dai kalar kayan dabam yana rike da farin glass dinsa,yayinda hannunsa daya na soke cikin aljihun wondonsa kmr koda yaushe yayi shiru yana jifan da wani irin mayataccen kallo mai tsantsar kashe sansar jiki .”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 20
A matukar rikice ta juya tana mai had'e hannu wanta waje d'aya tana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba mai tsanani "gabad'aya yanayinsa yayi matuqar tsoratata. a bangaren mr ata kuwa wani sanyi dadi ne ya mamaye sansar jikinsa sakamakon d'aura kwayar idanunshi da yayi akan sanyi idaniyansa da sanyi safiyar nan , wani tunani maryama tayi wanda yasa ta juyo da sauri tayi taku biyu ta tsaya kusa dashi muryarta na rawa tace "good morning sir"! bai amsa mata ba ya qarasa shigowa cikin office din sosai yayi kmr yadda yake
yi a duk sanda ya shigo hannunsa d'aya cikin aljihun wondonsa yayinda d'ayan hannun kuma ya d'aura akan table . shiru tayi tana ciza harshenta kamar tayi dariya dan wannan salon nasa yana matukar burgeta kuma yana sakata jin nishad'i acikin ranta sai dai ganin yadda yayi mugun had'e rai fiyye da kullum dan fuskar nan tashi sam babu annuri kirki yasa tayi maza ta sanyawa jikinta natsuwa tare da lumshe idanunta na second biyar sannan ta bud'esu fess akan kyakkyawar fuskarsa ta sake gaishesa a karo na biyu ". “good morning sir ?!
“still shiru ne ya sake biyowa baya batare daya kalli inda take tsaye ba "maganar me kike yi ?taji saukar muryarsa ta doke dodon kunnenta,a natse ta kallesa qirjinta na dokawa da qarfin gaske tace"ba maganar komai nake yi ba "!tsumammun idanunshi ya waigo ya kalli inda take tsaye har lokacin tana wasa da yatsun hannunta ,kana kallonta kasan tayi kama da mai laifi domin ko a iya haka ma rashin gaskiyarta ta nuna ,ya motsa lip's dinsa ahankali yace "ya zakice ba maganar komai kikeyi ba byn da na shigo naji kina cewa wani abu me kikeyi cewa ?"nan take hantar cikinta ya kad'a ilahirin jikinta ya kama rawa.
sosai ta firgita "kar dai yaji abinda ta fad’a?"inna lillahi!" ta furta acikin ranta ,zuciyarta cike da matsanancin tsoro take kallonsa."ya gyara tsayuwarsa sannan ya fuskanceta tare da zura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ya tsura mata tsumammun idanunshi masu firgitarwa “maryama kince wani abu, abinda kikace nake son na sani ".
muryarta cike da in ina tace "ina..ina.. dai magana da zuciyata ne yayi shiru still kwayar idanunshi na yawo a sansar jikinta wanda ke qara saka zuciyarta shiga rud’ani bayan kamar second goma ya sake motsa lip’s dinsa " amman kamar kina raact kmr ni ?da sauri ta fito da shanyayyun idanunta waje tana cewa "no no sir me yasa zanyi haka?" ni sam ban yi haka ba kawai dai ..."sauran design's din dana baki aikinsu last week sunyi ready "?ya katseta ta hanyar fad'ar haka yana cigaba da kallonta kamar zai cinyeta, shiru tayi ta kasa cewa komai dan tuni ta ajiyesu a gefe tana kan new desing's din da zasu gabatar ne ,wani kyakkwan shu'umin kallo ya d'auketa dashi wanda yasa take tsigar jikinta d'aya bayan d'aya suka fara mikewa tayi saurin cewa "no basu yi ready ba sir "ko zan iya sani dalili ?."tayi shiru qirjinta na lugud'en bugu da qarfi .”
"wai mai yasa kika rainani har haka ?"sake fito da idanuwanta tayi sosai tana kallonsa zuciyarta na sake shiga tashin hankali "na shiga uku ta fad'a acikin ranta “wallahi ta d'auka bazai nemesu da wuri ba yasa ta tattara ta ajiyesu "yaushe zaki fara bin umarnina?" yayi mata tmbyr yana qara taku d'aya zuwa gareta "yaushe ne idan na baki aiki zakiyi min shi cikin dad'in rai batare da 'bata lokaci ko jayayya ba "?ya qarasa maganar yana sake yin taku d'aya ya matso daf da inda take sosai yana mata wani wahalallen kallo." tayi saurin ja da baya tana furta kalmar "inna lillahi !”yau na bani me ya kai ni shiga wani aikin bayan ban qarasa masa nashi ba "?lallai maryama kin tarp match dan kin fara wuce limit dinki ,amman duk abinda nake ai ina yi ne domin shi ,ina yi dan na wanke masa zuciyarsa akan kuskuren da nayi masa, ya sake matsota sosai "ina jinki ki bani amsar tmbyoyina "saboda kin rainani yasa kike aikata min haka ko?
takure jikinta tayi waje d'aya tana wata irin kyarma tace "wayyo allah tsigar jikina " gbdy ta kasa motsi duk ta rikice sakamakon kusancinsu da yayi yawa dan har suna iya jiyo bugun zukatansu da saukar numfashinsu "wannan shirun ma kanshi cikin rainin da kika min ne ko ba haka ba ?"da sauri ta girgiza masa kai "alamun a’a!”idan ba haka bane taya ina magana kina jina amman kiyi min shiru?" kayi hakuri sir sabon aikin dana nemi izininka na fara "wa ya sakaki ?"wa ya baki izini ?yayi mata tambayar ajere yana sauke mata zazzafan numfashinsa a fuskarta da wuyanta ,ta firxgo numfashi da kyar sannan ta d’ago ta kallesa zuciyarta na karkarwa “banace bana supporting ba ?"kayi hakuri kace but .."but what ?wannan karon a matukar tsorace yayi maganar wanda yasa tasa hannunwanta duka ta toshe kunnenta tana durkushewa qasa a gabansa.”
wani dogon numfashi ya sauke yana binta da kallo ganin yadda ta gigice ta rikice ta mugun bashi dariya kasa rike dariyar yayi har sai data bayyana akan fuskarsa ,inda ya kamo gefen lip’s dinsa na kasa ya fara cizawa ahankali ahankali,suna cikin wannan halin sai ga oga amar tun daga nesa ya hango bayan mr ata kuma nan take jikinsa ya bashi maryama ce durkushe a gabansa domin dai yayi imani babu wannan macen a duniya da ata zai tasata gaba irin haka ."Jin shiru yasa maryama d'ago idanunta sha'be sha'be da ruwan hawaye ta zuba masa tana “kayi hakuri nayi kuskure sir,amman zan ‘bata komai na aikin ,haka zalika zan dakatar da kowa kuma in sha allahu gobe zanzo maka da desing’s dinka .”ta qarasa maganar wasu hawaye masu zafi suna gangarowa akan kuncinta adaidai lokacin oga amar ya samu qarasowa wajen. ya tsaya yana kallonsu da bayyana nen mamaki akan fuskarsa kafin daga bisa yace "ya haka ata ?".
Mr ata ya juyo ya kallesa alokacin da oga amar ya bud’e baki zai sake cewa wani abu nan take mr ata yaja hannunsa suka fita daga office din dan yasan zai iya masa ' baran 'barama a gaban maryama shi kuma bai shiryawa hakan ba tukun, yana da plan akanta suna shiga office dinsa oga amar yace "ata ka dinga jin tsoron Allah fa “me nayi?!” dan ubanka ya kake tsoratar da yar mutane kaga yadda yarinyar nan ta fita haiyacinta tana zubar da hawaye wallahi zaka ballowa kanka ruwa ,kai yanzu soyayyar ma sai ka nuna mata seniority?"mr ata yayi bayyana nen murmushi mai d’an sauti kad'an abinda bai ta'ba yi ba kenan a tsawon rayuwarsa sannan yace "yarinyar nan wallahi bazaka ta'ba gane rashin kirkinta ba bugani take kamar ta samu kwallon kafa ga rashin bin umarnina ka shigo min da kaidodin na babu gaira babu dalili ." karya kakeyi ata " kai dai wallahi mugu ne sam maryama bata haka kawai dai kayi niyyar kasa yarinyar mutane kuka ne da sassafe "ai daman nasan haka zakace tunda kai ma sonta kake yi ."
Oga amar ya kyalkyace da wata dariya yana kaiwa kafad'ansa duka "gsky ata ka gama dani amman kasani da son maryama nake da tuni an wuce gurin da sai dai ka bud'e idanunka ka ganta a gidana a matsayin matata "da kuwa anyi burouba!"ya fad'a yana zabga masa wata qatuwsr harara "sorry friend maryama taka ce kai kad’ai daman kace babu macen da zaka bi sai ita kuma naga hk sauran ka zama bita zai zai ko da yake shima ka fara zama " anji cewar oga amar "ai soyayyar yarinyar nan tana wujijjjiga rayuwata ,ni yanzu kiran da nai maka nace mu hadu anan shawara zamuyi ina son naje nema aurenta "
“waya fada maka barno gabas take ,suka kwashe da dariya "suka samu waje suka zauna alokacin da karfe takwas ta buga wanda zuwa wannan lokacin wasu daga cikin maaikata sun fara zuwa "ina jinka abokina wannan labari yafi kowani irin labari dadi domin ina matukar son na g maryama a qarqashinka ."
Mr ata ya numfasa kana ya cigaba da magana a natse "ina son naje neman aurenta koma nace ina son tazama mallakina acikin tsukukun lokacin nan dan sai nafi samun kwanciyar hankali idan na aureta ahankali kuma sai na shigar da soyayyata sai dai kasan wani abu bana son sweetheart da kowa nawa su san da wannna auren zai tsaya ne a tsakaninmu dagani sai kai ita kanta yarinyar bana son tasani yanzu “ya qarasa maganar tare da yin shiru ya zuba ma oga amar idanu yana son yaki me zai ce "Ko me yasa ka zabi kayi haka ?bayyana maryama a halin yanzu zai iya janyo min abubuwa da yawa. abu na farko idan sweetheart da sauran yan’uwana suka san mafarkina ce zata fuskanci mummunar tsana daga garesu kasamcewar naki zama da zabinsu abinda ka rigada kasani ne bazan d'auki raini ga matar danafi so ba haka zalika bazan wulakanta yanuwana da Mahaifiyata akanta ba,shiyasa nake son na aureta a boye ,muyi rayuwarmu dagani sai ita da yaran da zata haifa min ".
numfashi oga amar ya sauke "amman kace itama maryama din baka son tasani ?"a yanzu ba amman daga baya ai dole zata sani idan lokacin da ya kamata tasani yayi, zan aureta a yanzu na dinga janta ajikina ina d’an rage zafi "tunda ita shasha ce da zata yarda ka dinga ta'bata batare data san meye matsayinta ba "wannan kuma matsalarta ce tunda ni nasan matsayinta ai shikenan."kai dai wallahi mugun jarababbabe ne “sosai kuwa number one ma ni kad'ai nasan irin dauriyar da nake akanta wallahi amar ina da mugun karfin shaawa akanta idan shaawarta ta taso mun kwana nake gabana a mike duk na rasa yadda zanyi ,inga ya maka jijiya ta bata kwanciya har sai asuba tayi wata rana ma haka zan yini kaga gara nasan abunyi.” naunayen ajiyar zuciya oga amar ya sauke yana cewa "ni dai gsky kayi tunani sosai akan wannan raayi naka gara ka fahimtar daita idan yaso sai abar maganar daga kai sai ita sai kuma ni da zan zamo sheida saboda halin rayuwa ".
“kai ma kazo da magana mai kyau amman kasan wani abu ?oga amar ya girgiza masa kai "bazan iya fahimtar daita da bakina ba "akan wani dalili ?i don’t know,kai dai kace tsoronta kake ji “wani irin tsoro kuma amar yarinyar da loma d'aya zanyi daita na gama daita ni kawai damuwar sweetheart ne data yanuwana ce banaso, sun dade suna tautaunawa a qarshe suka ajiye ranar da zasuje su samu baba gali ."qarfe goma daidai oga amar yayi masa sallama ya wuce yayinda maryama ke ta faman kuka surayya wacce ta shigo ta isketa tana kuka ta fara rallashi tana tambayarta dalilin kuka sai dai bata ce mata kalallahu ba dan haka taje ta kira yusura itama dai tmbyrta dalilin kukanta tayi a qarshe tace "ko dai mr ata ne ?"maryama ta gyada mata kai alamun eh me ya had’aki dashi ?tayi shiru dan bazata iya fad'a ba ,da kyar yusura ta rarrasheta ta tsaida sheshekar kukanta tana cigaba da tmbyeta "aikin banza kawai kuna damun kanku akan wannan figaggar yarinyar kuma tunda kukaga tayi shiru har yanzu taki cewa da ku komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki irin nata ai sai ku rabu daita haka ".sultana dake tsaye a bakin kofa ta fadi haka tana mazurai yusura kam ta yarda maryama tana da zurfin ciki sosai "ban wani d'auki lokaci mai tsawo daita ba amman na karanci maryama din nan tana kafiya da zurfin ciki maryama ta kalleta da idanunta da suka canza kala "kina kallona kamar karya na fad'a akanki “tana gama fadar haka maryama ta d'auki jakar aikinta ta rataya a kafad’anta ta fita ta bar office din