Showing 75001 words to 78000 words out of 182919 words
cewa “kai maryama ya kika firgita haka da sauri ?dole na firgita umma dan dai baki san shi bane halinsa fa yafi wanda na fad’a miki muni wallahi kullum ina tausayawa matar dake aurensa dan nasan ba qaramin hakuri take dashi ba “ai irinsu kuma a wajen mata sauki kai garesu”umma ba dai wannan mutumin ba ,karfa wata rana soyayya tasa kizo kina yabonsa”kai umma kin dai kasa fahimtar irinsu mr ata bama zai ta’ba cewa yana son irina ba wacece ni tukun ma ?” ko girman kanshi bazai bari ba bare ma ni yanzu babu wani budget din aure a gabana so nake na d’an tara albashina na wata shida na siya mana wani qaramin gida mu tattara mu bar gidan nan mu canza emvaroment”.
“Umma ta sakar mata murmushi Allah ya gani tana matukar qaunar maryama kuma taso hada zuri'a da wanna natsattsen yarinya kamarta mai kyakkyawar zuciyata da natsuwa tare da sanin ya kamata amma Allah bai nufa ba, ina ma ace tana da wani d’an bayan sadam , tabbas data sake nema masa aurenta amman haka Allah ya qaddara mata haihuwa d’aya zatayi arayuwarta ,amma ba komi zata cigaba da mata addu'a Allah ya bata miji na gari wanda yafi sadam komai .”sun dade suna tautaunawa har
Qarfe goma da minti goma sha biyu maryama ta mike tsaye tare da cewa “umma bari ma shiga ciki zan d’an yi aiki kafin na kwanta sai da safe “acikin duhun nan zaki yi aiki ?”to ya zanyi umma tunda sunki kawo wutar nan ? nafi tunanin wutar lalacewa tayi dan yinin yau basu kawota ba “inji cewar umma maryama tace “ai yan nepa na abinda ransu yake so Allah dai ya kyauta bari naje dan muddin ina son zaman lafiya da mutumin nan na qarasa masa aikinsa kawai na bashi “to shikenan Allah ya tashemu lafiya maryama ta nufi d’akinta itama umma batá dade ba ta mike ta shige ciki “.
Bangaren mr ata ruwan tea kawai ya sha ya shige bedroom dinsa inda ya soma ya cigaba da neman layin maryama sai dai har wannan lokacin kiran baya shiga hakan nan yaji damuwarsa ta ninku daren ranar haka ya zauna yana tunaninta duk juyin da zai yi tana makale da zuciyarsa da jikinsa sosai yake tsananin buqatar aurenta,domin a yanzu a matse yake tamkar yaci babu “yanzu kai adam kana ganin hanyar daka bullo daita mai bullewa ce agareka kayi aure a boye batare dasanin danginka ba ?ya kamata dai kayi nazari sosai kafin ka aikata haka .”yayi wani juyi ya sake kamkame pillow a qirjinsa yana jin tamkar maryama ce ajikinsa har wani shafa jikin pillow yake yana sake zurfafa tunaninsa .”sannu ahankali bacci yayi awon gaba dashi “yayinda maryama ta baje takardu masu yawa a tsakiyar gadonta ta soma aikinsa daya bata kusan awa biyu ta d’auka tana aiki kafin ahankali ta lalubo wayarta ta kunna tana gama kunnawa kira ya shigo tai shiru tana duba fuskar wayar gabanta na fad’uwa cike da karfin zuciyata ta d’aga tasa wayar a handsfree “kamar dai daren jiya akace “ko ina magana da maryama hussein ne ?”yes itace !”ta fad’a tana kai pencil din hannunta baki tana taunawa .”
“Okay daga kamfanin AGC ne jiya mun kiraki akan kizo da wuri kasancewar akwai aikin da zamu baki inda aka samu matsala jiya ban samu damar zuwa aiki ba sakamakon wani uzuri daya taso min amman in sha Allahu gobe kizo da wuri zan zo na sameki da kaina muyi magana .”wani naunauyen ajiyar zuciya ta sauke sai yanzu ta tuna da jiya an kirata shine ma dalilin zuwanta aiki da wuri da har mr ata ya samu damarta kuma sai yanzu ta fahimci mai kiran kamar muryar sultan ne “kafin tace wani abu dif idon taga ya d’auke”hello mr sultan ne ?hello !”jin shiru yasa ta danna gefen wayar ashe babu caji ne yasa ta mutu gbdy dogon tsaki taja tana dungurar daita akan katifar da take daman nasan haka zata iya faruwa shiysa naki hawa online tun dazu saboda rashin wutan nan da suke fama dashi a unguwarsu tayi yawa .”ahankali ta cigaba da aikinta
Qarfe biyu saura ta kammala komai ta tattara aikin ta zuba acikin jakar aikinta tayi addua ta shafa a gabad’aya ilahirin jikinta ta kwanta kasancewar akwai bacci a idanunta nan take bacci yayi awon gaba daita .”sadaf sadaf ya shigo ta kofar baya d’akin maryama ya fara lekawa ya ganta kwance ta kamkame jikinta waje d’aya tana bacci ahankali ya janyo kofar ya rufe ya nufi d’akin ummanshi ya tura kofar ahankali ya rabe daga wajen d’akinta,kai tsaye hannunsa ya kai inda makunnin wutan d’akinta yake ya kunna bayan haske ya gama haskaka d’akin ya turo kanshi kad’an ya leka tana kwance tana bacci abunta hannunwanta rungume da fream wanda ko bai duba ba yasan hotonsa ne .”gefenta kuma tulin uniform dinsa ne tun daga kan primary har zuwa secondary har ma dana islamiyyar sa .”wani irin bugawa zuciyarsa tayi da mugun qarfi ya soma d’aga qafafuwansa ya shigo d’akin cikin sand’a ya qara taku biyu ya iso zuwa inda take kwance ya tsaya akanta yana kallonta ya sani bai kyauta mata ba hakika mahaifiyarsa bata cancaci haka daga garesa ba ,yayi mata butulci yayi mata muguwar sakayya da wani ido zai kalleta dashi aranar da zai bayyana mata kanshi.”?
zazzafan numfashi ya sauke ya soma tafiya cikin sand’a ya isa durowarta inda yafi tunanin anan zai ga sauran documents din da yake nema dan jiya dayazo ya duba koina a d’akinsa bai gani ba wanda nadia ta kawo masa ba iyasu kawai yake bukata ba akwai wasu masu mahimanci.kafin ya kai hannu ya bud’e sai daya waiga ya sake kallonta tana sauke numfashi ahankali tana sake kwakume hotonsa ajikinsa nan take idanunshi ya ciko da ruwan hawaye cike da qaunar mahaifiyarsa ya d’auke idanunshi akanta ya maida kan durowar ya bud’e ya soma duba abinda ya kawo shi hawaye nabin kuncinsa ‘hawaye ne kawai yake zuba daga cikin idanunshi alokacin da yake tunanin irin qauna da soyayyarta da ummansa ta nuna masa tun yana qaraminsa har zuwa girmansa da irin rayuwar da sukai idan taci yaci zata iya hakura da komai akanshi duk son da take ma abu muddin bai so to itama in sha allahu yafi ranta kallonta ya sake yi ita kadai ce fa ta rage masa a nan gidan duniya gashi ya barta akan wani dalili mara tushe .”
bai wani ‘bata lokaci ba ya ga document din daya kawoshi ya d’auka tare da maida durowar ya rufe ahankali ya dawo gabanta ya tsugunna yana furta “umma nah ina tsananin sonki ,daidai da minti d’aya tunaninki da soyayyarki basu ta’ba barin zuciyata ta huta ba ki ya fé min umma nah Kiyi hakuri umma nah..”ya fad’a yana shafa gefen fuskarta inda ta motsa yayi saurin cire hannunsa ya mike da sauri ya fice yana fita ta bud’e idanunta ta kira sunansa da karfi “sadam ..” gabanta na wani irin fad’uwa .”d’akin ta dinga bi da kallo kafin ahankali tace “ashe mafarki ne”. ta furta tana kallon fuskar fream din hannunta tana shafawa Allah ya jikanka sadam ,allah yasa ruhinka yana aljanna ina tsananin sonka dana amman Allah daya bani kai ya fini bukatarka tana gama fadar haka ta fashe da wani rikitaccen kuka hade kamkame hotonsa tun sanda umma ta farka da sunan sadam abakinta maryama tayi zumbur ta farka daga baccinta.”
da sauri ta shiga kokuwar saukowa daga kan gado ta fito ta banko d’akin umma in da ta iske umma zaune kwakume da hoton sadam tana kuka tana zuba sambatun “ya Allah bana bakinciki da wannan rayuwa, bana bakinciki da hukuncinKa Allah .”
Allah kabani ikon cinye jarabawar wannnan da sauri jikin maryama na kyrma ta zauna kusa daita hawaye na zuba a idanunta ,maryama kuka ummah kuka umma ta kamo hannunta ta damke cikin nata tace “maryama mafarkin sadam nayi maryama ina matuqar qaunar sadam amamn ma rasahi “umma ki daina kuka ki dinga tuna cewar kina dani wallahi zan zame miki tamakar yaya sadam bazan ta’ba juya miki baya ba, nasani maryama “Allah yayi miki albarka a rayuwarki Allah ya baki miji na gari “amen ummah ki bar kukan haka banason kina daga hankalinki in sha allahu sai kinyi alfahari dani bazan tabayi nisa dake ba zan kasance tare dake dan Allah ki daina damuwa kinji, Allah yayi miki albarka data yayan da zaki haifa in sha allahu bazaki dangwama a haka ba ,Allah zai saukaka .”
“Allah zai hadaki da miji na gari mijin da zai rikeki amana mijin da zai qaunace da dukkanin rayuwarsa
ta qarasa maganar tana zubar da hawaye baccin da umma da maryma basu koma ba kenan umma ta mike ta ajiye fream din hannunta a inda yake akan durowarta sannan ta soma tattara uniform din sadam tana hawaye maryama tayi sauri ta kar’ba a hannunta ta maidasu inda suke sannan tace “umma kije kiyi alwala kizo Kiyi sallah in sha allahu zuciyarki zatayi sanyi kai kawai umma ta iya gyda mata sannna ta shige bayi ta dauro alwala koda ta fito ta iske maryama ta shimfida sallaya tazo ta shiga gabatar da nafilflii inda maryama ta fito ta shiga kitchen ta daura mata ruwan zafi shiru tayi tsaye rungume da hannunwanta a qirji kwakwaluwarta na tunani mai zurfi “ita fa data shiga d’akin umma taji kamshin turaren yaya sadam daman idan akayi mafarki da mutun har kamshin mutun zaa iya ji ?”
Sosai kwakwaluwarta ta shiga cajin tunanin jiki a sanyaye ta had’awa umma tea ta kai mata alokacin ummah ta sallame tana zaune tana nemawa d’anta rahma a wajen allah ”
“Umma ga tea ki sha “sannu maryama na gode Kwarai Allah ya shiga cikin lamarinki “Ameen ummah ,cike da tsinkewar zuciya umma ta kar’bi cup din bakinta maryama ta dawo gabanta tana mammatsa mata qafa umma tayi murmushi “kije ki kwanta kinji maryama .ta girgiza mata kai alamun “a’a ni dai dan allah umma ki kwantar da hankalinki kice fa kike bani kwarin gwiwa idan ina ganinki haka walalhi nima zaki rasani da sauri umma ta girgiza mata kai “allah bazai sa naga mugun abu ba in sha allahu sai naga aurenki da ya’yanki sai nã goya ya’yanki da wannnan bayan nawa maryama tai murmushi kawai tana mai sake jin qaunar umm aranta wanda ta dade dasanin qaunarsu daga Allah ne “jin an fara kiran sallah farko yasa maryama mikewa tace “umma bari nasoma aikina dan yau ma ina ganin da wuri zan fita to shikenan Allah ya taimaka ta fice tana janyo mata kofa .”
********
washegari mr ata yana idar da sallah asuba gym ya shiga domin motsa jiki dan ya kwana biyu bai motsa jikinsa ba ya d’auki tsawon awa uku zuwa hudu masu kyau yana motsa jikinsa inda ya had’a gumi ya ajiye qarfen da d’aukarsa ke murd’ewa duk wani mai yin gym jiki ,ya dauki towel yana goge fuskarsa tare da fitowa ya hau samansa kai tsaye bathroom ya shige yayi wanka ya fito ya soma shirin zuwa office .”
Qarfe bakwai da wasu mintuna maryama ta shigo AGC inda ta iske madam some ita kad’ai tsaye acikin office dinsu sai sai dai akwia wasu tairarrun ma’aikatan data gani a kasa amman a office dinsu daga ita sai madam some ne “good morning ma ?”morning maryama “jiya kuma sai muka nemeki muka rasa tsuke bakinta tayi tana cewa “wani uzuri ne ya taso daga gida hope dai lafiya ?” lafiya !”ta fad’a atakaice tana jona wayarta caji .”
maryama bata jima da shigowa ba shima mr ata ya shigo cikin takun nan nasa na isa inda madam some da dan hanzarinta ta gaishesa amman ban da maryama tayi kamar bata ganshi ba sai dai aranta tace “meke faruwa yau ma kamar jiya mr ATA da wuri yazo shima.” ya zuba mata tsumammun idanunshi yaga yadda ta bala’i hade fuska gabansa yayi mummunar fad’uwa cikin wani irin yanayi yake Kureta da kallon shi Kafin yaja ajiyar zuciya ya karaso gefenta “kaga mata masu mulki,da alamun har yanzu zuciyarta akwia haushin jiya ?ya fada a ranshi jin yadda idanunsa ke yawo akan at the same time yana magana da some yasa cikin yin kasa da murya tace “good morning sir “juyawa yayi ya nufi office dinsa bayan yaji gaisuwarta amamn dan tsabar wulakanci ya shareta inda Allah ya taimaketa madam some ce tasan da sultana nan da ta mata dariya wannan abu yayi matukar yi mata zafi zuciyarta ta dinga bugawa da sauri sauri .”tana kallon madan some ta bishi abaya daga inda take zaune ta janyo wayarta ta kunna ta soma neman layin jiya da’aka kirata dashi sai kira uku tayi baa d’aga burinta a d’aga idan sultan ne Ke bukatarta aiki wallahi zatayi aiki dashi ta huta da bala’i wannna mutunmi.”
qarfe tara daidai some tazo ta tsaya akanta “maryama kije mr ata yana son ganinki sai da gabanta ya dan fad’i kad’an dan tasan kiransa ba alkhairi bane ba ,amman bata da yadda zatayi dole ta mike ta nufi office din ta tsaya abakin kofa tayi knowking “may I coming sir ?yayi shiru itama shiru tayi tsaye tana jiran izininsa yayinda zuciyarta ke dokowa gashi tana hangosa zaune daga cikin amman yaki cewa komai sai tayi kamar ta bude kofar ta shiga sai ta fasa tasan yayi haka ne dan ya samu hanyar da zai kamata da laifi tana tsaye qirjinta nata faman Lugudan bugu dum!dum!”sake knowking tayi da neman izinin a karo na biyu still shiru yayi mata lokacin ma ya soma waya taji zuciyarta ba zata jure ba sai kawai ta bude Kofar ta shiga ta qarasa gabansa ta tsaya still juyi ya cigaba da yi yana waya har kusan mintuna talatin bai kalleta ba ,ta duba agaogon hannunta taga ta bata lokaci a tsaye kawai ta juya tana Kokarin saka kafafunta dan fita daga cikin office din taji sassanyar muryarshi mai tsananin kashe sansar jiki “ke dawo nan "tayi shiru tsaye tana jin zafin abinda yayi mata a yanzu, tasan da mutane sunzo da yanzu hankalinsu da idanusu yana kansu, most especially sultana da bata da buri da wuce taga ya wulakantata sai data rarrashi kanta sannna ta dawo ta tsaya agabansa ta sunkuyar da fuskarta kasa dan wani irin take ji a gabad’aya ilahirin jikinta “.
“Maryama ." ya kira sunanta cikin wani salo mai kashe sansar jiki dagowa tayi ahankali tana kallonshi da shayayyun idanunta masu narkar masa da zuciya sai dai kallo daya tayi masa tavi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta dan bata iya jurar irin kallon da yake mata dan kallo yake mata mai dauke da ma'anoni iri iri daga inda yake zaune yake jin kamar ya mike yaje ya d’ago fuskarta damuwar fuskarta ta damesa matukar baya son ganin fuskarta hk “maryama “!ya sake kiran sunanta a karo na biyu ta dago ta zuba masa shayyyun idanunta tana shirin sake sunkuyar da kanta kasa yace “karki kuskura ki tsaya a yadda kike koni sirinki ne ?”numfashi kawai ta sauke ta cigaba da tsayuwa a yadda yake bukata “to yau kuma me yake nufi daita ?da wani sabon iskanci yazo mata dashi ?”tayiwa kanta tambayar ajire tana sake tsuke fuska “shi daya zo da zumar zuba mata ruwan bala’i amman ya kasa sai ma ya qare a tsura mata kwayar idanunshi masu sata shiga taitayinta ,duk sanda zai daura mata su a jikinta wani irin sanadari ne akwai cikin idanun TARIQ ADAM ABDULLAH masu hargitsa lissafin dan adam kallo daya zai yi maka ka dabarbarce sai kayi da gaske kake samu ka maido natsuwarka so take ta maida kanta kasa dan zai fiyye mata zaman lafiya amman yaki bata damar sai ma hannunsa d’aya ya kai ya dafe gefen fuskarsa yana taune lip’s dinta still kuma kwayar idanunshi na kanta.”
Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 22
Mr ata ya tasa maryama gaba da kallo tamkar wani tsohon maye ido cikin ido yake kallonta dan sosai ya sanya kwayar idanunshi cikin nata ai ko tana lumshe idonta sai hawaye sharrr ..”suka shiga gangarowa akan kuncinta,bai san sanda ya mike tsaye ba ya soma taku ahankali har ya qarasa inda take tsaye Ya tsaya yana qoqarin kamo laulausar tafin hannunta cikin nashi tayi saurin zame hannunta cike da jin haushinsa amamn sai da yayi nasara riko yatsun hannunta yana murzawa a hankali tare da hura mata iskan bakinshi a saman fuskarta.”
sun kai minti goma a haka tana hawaye shi bai rarrashinta ba ,shi bai sakar mata hannu ba har sai data gaji dan kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya a jere murmushi yayi aciki yana cewa “kin d’auaka d’an wannnan hawayen zai sa na tausaya miki ,”?” “yarinya baki san adadin hawayen dana zubar akanki ba ,baki san kalar wahalar dana sha akan zafin soayyarki ba ,baki san tashin hankalin da dana shiga akanki ba, nayi kuka nayi hauka duk akanki a qarshe har aka so a d’aukeni mahaukaci alokacin da nake jin cewar kina cikin duniyar nan amamn aka nuna min ke din iya mafarki ce ,wannan wahalar kad’an ce