Showing 129001 words to 132000 words out of 182919 words

Chapter 44 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

367

ba sakamakon ganin mr ata durkushe yana rike da hannu rigar maryama yana qoqarin janye mata dan kar ya had'a da murfin mota wani dogon tsaki sultuna taja tana sake mamaki mutumin da tasani mara fara'a da sakin fuska mai nuna ma mata tsantsar rashin kulawa da soyayya mara son farincikin mutane ,mara damuwa da damuwar wani wai yau shine durkushe agaban wata ,watan ma ma'aikaciyarsa bayan ya gama rungumeta anya kuwa duk wad'an nan babuwan ba gizo yake mata ba ?" ta kai hannu da sauri ta murza idanunta adaidai lokacin daya mike tsaye yana aika ma maryama wani kallo wanda bashi da maraba da kallon soyayya "sannan ya  maida murfin kofar a natse ya rufe ."



ya zagaya  Wanda shi tuni an bud'e masa bangaren da zai zauna ya shiga ya zauna yana d'an kallon fuskarta da tsumammun Idanunshi har a ruwa ya já motar kwayar idanunshi da hankalinsa na kanta ya zuba mata ido yana qare mata kallo ."ya rasa wani irin mahaukacin so yake mata "numfashi maryama ta sauke sanda ta tuna  girman taimakon da yayi mata a yau din nan ,ya daukar mata alqawarin had'ata da nadiya kuma ya cika wannan alqawarin ."
hakika ya cancanci ta yaba masa idan ma da hali ta had'a da godiya dan gabdaya wani abu daya tsaya mata a qirjinta ne taji ya fad'a zuwa cikinta wanda take jin babu tantama tarin damuwa da bakinciki da ta dade tana fama dashi na tsawon lokaci ne ya bar rayuwarta .saukar laulausar tafin hannunsa a saman hannunta yasa ta bud'e idanunta ahankali ta waigo gefen da yake zaune yana faman kallonta kamar zai cinyeta ."nan take idanunsu ya tsarkar cikin juna sukai shiru suna kallon juna cikin wani irin yanayi mai tattare da shauki kafin ahankali maryama ta maida idanunta ta runtse dan bazata iya cigaba da kallonsa ba dan wani iri take ji a sansar jikinta .”
kallon da yake mata ma ayanzu da tana da hali zata iya hanashi domin kallo ne dake nukurkusa mata
garkuwa jiki ,ahankali ya tsarke  yatsun hannuwan su waje d'aya ya fara  murzawa a tare suka ji  wani abu ya tsarga masu a gabad'aya ilahirin jikinsu da sauri ta sake bude idanunta ." gani tayi ya mugun  tsareta da idanunshi  masu firgita  mutum Iokaci daya tayi saurin kawar da kanta gefe tana jin wani irin fad'uwar gaba kmr tasa masa  kuka tace masa stop touching my body amman ta kasa  aiwatar da komai ."




Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 37




Sadam ne zaune a babban parlour’n hotel din da suka kama dake  lejico wanda ke cikin ikoyi hotel shiru yayi cikin tsananin damuwa sanye yake da jallabiya brown colour mai gajeren hannu,a natse ya kai kwayar idanunshi zuwa ga had’ad’den agogon dake manne a bangon parlour’n.” karfe shida na yamma daidai yanzu ta buga, ahankali ya d’auke kwayar idanunshi cike da damuwa ya maida zuwa bakin kofar shigowa parlour’n zuciyarsa na wani irin bugawa da qarfin gaske numfashi ya sauke sannan ya kai hannusa ya shafa sumar kanshi yana sake duba agogo,” a lissafinsa zuwa yanzu nadiya na can ATA company ,gabadaya ya rasa dalilin da yasa yaji ya kasa samun natsuwa ko dan yana jin kamar akwai wata a qasa ne ?”ya rab kasa ba wani shiri bane aka shirya wa nadiya yayi maganar a fili yana d’auke kanshi zuwa kan ‘dan qaramin stood din dake gabansa wanda ke d’auke da tiren kayan marmari .”jiki a sanyaye ya d’auki Koren apple ya kai bakinsa ya gutsura kad’an tare da cigaba da kallon tauraron d’an adam din daya kunna "knocking din kofar parlour da yaji ana yi shi yasa ya d’auki remut da sauri ya rage sautin qarar TV sannan ya yunkura ya mike  yaje ya bud’e kofar .”



“nadiya ya gani tsaye rungume da hannuwanta duka a qirji tana dubansa,da wani irin sauri ya riko hunnunta ya sanyata ajikinsa ya rungumeta tsam tsam yana sauke numfashi da ajiyar zuciya atare . bayan kamar second goma ya janyeta zuwa gefensa domin ya samu damar maida kofar ya rufe.”cike da tsananin son juna suka tsurawa junansu ido suna kallon juna kafin ahankali suka tsakarwa juna murmushi,sadam na cewa “banyi expecting zaki dawo lafiya ba , na d’auka shiri ne aka shirya miki dan a gano wani abu akanmu “nadiya ta sauke numfashi kana tace “sosai kuwa my heart shiri ne kamar yadda kayi expecting sai dai na nuna masu kwarewa domin kuwa na d’aurasu a wani bagire da bazasu ta’ba fahimtar Komai akanmu ba ,domin kuwa na shirya masu bayanan qarya kuma sun yarda da hakan kuma sun amince dani .”tana gama fad’ar haka suka samu waje suka zauna cike da kulawa sadam ya turawa nadiya tiran kayan marmari nan na gabansa sannan ya nufi fridge ya kawo mata maltina da ruwa mai sanyi" tare da tsura mata idanunshi .”



“Uhm fad’a min wani irin bayanan qarya kika fad’a masu ?”nan take nadiya ta shiga zayyano masa qaryar data fad’a masu tun daga farko har qarshe sannan ta qara da cewa ko kasan cewar maryama baqaramin tashin hankali ta shiga ba sakamakon jin cewar ni da kai masoya ne ?”ta fad’a tana wata irin dariya mai sauti ,”na tabbatar mata kai din nawa ne alokacin baya, amman kuma data lura alokacin da nake mata bayanin soyayyarmu,data fahimci har a yanzu ma kai din nawa ne amman dake wannan yarinyar mahauka ciya ce sai kuka take mai tattare da jimamin rashinka .”my heart sosai fa yarinyar nan ta kamu da sonka anya kuwa my heart wani abu bai shiga tsakaninku ba ?”domin kuwa a irin kallon da nayi mata da tawa fahimtar ta d’an dani dadin ka ne yasa ta damu da rashinka ?”fad’a min menene gaskiyar magana ka kusanceta ko .”?ta qarasa maganar fuskarta tana nuna alamun damuwa da kishi.”



Yaya sadam yayi shiru kawai yana kallonta da sauraronta cike da Jin haushin maganar haka ma zuciyarsa sam taji babu dadi kiran maryama da mahaukaciya datai .” karta ga ya guji kowa akanta ta nemi ta dinga ci masa fuska duk fa lalacewa maryama tashi ce kuma jininsa ce kuma har zuwa yanzu tana nan amatsayin matarsa “kin sha furta min wannan kalmar atsakanina da maryama ko mun d’an d’ani dadin juna ne yasa na kasa furta kalmar saki agareta,wannan kalmar baya damuna kamar kalmar haukan da kike danganta maryama dashi ,”karki manta dangan takata da maryama ,ni daita dagin juna ne da suke da tsananin shakuwa amman ina son daga yau wannan kalmar ta zamo qaro na qarshe da zai sake fitowa daga bakinki shiru tayi tana kallonsa da bayanannen mamaki “yes karki sake dangatata dashi banason dan zamu iya samun gagarumin matsala dake.” ya qarasa maganar yana had’e fuska “numfashi ta sauke sannan tace “okay shikenan naji kayi hakuri “.ta fada tare da kamo hannunsa cikin nata a natse bai ce daita qala ba ta cigaba da magana “kayi magana mana kayi shiru kana kallon wani gefe dabam huci ya furzar yana Kai hannunsa goshinsa “na fa baka hakuri duk da ni nasan ba wai laifi nayi ba.”



“Saboda me to zaki bada hakuri tunda kinsan bakiyi laifi ba?”ya fad’a a fusace yana qoqarin zare hannunsa cikin nata tayi saurin rikewa tana shagwabe masa “yanzu akan maryama zaka canza min “.ba akanta bane akan kalmar hauka ne banason kina kiranta da kalmar hauka domin ke kanki kinsan babu alamar haka a attare daita “naji kayi hakuri bazan sake ba shiru yayi mata yaki cewa komai “haba mana my heart ka saki ranka mana wallahi idan kana nuna min haka sai naji kamar kana sonta ne “ta qarasa mgnr tana kwanto masa ajiki numfashi ya sauke tare da cewa “shikenan naji naji !! ta dan dago daga jiknsa tana kallonsa “to kayi min murmushi .”
murmushin takaici yayi itama dai murmushin tayi kana ta cigaba da magana “ga dukkanin alamu company ata sun nuna zan samu aiki da company dan nasan tunda suka d’aukeni dole zaa sake nemana still dai shiru sadam yayi sannan yayi kicin kicin da fuskarsa “my heart!”ta kirasa bai amsa mata ba amma hakan bai sa ta damu ba ta cigaba da maganarta “da zarar na samu aiki kudi zasu samu kenan ,da zarar mun samu kudi zamu bar wannan wajen ko ba haka ba ?”shiru dai yayi mata .”



ta numfasa tare da gyara zamanta “what’s our next plan my heart ?”stil dai shiru yayi dan shi baya jin zai wani barta tayi aiki da wannan kamafanin “my heart kamin magana mana ?”tai maganar tana kai hannunta sansar jikinsa “ba batun samun kudi bane damuwatq dan banason Kiyi aiki a wannan kamfanin ,domin ina son muyi nisa da nan ne mu qara gaba muje inda babu wanda zai ganmu ko wanda ya sanmu far away from everyone “.and far away from maryama ba ..”ta fad’a tana tsarke yatsun hannunsu tare da rungumesa ajikinta” amman kuma duk wannan abun daka lissafa suna bukatar kudi “karki damu zamu samu kudi qasar ma zamu bari gbdy dan haka kar na sake jin batun zakiyi aiki da wannan kamfanin matsawar kina son ki cigaba da ganina a tare dake ko kuma yuwar aurenmu dan kina sake tada maganar aiki da wannan kamfani wallahi na fasa aurenki .”sake rungumeshi tayi tsam ajikinta tana shakar qamshin jikinsa.”shikenan naji duk abinda kace shi zanyi.”


*****

Qarfe takwas da wasu ‘yan mintuna motar mr ata ta qaraso titin capitor sakamakon hoodop din da suka iske akan hanyarsu ahankali suka shigo unguwarsu maryama ,direba ya samu waje a gefen titi yayi parking ya fito daga cikin motar ya rufe murfin mota yayi gaba kad’an abunsa inda mr ata ya maida kwayar idanunshi kan maryama still yana rike da yatsunta hannunta muryarsa a kasalance ya kira sunanta “maryama .”!
bata amsa ba sai dai ta waigo inda yake zaune tana kallonsa tana kallon yadda yake ciza lips dinsa ,gefe guda kuma tana jin sauyi a sansar jikinta sakamakon hannunta dake cikin nashi sosai ya sanya kwayar idanunshi cikin nata duk da babu wani wadataccen haske acikin motar amman tana jin kwayar idanunshi ajikinta ta Lumshe idanunta hasken wayarsa ya kunna ya haska fuskarta ya tsurawa fusakr ido yaga yadda idanunta suka kumbura sukai wani irin girma fuskarta tayi jajir .”cikin wani irin yanayi yake kureta da kallonshi kafin yaja ajiyar zuciya ya sauke sosai ya kwantar da muryarsa“ya kike jin zuciyarki yanzu ?”kina jin damuwa har yanzu ?yayi mata tambayar ajere sai data had’iye wani abu daya tsaya mata a makoshi kana ta soma magana a natse “ban ta’ba tunani cewar cikin lokacin kankani irin wannan zai sa naji damuwata ta wattanni sun gushe ba ,ta qarasa magana muryarta da alamun son yin kuka “wallahi naji relief sosai amman hakan bazai sa na iya mantawa da d’anuwana ba “ta qarasa maganar tana runtse idanunta “maryama wannan duk mai sauki ne akan ki cigaba da rainon soyayyar matace acikin zuciyarki ,sannan rage damuwar zai sa ki cigaba da rayuwarki cikin salama kamar kowa ,forget your past and leave your present “ko kin fahimci abinda nake nufi.”



“naji zanyi duk abinda kace kuma naji dadin gudumuwar daka bani dan ka taimakeni kuma naji dadi sosai “maryama kin yarda sosai da wannan mutumin kuma ina ji a zuciyata har yanzu akwai wani space da kika bashi acikin zuciyarki “wannan haka ne ban ta’ba jin na yarda da wani halitta kamar yaya sadam ba amman ta yaya kasan har yanzu sadam yana da sauran space acikin zucyta?”shiru yayi kawai yana kallonta yana jin wani iri acikin ranshi “sir !”mai yasa kayi shiru kana kallona ?still dai shiru ya cigaba dayi yana cigaba da kallonta zuciyarsa cike da zallar kishi “sir me kake tunani ?bai ce mata komai ba illa ya runtse idanushi “amman nace sir yaakayi kasan cewar idan nayi kuka irin na yau zanji relief ?”ya sake damke yatsunta da karfi tare da sake runtse idanunshi gam “sir ko kai ma ka ta’ba tsintar kanka cikin irin yanayin dana tsinci kaina ne ?”shiru yayi kawai yana tunanin irin rayuwar wahalar da yayi akanta wacce bazai ta’ba mantawa ba “bazai iya kirga sau adadi nawa ya sha giya akan zafin rashinta ba sigari kam ma baa maganarta bare kuma zubar hawayensa “.



“sir !sir !! ta sake kira sunansa ahankali har sau biyu ajere sakamakon ganin moond dinsa ya canza “sir me kake tunani ne ko maganata ta ’bata maka rai ne ?”no !”ya fad’a atakaice bata bata min rai ba amman abinda nake baqata dake ki goge wannan soyayyar dake binne a zuciyarki domin bawa wata soyayyar dama shiga rayuwarki yana gama fad’ar haka yace muje ko “.ta kasa fita daga cikin motar ta tsura masa idanunta tana tunanin abinda ya bata masa rai ganin ta kasa tuno wace kalma ce tai sanadiyyar canza masa mood dinsa taga gara kawai ta bashi hakuri sosai tayi kasa da muryarta “kayi hakuri .”!
“ba hakurinki nake bukata ba ki goge wannan banzar soyayyar shine abinda nafi buqata “naji zanyi qoqarin yin abinda ka buqata duk da hakan ba abu ne mai sauki agareni ba bayan halaccin ya sadam agareni umma ma abar dubawa ce taso ni ada baya can kuma har a yanzu tana qauna ,ta bani dukkanin wani gata da kulawa tun ina qarama har zuwa girmana ,bata son damuwata yanzu haka tana can zaman jirana bata bacci matsawar bata ga shigowata ba tana girmamani kuma tana tsananin sona zatai iya yin komai akaina “the most special thing in this world to me is my special mumy wato umma wannan yana daga cikin dalilin da yasa cire ya sadam araina zai yi matukar wahala agareni dan umma bazata iya ciresa a rayuwarta ba amman zanyi qoqarin ragewa da fatan bazaka damu da jin haka ba ?”ta qarasa maganar tana kallon yatsun hannunsu dake tsake cikin juna.”



Numfashi ya sauke yana cewa “is okay na fahimceki” na gode sosai Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi a kasan zuciyarsa ya amsa da” ameen!”tana qoqarin fitowa daga cikin motar kira ya shigo wayarta ahankali ta koma ta zauna tare da ciro wayarta sunan umma ta gani yana yawo akan screen din wayar da sauri taja koren maddani tana qoqarin kai wayar kunnenta ya rike tsintsitar hannunta tare da saka wayar a hands free “maryama kina ne ?”kiyi maza ki qaraso gida yau alkubus nayi mana nasan zakiji dadi sosai”kyakkywan murmushi ne ya bayyana akan fuskar maryama sannan tace “sosai kuwa umma nah gani nan yanzu zan shigo ,to shikenan kiyi sauri kinsan idan yayi sanyi bashi da dadin ci” umma ta fad’a cike da kulawa “yanzu nan zaki ganni ummata sai kin shigo umma ta fad’a tana katse kiran inda maryama ta kalli mr ata fuskarta da bayyananne murmushi “tabbas ya yarda matar na tsananin sonta wanda hakan yasa yaji zuciyarsa ta dan bata wani matsugune acikinta har bakin get din gidansu ya rakota sai daya ga shigarta sannan ya juya ya wuce gida .”



Ahankali ya shigo parlour mami ya ajiye yar saman suit dinsa akan hannun kujera idanunshi na kan mami dake tsaye ta d’ago ta kallesa a natse kafin ahankali ta qaraso zuwa inda yake ta tsaya tana tambayarsa”lafiyarka meke faruwa na ganka haka ?”shiru yayi kawai yana hura hanci tasan halinsa a duk sanda yayi haka baya bukatar acigaba da damunsa akan abu “ ka qarasa d’akin ka kayi wanka kazo kaci abinci kanshi kawai ya gyada sannan ahankali ya zagayeta ya haye sama bayan wasu mintuna mami taji shiru bai sauko ba ta nufi dakinsa a zaune ta iskeshi shiru cikin yanayi na tsananin tunani ta zauna kusa dashi “wai meke damunka ne “?ta tamabyesa cike da kulawa “babu abinda ke damuna sweetheart ko kina tunanin akwai abinda zan iya boyewa kyakkywar mahaifiyata ?”harara shi tayi tana cewa ”akwai mana sau nawa ina tambayarka abu kace min babu komai alhalin kuma ni nasan da komai din .”shiru yayi batare da yace uffan ba “nifa nasan halin d’ana,nasan yanayinsa kuma nasan yanayin damuwarsa kawai dai ka fad’a min “ya kamo yatsun hannunta cikin nashi yana cewa “babu komai sweetheart just believe me, I can’t believe you adamcy amman dai me kake son kaci muna da rice and stew da farfesun kan rago muna da tuwon semoveter da miyar danyar kubewa da cat fish, muna da light soup daakayi mix dinsa da kan rago da kayan ciki da busashen kifi muna da ..” sweetheart alkubus zanci .”



“ alkubus zaka ci bayan shekaru masu yawa rabon daka ci “?“yes shi zanci sweetheart ya fad’a yana lunshe mata tsumammun idanunshi shiru tayi kawai tana kallonsa ,kin bude idanunshi yayi saboda gabadaya jinsa yake acikin wani iri yanayin kamar ya yi kuka ko ya samu salama a zuciyarsa da Kyar ya bude idanunshi sakamakon jin shirun mami “kiyi hakuri sweetheart nasan bazan samu ba “babu wannan ranar da d’ana zai ce ga abinda zai ci ni kuma na kasa masa tayi maganar kamar zatai kuka “na dade ina expecting haka kullum burina naji kace zakaci abinci da mahaifinka yafi so shiyasa naji maganar wani iri”bari naje nayi maka just ka bani lokaci kad’an yanzu zanje nayi maka alkubus “ ta mike ta fita da sauri tana goge gutun hawayen daya cika gefen idanunta.”




“Kai umma qamshi allubus din ya cika koina agidan nan ,da gaske maryma?allah kuwa barin ma qamshin miyar maza maza kije kiyi fresh up kizo kici tun kafin yayi sanyi “okay umma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login