Showing 9001 words to 12000 words out of 182919 words

Chapter 4 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

342

sakamakon fuskarsa da ta dinga mata gizo acikin kwayar idaninta.”



ta runtse kwayar idanunta gam tana jin ranta na sake 'baci zuciyarta na tafarfasa ita dai umma idanu ta tsura mata kawai tana kallon ikon allah tsaki taja tare da yage takarda ta dukunkune ta jefar daita ta koma ta kwanta tana sauke numfashi "kin fasa rubutawa ne ?"shiru tayi ta kasa bawa umma amsa dan bazata iya fada mata abinda idanuwanta suke gane mata "bazan gaji da fada miki kalmar kyi hakuri ki manta da abinda ya faru domin komai mai wucewa ne bahaushe yace wata rana sai labari ga gabe can tana d’ago miki hannu jikina na bani aiki nan har gida zai biyoki “kanta ta d’aura akan cinyar umma tare da runtse idanunta tana jin maganar umma na bin jinin jikinta suna sanyayya mata zuciya .”hakika bata da kamar umma acikin zuciyarta ita din cikakkiyar uwa ce gareta ta maye mata gurbin komai arayuwarta “daga yau bana son ganinki cikin damuwar nan matsawar ba so kike damuwarki ta juye zuwa jikina ba ayi uwa kwance ‘ya kwance ba shiru sukai umma ta kai hannunta saman gashin maryama tana cewa “a duk sanda na ganki cikin danuwa zuciyata tafasa take bana samun kwanciyar hankali har sai na ganki cikin walwala Kmr sauran mutane “love you mumy “!umma tayi murmushi tare da d’aga kanta ta kamo hannuwanta “ki manta komai kiji maryama ta gyad’a mata kai “in sha allahu mumy komai ya wuce zan cigaba da rayuwata kamar yadda nakeyi “yauwa diyar Allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi.”



daddare da misalin karfe takwas da rabi na dare ma’aikatan dake kula da bangaren kitchen ne suke ta faman kai kawo daga kitchen zuwa dining area kowannensu sanye da uniform kamar koda yaushe yayinda babbar yarinyar hjy zulai ke zaune tana kula da duk abinda suke abinci kusan kala shida ne akan dinning had’e da lemuka da ruwa sha marasa sanyi sosai ahankali ATA yake saukowa daga samansa jikinsa sanye da riga ash colour da wondo baki ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa wandonsa yayinda qafafuwansa ke sanye da wani hadadden silifas baki mai shegen kyau idanunshi sanye da glass ga wani kamshi na musamma mai natsar da zuciya na tashi ajikinsa .”ahankali yake saukowa tamkar wanda bashi da jini a jikinsa a d’age ya dinga kallon ma’aikatan dake jera kulolin abinci akan dining yana qare masu kallo domin qara tabbatar da ingancin aikinsu ,suna ganinsa duk suka shiga hankalinsu tare da qarawa jikinsu natsuwar aiwatar da aiki dan sun san halinsa muddin akai kuskuren ya gani zai ce ya dakatar da mutun aiki ,shiyasa komai cikin takatsantsan da kulawa suke yinsa .”cike da tsoro da fargaba suka cigaba da komai yayinda shi kuma ya cigaba da taku yana kallonsu duk ma sai suka sha jinin jikinsu dan wasu ma daga cikinsu sun fara tunanin wani acikinsu zai bar aiki gobe.”


A natse cikin isa da takama ya tsaya akan step na qarshe shi bai sauko ba shi bai koma ba yana ciza gefen lip’sdinsa na qasa yana sauke numfashi ahankali,byn kmr minti biyar ya sauko still hannuwan sa duk na cikin aljihunsa bai tsaya akoina ba sai inda mahaifiyarsa Take zaune akan kujera tana duba jarida punch wacce ke d’auke da hotonsa .”ya cire hannunsa d’aya ya d’aura akan hannun kujerar da take yana mai juya mata baya .”
ta waigo a natse ta kalli bayansa kawai dan tun shigowarsa ta fahimci yana tattare da damuwa bari tayi sai ya huta ta tuntu’besa abinda ke damunsa “ya’akayi Adamcy meke damunka duk na ganka wani iri ?bai juyo ya kalleta ba haka zalika bai zauna ba “ka zauna mana Adamcy “bai zauna ba ya soma mgn cikin sanyin murya kamar zaiyi kuka “sweet heart ko zan iya tambayarki wani abu ?”.da sauri tace “sosai ma kuwa ka tambayeni duk abinda kake so a shirye nake dana baka amsar kowace irin tambaya “.ta fad’i hk cikin d’an damuwa dan duk lokacin data ganshi cikin damuwa tana finshi shiga damuwa ya juyo gabad’aya ya tsura mata tsumammun idanunshi “alal misali mutun ne ya zamanto yana da fikira sannan kuma shi mai wannan baiwar yana da katuwar matsala bayan haka kuma kana jinsa acikin rayuwarka sannan bazaka iya tafiyar da ayukanka batare dashi ba ko mutun zai iya janyo shi wannan mutun kusa dashi ya zama mallakinsa gabadaya ?”.


numfashi ta sauke da karfi sannan ta numfasa ta riko hannunsa ta zaunar dashi a gefenta kana ta fara magana cikin salon hikima irin nasu na manya “kowani bawa dake rayuwa acikin duniyar nan yana da matsala ,mutane mabam bamta amman akwai wasu matsalarsu bata kai ta wasu ba dole duk wanda zakayi muamula dashi sai kayi hakurin zama dashi saboda duk dan Adam yana tattare da matsala kawai na wani ne yafi na wani ,dan haka shi mai wannan fikira idan kaji har acikin zuciyarka ya samu matsuguni karka damu da matsalarsa dan matsala bata qarewa arayuwar d’an adam hakuri zakayi ka janyosa ajiki ka bashi kulawa idan akayi sa’a sakamakon hkn sai kaga matsalarsa ta ragu sannan km ka amfana da fikirarsa kaga anan ma ka samu riba biyu ka sanyashi ya samu natsuwa sannan ka amfana dashi na baka amsar tmbyrka ko nima zan iya tambayarka ?”tsura mata tsumammun idanunshi yayi yana kallonta haka nan yaji zuciyarsa ta gargadesa da kar ya yarda tai masa nata tmbyr dan haka ya girgiza mata kai alamun a’a “ok mr ATA muje kaci abinci ammi ta kwalla ma tabawa kira har sau biyu .”



cikin kankanin lokaci ta bayyana sanye cikin doguwar riga tace “mami gani !“muje kiyi serving din Adamcy abinci cewar mami kai kuma muje ko ? “no sweetheart barni kawai anan “shikenan bari akawo maka abincin nan bai yi mgn ba ya runtse idanunshi shi kad’ai yasan me yake ji a gangar jikinsa damuwarsa ta ninku fiyye da can baya “mami ta janyo qaramin table gabansa “adaidai lokacin da mai aiki ta qarasa da d’an hanzarin gudun karta tafi da sauri ta sha zagi a gurinsa mami ta mike tabi bayanta .”a natse take komai duk bai motsa ba ta wuce taje ta tsaya kusa da mami “mami !naam !”wani abinci zan zuba masa ? Kinsan shi yafi son shimkafa ki zuba masa kiyi masa plet din salad dabam ta amsa da to ta yi Kmr yadda mami tace ta d’auka ta kai Kan table din gabansa ta ajiye har ta juya tayi taku biyu taji sautin muryarsa a dake “Ke!ta tsaya cak hantar cikinta na wani irin kad’awa yayinda jikinta ma ya d’auki rawa ta fara sauke numfashi da karfi tana addua allah yasa ba wani laifi tayi masa ba “ba dake nake mgn ba ?ta juyo da wani irin sauri ta tsura masa ido abun mamaki idanunshi a runtse suke cikin hanzari mami ta qaraso wajen tana cewa “Lafiya Adamcy ? numfashi ya sauke yana bud’e idanunshi akan mami “kiyi tafiyar ki sweetheart tace “to ! ta kama gabanta sai dai duk hankalinta na kansa ya kalli mai aiki cikin isa da kamewa “ meye aciki ?muryarta cike da tsoronsa tace “rice and stew “.daukesu bana bukata?” shiru tayi can tayi karfin hali ta kwantar da murya tace “yalla’bai to me zakaci ai sai a dafa maka komai ka kake so ?ware idanunshi yayi sosai “waye zai ci jagwalgwalonku I think you’re cray.”


tace “to yau kuma abun ya motsa ta koma da baya ta kame tana cigaba da addau acikin ranta allah yasa maganarta bata hassalasa ba yaje ya koreta ta shiga ukunta bai qara magana ba ya tashi ya canza wurin zama ta kwashe komai ta maida kitchen tana yiwa mami bayani “barni dashi bari naje na samesa dan da alamun yau rigima yake ji “Adamcy nah ya’akayi kuma kace baza ci abincin ba ?yatsina face dinsa yayi “am not feeling eating any…”haba Adam ka dinga qoqarin bawa cikinka hakinsa ko na dafa maka kusku ne ?kamar yace “a’a !sai kawai yaji tausayin mahaifiyarsa ya kamashi tana matukar kula dashi da rayuwarsa dan haka ya gyad’a mata kanshi kawai tamark wani qaramin yaro.” ta juya ta koma kitchen da sauri tana kiran tabawa tazo ta tsaya kusa daita “ dauko min abubuwan da zamu had’a joluf din kuskus zan masa a natse mami take yin komai cikin kankanin lokacin ta dafa masa joluf din kusku wacce ta wadatu da korrot,green beans da kayan kamshi hanta da koda a madadin nama nan da nan kamshi curry da tyme ya soma tashi kusku din yayi kyau sosai sannan tace maza tabawa d’auko ki biyoni dashi “.


Turus mami tayi tsaye sakamakon rashin ganin ata a inda ta barshi “ina kuma yayi ?tayiwa kanta tambayar “kardai fita yayi ?Aa bazai fita adaidai wannan lokacin ba sai dai idan dakinsa ya koma kai tsaye hanyar step ta nufa inda mai aiki tace “mami na biyoki da abincin ne ?”eh tabawa biyo dashi da hanzari mami ta tura kofar parlour’nsa tare da sallama taga baya nan wani yawu tayi qoqrin hadiyewa sannna ta dakatar da tabawa da cewa ajiye tray kiyi tafiyarki ta nufi d’akinsa nan ma baya nan ta sake fitowa da sauri ta shiga d’ayan bedroom dinsa tsaye ta gansa ya rungume hannuwansa duka a saman faffad’an qirjinsa ya tsurawa zanen hoton maryama ido a tsorace take kallon bayansa inda shi kuwa yayi zurfin cikin tsananin tunaninta “bazai iya hakura daita ba tabbas soyayyarta tana da matukar tasiri a rayuwarsa ,ji yayi kamar da ba sonta yayi ba a yanzu ne ma ya fara sonta yayi shiru tare da runtse idanuwansa sosai yana kiran sunan Allah zuciyarsa na sake nitso acikin tafkin qaunarta ” a hankali ya bud'e idanuwanashi wanda suka kad'a sukayi ja saboda wannan qaddarar tafi komai yi masa ciwo acikin rayuwarsa a fili kuma cewa yayi "adam ka hakura daita karka kuskura ka shiga hurumin Allah ballantana ka bayyana mata  soyayyarka bare ma kasan yarinyar nan bazata soka ba sakamakon abinda kayi mata. bugu da qari kuma matar wani ce Ya qarasa maganar wasu hawaye masu zafi suna saukan masa akan kumatunshi “wace yarinyar ce matar wani ?yaji saukar muryar mami ?daga sama cikin sauri ya share hawayensa dan kar mami ta gane halin da yake ciki a dan tsorace yace “amm ..” sai kuma sai yayi shiru yana tunanin abinda zai fad’a mata dan bai iya karya ba duk abinda zai fito daga bakinsa to gsky ne “.



mami ta tsura masa ido jikinta ya kama rawa numfashinsa ta hango yana fita da karfi saboda zubar hawayensa “kayi min bayani wai meke damunka ne kake zubar da hawaye?ko dai har yanzu matsalar yarinyar nan ce ?shiru yayi ya kasa cewa komai dan bazai iya mata karya ba kuma bazai iya fad’a mata cewar ya ganta amatsayin matar wani ba .”mami batayi mamakin shurin da yayi mata ba domin tasan halinsa a duk lokacin da yayi shiru haka baya son fad’ar gsky abinda ke cikin ransa ne tana kallonsa ya nufi kofar fita jiki a sanyaye ta biyo bayansa alokacin da ya samu waje ya zauna akan kujera ya d’aura kafarsa d’aya akan d’aya yana kallon saman parlour’n yana cizan lips dinsa dan shi ne kawai abinda yake ganin zai iya yi a halin damuwar da yake ciki dan zuciyarsa tafarfasa take ta sake nitso acikin tafikin qaunar maryama .”ahankali ta zauna a gefensa “adamcy ga abincin kaci kar yayi sanyi lumshe tsumammun idanunshi yayi ,shi dai baya jin zai iya sakawa cikinsa komai bashi da wannan kuzarin ,bashi da wannna natsuwar ,bashi da wannna ‘yancin tun da ya rasata yasan ya rasa komai nashi bazai sake morewa ba ko kuma yace rayuwarsa tazo qarshe dan idan babu ita cikin rayuwarsa shima babu shi .”



sunkuyar da kanshi yayi kasa yana kallon zara zaran yatsun qafafunsa masu kyau da haske “shikenan wahalar bazan nayi adamcy bazakaci komai ba ?shiru yayi batare da yace mata qala ba “sanin halin yanayinsa tamkar mai nasaba da jinin sarauta yasa ta matso da table din da tabawa ta daura tray abinci akai gabansa tana cewa “yau dai da alamun miskilanci ya motsa?” ta fad’a tana bude masa kula abinci tana zolayarsa sannna ta mike ta qarasa inda fridge dinsa yake ta bude ta dauko ruwa mara sanyi sosai tazo ta ajiye masa kallonta yayi cike da tausayawa yana wahalar da mahaifiyarsa over “kiyi hakuri sweet heart .” dakayi me adamcy ?ina wahalar dake dayawa “babu komai Allah yayi maka albarka ni dai fatana da adduata Allah ya yaye maka tunanin yarinyar nan dan idan akwai abinda ke cin raina bai wuce naga ka zauna kana bata lokacinka akan tunaninta ba .”numfashi ya sauke kawai batare da yace komai ba “nifa banga abun so a wajen wannna aljanar yarinyar ba bai san ya akayi ba murmushin ya bayyana akan fuskarsa yana cewa aljana kuma sweetheart?sosai ma kuwa aljana ce mana shiyasa kullum nake nemar maka tsari daita domin tana cikin ta bada gudunmuwar rabuwarka da matarka da har yanzu baka waiwayi inda take ba, ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe ina ganin ma kusan tare zasu haihu da auta “rayuwar maryam na matukar bani tausayi adamcy domin nasan duk abinda tayi ba da son ranta bane tursasata akayi bugu da qari soyayyarka ..”


Lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud’e yana kallonta a tsanake dan shifa sam ya manta da wani labarin wata maryam arayuwarsa dauke da ciki sai yanzu da tayi maganarta “sweetheart !ya kira sunanta “na’am adamcy ka tausayawa maryam tana bukatar tausayawarka “dan Allah sweetheart ki bar maganr wannna yarinyar ta rigada ta zama tarihi arayuwata ita kuma aljanar da kike magna akanta itama an bar tunaninta kai na ma cireta arayuwata sai yanzu na fahimci cutar da nayiwa kaina akanta na ‘bata tsawon shekaru akan abinda ba samu zanyi ba yayi maganar cike da raunin zuciya “alhamdulillah Allah na gode maka kai gsky ka wanke min zuciyata yau “yanzu dai ka fara cin abinci!babu mutsu ya fara cin abinci a natse ficewa Mami tayi daga dakin ta sauko zuciyarta cike da farinciki shi kuwa bayan fitarta kasa cigaba da cin abinci yayi ya kai tafin hannunsa ya shafa sumar kanshi zuwa fuskarsa ya had’a tagumi yana tunani .”
duk inda ya motsa yarinyar yake ji acikin ransa ji yake tmkr ransa zai bar gangar jikinsa ranar dai kwana ata yayi yana juyi da tunanin maryama sai yayi kamar ya saita tunaninsa yayi amfani da karfinsa sai ya sake shawara saboda jin tsoron allah duk yadda ya kai ga sonta bazai iya taka dokar Allah ba .”



Washegari bai tashi da wuri ba sakamakon rashin baccin da bai samu ba adaren jiya ,sai bayan sallah asuba bacci mai nauyi ya daukesa ,shigowar mami biyu dubasa bai tashi ba ,da misalin karfe d’aya ya sauko nan ya iske mami tare da zabiba da yaranta biyu suna ganinsa suka zo gurinsa da gudu suna kiran sunansa d’aukar ammi yayi mai sunan mami ya cillata sama yna mata wasa sannna ya riko hannun siyam yana cewa “yaushe kuka zo gidan “? zabiba tayi murmushin jin dadi tace “bamu jima da zuwa ba ina yini yaya ?shareta yayi tmkr ba dashi take ba yace “good morning sweetheart?morning or afternoon adamcy ka kalli lokaci ka gani bai kalli agogo ba yace “ai dan bamu had’u bane da safen shiyasa sai yanzu .”murmushi ta saki tare da dafa hannunsa dake kan nata kai dai wallahi bahagon mutun ne” numfashi kawai ya sauke yana jan yatsun hannun ammi “mami ta kallesa a tsanake “yaakayi kanwarka tana gaisheka amman kayi mata banza ?ka dinga yiwa yanuwanka uzuri ka yafe masu wannan matslar fa ba wata matsla bace da zaka riketa gam a ranka yanzu ko bayan raina haka zaka dinga hukuntasu idan sunyi maka laifi ?” to a ina kake son su saka ransu idan wata matsla ta kunno kai cikin rayuwarsu ?.”uncle see aunty girl ta hanamu mu fita muje wajen yesmen kuma mu muna son zuwa siyam tayi maganr tana nuna masa mami da yatsanta .”


“murmushi yayi jin suna da take kirata dashi “karki damu aunty girl zata bari kuje kuga yesmin no kace ta barmu muje yanzu saboda yesmin mukazo inji cewar siyam “siyam take your sister and meet tabawa idan zamu wuce zan kaiku ku ganta shikenan tashi sukai suka wuce rike da hannun juna yayinda ata ya bisu da kallo yana lumshe ido yana jin ina ma yaransa ne .”ahankali ya bude idonsa yana motsa lips dinsa “shikenan sweetheart komai ya wuce amman gsky ban so na sauko hk da wuri ba har sai bayan shekaru masu yawa “Au yanzu nan ka sauko da wuri kenan wajen wata biyar ?ya lumshe mata tsumammun idanunshi kawai kallonsa zabiba tayi cike da tausayawa tace “allah dai ya huci zuciyar babban yaya in sha allahu bazamu sake ba “kuma sake ya fad’a tare da mikewa ya nufi kofar fita yana cewa “sweet heart sai nã dawo “bazaka karya bane ?bana jin cin komai sai dai na dawo kawai “to a dawo lafiya Allah ya tsare “Ameen !” ya amsa ya nufi kofar fita .”



kai tsaye hanyar kamaninsa aka nufa dashi yana zaune hannunwansa rike da jaridar daily trust yana karantawa yana son wani abu ya d’auki hankalinsa na son kawar da tunanin maryama acikin ransa amman aikin banza yayi domin duk shafin da zai bud’e sai fuskarta sai ta bayyana aciki wani dogon tsaki yaja ya ajiye jaridar hannunsa ko da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login