Showing 87001 words to 90000 words out of 182919 words

Chapter 30 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

363

" bai ce daita uhm ba bare uhm uhm kawai sai ji tayi ya riko tsintsiyar hannunta da qarfin ya soma tafiya daita, nan take ta turje amman yaki sakar mata hannu dole tasa tace "ka sakar min hannu nayi tafiya da kaina ."yana jinta yayi mata banza tamkar ba dashi take magana ba ."
"acikin unguwarmu muke idan wani ya ganmu haka wata fassara daban za'a mana "ta fad'a tana 'dora hanunta a saman shi a qoqarinta nason zare hannunta,  shareta yayi batare da yace mata kala ba sai ma sake damke tsintsiyar hannunta yayi ya cigaba da tafiya "shi ina ruwansa da wasu , ita din tashi ce kuma kome zaa ce akanta zuciyarsa bazata d'auka ba ."




      "jin yaki sakar mata hannu yasa jikinta ya fara rawa dan tasan tunda ta bari ya tunzura sai abinda yaga dama zai yi." alhankali muryarta ta fito "please sir kayi hakuri wallahi bazan sake jayayya da kai ba ka sakar min hannu"dogon tsaki yaja yace "wannan kuma problem dinki ne ".bai tsaya daita akoina ba sai daf da bakin get din gidansu sai dai yaki sakar mata hannu ,inda zuciyarta ta shiga tashin hankali mai tsanani da jin tsoron abinda zai biyo baya, dan bazata  so wani acikin 'yan unguwa ya fito ya gansu haka, bare wani daga cikin 'yan gidan su. shi kuwa tsura mata ido yayi acikin duhun yana kallonta yana jin kamar ya janyota jikinsa ya rungume tsam tsam!!
maryama bata gama tunaninta ba sai ga fitowar husna diyar aunty hassana daga cikin gida tana waya tana waige waige da alamun wani ta fito nema jin sautin muryarta yasa maryama ta d'an juyo cike da tsoro ,ganin husna yasa wani bakinciki ya tokare mata kahon zuciya wanda yasa hawaye zuba daga idanunta ,da sauri ta dawo da kallonta garesa muryarta can kasa cike da shagwa'ba tace "ka gani ko ."



Shima muryarsa a kasalance yace "me nã gani ?
"cousing dina ce ta fito yanzu "so what ina ruwana da fitowarta ?ko gani tayi ina miki wani abu ? "ba zaka gane abinda nake jin tsoro ba, abinda zai je yazo nake gudu ".tayi maganar muryarta cike da matsanancin tsoro "ki ganar dani zan gane "ya fad'a cike da kulawa yana sake motsata so take taja baya saboda bata són kusancinta dashi amman tana gudun husna ta gane itace tsaye a wajen "menene damuwarki a gidan ?yayi maganar cikin wani irin salo "da sauri ta girgiza masa kai tana cewa "no karka damu kawai sakar min hannuna na wuce "ke matsalarki kenan kinsan bana son taurin kai da jayayya bare kafiya amman a dole sai kinyi min "ya qarasa maganar yana hura mata hucin bakinsa a fuskarta da wuyanta sakamakon kusancin da suka samu saurin lumshe idanunta tayi zuciyarta na wani irin tsinkewa ."yayinda husna tayi shiru  tana duban inda suke tsaye sun yi mugun yin kusa da juna wanda bai fi taku d'aya zasu qara jikinsu ya had'e ba . "a fili tace "wacece wannan kamar maryama ?"



"aiko jin haka yasa hankalin maryama yayi matukar tashi tun da take arayuwarta baa ta'ba ganin tasamu kusanci irin haka da wani d'a namiji ba ."ganin husna na qoqarin tahowa inda suke tayi saurin jan hijab dinta ta rufe rabin fuskarta iya bakinta da rabin hancinta ne kawai a waje tun kafin ta qaraso ta ganta taje ta bazawa aunty hasana ita kuma tasamu abun zaginta dashi ."husna na gama qarasowa kusa dasu ta tsaya tana cewa "maryama !" ko ba maryama bace ?" maryama na jinta amman tayi mata banza a zuwan ba ita bace ,shi kam mr ata kallon d'aya yayi mata ya d'auke kanshi ya cigaba da kallon princess dinsa ." ganin da husna tayi ba'a kulata ba gashi wanda take waya dashi yana sheida mata inda zata zo ta samesa yasa ta juya tana taku tana cigaba da wayarta sai dai zuciyarta cike take da wasi wasi akan maryama ce ko kuma wata ce daban tsaye a kofar gidansu amman wani bangaren na zuciyarta yafi amince mata da maryama ce."



sai sanda mr ata yaga dama sannan ya sakar ma maryama hannu tana jinta free ta juya ta nufi cikin gidansu da sauri batare data waiwayo ba ,tana shiga bangaren umma ta nufa tana haki bata iske umma ba da alamun tana ciki tana sallah ta zauna akan kujera ta kifa kanta akan hannun kujera kawai sai hawaye ya soma gangaro mata kukan da bataso tayi akan shi shine ya kufuce mata ba dan taso ba dan hakan ne kawai zai iya sanyaya zuciyarta akan wulakancin da yake mata "yana son ya maida mata jiki banza, babu wani shamaki kawai daya so zai riketa, ita kam sam bazata d'auki wannan wulakanci ba gara tun wuri ta takawa abun burki  bazata sake yarda ya dinga ta'bata anyhow ba ,jikinta mai daraja ne ,jiki ne data d'auki tsawon shekaru tana killace abunta bazai yuwu lokaci d'aya yazo ya dinga wasa dashi son ransa ba ,ya hanata saka hijab da nikaf  ta yarda amman jikinta kam tana da rowarsa bana ta'bawa bane nã aure ne, tana kuka tana zancen zuci sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru ta shige d'akinta tun kafin umma ta fito ."



Tsaye mr ata yayi a wajen gidansu maryama tamkar wanda aka dasa tsabar mamakin kansa da yake duk yadda yake son ya boye tarin soyayyarta da qaunarta acikin zuciyarsa abun ya cutura har yau gashi tsananin kishinta da son kare lafiyarta da mutuncinta ya kawo shi kofar gidansu a karo na biyu har sai daya ga shigarta cikin gidansu sannan ya samu natsuwa da kwanciyar ahankali ,yana tsananin qaunarta ita kuma tana tsnanin qaunar waninsa . "
"wasu hawaye masu zafi da ciwo ne sukayi nasarar biyo fuskarsa a lokacin daya tuna tun sanda  ya fara ganinta a mafarkinsa wanda shine asalin lokacin daya fara  jin zazzafar soyayyarta acikin zuciyarsa haka rayuwar take cike da tarin abin mamaki  da fari ya d'auka komai da sauki ake samusa ashe abun ba haka yake ba ,abun ba kamar yadda ya taso bane da duk abinda yace yana so ya zama dole ayi masa, idan kuma babu dole sai an nemoshi a duk inda yake an bashi."



Ahankali mr ata ya d'auke kwayar idanunshi akan kwara'babben get din gidan su maryama ,ya juya cike da sanyin jiki, ya soma tafiya zuciyarsa na sake nitso cikin tafkin  shaukin qauna da tunani  da kyar yake iya d'aga qafafuwansa tamkar wanda bashi da laka haka yake ji a sansar jikinsa inda zuciyarsa ke wani irin bugawa da karfin gaske "wai shine yau acikin irin wannan kwarababbiyar unguwar a karo na biyu ?" a tun tasowarsa idan aka fad'a masa cewar a irin wannan unguwar zuciyarsa zata mace zai karyata wata killa ma sai anyi mugun rigima dashi."
sannan duk tsawon shekaru da yayi yana nemanta bai d'auka daga irin wannan family zata fito ba ,ya d'auka daga gidan mulki ko gidan wani shararren attijira ko d'an siyasa da duniya tasan da zamansa sai gashi zuciyarsa ta tsallake tarin mata bilaadadin masu tarin arziki mulki tattare da boko soyayya tayi wuji wuji dashi ta wullosa cikin wani ahli da ba kowa bane ,bama kowa ne ya sansu ba a iyakar agage ma yayi imani ba kowa ne yasan da zamansu ba ."


a natse ya cigaba da taku yana cigaba da zance zuci still yana jin dinga hawayensa akan kuncinsa shi ba gudun ahlinta yake ko kyamar ahlinta yake ba a'a tsantsar mamaki ne kawai cunkushe a zuciyarsa da tarin iliminsa da tarin dukiyarsa da tarin nasabarsa da tarin nuna isarsa amman Allah ya nuna masa shi din ba kowa bane face bawansa kuma wanda yake qarqashin ikonsa ,ya nuna masa wannan itace  irin kalar qaddarar da zai d'aura masa kuma bai isa ya canzata ko ya gudarwa qaddarar dake biye dashi ba ko akan maryam ya kamata ace  ya fahimta duk yadda ya kai ga kin yarinyar yadda ya dinga gudun aurenta babu irin qiyayyar da bai nunawa yarinyar ba amman a qarshe sai  da allah ya nuna masa shi din bakowa bane ya aura masa ita ya kuma zauna daita  a qarshe ga ciki  "ya rabbi " ya furta a fili alokacin daya tsoma qafarsa d'aya cikin ca'balbali ai bai tsaya dubawa ba dan yasan zuciyarsa bazata d'auki  kallon inda ya sanya qafarsa ba gara ya cigaba da tafiya zai fiyye masa alkhairi da kwanciyar hankali ."



" ya d'auki tsawon shekara shatakwas yana tsnanin sonta shi kad'ai yasan irin wahalar da zuciyarsa ta sha akanta ,babu dare babu rana kullum muradinsa da rokonsa  ya ga ko mai kama daita ne a zahiri  sai gashi allah ya amsa rokonsa ya had'asu a gaske ai duk yadda maryama  take ya amsa koda kuwa zata kasance bata da kowa ,bata da komai bata da galihu kai koda kuwa acikin tsatson bayi ta fito zai 'yantata da ko nawa akace ya maidaita mallakina  take wani bangarensa na zuciyarsa yace "tabbas adam kai din masoyi ne tunda kana sonta a duk yadda take "wallahi ina matukar son maryama ya bawa zuciyarsa amsa da haka .bayan mahaifiyata itace abinda nafi só a kaf duniya yana tafiya yana ciza lip's dinsa yana ganin hanya da kyar kasancewar unguwr nada mugun dubu. naunayen ajiyar zuciya ya sauke yayinda soyayyar maryama ke cigaba da kutime meniya da zuciyarsa da gangar jikinsa qaunar maryama ya dinga bin dukkanin sansar jikinsa ji yake kamar ya zarta duk mazan duniya saa da allah ya kwatota a hannun wani ya dawo masa da farinciki rayuwarsa."



" hakika Allah yana son shi domin daya had'u daita da aurenta da lallai zaayi gagarumin tashin hankali dan ko ta kashe auren ta dawo garesa ko kuma ta kasance mai maza biyu amman bazai ta'ba yarda ya barwa wani ita ba ,amamn dake Allah yana son shi da rahma kuma had'uwarsu tana cikin qaddararsa sai ya kashe masa tsohon mijinta saboda shi ya sameta ."Allah kenan yadda yaso haka zai yi inda yayi parking din motarsa ya qaraso da kyar yana kakkabe qafarsa data fad'a cikin cabalbali ".
Mr ata ya iske tarin samarin unguwar dake zaman banza a bakin titi kamar safiya haka yaga wajen kasancewar zuwa wannan lokacin an kunna street light suna ganinsa duk suka matso suna sara masa a hakan ma basu san ko waye shi ba kawai dai kyawun motar daya zo daita ne yasa sukai masa kyakkyawan zato, bud'e motar yayi ya shiga ya zauna sai daya saka seat belt sannna ya d'auko bandir din yan dubu d'aya d'aya guda uku  yayi warning glass din motar  kad'an ya miko masu yace su raba . nan take ihunsu ya karad'e unguwa wad'an da ya bawa kudin suka shiga bashi hanya suna korar mutane a guje ya figi motar ya hau babban titi yana tunani"yana son dauke maryama daga wannan unguwar amman yana tunanin soyayyarsa ."


"Zai so ya fito mata da zahirinsa amamn kuma jin tsoron tace bata son shi "kai kuwa adam akwai macen da zatace bata sonka ?" Wani bangaren ba zuciyarta ya tambayesa .zata iya cewa bata sona mana tunda zuciyarta da  hankalinta yana kan matacce tunda gashi tna mata maganar aure amamn ita ba wannan maganar bane arainta “akwai tarin abubuwa dayawa agabana wanda aure ne zai zamo last .”kwakwaluwarsa ta tariyo masa maganrta tsaki yaja yana sake ganin aurenta a boye shine kawai mafuta agaresa idan yaso ahankali zai koyar daita yadda zata shi fiyye da wancan mataccen ."qarfe shadaya  na dare da mintuna ashirin ya tako cikin babban parlour'n mami wanda babu motsin komai da kowa acikinsa sai nã makeken tv bango da ac nan dake aiki ,kai tsaye samansa ya nufa yana furzar da hucin iska daga bakinsa yana shiga ya fad'a bedroom dinsa ya fad'a kan makeken gadonsa yana sauke wani wahalallen numfashi."



Yana kwance mami ta shigo har cikin bedroom dinsa ta tsaya akanshi tana qare masa kallo tsab dottin data gani tun daga step har parlour'n kenan a takalminsa ya kwaso ?” to ina yaje ma har ya kai by this time ?shi da matukar yana gari duk tsanani takwas a gida take masa "adamcy !"mami ta kira sunansa ahankali ata ya juyo yana kallonta kafin ya dauke tsumammun idanushin daga cikin idanun maminsa ya yunkura ya tashi ya zauan yana dafe goshinsa da hannunsa daya kusan minti goma mami ta dauka tana kallonsa batare da tayi yunkurin cewa komai ba sai dai yanayinsa take karanta yanayinsa yau tamkar wani mara lafiya tana kallonsa ya gyara zamansa tare da numfasawa ya zare takalmin qafarsa da duk dottin unguwar maryama ne yayi shiru kawai yana kallonsu gabansa na fad’uwa .”
tsawon lokaci mami ta dauka tana dubansa yayinda cikin zafin rai ya kamo lips dinsa na kasa ya soma cizawa da karfi sakamakon hawayen da yaji yana kokarin son zubo masa." wani irin nauyin zuciyarsa tayi "yana ji yadda qirjinsa ke masa zafi da ciwo tamkar an daura masa dutse mai shege nauyi a sama kirjinsa yanayinsa yasa hankalin mami yayi matukar tashi duk abinda kaga ya maida adamcy haka baqaramin abu bane ."



guri mami tasamu nan kusa dashi ta zauna tare da kamo tafin hannushi cikin nata tana mai cigaba da nazarin yanayin daya yake ciki ,ka natsu ka kwantar min da hankalinka adamcy ka daina sakawa zuciyarka damuwa too much idan ba haka ba zaka Sakani a tashin hankali. fad'a min wani abu ya faru ne a AGC ?tayi masa tambayr cike da kulawa irin ta uwa hannusa ya kai goshinsa yana sauke numfashi "zuwa Ibrahim uku bai sameka ba ko akwai wata matsala ne data taso ?dago tsumammun idanushi yayi yana kallon mami dasu "ni a wajena babu wata matsala sai dai ko daga garesa "to allah yasa shima haka .ka kai dare a waje a ina ka tsaya haka”?shiru yayi gabansa na cigaba da luguden bugu “ko kuma nace ina kaje daka kwaso dotti mai muni haka .”
Takalmansa yabi da kallo yana mai runtse idanunshi “duk takalminka ya 'bata step da parlour'n ka ?shiru yayi kawai yana soso gefen kanshi "ko wajen wannan sabuwar maaikaciyar kaje ?sake kallonta yayi a d’an rikice "adamcy kana son yarinyar nan? "take yaji wani abu ya tsigar masa a gabad’aya ilahirin jikinsa yana yawo cikin ’ bargo da tsoka tsayawa yayi yana kallonta ya kasa kwakwarar motse ballanantana yace mata wani abu .”



ahankali 'mani ta numfasa sannan ta cigaba magana “wannan shine karo ba biyu dana tambayeka , irin wannan soyayyar zaka boyewa sweetheart dinka "?zan so naga yarinyar nan naga abinda tafi maryam dina dashi, nasani baza tafi maryam dina da komai ba, maryam dina yar asali ce yar dangi ce ,yar gata ce, kuma mai galihu ce ace mutun yana da dangina kamata ai abun ayi alfahari dashi ne “shiru yayi yana duban mami yana nazarin inda maganrta ta dosa "kenan dai hasashensa ya tabbata idan ya kawo maryama matsayin matar da zai aura ahlinsa bazasu amince ba, idan kuma sun amince zabasu sota ba zasu kyamaceta ?yayi wa kanshi tamabayr "ina son naganta adamcy da kyar ata ya samu ya had'iye abinda yaji ya tsaya matsa a makoshinsa sannan 'ahankali ya iya motsa lip's dinsa tare da kiran sunan mami " sweetheart ki bar maganr nan zamuyi later mami ta katse shi ta hanyar daga masa hannuta, nasan halinka adamcy bazaa qara maganar ba "ki kwantar da hankalinki yarinyar zata zo a gidan nan zaayi presentations kinga dole zaki ganta amamn fa babu komai a tsakanina daita bayan shaani na aiki ."ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa."



"yanzu kai haka zaka qare rayuwarka ?we will talk about it later “yana gama fadar haka ya shige bathroom."shiru mami tayi tare da bin kofar daya rufo da ido ."tarasa gane abinda ke damun tunanin d'anta shine zurfin ciki shine miskilanci shine jin kai shine rashin son magan shine rashin kunya ya rabbi ka taimakeni ni idan son yarinyar ma yake ya kawo min ita amatsayin wacce zai aura zan fi samun natsuwa dan gara yayi aure da zaman da yake haka tana bukatar ganin ya'yansa masu tarin yawa gashi ance maryam mace zata haifa tana son duk abinda ke cikinta amamn taso ace d'a namiji zata haifa masa domin kuwa haihuwar da namiji yana bawa uwa kariya daga duk abinda zai taso gaba na tashin hankali ,domin ita karon kanta misali ce tayi imani da babu adamcy acikin rayuwar ita da ya'yanta mata da tana ji kuma tana gani zata kaskanta acikin dangin ubansa amman tun yana yaro yake takawa duk wanda ya nemi ya kawo mata rainin hankali burki ."



Bangaren maryama har qarfe d'aya na dare idanuta sun kasa runtsawa ta yunkura ta tashi ta zauna sosai a tsakiyar katifarta ta janyo pillow ta rungume tsam a qirjinta tana going over maganganun mr ata tana son ta gano wata gaskiya da yake qoqarin boye mata ,wani bangaren na zuciyarta sai taji tana so ta yarda a cikin yanayinsa akwai alamun soyayya amma kuma acikin maganganunsa kwata kwata babu wata alama ,acikin kwayar idanunshi ma zaa iya tabbatar da akwai wani abu acikin zuciyarsa .”shiru tana tana tariyo irin kallon da yake mata domin son gano wani abu .”girgiza kai tayi tace “wad'an mugayen idanuwan nashi babu komai acikinsu sai tarin firgici "Idan kin san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login