Showing 78001 words to 81000 words out of 182919 words

Chapter 27 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

375

daga cikin wahalar dana sha akanki maryama dan kukan dadi kike yi a yanzu tunda kina dani .”



Office din ya d’auki shiru bakajin motsin komai sai na saukar numfashinsu wanda ke sake haddasawa zuciyar maryama shiga tashin hankali yayinda shi kuma zuciyarsa ke narkewa akanta gabad’aya marayama a matukar rikice take dan bata qaunar kusancinsu haka, dan ma Allah ya taiamketa har zuwa lokacin sauran abonkan aikinta basu qaraso ba
batayi tsammanin zai yi magana dan a tunaninta a haka zasu tabbata sai kawai ta jiyo muryarsa a kasalance “menene dalilinki na barin office jiya ?”kamar tace masa takurawarsa ce tayi yawa sai ta share tace “am very sorry sir jiya kaina ke ciwo “tana fad’ar hk ya sakar mata hannu yana cewa” I hate lies “ya fad’a yana jan tsaki .”nan take ta diririce “shi kuma wayarki me yasa kika kashe ?“saboda matsalar wuta ne “ta bashi amsa da haka bakinsa ya ta’be “daman yaushe zaa samu natsuwa a wannan banzar unguwar taku, kiyi qoqari kiyi aure ki bar wannan banzar unguwar “kamar tace masa unguwarsu ba banza bace dan duk lalacewarta tayi wa rayuwarta amafani ,kuma ta rufawa ahlinta asiri na tsawon shekaru amamn saboda alqawarin data d’aukarwa kanta na bazata sake yin abinda zai hassalashi ba saboda abincinta dake qarqaahinsa yasa ta sauke nunfashi kawai tana jin quna aranta dan taji zafin mgnrsa amman bata da zabin daya wuce tayi shiru .”



"new design dinki sunyi ready "?new desing kuma ?ta tambayesa zuciyarta na rawa dan ta manta da wani batunsa Kallon da ya dauketa dashi ne yasa tayi saurin cewa "yes ready ready sir” good kije ki kawo min yanzu na gani yana gama fadar haka ya juya ya wuceta ya fita daga office din ta juya a natse tana kallon bayansa tana sauke wani naunayen ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta “kai wannan mutumin zai iya kashe mutun da ransa .”
ahankali ahankali take d’aga qafafunta tana kallon tafiyarsa, tafiyarsa ma abun burgewa ne har sanda ya shiga wani office dinsa yana shiga ya d’auki wani file green ya fito ya sake shiga office din daya baro ya zauna ya d’aura kafarsa d’aya akan d’aya .”
tana fito da desing’s din tana mita “wannan mutumin mugun dan rainin wayo ne cewa yayi babu ruwansa da wani new designs din da zaayi yanzu kuma yazo yana tmby dana yagasu dana shiga uku ko kuma da nice nayi masa magana da yanzu yau ni da maseefa, takardu ta rike ta fito zuwa office dinsa ta nemi izinin shiga ya bata izini ta shiga ta qarasa daf dashi ta tsaya tana dubansa yana duba file .”can ya ajiye sakamakon kiran wayar office dinsa da akayi ya amsa kiran.”


ta cigaba da tsayuwa can ta duba agogon hannunta byn ya gama ya ajiye wayar yana dan waigo inda take fuskarta ahade da alamun jin haushi muryarta a dake tace” Mr ATA sir !” ya sake tsura mata idanu alamun yana saurarenta”a sanina baka zuwa office da wuri amman me yasa jiya da yau kazo da wuri ?a d’an tsorace yace “why are you asking me foolish question?ya qarasa fad’a tsawace yana mika mata hannunsa alamun ta bashi desing din ya gani zuciyarta a dake ta mika masa a hankali ya kar’ba ya fara budewa yana kallo zanen mace ce sanye da doguwar riga da abun hannu da sarkar wuya yayinda take tsaye a gefensa tana ciza harshenta ya dan waigo kadan ya kalleta ya dauke idanunshi ya sake maidawa kan desing din hannunsa.” byn second goma ya ajiye ya dauki dayan takardar zane zane ne masu matukar kyau da daukar hankali  ta zana ta sake kai dubanta ga agogon hannun
“wannan dabia nata na mugun bashi haushi ita da bata bawa lokaci mahimanci sai yaransa uwar me take dubawa a agogo ,yaja tsaki yana shafa sajen fuskarsa sannan ya dauki pencil ya daura akan takardar zanen tana ganin hk tayi saurin cewa"sir what are you doing?


kallon da yayi mata yasa tayi kasa da muryarta sosai "sir idan akwai abinda bai yi maka ba kamata yayi kabari na gyara da kaina ba sai ka wahalar da kanka ba ,ta fad'a tana kokarin kwace takardar ya hana akwai abinda bai min ba a desing din kuma zan gyara any problem?"No sir !ta fad'a ba dan ranta yaso ba can tace “amman shekaranjiya da mukayi magana akan plan dinmu kin amincewa kayi amman kuma me yasa yau kayi mgn akanshi "bana son yin mgn akan abinda ya wuce yanzu zamuyi aiki ne ko kuwa tmby zaki kasheni daahi ?numfashi ta sauke tace “ muyi aiki “ta fad'a am tana d’auke kanta .”
"your design are very nice but there's something mistake kina bukatar taimakon irinmu kafin ki zama expect, nan take ya shiga mata bayanin abinda zatai tasa hannunta acikin bakinta ta dan ciza tana lumshe idanuwa wanda kadan ya rage mr ATA bai sume ba gabadaya yanayinsa ya sauya hatta tsigar jikinsa sun tashi, allah dai ya tamaikesa sanye yake da suit da babu abinda zai hana bata gani ba ."



Yadda yake mata bayani itama batayi sanya agwiwa ba ta shiga yi masa bayani tana juya hannuta da kwayar idanunta ta a qarshe ta saka yatsan hannunta cikin bakinta duk sanda tayi haka sai yaji wani iri yerrr ajikinsa kuma ya lura dabiar ce haka ya mike tsaye daga mazauninsa ya qarasa inda wasu manya takardun zane suke ,ya dauki guda daya ya bude yana dubawa har ya taho gareta ya tsaya kusa daita yana nuna mata kokuwa tashiga yi da numfashinta dan kamshin turarensa mai tsuma zuciya da gangar jiki ne irin turaren da nmj yayi amfani dashi yazo gareka babu tantama zaka iya sakar masa ragamar rayuwarka ,ta dan kallesa tana yatsina fuska bayan wani lokaci ya rufe ya ajiye ya amshi takardar hannunta ya bude yna nuna mata bayanin abinda zatai wanda zai sake sakawa ta dauki hankalin client yana gamawa ya nuna mata kofar fita da hannusa sannan ya koma mazauninsa.”


ta fara tafiya a hankali tana cigaba da kallon takardar hannunta yayinda aranta tana sake mamakinsa wani irin juyayyen hali garesa idan mutun bai da tsananin hakuri bazai ta’ba jin dadin zama dashi “Ko me ta tuna sai ta juya ahankali nan take kwayar idanunsu ya tsarke cikin juna dan shima bayanta yake kallo dayar takadarta dake kan table dinsa ta nuna masa ,ya dauka ya mika mata ta sake juyawa shi kuma ya gyara zama yana cigaba da kallon yadda take bada step ."bayan kmr minti goma ta sake shigowa "sir dan allah ko zaka taimaka min ina son nayi aiki amman kayan aikin duk suna cikin wancan durowa din nayi nayi na bude na kasa ko zaka taimaka min dan Allah ?shiru yayi yaki cewa komai "please sir !"okay ya mike yayi gaba ta biyo bayansa har zuwa office dinsu ta nuna masa durowan da hannunta ya qarasa cike da kwarin gwiwa yaja sai dai ya kasa budewa.”


ya waigo ya kalleta ta hade fuska tamau tmkr wacce bata ta’ba dariya ba tana ciza harshenta dan daman tana sane ta bashi aiki ,shi kullum bashi da aiki sai zama Kan kujera yana amsa waya da zarar kayi mistake ya kiraka da nonsense,stupid ,ko sai gama shan wahala kayi aiki yace bai masa ba .”ya sake ja still the same  ya saka iya karfinsa ai ko yana já durowar ya bude shi kum yayi baya zai fado kanta itama tayi baya luuuuu yasa duka hannuwansa yayi mata riko mai kyau batare daya sani ba hannuta ya sauka akan daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da mahaukacin qarfi shima hannunsa daya ya rike tsintsiyar hannunta dake rike da zane dayan hannunsa kuma ya zagaye kungunta dashi .”


ido cikin ido suke kallon juna yana kallonta cike da tsananin soyayya yayinda ita kuma abun ya zame mata bakon alamari dan tunda take hakan bai ta faruwa daita ba, hasalima kullum cikin hijab da nikaf take shine silar canza mata rayuwa sun dade tsaye suna kallon juna yana kwakume daita jin saukar tafin hannunsa a gefen fuskarta yasa ta dawo haiyacinta da sauri ta zare jikinta tana juya masa baya tare da rungume takardar aqirjinta tana jin wani irin kasala ajikinta numfashi ya sauke yana kallon bayanta kafin ahankali ya tura hannunwansa duka cikin aljihunsa muryarta a matukar sanyaye ta furta "am sorry sir ?babu abinda yaji hakan ma dadi yayi masa .”


ta juyo ta sake bude bakinta zata sake furta masa am sorry "ki zauna Kiyi aiki dake gabanki “ ya fad'a yana juyawa ta lumshe idanunta, ta zauna masa dariyar mugunta ai taso ya kasa ne ,tana cikin aiki ya sake shigowa hannunsa rike da cup biyu ya ajiye mata a gabanta ta dago ta kallesa a natse da shayayyun idanunta "coffe !
"Thanks “. kawai ta fad’a atakaice taso tace masa bata sha sai dai tayi shiru zuciyarta cike da mamakinsa yau din kamar bashi ba ta cigaba da aikinta a natse ya dinga tafiya acikin office din yana kurban coffe yana lumshe idanun har zai wuce yaga bata da alamun shan coffe "me yasa bazaki sha coffe ba ? ya fad’a domin a tunaninsa tunda tazo da sanyin safiyar nan ba lallai ta karya ba sai data yatsina fuska tace “ bani da raayin shan abu a waje bare abun hannun nmj ba kuma dan rashin  yarda bane raayi ne kuma ma I don't like drinking coffee ai kamar na fad’a maka last time .”


shiru yayi yana kallon qaramin bakinta komai nata dabam ne da sauran mata ya koma bakin kofa ya tsaya yana rike da kugunsa yana kallonta ta maseefar burgesa "maryama !ya kira sunanta cikin wata irin murya mai kashe jiki” yes sir !” ta amsa ko zan iya sakaki wani aiki ?why not sir “ta fad'a ya ajiye cup din hannuna yace biyoni ya fita zuwa  office dinsa ta biyosa  ya mika mata wani jaka mai shegen kyau "ta karba ta bude taga kaya ta tsaya tana dubansa da jakar hannunta "ki bude ki gani?”


batai mutsu ba ta bude ta fito da kayan ciki doguwar riga ce wacce akayiwa aiki da stone tun daga sama har kasa "ko zaki gwada naga yadda zai yi ajikinki ?da sauri ta tsura masa ido tana kallonsa da mamaki"
Muryarta cike da tashin hankali tace “but sir !"Kar dakikiyar kwalkwaluwarki ta kawo miki wani abu matata na siyawa "sir tunda matarka ka siyawa ai kamata yayi ka kai ma.."Ke nake son ki gwada ajikinki na gani so kije kiyi abinda na sakaki ga daki can ki shaga karki bata min lokaci jiki sanyaye ta wuce tana yatsina face ta murda handle ta shiga .
"shi kuma ya dauki cup din coffee dinsa ya shiga sha yana kai kawo .”


Byn wasu mintuna ta bude kofar ta tsaya batare data fito sosai ba ta hade hannunwanta waje daya tana jin faduwar gaba kafin daga baya ta soma taku a hankali ya ajiye cup din hannunsa tun daga sama ya dauki kallonta har kasanta ahankali ya zuba hannuwansa cikin aljihunsa yana cigaba da kallonta kafin a natse ya qaraso ya  tsaya abayanta yana sauke numfashi sannan ya cire hannunsa daya acikin aljihunsa ya ta'ba kayan a hannunsa yana dubawa can taga ya dauki takarda yana rubuce rubuce yana mata bayani ina bukatar zanen mace da irin wannan kayan har komai da komai exactly ta tsura masa ido tana masa wani irin kallo "ko bazakiyi ba ?.


Jikinta a sanyaye tace “zanyi!” só sai kije ki fara ya gbdy ta kasa magana kai kawai take gyada masa dan yanayin da take ji ajikinta babu sauki yanayin da bata ta’ba jin irinsa bane ,ya sake yin taku biyu yayi kusa daita sosai  ya kai kansa daidai saitin wuyanta yana sauke mata numfashinsa a wuya ya motsa bakinsa a hankali "mar ..."sautin muryar sultana ta katse masa hanzari ..."cak ta tsaya  mamaki qarara kwance akan fuskarta tana dubansu , jikin maryam yayi sanyi sakamakon matsananciyar kunyar data rufeta, ta dan saci kallon sultana ta kasan idanunta taga irin  kallon tsanar da take mata  mai cike da tsantsar kishi ."



mr ATA bai  kalli inda sultana take tsaye tana kallonsu da mamaki ba ya bawa maryam umarnin kije ki cire kayan  "good morning sir “! amman me Ke faruwa haka ?ya lumshe mata tsumammun idsnunshi yana sauke numfashi sai maryama ce tayi mata bayani dan shi bashi da lokacinta "you could have called me ya Adam I can do more than this for you ,ita nayi raayi ta min any problem?amman me yasa sai ita bayan gani dana kasance jininka ?ya ma akayi kuka kasance tare adaidai wannan lokacin ko tare kuka zo ne? gaban maryama ta rikice ta dinga jin wani irin mummunar fad'uwa gaba yayinda jikinta ya dauki rawa ta kasa motsi bare taje ta cire kayan jikinta shi kuwa wani irin mugun kallo yayi ma sultana sannan ya wuceta zuwa mazauninsa batare daya ce mata komai ba dan bata isa ba.”


da sauri maryama ta shiga ta cire kayan ta fito zuwa office dinsa wanda zuwa lokacin mutane sun fara zuwa "good morning!!!ta furta tana zama sannan ta kallesu daya byn daya mr ATA fa ya amince da new desings din mu "me Kike qoqarin kice ya amince maryama cewar surayya maryama ta gyada masu kyau tana lumshe idanunta suna cikin haka sectray ta shigo "maryama !yes ma !gabadaya desings dinku sun kammala dan zaa fara shirin aiki akansa ?eh !ni dai nawa ya kammala har na shiga sabon aiki na sauran ne dai sauran kadan su qarasa madam some ta juya maryama tace “excuse me ma!” ta tsaya dan Allah idan zaa dinka kayan ayi kamar yadda na zana "okay ta fad'a tare da juyawa ta fita gabadaya kowa ya fuskanci aikinsa ."


******


Suna zaune mr ata ya shigo yana magana da some yayinda gabadayansu suna tsaye cike da girmamawa yana cikin magana wayar sultana ta dauki qara ya juyo ahankali yana mata kallon banza irin kallon da yake mata yasa taji jikinta ya dauki rawa qoqarin kashe wayar ta fara dan a dokarsa baa kiran mutun idan yana magana sannan mutun bai isa ya amsa kira ba ,ta dan saci kallonsa kamar yadda maryama tayi ,sultana ta aikata laifin amman gabadayansu zuciyarsu rawa take kallo daya zaka masu ka fahimci haka muryarta a hankali tace  sorry sir "lumshe lumtsatsun idanunshi yayi ya cigaba da magana zamuyi qoqarin mu gabatar da new desings din nan in sha allahu idan kunci saa zaa da.. .."wani kiran ya sake shigowa ya katse masa mgn wannan karon qarara ake iya hango bacin ransa yaji kamar ya kifa mata mari ita kuwa idanunta ta kai ga kallon screen din wayar sunan Aunty abida tagani yana yawo numfashi ta sauke "ko me zan mata adaidai wannan lokacin "me Ke damun tunaninki ne sultana “?me zai hana kisa wayar a silet me yasa bakya yin abinda dan Adam yake ?”kalli maryama kwararriya ce a gurin iya zane amman kin ta'ba ganin wayarta na qara . koda yaushe wayarta na silet nan take maryama ta sha jinin jikinta ta fara zazzare idanuwa” to be your last warning nonsense girl kawai da batasan komai ba sai zallar shirme “yana gama fadar haka Ya juya ya koma office dinsa yana fita maryama ta dubi surayya da sauran matan tace “kuyi ku qarasa aikinku kafin ya sake shigowa ."



Sultana na fita ta kira Aunty abida tana dauka ta hau magana cikin zafin rai  "me yasa kika daukar wayata ? taya zan dauka ina tare da ya Adam sister idan kinga abinda yayi min a gaban abokan aikina sai kin tausaya min” what akan me kenan “?nan ta shiga koro mata duk abinda ake ciki da new desings din da'a zaa gabatar batare da sanin kamfani ba na fad’awa sultan amman ban san me ye shirinsa ba dan har yanzu bai zo office ba bare naji yadda sukai da baba qarami .kice wannan yarinyar ta samu dama haka lallai akwai sabon aiki agabanmu shiyasa banason ayi aikin ba kuma wai dan banason cigaba yaya adam bane idan akayi nasara maryama ce nasara saboda ita ta kawo tsarin kinga dole zai Bata mahimanci arayuwarsa .”


“naji bari na kira Ibarahim naji ko yasan abinda Ke tafiya suna gama wayar ta kira yaya Ibrahim byn ya dauka tace "ka natsu da kyau akwai abinda zan fad'a maka very important sultana ta fad'a min tun last week a office anyi shirin gabatar da new desings batare da sanin kamfani ba” what”! ya furta da karfi yana mikewa tsaye cike da bacin rai me kike qoqarin fad'a min?” abinda muke gabatarwa duk qarshen wata me yasa zai shirya haka byn shine ya karfafa wannan dokar” wannan ba shirinsa bane shirin wannan tsinanniyar sabuwar maaikaciyar ce maryam ne sunanta ko maryama shiyasa nace nayi sauri na fad'a maka kayi duk yadda zakayi hakan bai tabbata ba ai wannan maganar dole sai baba yaji amman bari na bincika na gano gaskiya mgn yay discounting din kira.”



Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 23


mr ata kam tunda ya gama yiwa ma'aikatansa bayani tsabgar gabansa kawai yake ya manta da yayiwa wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login