Showing 57001 words to 60000 words out of 182919 words

Chapter 20 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

389

!.



shiru taji bai amsa ba ,dan a can  bangarensa bai san kiran ya shiga har ta d'aga  ba yana can yana  tunaninsa sai jin sautin muryarta yaji "assalamu alaikum .""hello ta sake maimaitawa duk da yana jinta amman yayi mata  shiru yaki yin magan yana shan kamshi kamar tana gabansa .  ji tayi  kamar ta saki fitsari ajikinta tsabar yadda gabanta yake dukan tara tara ."jin shirun yana son yayi yawa ta sake motsa labbanta cike da girmamawa tace "good morning sir" morning !ya fad'a atakaice yana ciccin magani sannan ya juya ya cigaba da tafiya acikin d'akin batare da ya sake cewa  komai ba." itama shiru tayi .”har kusan second talatin bai ce komai ba ga mutane sai faman wuceta suke suna kallonta dan Allah yayi mata baiwar kyau mai d’aukar hankali da tafiyar da ruhi ,dole ne idan ka kalleta ka sake kallonta sannan ka yaba da irin zallar kyawun da Allah tabaraka wata ala yayi mata .”



ta sauke naunayen ajiyar tana sake duba screen din wayar ta gani ko kiran ya katse ne yasa taji shiru gani tayi still yana kan layi can dai tace "sir ko akwai abinda zakace ne ?"no...sai kuma yace "yes !"what !?
“what do you want to say sir ?ta furta a dan kid'ime shiru yayi yana sauke mata numfashinsa a kunne wanda hakan ke sake haddasawa zuciyarta mummu nar kidima da shiga tashin hankali muryata a matuqar raunane ta sake tambayarsa ” me kake son kace sir ? "abinda zance kizo office akan lokaci "okay  sir ..!kafin tace wani abu ya katse kiran murna da farinciki suka taru suka  lullu’beta ,kafin ahankali tayi shiru tsaye  tana nazarinsa " ko me yake son fad'a mata? kamar ba wannan maganar yaso fad'a mata ba" kai koma dai  menene  matsalarsa ce wannan tunda har ya furta tazo tana  da hujja kare  kanta idan zai tozartata  .""wayyo allah dadi "ta furta a fili cikin tsananin farinciki bai ma san na kusan shiga office ba, allah na gode maka da kasa ya furta nazo  da bakinsa .”



Cike da kuzari ta soma tafiya cike ta shiga office dinsu lokacin kowa ya hallarar "sautin muryarta suka jiyo daga sama "good morning !good morning!!ta furta gbdy suka mike sakamakon ganinta sectary tace "me yasa shekaranjiya da jiya baki zo aiki ba ?”gsky baki kyautawa mr ATA ba kin kunyata shi tunda nake aiki dashi ban ta'ba ganin abokan kasuwamcinsa sun masa haka ba yusura  da surayya duk suka matsota suma dai tmbyarta dalilin rashin zuwa kwana biyu  suke "nima ba haka naso ba  na .."
“ba haka kika só din  wa ba ?”daman dayawa ya'yan talakawa basu iya samun guri ba sannan basu iya d'aukar aikinsu da mahimmanci ba "inji cewar sultana dake zaune tana watsawa maryama wani mugun kallo ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan tace "haba sultana gsky banji dadin kalmarki ba rayuwar nan fa da mai arziki da talaka duk daya né a wurin allah babu bambamci sai wanda yafi wani jin tsoron allah ."



Maryama tana cikin wannan bayanin mr ata ya taho a hankali hannunsa daya cikin aljihun wondonsa tun kafin ya qaraso kamshin daddaren  turarensa ya kawo masu ziyara, bai tsaya a koina ba sai a bayan maryama  yana kallonta” tayi kmr zata juyo ya bar gurin kad'an still dai yana bayanta kuma idanunshi na kanta numfashinta kawai take janyowa da kyar tana fesarwa dan gbdy acikinsu babu wanda bai firgita da ganinsa ba kafin a hankali suka shiga gaishesa daya byn daya da girmamawa ."itama maryama ta bude baki da kyar ta gaishesa  dan zuwa alokacin ya dawo gabanta  ya tsaya kyam  yana kallonta sai dai bai amsa gaisuwarta ba illa tsura mata tsumammun idanunshi da yayi ta cikin medical glas  dinsa yana kallonta itama shi din take kallo sai dai ita a dan rikice take ."



“sosai ya tsareta da idanunshi duk tayi masa laifi mai girma amman  kallonta a yanzu ya d’an rage masa kashi hamsin na cikin damuwar data haifar masa sakamakon wani zazzafan kyau datai masa domin sosai kayan dake sanye a  jikinta suka mata masifar kyau gashi dai bata  bayyanar da surarta afili, amman kowani kaya ta saka sai ya zauna ajikinta kuma suyi mata kyau “princess kinyi masifar kyau yau..."ya furta a can qasan ranshi  yayinda ita kuwa tashiga tsananin damuwa dan a zahiri yake iya kallon yadda take hadiyar zuciya
irin kallon da yake mata yasa numfashinta ya soma qoqari d'aukewa "sir ..!tana furta hakan ya juya ya wuceta da sauri ya shige office dinsa .”aiko nan take wani sabon fargaba da tsorone sukayima maryama  dirar mikiya, jitake kamar tasaki fitsari mai wasali a wando tsabar yanda gabanta yake bugawa .”




Yayinda duka wata gaba da Allah subhanahu wata'ala ya halitta ajikinta rawa takeyi,kallo daya zaka mata kagane hankalinta amatukar tashe yaje . qafafuwanta  dake karkarwa ta shiga motsawa ta juya da zumar   zata bi bayansa gbdy sukayo kanta har sectary "karki kuskura ki shiga office dinsa yanzu “ki barshi zuwa wani lokacin sai ki gansa "cikin tsananin tashin hankali tace "karku  damu  ku barni  na gansa yanzu domin  a yanzu ya kamata naje na nemi yafiyarsa ba sai an dauki lokaci ba , idan naki zuwa yanzu  zai dauka cewar da gangan nayi , ko ya d'auka girman kai zan masa ,ku dai kuyi min addaur da fatan nasara tana gama fad’ar haka ta wuce su "uhmm ba dai ya Adam ba sai kin gwamace baki je ba sultana ta fad'a a kasan ranta tana  murmushin mugunta sannan  ta gyara zamanta zuwa kallon office din mr ata tana jiran taga irin korar wulakancin da zai mata."




Ahankali maryama tayi knowking tare da cewa" ko zan iya shigowa sir "abun mamaki sai ji tayi yace "comming "! zazzafan numfashi da ajiyar zuciya ta sauke tana mai  tura kofar glass din ta shiga idanunta kyam  akanshi  tare da maida kofar ta rufe ahankali batare data juya ba, yana tsaye yana waya  ahankali cikin yin kasa da murya  "okay kuna bukatar qarafe kimanin adadi nawa ?okay okay !!
"shikenan zan hadaka da ahmed zan tura masa komai yanzu zai nemeka amman fa bazan qarfi wannan farashin ba zaa sauke komai akan tsare no gsky bazan bada a wannan farshin ba gbdy mun qara  farashin komai namu saboda ingancin abubuwan da muke amfani dasu dan haka ka tura kudi sai tura maka kaya."


Cike da sanyi muryar maryama  ta bude baki "sir ! ya dakatar daita da yatsan hannunsa yana cigaba da magana "ka tsaya ka fahimceni wannan matsalar ba daga gareni bane ,Okay idan yayi maka shin kenan sai najika idan kuma bai maka  ba babu matsala ma hadu zuwa gaba".shayayyun idanunta ta tsura masa tana kallon yadda yake magana a natse cikin harshen tsadadden turancinsa bakinsa ma da kyar yake motsawa har sanda  ya ajiya wayar office yana kallonta tare da qara  girman idanunshi akanta tunda daga kasanta  ya dauki kallonta har zuwa samanta yadda bai ce mata komai ba  haka itama bata ce masa ba saboda gudun wulakancinsa.”



ta lumshe idanunta ta sake rungume littafin dake hannunta "dan kawai ki tsareni da wadan nan idanuwan naki kika shigo min office? "no sir ammm actually actually ..!!sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da magana  "actually what ?"ya tambyeta yana sake tsareta da tsumammun idanunshi ."idan baki da abun cewa kina iya wucewa  ki bar min office dina "no sir  ina dashi daman nazo maka design din shejaranjiya ne  na qarasa shi ajiya gashi nazo dashi ta ajiye agabansa ."tana mai sunkuyar da kanta kasa tare da jin wani sabon fad'uwar gaba mai tsanani ."
"this is totally nonsense maryama  “me zanyi dashi?ya tamvayeta cikin zafin zuciya yana tsareta da kwayar idanunshi .”



ahankali ta dago kanta ta zuba masa idanunta " ki dauke min wannan shirmen daga gabana dan basu da wani amfani a wajena yanzu dan takalmin kafarki ma  ya fishi daraja a wajena  dan hk ki daukeshi banason ganinsa .”tana kallonsa jikinta na rawa dan azahiri ake iya ganin yadda  jikinta  yake rawa  Matsowa tayi kusa dashi kad'an still tana kallonsa tana jin kamar ta kamo  hannuwansa gabadaya cikin nata ta rike ta rarrashesa dan tabbas ta aikata masa ba daidai ba.” manzon Allah sallallahu alaihi wasalam yace “idan aka ‘bata maka ka nuna fushinka dan kai ba jaki bane ." haka zalika idan aka baka hakuri ka hakura dan kai ba sheidan bane sai dai tasan duk abinda zatayi a yanzu bazai sauko ya karbi aikin ba sakamakon mugun taurin kan dake garesa uwa uba zuciya " kin wani  tsaya kina kallona ?”
ta marairaice masa fuska kamar zatai kuka .”



"maryama leave my office right now I don’t want to see your face ." ya fad'a yana nuna mata kofar fita ."
"Dan girman  Allah sir ka sake bani wata dama .”
"babu wata dama da zaa baki domin ke kullum cikin matsala kike sannan  rayuwarki kullum acikin second chance take ko wace dama zaa baki sai wannan mataccen yasa kinyi loose "ya fad'a yana jan tsaki tai shiru tana nazarinsa da mamakinsa ta rasa dalilinsa na daukar zafi har haka akan mijinta "bata gama tunaninta ba ta sake jiyo muryarsa "there's no second chance maryama go back to your  work ."
"am  so sorry sir ..."I said go back to your  work ya fad'a a tsawace "go! ya sake furtawa yana nuna mata kofa da bakinsa jikinta a sanyaye ta kallesa sai dai hankalinta a tashe yake, ta juya da sauri tun kafin ya rufeta da duka dan taga alamun zai iya aikatawa yabi bayanta da kallo kafin a hankali ya zauna akan kujera ya sauke numfashi ya dauki wayarsa dake ringing "yes sweetheart daga can bangaren tace "fatan ka isa office lafiya ?lafiya sweetheart “yarinyar tazo office ne ."?



"yes sweetheart !" fatan kayi abinda nace kayi "? ya juya ya kalli kofar da maryama ta fita  yanzu "ai nasan bazakayi ba ,wacece ni da zance kayi abu kayi min alokacin da nace ? tana gama  fadar hk ta katse yayi shiru kawai yana tuna maganar daya gama fada mata tanzu  "I said go back to your  work yana cikin wannan halin ya sake jiyo  muryarta tana neman izinin , itama  kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali tayi koda ta koma office dinsu bata iya aikata komai ba ,zuciyarta ce  ta dinga azalzatar ta dawo garesa ko zai kasheta gara ya kasheta ta huta."
ya tsura mata ido kawai ganin irin kallon da yake mata ya sake kidima ta tana qoqarin sake juyawa ta fice idanunta suka sauka akan takardar zanen data ajiye masa da hannu ta nuna masa saman table dinsa "sir na manta file dina .”


ya nuna mata da hannunsa alamun ta d’auka tasa hannu ta d’auka "madadin ta wuce sai tayi tunanin ta sake bashi hakuri "kayiwa girman allah da girman iyayenka kayi hakuri akan laifina bazan sake aikata wannan Kuskuren ba idan nayi ka d’auki kowani irin hukunci akaina “ ta qarasa maganar cike da raunin zuciya   wanda adaidai lokacin ya juyar da kanshi gefe ganin hk yasa  itama ta juya cikin sanyin jiki ."
Har  tayi taku biyu  taji sautin muryarsa ta doki dodon kunnenta "am sorry  too for yesterday ."da wani irin mugun sauri ta juyo ta tsura masa ido.”



Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 17


Tunda mr ata ya furta mata kalmar “am sorry too for yesterday bai sake juyowa ya kalleta ba illa zuciyarsa dake mugun bugawa da sauri sauri, kallonsa take tana mamaki me zai faru ?wannan wani sabo alamari ne ?mr ATA da kanshi ya furta hakuri gareta .?”anya kuwa abinda kunnuwanta suka jiyo mata kenan ?”shine mana to idan shine anya kuwa wannan kalmar daga bakinsa ta fito ?”ta yiwa kanta tambayar ajere tana jifansa da wani sanyayyen kallo zuciyarta na bugun tara tara.kusan suman tsaye maryama tayi a wajen dan tsananin farincikin data tsinci kanta ciki .”ta kasa d’auke kwayar idanunta akanshi ta cigaba da kallonsa rungume da file aqirjinsa”office din yayi shiru tamkar babu wata halitta tsaye agabansa wanda hakan yasa zuciyarta ta fara wasi wasi “kai bana tunanin shi yayi wannan maganar. wannan maganar ba daga bakinsa ta fito ba “.



shi kuwa tunda ya furta maganar ya kasa kwakwaran motsi tamkar wanda aka dasashi zaune kunya da tsananin fargaba tasa shi ya kasa juyowa ya kalleta duk da ta gefen idanushi yana tsinkayo mamakinta "sir did you say anything? ya juyo ahankali yana kallonta qirjinsa na dokawa da kafin gaske sannan ya sake kawar da kanshi gefe muryarsa a kasalance yace "nothing!ko kinji nace wani abu ne ?”idan ma bakace wani abu ba sir ni ina son nace wani abu ko zan iya ce…”?kafin ta kai qarshen maganarta ya jefa mata wani mugun kallo zuciyarsa na bugawa da karfi wanda ya sanyaya maryama gaggawar yanke maganarta babu shiri .”murmushi yayi a ciki yana cewa “ga tsoro ga tsoratar da mutane kalleta kamar wata ta kirki “.



“ganin irin kallon da yake binta dashi yasa ta sunkuyar da kanta qasa tana kallon zara zaran yatsun qafafunta sannan ta cigaba da magana dan tasan muddin bata ce ba bazai ce ba sai dai ta qaraci tsayuwarta bazai ce mata ba “sir ko zan cewa wani abu “?sai daya gama shan kamshinsa da jin kai tare da nuna qarfin iko sannan yace “say it “!yana fesar da numfashi “dan ..”dan allah kayi hakuri akan laifin da nayi maka abun ya dameni sosai gabadaya na kasa samun sukuni da kwanciyar hankali hakika nayi kuskure mai girma d'an darajan allah da darajan iyayenka kayi hakuri yanzu haka wannna zuwan da nayi aiki ,nazo ne saboda kai .””saboda shi kuma ?yayi maimaita abinda ta fad’a yana mai lumshe mata tsumammun idanunshi yana jin wani sanyi dadi na ratsa ilahirin sansar jikinsa har tsigar jikinsa na mikewa "nazo a karo na biyu saboda kai am very very sorry sir and I mean it.”



“kallonta ya cigaba da yi kamar ya fixgota zuwa jikinsa ya bata kyakkyawan runguma “zanso ka sake bani dama ta biyu dan allah zan tabbatar maka da abinda nake nufi please give me a second chance sir bazan sake kawo maka wata matsala ba nayiwa kaina wannan alkwarin sosai ta dinga bashi hakuri tana bashi tabbacin bazata sake ba “.amman tsit kake jin mr ata yaki cewa komai illa janyo murfin durowa yayi ya ciro kwalin sigari ya bud’e ya zari kara d’aya ya kai bakinsa ya rike yana neman abun kunnawa ,ahankali maryama ta fara taku ta nufi inda yake zaune ta tsaya kusa dashi wanda tazarar dake tsakaninsu bata fi taku biyu ba tana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba hankalinta yayi mugu mugun tashi , baza tace ga dalilin da yasa taji wannan mummunar tashin hankalin ba na ganin mr
ata da sigari ne ko kuwa na rashin maganar da yaki mata ne “sir ..”



Ta kira sunansa a raunane ya bar abinda yake tare da tsareta da tsumammun idanunshi “ka ajiye sigarin sannan kace min wani abu ko zan samu natsuwa .”still dai shiru ne ya biyo baya wanda alokacin ma tuni ya kunna sigarinsa ya fara zuga ahankali,iya tashin hankali maryama ta shiga alokacin ,dan ko lokacin daaka bata tahirin mahaifinta yadda rayuwarsa ta kasance cikin shaye shaye bata ji tashin hankali irin wannan ba .”
bata san dalili ba wannan tashin hankalin yafi komai d’aga mata hankali da dagula mata lissafi tana nan tsaye ya cigaba da zugar sigarinsa hankali kwance .sai kai hannu tayi ta toshe bakinta zuwa hancinta dan bata son warin sigari acikin ranta take maganar zuci mutun duk rayuwarsa tana cike da kalubale da matsaloli amman baud’adden halinsa ya hanashi ganewa bare ya gyara “ko yaya matarsa take fama da wannan hali nashi?” shine kullum cikin quna rai da zafin zuciya da miskilanci byn duk wad’an nan abubuwa sai daya had’a kanshi da shan sigari killa ma bayan sigarin yana shan wasu abubuwa,sai ya jifa kanshi cikin matsala ya jefa matarsa da iyayensa cikin matsala suma .”



“Wannan wacce irin rayuwa ce ?mutun har mutun amman ya jefa kanshi cikin rayuwar shaye shaye sam bata ta’ba masa kallon mai shan wani abu ba kuma koda fad’a mata zaayi zata karyata wanda ya fad’a mata kasamcewar bashi da kamani da masu shan sigari ,kallonsa ta cigaba yana zugar sigari cikin wani irin salo da kwarewa ,zazzafan numfashi ta sauke da qarfi alokacin data ga ya shanye sigarin hannunsa ya zaro wani ya kunna data bakinsa “Ke maryama ki kama kanki matsalar rayuwarki ma ta isheki karki qarawa kanki damuwar wani ba
Ya juya ahankali ta nufi kofar fita daga office din .a natse yabi bayanta da wani shuumin kallo”exactly yadda take a mafarkinsa haka komai nata yake shape mai kyau ya furta a fili yana lumshe ido yana Aiyana ranar da zata shigo hannusa shi kad’ai yasan irin rikon da zai mata ."



Jiki a sanyaye ta koma office ta zauna kusa da surayya hira suka fara yi ahankali tana bata labarin yadda suka qare da mr ata da alamun dai ya dan sauko surraya ,yusura atakaice dai maryama ta tara matan dake aiki a cikin office din har da masu aiki a qarqashin sultan tace “ ina son muyi wani aiki ne daku “yaushe ne zaa sake yin wani presentation?”“ ai yana faruwa ne duk bayan wata d’aya “ okay ina ganin zamuyi aiki tare domin muyi surprise din sir” “kai ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login