Showing 141001 words to 144000 words out of 182919 words
ta ‘bata maka rai amman ka duba lamarina bazan iya ju…” tun kafin ta qarasa maganarta ya mike tsaye yana jan tsaki ya nufi step bayansa tabi da kallo tana jin radadi acikin zuciyarta tana durkushe maryam tazo ta wuceta ta shige kitchen da sauri sultana ta dawo haiyacin ta tabi bayan mrym da kallo kafin ahankali ta mike da sauri ta fice daga parlor tana share hawaye da gefen rigarta tana jin kamar ta mutu.”
Washegari
Ahankali maryama ta shigo ma’aikatar tana tafiya tana zance zuci “zan rage dan kusancin da muke samu dashi dan ina ganin yana d’aya daga cikin abinda yasa madam some ta soma zargin ko ina son shi ne ,haka zalika shima tunaninsa kenan akaina tunda har ya furta ahankali ta cigaba da taku har ta isa office dinsu fuskarta babu yabo babu fallasa tai sallama sannan tace “good morning everyone.”sai dai duk suka mata banza tamkar babu mutane acikin office din ta kalli yusura da mamaki a saman fuskarta dan a tunaninta idan kowa zai wulakantata ban daita jikinta a sanyaye ta ajiye jakarta akan table ta fito ta shiga office din madam some, tana tafiya ta fara jiyo qamshin turarensa wani irin luguden bugu zuciyar ta yayi da qarfin gaske ,sosai bugun zuciyarta ke qaruwa sakamakon kusanto inda take da yake ,kusan atare suka qaraso inda madam some take zaune ta gefenta ya ra’ba zai wuce tai saurin gaishesa “good morning sir! aciki ya amsa
mata ya wuceta ko kallon inda take bai yi ba dan haka ta maida kallonta ga madam some tana cewa” good morning ma !itama bata amsa mata ba tamkar yadda abokan aikinta suka mata “meke shirin faruwa ne yau ?”nan taji wani tsoro mai tsananin ya shigeta “ma..”sai kawai taga madam some ta mike da sauri tabi bayan mr ata cike da tsananin mamaki take kallonta cikin mintunan da basu wuce uku ba madam some ta dawo maryama tace “meke faruwa ne ma naga gaisheki baki amsa ba ?”ki koma office dinku ina da abubuwa masu mahimanci da zanyi yanzu.”wani sabon mamaki ya kama maryama“
meke damunsu ?”ko kuma tace meke faruwa?lallai akwai abinda ke faruwa wanda ita batasani ba kuma lallai yana da kyau tasan abd ke faruwa amman zata kama kanta zuwa wani lokaci taga iya gudun ruwansu .ahankali ta juya ta koma office tare da jan kujera ta zauna jiki a matukar sanyaye can ta kasa hakuri ta kalli yusura “yusura wai meke faruwa ne yau ?zakice bakisan abinda ke faruwa ba ?ta jiyo muryar sultana wacce ke tsaye abayanta rungume da hannuwa nta a qirji,shiru maryama tai tana tunanin abinda tayi kafin ahankali ta juyo tana kallon sultana fuskarta d’auke da tarin mamaki.”
ahankali ta mike ta isa inda sultana take ta riko hannunta cikin nata zuciyarta na wani irin tsinkewa inda sultana tai saurin zame hannunta cikin nata tabi hannunta da kallo “naji kince wani abu kuma naga kowa yaki kulani ko zaki taimaka ki fad’a min abinda nayi ?”rashin tarbiyar da kika saba yi a boye ne ya fito fili yau kowa yasan wacce ke” gaban maryama ya bada wani irin dum da wani irin tsoro take kallon sultana “me kike nufi dani sultuna?tai maganar muryarta na rawa sultana ta jefeta da wani mugun kallo “ai bakiyi tunanin asirinki zai tono ba suma sauran abokan aikinki basuyi tunanin haka kike ba dan sun kasa yarda sai da suka ga zahiri sannan suka san wacece Ke jikinta ya sake daukar rawa “dan girman allah sultana ki fad’a min me nayi dan ni dai bansan nayi wani laifi mai muni ba amman dan allah ki taimaka ki fad’a min abinda nayi wannan karon kam har idanunta sun ciko da ruwa hawye cike da gadara sultana ta ciro wayarta ta nunawa maryama “.
mutuwar tsaye maryama tayi sakamakon ganin hotonta ita da mr ata rungume da juna cikin wani irin yanayi “gashin nan kiga irin karuwanci da kike a boye sul..”sultana a ina kika samu wannnan hoton .”nima tura min akayi da wata number “wa ya tura miki ?nima bansan ko waye ba kuma kowa dake cikin office din nan an tura masa kenan kowa yana dashi kema ki duba wayarki zaki gani “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun da sauri maryama ta mikawa sultana wayarta ta juya da sauri ta isa inda jakarta take ajiye ta bude ta ciro wayarta ta kunna data kai tsaye WhatsApp dinta ta shiga inda messgees suka dinga shigowa jikinta na karkarwa ta shiga duba sakannin ko zata ci karo da mugun abun data gani wani number ta gani babu suna ta shiga nan taci karo da hotunan”waye yayi mana wannna hoto ?”
”muma bamu san wanda ya daukeku hoton ba amman dai Kinsan dole idan kana yin abu mara kyau wata rana sai allah ya tona maka asiri gaban maryama ya sake bada rasss yan office din sun kasa yarda cewar kece ni kuma na tabba tarwa yan office din nan kice dan wadan nan hotunan basuyi kama da had’awa akayi ba Sul .”sultana“ sai kuma tai shiru ta kasa cewa komai kema kin mamakin yarda asirinki ya tono ko ?”sul..” sultana !ai kafin ta cigaba da magana sultana ta juya ta bar office din da sauri “ya rab garin yaya hakan ta kasance ta fad’a tare da dafe goshinta cikin tsananin tashin hankali cike da zafin zuciya ta dunkule hannunta tana son tono wani abu .”bata san sanda wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata ba .”
Sultana na fita ta kira aunty abida “aunty baki ga yadda hankalinta ya tashi ba ai kad’an ta gani tabbas kuwa dan wannna hoton na maryama da adam duk sai na yad’asa a social media kinsan har aunty’s dinsa na turawa uhm ai wallahi sai na bashi mamaki nasan sai yayi haukan neman wanda yayi masa wannna sharrin sai dai bazai sani ba tana magana tana juya bayanta wannna haka ne amman kafin ki yadashi ki barshi iya tsakanin ma’akata da yanuwansa ko yanzu zata fuskanci tsana mai tsanani daga garesu sauran aikin ki bar min ni zan qarasa nasan adam dole zai tsaneta kuma idan akwai wani abu acikin zuciyarsa akanta dole zai hakura wallahi aunty sai kinga kallon tsanar da ma’akatan office dinmu suke wa professional maryama yau ta qarasa maganar tana murmushin farinciki “ai tunda taso shiga rayuwamu tofa ta saka kanta cikin tsaka mai wuya kafin mutuwarta dan ba iya ma’akatan zamu tsaya ba har duniya sai sun san halin da tantiriya irinta take ciki a wajen aiki sultana ta sake washe baki kina jina sultana ?ina jinki aunty” Kiyi taka tsantsna kada a gano shirinmu ne baki da matsala aunty Kinsan irin farinciki da nake ciki kuwa ni nama fi son hotunan su isa gidansu kamar anyi an gama dan Allah aunty kiyi duk yadda zakiyi ya aureni nan kusa kafin ya auri wata dan jikina yana bani zai auri wata ne bani ba “babu wacce zai sake aure dan ko wacan shegiyar yarinyar daya aura rashin baki kusa ne yasa ya auresa ,ki kwantar da hankalinki ko da tsiya koda arziki sai kin auresa muddin ina raye ke ko zanyi yawo tsirara sai adam ya zamo mallakinki yanzu haka akwia wani malami daakayi min maganrsa matsa larsa shi sai ya kwanta da mace kafin yayi aiki ,naga bazan iya bari wani katon banza ya kusanceki ba dan haka nace a samo min mai dama dama .”
“ gaky aunty a nemo wani dan bazan iya yarda wani malamin can ya ta’ba min jiki ba bare har ta kai ga sex ta qarasa maganar tana jan tsaki.”
bangaren maryama kuwa cikin tsannin tashin hankali tace “na shiga uku ta soma kuka tana zariya tabbas tasan itace da mr ata to waye wanda yayi mana hoton ?tayiwa kanta tambayar da bata da mai bata amsa to yanzu menene riban wanda ya daukesu wadan nan hotuna ?cikin tsananin tashin hankali ta koma gefe ta rike kugunta tana mai jin bakinciki tana magana hawaye na zubo mata ta qarasa ta d’auki pencil ta tura cikin bakinta ta cigaba da zariya kafin ahankali ta koma ta jingina jikinta da bango bata an kara ba sai gani tayi an miko mata cup din pencil din gbdy wanda ke d’auke da tarin pencil mai yawa take ta dago idanunta dake cike da ruwan hawaye tana dubansa “tunda kina ra’ayin cin pencil ga qari na kawo miki ki cigaba da ci har ki koshi “ta tsura masa ido tana goge hawayenta tare da cewa “no sir bana bukata !”ta qarasa maganar tare karbar cup din pencil ta ajiye da qarfi akan table wanda yasa abokan aikinta sake maida hankullansu garesu “da alamun fa shi wannan mutumin bai san halin da’ake ciki ba ?maryama ta fad’a akasan ranta tana duban abokan aikinta da suka zuba masu ido “ban san dadin me kike ji acikin cin pencil ba da kullum yana cikin bakinki “tai shiru bata ce masa komai ba sai ma sunkuyar da kanta tayi “am talking to you !”ta d’ago kanta da sauri tana cewa “me kace sir ?matsota yayi yana cewa “meke damunki mryam!?kullum kuka kuka bakya gajiya da kuka?shiru tayi ta kasa cewa komai sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin tashin hankali ,ganin taki yin magana ya sauke numfashi tare lumshe idanunshi ya juya ya fita adaidai lokacin da take qoqarin yi masa bayani ya kiran sunan some !tace yes sir ta bishi zuwa office “maryama tai shiru tana dubansa tare da madam some tana zance zuci “ya kamata kije kiyi masa bayani abinda ke faruwa dan da alamun bai san abinda Ke faruwa ba cike da tsananin tashin hankali ta fito .”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 40
Mr ATA yana tsaye tare da madam some inda take masa bayani tare da nuna masa wani file da zai saka hannunsa maryama ta shiga office din a firgice hannunta rike da waya.”cikin tsananin tashin hankali ta qaraso inda yake ta nuna masa hotunansu da’aka tura mata.”Cikin wani irin yanayi wanda kwata kwata ba’a ta’ba ganinsa ciki ba yake kallon hotunansu tare da maryama ,”ba iya ni kad’ai aka turawa hotunan ba.”gabad’aya duk wani dake aiki a wannan bangaren an tura masa.” ta qarasa maganar tamkar mai shirin zarewa .” a sukwane ya maida kallonsa ga madam some yana cewa is that true ?! yayi maganar tamkar mai koyan magana .”a d’an gigice tace “ye ..yes sir!” “amman mai yasa tunda na shigo baki sanar dani ba ?tayi shiru zuciyarta cike da tsananin tsoro da fargaba “why !”ya fad’a a hassale yana mata wani irin duba mai hargitsa kayan ciki .”amm umm no I mean ..”
“You mean what ?”what’s the meaning of all this ?ya fad’a yana mai watsa mata kallon banza yayinda maryama ta sake shiga tashin hankali “ni yanzu ya za’ayi a goge hotunan nan a wayar kowa dan wannan hotunan zai iya zama barazana ga rayuwata sannan zai iya zama ‘batad’anci ne gareni .”ta fad’a tana goge hawayenta “karki damu mutane please .”!“kina magana akan ‘batad’anci ni bakya tunanin nawa mutun ci? yayi maganar yana zare mata ido kafin ahankali ya d’auke kwayar idanunshi akanta ya soma taku cikin Isa da kasaita yana hura hanci “ni kaina nasani saboda ni mace ce mutane zasuyi tayi dani sannan mutuncina zai zube a idanun mutane mutane zasu dinga min kallon kaskanci “ inna lillahi ni maryama naga ta kaina wace irin maseefa ce na tsinci kaina ciki yau ?”dogon tsaki yaja tare da tsayawa cak yana fuskatarta .”
tsumammun idanunshi ya zuba mata yana cewa “amman waye ya d’auke mu wad’an nan hotunan ?.”
Muryar maryama da jikinta suna rawa tace “ni..”nima bansani ba dan allah ka taimakeni ka taimaki rayuwata kayi wani abu akai kar sunana ya ‘baci a idanun duniya “wani tsaki ya sake ja yana mata kallon ta shiga hankalinta “ some ! yes sir “
“waye ya turo miki hotunan “. Madam some tayi shiru tana kallonsa tare da nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sauya cikin kankanin lokacin tamkar bada son ranshi komai ya faru ba .”“waye wanda ya turo maku hotunan?”ya sake tambayarta a karo na biyu “lallai ina son nasani.”muryarta na rawa tace“ I don’t know the person sir an dai yi amfani da wata number ce .”“okay zan san abun yi amman irin abu haka ya faru kiyi shiru kina kallona ki kasa ce min komai ,abinda ya faru ba wai ya dameni bane amman lallai ina son nasan wanda yake min shishigi acikin rayuwata.”haka ne sir kuma na fahimceka amman maryama ..“kinga ni karki kira sunana ni dai nasan Kinsan komai kawai kiyi duk yadda zakiyi a goge hotunan akan wayar kowa ..”
“Nasan komai fa kika ce ?”maryama tayi shiru ta rasa me zata ce dan sai yanzu ta fahimci ba abinda ya kamata ta fad’a mata kenan ba .”
Mr ata yayi taku biyu ya isa inda maryama take tsaye cikin tsananin damuwa da tashin hankali “kina jina maryama ki natsu zan san abinda zanyi akai kisani ba iya mutuncinki kad’ai ake qoqarin zubarwa ba har da mutuncina ake son zubarwa “.“exactly sir exactly sir”. inji cewar madam some “ni dai babu ruwana da wani mutuncinka ni dai nawa mutuncin nasani kuma ina matukar son shi dan shine silar da mutane dayawa suke sona da ganin mutuncina idan hotunan nan suka fita mai zance ?”me zan cewa mahaifi yata?” me zan cewa umma da habib?” ki yiwa mutane shiru ana .”yayi maganar a matuqar tsawace yana dubanta “saboda mai zanyi shiru ?”ina da ‘yancin da zanyi magana tunda an cuceni an cuci rayuwata”kai nmj ne nifa? duk wanda yaga wad’an nan hotunan bazai sake ganina da kima ba a qarshe ma bazan sake auruwa ba” so what idan kin kasa auruwa dole ne sai wani ya aureki? yayi mata tambayar yana kallonta a d’age “ko ba dole bane mutuncina fa ?itama tayi masa tamabayar tana dubansa da shayayyun idanunta wad’an da suka canza kala tsabar zubar hawaye .”
wasu hawaye yaga suna turereniyar zubawa daga kwarnin idanunta daga inda yake tsaye ya tsura mata ido yana jin yada sautin kukanta ke ratsa kunnuwansa “.“dan Allah sir kayi hakuri ka daina biyewa yarinyar nan “.“sorry may I coming aka fad’a daga bakin kofar shigowa“yes coming! d’aya daga cikin ma’aikatan ne” ma ga wata akan layi tana son magana dake “okay kaje kace gani nan zuwa “okay ma ya fad’a tare da juya wa ,numfashi madam some ta sauke tana dubansa kafin ahankali tace “dan allah gaba d’ayanku kuyi hakuri na wani lokaci yanzu zanje na amsa kira zan dawo muyi magana akan wannan matsalar kuma in sha allahu zamu nemi mafuta akan matsalar “tana gama fad’ar haka ta juya ta fice daga office din cikin sauri .tana fita maryama
ta sake fashewa da wani rikitaccen kuka tana dafe goshinta .”gabad’aya ta rasa abinda zatai, ta rasa meke mata dadi tana jin idan ba kukan tayi ba bata san me zatai ba dan cuta tasan an mata an cuceta an cuci rayuwarta ana son ‘bata mata suna ta qarfi da yaji. sosai take kuka har da shesheka .”ta rasa waye yake son ‘bata mata suna da rayuwarta a iya saninta bata gaba da kowa abinda yake gabanta shi take yi ,bata da matsala da kowa tana qoqarin zama da kowa lafiya “to mai yasa za’ayi mata haka ?” kuka maryama take sosai .”
wani irin tausayinta ne ya dinga ratsa sansar jikinsa har tsigar jikinsa na mikewa,bai san me yasa take d’aukar abu da zafi haka ba,shi a ganinsa wannan ba wata matsala bace ahankali zai gano wanda ke da hannu ciki .”taku biyu ya qara zuwa inda take tsaye tana risgar kuka ya kai hannu zai dafa kafad’arta tayi saurin zamewa tana masa wani irin mugun kallo mai d’auke da gargadi.”cak ya tsaida hannunsa tamkar wanda aka dasa yana kallon cikin kwayar idanunta dake tsiyayar da ruwan hawaye .”cike da sanyin jiki ta samu waje ta zauna ta kwantar da kanta Akan table din dake gabanta tana cigaba da rera kuka mai tsuma zuciya yayinda mr ata yake tsaye yana kallonta jikinsa yayi matukar yin sanyi.”
Ahankali madam some tace “hello good morning !”daga can bangaren aka amsa mata madam some tace “ko zan iya sani dawa nake magana ?”okay okay!! ta fad’a tana gyara tsayuwarta babu matsala akwai su a qasa nuna da desing’s masu matukar kyau da d’aukar hankali karki damu sai dai kuma idan kina da desing dinki da kike so wannan ma babu wata damuwa zan tura miki sako nan da awa d’aya .”“okay thank you “ta fad’a tare da ajiye kan wayar ta juya ko cikakken taku uku batayi ba wayar ta sake d’aukar qara ta dawo da sauri a tunaninta ko abokiyar kasuwancinta ce amman sai taga number landline din mami ne dan haka da sauri ta d’aga cike da girma mawa ta gaisheta “good mrning ma!sannan ta qara da cewa “momy kina son magana da mr ata ne ?”no no! dake nake son yin magana “ni kuma mumy?”madam some tai tambayar cike da tashin hankali “eh !”.“okay ma ina jinki !”ina son nayi magana dake ne amman ba anan ba idan bakya wani aiki yanzu kizo gida kar kuma ki bari adamcy yasan nace kizo don’t tell him anything tai shiru tana sauraronta har ta dasa aya madam some tace”okay