Showing 42001 words to 45000 words out of 182919 words

Chapter 15 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

356

amman ko kallonsa batayi ba, ta cigaba da abinda take dan tunaninta ba’a wurinsa yake ba tunanin yadda zata masa abinda yake bukata ta kama gabanta take ."



Ya cigaba da kallo mace ta fara zanawa sanye da kayan weeding ajikinta a hankali ta d’ago tana kallonsa tsaye ya d’aura hannusa d’aya akan kujera ,d’ayan kuma yana rike da takardan ahanakali ta mike tsaye a daidai lokacin ya kalleta cikin sa’a idanunsu ya tsarke ckin juna saurin dauke idanunta tai ta maida Kan aikinta tana tunanin tare da sa pencil abakinta shi kuwa tundaya daura idanunshi akanta bai dauke ba sai daya kai minti talatin "sir sir!! ammm "Nace kice wani abu ne ?shiru tayi kawai tana kallonsa ya maida idanushi kan zanen da take yanzu wani yanayi suka tsinci kansu “set! ta kasa zama Kmr yadda ya bukata  ya mika mata hannu alamun ta bashi pencil din hannunta ,babu mutsu ta goge kan pencil din saboda ta sakashi cikin bakinta ta mika masa ya kar’ba ya d’aura akan zenen da take ."


"Me kike qoqarin zanawa anan ?”Abinda ka bukata ne sir “ta bashi amsa anatse cike da kwarewa ya shiga gyara mata yana mata bayanin yadda zatai sun d’auki lokaci yana mata bayani sultan yazo ya wuce kasancewar koina a wurin glass ne duk yadda zaka wuce zaka ga mutun kawai idanunshi ya sauka akansu ya tsaya yana qare masu kallo batare da sun sani ba amamn yaso ace yasan me suke tautaunawa akai sai dai babu damar hakan dan hk ya wuce ya kama gabansa ."


Mr ATA yayi mata gyara sosai kinga yadda zakiyi amman kin tsaya salo da son nuna iyawa alhalin duk nonsense kike zanawa.” yana gama fad’ar haka ya ajiye pencil din hannunsa duk da ya zageta amman fuskarta cike take da farinciki ,tace "kai gaskiya yayi kyau sosai ,ya kad’a kai ai kinga yadda ake yi amman kin damu mutane kin iya zane yanzu kin fahimci ba iya kwarewarki yasa aka nemoki kiyi aiki anan ba ?”ta gyad’a masa kai alamun “”eh!har ya juya ta kirasa "sir! ya juyo yana kallonta a tsanake yana jin wani iri akanta abinda yake ji akanta na dabam ne ,abu ne da bai ta'ba jinsa akan kowace mace ba. abun ne mai tsaya wa arai .”


“Ko zan iya cewa wani abu ? karki ce komai dan bana son jin komai ki zauan ki cigaba da aiki kawai kai ta gyd’a masa shi kuma yasa kai ya wuce ."ta sake zama ta cigaba da aiki bayan kamar second goma ya shigo hannunsa rike da cup biyu d’auke da coffee ya ajiye mata cup d’aya mai d’auke da sunan kamfaninsu sannna ya kalli aikinta ta kallesa “sir dan allah ka bari na tafi gida lokaci ya soma ja hankalin iyayena zai tashi “babu inda zaki sai kin gama min aikina ya sake juyawa rike da nashi cup din yana kur’ba ahankali .”


Sosai tayi concentrate akan aikinta ta sake zaro wata takarda ta cigaba a natse ya fito daga office dinsa zai fita idanunshi ya sauka akanta diret inda take ya nufa ya tsaya yana kallonta yana tsaye sectary dinsa ta qaraso ta tsaya tana cewa” sir ina bukatar ka saka hannunka anan ya cire hannunsa d’aya cikin aljihunsa ya amshi biron hannunta ya saka hannu yana saka hannu amman hankalinsa da idanunshi yana kan maryama ita kanta sectary tana lura dashi tana mamakin yadda ya damu da yarinyar da yadda yake yawon kallonta byn duk ba haka yakewa sauran yammatan dake aiki akarkashin ba ."


Bayan ya gama ta wuce shi kuma ya qarasa kusa da maryama yayi daf daita sosai ,hannunsa d’aya cikin ajihun wondonsa yana duban aikin da take ,jin tsayuwar mutun yasa ta d’ago idanunsu suka tsarke cikin juna suka dinga kallon juna har basa son ko kifta idanunsu da kyar ya iya d’auke idanunshi ya kalli zanen da take "har yanzu kina Kan aikin nan ?"eh ina kai sir kokari nake na qarasa na wuce na tafi gida “yayi shiru yana tunani dan baya son ta wuce abu biyu ne aransa yana son hukuntata ta hanyar ‘bata mata lokaci haka kuma baya son tayi nisa dashi dan yana son akoda yaushe tana kusa dashi yana matukar son ya bayyana mata sirrin dake ranshi amman ya fuskanci yarinyar tana da matukar zafin kai da tsautsauran raayi tare da rainin hankali ,ba lallai lokaci daya ya samu had’in kanta ba ."


Ya kalli zanen sannan ya d’auki pencil yana sake mata bayanin yadda zatai daga can bayansu kuwa sultana ce tsaye tana dubansu ashe bata wuce gida ba idan fa tayi sakaci wannan yarinyar zata yi galaba akan ya Adam zata iya mallake zuciyarsa dan taga gbdy ya maida hankalinsa kanta abinda bata ‘bata gani ba kenan sauraran wata yarinya ko kula da ayyukan ma'aikatan dake kula da kamfanin yayinda a bayan sultana sultan ne ya tsaya yana sauke numfashi "kiyi hattara wannan yarinyar ta kware sosai akan aikinta irinsu ATA yake bukata dan tasan aikinta ni nayi danasani da ban d’auketa ba idan kikayi sake zakiyi loosing opportunities dinki na zuwanki wannan kamfanin domin ki siye zuciyarsa ,ya kamata kiyi duk abinda zakiyi wannan yarinyar ta bar kamfaninan .”


ranta a matukar ‘bace ta juyo tana kallonsa “ kai me yasa bakawa mutun fatan alkhairi sai na tsiya addua ya kamata ka min saboda kasan yadda nake son ya Adam arayuwata bai kamata ka fad'a min hk ba ,ba wai bai kamata ba kawai Kiyi abinda ya dace ba sha shanci ba yana gama fad’ar hk ya juya ya koma office dinsa itama ta juya ."


Mr ATA ya ajiye pecil din hannunsa sannan ya juya ya wuce har yayi taku biyu tace"sir ko zan iya wucewa gida yanzu saboda lokaci ya tafi sosai tayi mgnr tana duba agogon hannunta ya kalleta a natse yace " bake ba barin wurin nan sai kin qarasa aikin nan domin ina bukatarsa karfe bakwai daidai zaa zo akar’ba yana gama fadar haka ya juya ta koma ta zauna hankalinta a matukar tashe tare da saka pencil acikin bakinta can dai taga bata da wani mafutar da ya wuce ta cigaba da aikinta  fitsari ta soma ji sosai  marayama ta mike tsaye sakamakon marata dake kokarin kulewa ta nufi bayi tana shiga sultana ta qaraso taga yanayin zanenta yayi kyau sosai zane ne da zai d’auki hankali mutun hakan yasa haushi ya kamata lallai sultan yayi gsky idan batayi hattara ba wannna yarinyar zata gama da zuciyar ya Adam dan haka ta d’auki cup din coffe din da mr ATA ya ajiyewa maryama ta  juye gbdy akan zanen ta bar wajen da sauri ta koma gefe ta tsaya tana jiran taga me zai faru ."


maryama na dawowa ta iske tashin hankali nan take ta gigice ta dinga kallon zanen tana kuka ta d’auki d’aya daga ciki takardan wani ma har ya fara yagewa tana kallo "waye yayi min hk ?garin yaya haka ta kasance ?cikin haka mr ATA ya shigo sakamakon jin sautin kukanta idanunshi ya sauka akan zanen "what !?ya furta da karfi me ye haka zan gani Ke fa nake jira dan by this time ya kamata ace ina gida "?nima haka na gani na shiga toilet nayi fitsari na dawo na gansu haka "you're very stupid” ya fad'a a zafafe yana duba zanen sultana dake gefe babu abinda take sai murmushin jin dadi tayi Kmr bata gansu ba "amman dai ke anyi dakikiyar yarinya wani irin iskanci ne hk ?garin yaya ma haka ta faru ?”


“Wallahi sir ban san yaakayi ba ni me yasa ma ka kawo coffe tunda ai bance maka zan sha ba ."?ta fad’a cikin muryar kuka ."Okay  dan na kawo miki coffe shine ya zama laifi ?“yes dan bana shan coffe bashi da kyau kai ma ka daina sha yana da illa shiyasa ni bana sha "okay zaki gane baki da wayo dan babu inda zaki yau sai kingama min aikina” ya fad'a tsawace tare da juyawa. tabi shi da kallo hawaye na zubo mata bata jin zata iya dan bata san ta inda zata fara ba dan haka ta tattara takurduta ta zuba acikin jakarta ta nufi office dinsa tayi knowking ya bata izini ta shiga yana zaune sectary dinsa na gefensa itama ta gaji sosai amman babu yadda zatai yi tunda mai gidanta bai wuce ba bata da damar wucewa "karki soma kawo min wani uzuri ko bani hakuri ."ya fad’a amatukar fusace .”



"No sir babu daya daga ciki da zanyi nazo na fad’a maka ina son zan wuce gida ya juyo ya kalleta a kaikaice “ na fad'a miki babu inda zaki har sai kingama aikin da na baki a matukar fusace ta soma magan “sir karka manta ni macece ka duba lokaci yanzu ka gani ta kalli agogon hannunta ,gsky ni dare yayi ban saba kai wa dare a waje ba ,yanzu ma nasan hnakalin iyayena na can a tashe ni dai gsky zan wuce ko babu izininka “tana gama fadar hk ta juya da sauri sectary ta shiga kiran sunanta maryama !maryama!! amman ina ko juyowa batayi ba ta cigaba da tafiya.”shiru yayi yana tunani gbdy kwakwa luwarsa ta toshe ya rasa me yake son yayi, shima babu shiri ya mike yayi waje da sauri  sectary some ta daga hannunta sama tana cewa "thank you maryama ta fad'a tana tattara kayansa ta fito da sauri ta biyo bayansa .”

Babu yawa ayi hakuri dashi 😭🙏🙏

Mmn sudai💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


             Page 12

“Har mr ata ya fito haraban ma’aikatan zuciyarsa tafasa take . da wannan d’acin rai ya qaraso gida duk wani d’aga hannu da securities suke masa bai kalli inda suke ba ,hakan yasa duk suka shiga hankalinsu alokacin da jerin motoncinsa suka paka babu wanda yayi kaud’in isa inda yake dan duk lokacin da yanayinsa yayi haka to gagarumin bala’i ne zai biyo baya.haushinsa ba’a iya kan wanda ya ta’bosa yake tsayawa ba har akan wanda bai da ruwa da tsaki yake saukewa , dan a irin wannan lokacin yake korar mutun daga aiki ko kuma ya bawa mutun hutun satittika.” tun kafin yasa kai cikin babban parlour’n gidan ya soma jiyo hayaniyar mutane sai lokacin ya tuna ashe gobe ne zaayi sunan auta.” a dake ya sanyo kai cikin parlour’n fuskarsa babu digon annuri bai tsaya ba kai tsaye samansa ya nufa batare daya kalli tarin matane dake zaune a parlour’n mami ba, ita kanta mami bai nemita ba sakamakon kansa dake masa mugun sara .


“Ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerun cushions din parlour’n sa kanshi na cigaba da sara gabadaya ya kasa samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali.”ji yayi muddin bai kira maryama ya mata bala’i ba bazai ji dadi aransa ba sannan zuciyarsa bazata samu kwanciyar hankali ba dan haka ya soma neman layinta. shigowar maryama kenan tana yiwa umma sannu da gida inda umma Ke tako wa zuwa inda take tsaye tana tambayarta “yau kin dade a wajen aiki .muryarta a gajiye tace “wallahi wannna boss din namu ne sai ahankali nan ta shiga korowa umma abinda ya faru da yadda suka rabu dashi “ikon allah shi kuma haka nashi tsarin yake ?” “ke dai bari umma mutane na mugun shan wahala a hannunsa amman fa duk da wannan takurawar tasa wai haka suke son aiki akarkashinsa nifa ina ganin zan soma neman wani aikin dan bazan jura ba“Allah ya zaba miki abinda yafi zama alkhairi ko cigaba da aiki akarkashinsa ko samun wani aiki “amen umma “! maryama ta fad’a tana cire jakarta tana qoqarin ajiye jakarta kenan wayarta ta d’auki qara ta d’auka tana duba screan din wayar suann “sir ! ta gani wato sunan mr ATA ne yake yawo a screen din wayar tayi shiru tana jin kamr ta d’auka sai kuma tayi tunanin kar ta d’auaka dan batasan me kiran nashi zai haifar mata ba gara ta sharesa dan haka ta kashe wayar gabad’aya gaban ta na fad’awa ta shige d’akinta .”


Yayinda adaidai wannan lokacin mami na zaune agefen gadonta kusa da maryam tana cewa"haba maryam banason ina ganinki shiru , yawan tunani ko saka damuwa a zuciyarki shin zai miki maganin halin da kike ciki ne? "Jin haka yasa maryama fashe mata da kuka dan daman danne kukan take tana yinsa a cikin ranta “subhallah !”mami ta furta tana riko hannunta cikin nata “haba maryam daga magana meye kuma abun kuka ?”tunanin ne banaso bare ganinki cikin damuwa “akwai abinda aka miki ne kika dawo nan ke kad’ai ki baro yan’uwanki ?cikin muryar kuka maryam ta girgiza mata kai tana saka hanu ta rufe bakinta saboda wani kukan da yake kuma tahu mata suna cikin wannan halin sai ga nana hauwa’u ta shigo bayanta aunty khadija ce rungume da baby da sauri suka qaraso suna tambayar mami “lafiya mami me kuma faru maryam take kuka ? .”


“nan mami ta fad’a masu tsaki aunty khadija tayi sannan ta soma yi mata fada cikin zafin rai “ki zauna kashe kanki abanza ki cuci abinda zaki haifa dan wanda kike damuwa akanshi bai san kina yi ba wai shin dole ne da bazaki rabu dashi da tunaninsa ba ?”a’a khadija banaso haka dame kike son taji ?ke daya kamata ki rarrasheta ki kwantar mata da hankali tunda Kinsan ba'a son tana yawan shiga damuwa da tunani saboda cikin jikinta “.Allah mami maryam din ce da kayan haushi mutumin ko kallon inda take ba yayi bare ya duba situation din da take ciki amman ita kullum cikin damuwa take ,yanzu ki duba kiga kowa tsabgar gabansa yake cikin walwala amman ita ta dawo nan tana damun kanta da tunanin banza da wofi ta qarasa maganar tana jan tsaki sannan ta juya ta fice .”



nana hauwa’u zama tayi kusa daita suka saka maryam a tsakiyarsu .ita kam maryam kuka kawai take dan bata da abinda ya wuce kuka most especially idan ta tuna abubuwan da tayi duk akan adam amman babu abinda yayi tasiri akanshi da kyar suka samu tayi shiru ta share hawayenta tare da zabga tagumi still dai tunanin da basa son tayi shi ta sake lulawa ahankali mami ta dinga mata nasiha .” yayinda mr ata yake can bangarensa bai fito ba sai dai zuwa lokacin yayi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska .”wayarsa ya d’auko ya sake kiran number maryama sai dai amsa daya ake bashi wayar is switch off…..Oh my godness god wai me yake faruwa dani ne? komai ya zama worst a gareni? me ma yarinyar nan ta take nufi dani ?“anya kuwa yarinyar nan bazata haukata ni ba ? wannan shine tambayoyin da ya cigaba dayi a zuciyarsa yana jin zafi mai quna a ransa .”


Zaune yake shiru a parlour’nsa rike da waya layin maryama yake nema amman still a kashe ya duba agogon wayarsa karfe goma ta wuce tsaki yaja “may be tayi baccinta ya furta a fili yana rufe bakinsa aka turo kofar parlour’n aka shigo saurin waiwayowa mr ata yayi,ahankali kuma ya d’auke kanshi yana fesar da iska ganin yaya hisham ne ahankali yaya hisham ya dinga takowa har ya qaraso inda yake ya tsaya gaban Mr ata yana kallonsa kawai, rasa abun cewa yaya hisham yayi saboda yadda yaga fuskar mr ata alokacin tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa ko da ganin haka sai ya samu waje ya zauna ya zuba masa ido kamar yadda yayi masa, a hankali yaya hisham ya saki fuskarsa zuwa yanayin mur mushi, yace” ATA nazo maka da wani albishiri mai dadi mr ata yayi shiru yana kallonsa yana jiran yaji wani irin albishiri ne duk da baya tunanin akwai abinda zai wanke masa zuciya ahalin da yake ciki .”



“babynmu yaci sunan abbanku muhammed tariq ga mamakin yaya hisham murmushin ata ya fara daga yanayinsa sai daya bashi wasu mintuna sannan ya bud'e baki ya cigaba da magana ! Mr ata what this smile ?" wani sabon murmushin ya sake yi cike da tsananin farinciki mara misaltuwa cike da murya Ata Ya furta "ya Allah.! Amman gskiya naji dadin wannan alamarin allah kuma ya raya min ya kuma shirya ma mai sunan babana albarka “Ameen yaya hisham ya furta a fili fuskarsa cike da tsananin murna. yayi mamaki Kwarai da gaske domin bai dauka zai ji dadi har haka ba shikenan fad’a ya qare atsakaninsu a natse ata ya mike ya nufi hanyar fita waje fuskarsa dauke da murmushi yaya hisham ma ya biyosa kai tsaye dakin mami ya shiga anan ya iske mami da yaranta kaf har da maryam zaune .”


Kai tsaye gadon baby ya zarce ya tsaya shiru yana kallon baby kwance cikin showel haka zalika maryam shiru tayi tana kallonsa yana ta’ba qirjinsa yana murmushi kafin yaya hisham ya kai hannu ya d’auki babyn ya kai masa sumbata a goshi ya mika masa ya karbi baby ya nufo wajen mami ya zauna kusa daita “sweetheart!”ya kira sunanta “naam adamcy nah ran my prince ya dade yayi murmushi jin dadi har dimples dinsa ya lotsa “an dade baa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login