Showing 12001 words to 15000 words out of 182919 words
shima yasan dole abun zai damesa kuma zai hana rayuwarsa sukuni har suka qarasa office dinsa tunaninta ne fal acikin zuciyarsa bai dade da zama ba sai ga some ta shigo bayan ta nemi izinin shigowa wasu file ta ajiye agabansa cike da girmamawa tace "sir ana bukatar saka hannunka anan” bai ce mata komai ba ,ya kar’bi biron data miko masa batare da bata lokaci ba duk ya sign ta kwashe file din ta fice tana satar kallonsa dan da alamun yana cikin damuwa duk da dai ko yaushe fuskar nan tashi a hade take amman na wannan karon ya zarta na sauran lukuta har tayi taku biyu sai kuma ta juyo ahankali ta dawo inda yake zaune ya d’an d’aga kwayar idanun shi ya kalleta sannan ya d’auke idanunshi “sir ko zan iya cewa wani abu ?shiru ya biyo bayan mgnrta na second biyar sannan yace “zaki iya “sir yau yanayinka yayi wani iri Kmr akwai wani abu dake damunka “yes akwai abinda ke damuna wanda nake jin kamar na kashe kaina .”
”what ?ta fad’a tana zaro ido kafin ta sake mgn yace “you can leave shiru tayi tana dubansa rike da file ganin haka yasa ya janyo wasu file gabansa ya shiga dubawa duk a qoqarinsa nason ya manta da komai alokacin amman ya kasa duk shafin daya bud'e still dai hoton fuskarta yake gani tana hawaye cikin mummunar tashin hankalin data bar office dinsa jiya ."tsaki yaja yana dukan table din gabansa da karfi “what’s all nonsense ya fad’a yana mai rike goshinsa da hannunwansa duka yana jin wani irin zugi from no where”ke kuma tsayuwar me kike yi ?yayi mgnr a tsawace da sauri ta nufi kofar fita cikin zafin zuciya ya zabura ya mike tsaye ya fara zariya acikin office kafin ahankali ya tsaya cak a tsakiyar office yana dogon nazari kusan minti goma yana tsaye yana qoqarin nemawa kansa mafuta domin dole ya nemowa kanshi mafutar da zai rabu da tunaninta gabad’aya ya huta saurin waiwayowa yayi sakamakon jin sautin muryar ammar a bayansa .”
Bai ce masa uffan ba yaja wani dogon tsaki yana mai d’auke kwayar idanunshi akansa cike da jin haushinsa domin a yanzu ya gane shine ma damuwarsa ,shine mutumin daya bari ya rasa duk wani farincikinsa duk yadda yasan halin da yake ciki amman yana ji yana kallo yarinyar nan ta zama mallakin wani bashi ba .”
ahankali ata ya kasa dauke tsumammun idanunshi daga kan ammar yana jifansa da wani mugun kallo mai d’auke da fassara dabam dabam ahankali ammar ya dawo gaban ata ya tsaya yana kallonsa kamar yayi dariya amman sai ya share saboda ganin fuskar ata din har lokacin tana cikin yanayi na damuwa da tashin hankali wanda kuma yasan na rasa maryama ne shima ata kallonsa yake amman kallon tsana ammar ya saki fuska yana murmushi wanda bashi da maraba dana mugunta “mamaki murmushin ammar ata yake wato ya cucesa kuma yazo ya tasa shi gaba da murmushin mugunta ?sai da ammar ya bashi wasu mintun sannna ya fara magana “haba friend kar dai maryama ce ta gigita rayuwarka haka ?bai kulashi ba sai ma sake had’e fuska da yayi sannna ya juya ya bar wajen “cikin daga murya ammar yace “daman nasan sai tayi wuji wuji da rayuwarka tasa ka fad’i kasa warwasss cak ata ya tsaya yana cizan lip’s dinsa kamar yayi masa mgn sai km ya cigaba da taku ya nufi d’akin dake cikin office wata dariya ta subucewa ammar alokacin da ata yake qoqarin shigewa d’akin bai san sanda ya juyo a fusace yace “kai me kake nufi ne wai dani ?”
“Oho abinda kake nufi nima shi nake nufi yana daga inda yake ya girgiza kai had’e da cewa “ka shiga hankalinka ammar da wannan dariyar da kake “na shiga hankalina ko dai ka shiga hankalinka ina ta faman kiranka a waya tun jiya kaki dauka yanzu kuma nazo ina ta mgn ka min shiru sai faman cika kake kana batsewa “idan dan abinda ya faru ne kake fushi kayi hakuri amman dai yanzu abar duk wannna maganr nazo maka da wata magana ne mai mahimanci .”a wulakance ata yake kallonsa tare da cewa “bana bukatar komai daga gareka coz I hate you !I hate you ammar ganinka da maganarka babu abinda yake qara min ayanzu illa jin bakinciki da tarin tsanarka acikin zuciyata.” da sauri ammar ya matso kusa dashi yana qoqarin riko hannunsa yay saurin ja baya “don’t try me ammar! ya fad’a a matukar fusace ammar bai damu ba dan yasan halinsa ya matso sosai yana dubansa “wallahi ammar ka cuceni ,ka cuci rayuwata bazan ta’ba yafe maka abinda ka min ba sakamakon kasan duk wata damuwa dake tattare da shafukan rayuwata akan yarinyar nan amman dan mugunta irintaka ka cutar da zuciyata, yarinyar da zaka d’aukota musamman ka kawo min ita nayi tozali daita ba wai ka tsaya yi min wasa da hankali ba wallahi ka cutar dani ammar gashi har wani yayi galaba aureta “.
ka tsaya kaji mai zance maka yanzu “bana son jin komai ammar macuci mugu kawai mai bakar fuska ya fad’a yana hadashi da wani kyawawan mari. duk wannan maganar a zuciye yake yi yana cewa “get out from my office I don’t want to see your face again tare da point dinsa da hannusa kana ya cigaba da magana kamar zai zubar da hawaye” dan iska kawai da kai mai zaka fad’a ?bayan ka gama lalata min rayuwa sannna kazo kana cika ni da surutu banza da wofi “Adam ni ka mara ?an mareka wallahi idan ka cika da surutu zan qara maka kuma babu abinda ka isa kayi banza mara mutunci maci amanar abota wallahi ka gama cutata “enough ata bafa tsoronka nake ji ba na cuceka ko ka cuci kanka ?”ya fad’a tare da jan tsaki “.“Oh haka ma zakace kenan “?kenan har yanzu kana da karfin halin cigaba da bata min rai ?wai tsaya ma na tambayeka kai masoyina ko makiyina?”duk matsayin daka bani na kar’ba “okay na baka matsayin makiyina domin duk duniya kaine makiyina na farko kuma na tsaneka fiyye da tsanar da nayi maka daga yau ammar babu ni babu kai ka cire ni acikin duk wata danganta amman kafin nan zan shiga ciki dan girman allah ka cigaba da tsayuwa har na fito kaga yadda zanyi da kai yana gama fad’ar haka ya juya yana sauke numfashi sama sama .”jiki a sanyaye ammar yake kallon kofar daya shiga kamar ya shiga amman yasa shigarsa bazai haifar masu da mai ido ba kuma bazai sauraresa yaji abinda ya kawo sa ba cike da zafin zuciya ya fice .”
*******
Da sauri maryama ta shigo dakinta dake bangaren mahaifiyarta kunneta manne da waya ta qarasa inda kayan aikinta yake ta dauki biro da joter adaidai lokacin da mahaifiyarta ta shigo tana daukar kayansu dana habib zata hada cikin kayan wanki da sauri ta zagayo cike da farinciki ta daura joter akan gadon bayan mahaifiyarta ta soma rubutu tana cigaba da amsa kira “okay!!Ina jinka okay na fahimta shikenan zan tura muku da irin nawa kugani thank thank so much “.aunty ta mike rike kayan tana dubanta itama maryama dubanta take fuskata kunshe da dariya “Kinsan wani abu ?aunty ta girgiza mata kai itama fuskarta cike da farinciki “na samu aiki a alico insurance ta fad’a tana rungumeta ajikinta nan da kwana hudu zan fara aiki dasu “kin gani ba ai daman na fad’a zaki samu wani da yarda allah kofar allah ai tana da yawa in sha allahu daga wannan nasara kin dinga samu nasara kenan arayuwarki domin adduata tana tare daku akoda yaushe na gode sosai mumcy tana sake makale wa ajikinta tmkr yarinya.” karki damu princess maza kije ki fadawa ummanki nasan zataji dadi “okay bari naje wallahi zataji dadi sosai ta dauki qaramin hijab dinta ta saka ta fice .”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 4
Cike da sauri maryama ta isa bangaren umma inda ta isketa tsaye rike da waya tana mitar masu kiranta da numbobi dabam dabam basa magana ita kam wannan matsalar ta fara isarta maryama ta iso gareta tana fad’in “umma nah!! adduarki dai yau ta kar’bu ta riko hannuwanta duka cikin nata cike da tsananin farinciki “me ya sakaki farinciki haka maryama ?maryama tayi murmushi tana cewa “umma ki cinka mana !”umma ta tsura mata idanu cike da farinciki tana nazarinta kafin a tsanake tace “ina tunanin aiki ne ko ?gabadaya maryama ta rungumeta ajikinta tana murna “wallahi umma nah aiki ne ya biyoni har gida kamar yadda kika min addua maryamarki zatai aiki da aliko insurance kamfanin dake gogyaya da duk wani kamfanin ATA dake cikin qasar nan bama AGC ba.” alhamdulillah mahakurci mawadaci tabbas duk wanda yace Allah hakika allah zai isar masa yanzu dai bari na fita na siyo sweet na rabawa marayun unguwar nan Allah ya kawar mana da mugun ido, karki fad’awa kowa bayanin kin samu aiki bayan ni da ummanki “in sha allahu umma babu mai ji .”sosai maryama take jin dadin yadda umma take mata ,bata nuna mata damuwarta akan rashin sadam kawai nuna mata take itace a gabanta da cikar burinta ko da yake ai daman can umma ta tace koda kuwa babu yaya sadam a tsakaninsu .”Qarfe biyar daidai maryama ta mike tana cewa umma mai zamu daura ne ?mai zamu ci maryama ?itama umma ta tamvayeta cike da kulawa “ko nayi miki kunun gyad’a ni kuma sai na dama kostad na soya Kwai na hada dashi “kai maryama wai mai yasa bakya son cin abinci mai nauyi ne ?shiyasa gaki nan kullum a rame “wallahi umma abinci mai nauyi damuna yake bari na shiga kitchen ta nufi kitchen domin tanadawa ummah abinda zata ci yayinda ita kuma umma ta fita domin siyan sweet ta rabawa yara.”
Qarfe d’aya daidai na rana salim ya shigo cikin office din ammar ya d’ago a natse sukai 4 eye’s da salim numfashi ya sauke sannan ya maida idanunshi akan aikin da yake, salim ya samu waje ya zauna akan kujerar dake fuskantar ammar “salim yaakayi ne kwana biyu ka boye ba’a ganinka ?ya fad’a tare da mika masa hannu suka gaisa “wallahi ina nan ya harkoki ?to gamu nan acikinsa alhamdulillah .”office din ya d’an d’auki shiru na wani lokacin kafin salim ya cigaba da magana “tun shekaranjiya nake son nazo muyi magana da kai akan ATA “uhm ina jinka! ammar ya fad’a yana ture file din gabansa ya had’e hannuwansa waje d’aya ya rike ha’barsa dashi yana kallon salim .” ya kamata ka duba halin da ATA ya fara shiga , gabdaya duk ya fita haiyacinsa tafiya kawai yake yi amman baya cikin natsuwarsa da kwanciyar hankalinsa .”to ni meye nawa aciki yaga zai iya ne sai abarshi da damuwarsa “no no !! ammar bazamu biye masa ba kasan shi kasan halinsa ko nace kusan kowa yasan da wannan ,ka ajiye komai mu fuskanci matsalarsa kar ya sake rasata a karo na biyu mu shiga uku .”
zuba masa ido kawai ammar yayi yana sauraronsa yana jin wani zallar ‘bacin rai na rasashi “”wallahi komai ya cakud’ewa ata baya cikin kwanciyar hankali “kai kasan radadin da yake ji bazai tsaya iya haka ba tun daga kalmamominka na wancan ranar komai ya tsya masa “me zanyi ko me kake son nayi masa naje gurinsa domin na fad’a masa gskyar komai amman ya koroni da rashin mutunci ai Adam ya gama wulakantani marina fa yayi kamar wani yaronsa gsky ni yanzu na yanke shawarar ma bazan fad’a masa matsayin maryama ba dan kwata kwata maryama bazata iya dashi ba, ta ina zata fara irin wannan rayuwar da yake sam bazata iya ba .”
sororo salim yayi yana dubansa da mamaki kafin yace “gskyar adam yanzu na sake tabbatar da baka qaunarsa kanka tsaye kake fad’ar wannan maganr ?salim ya furta yana kallonsa a natse kamar yadda ammar yake kallonsa shima “kana kallona ai gsky ne ka fito ka fad’a masa gsky ko ni ka bani dama na fad’a masa yasan ta yadda zai bullowa lamarin yanzu haka na barosa a office dinsa yana shan sagari kai kasan waye shi idan yaji sigari bata kawar masa da damuwarsa wani abun zai koma sha kaga ai mun cutar dashi kuma mun cutar da kanmu domin dai duk abinda ya faru dashi a yanzu duk zamu shiga damuwa kuma kaine silar faruwar komai dan haka tun wuri kasan abunyi ni na gama maganata ya fad’a tare da mikewa tsaye ya nufi kofar fita daga office din.”
Bayansa ammar yabi da kallo kwakwaluwarsa na caji da tunanin maganganunsa “tabbas maganrsa gsky ce duk yadda ammar yaso yaki daukar shawarar salim a qarshe dai sai daya dauka domin bazai so ya rasa lafiyar danuwana kuma abokinsa ba yayi masa ma abinda yafi wannan abaya bare d’an wannan abun da bai taka kara ya karye ba idan da sabo ya dace ace ya saba da halinsa shi haka tashi qaddara take ahankali ya mike tsaye jikinsa a sanyaye ya d’auki wayoyinsa ya nufi kofar fita yana kiran direbansa .”ko daya sauka qasa har direba ya juya Kan mota yana tsaye yana jiran fitowarsa ya bude masa ya shiga .”
da hanzari ya bud’e masa bayan mota ya shiga ya zauna ya maida murfin motar ya rufe ya shiga mazauninsa ammar na fad’a masa inda zasu ahankali suka fito suka d’auki hanyar AGC cikin kankanin lokaci suka kawo ahankali direba yayi parking din mota ya kashe ammar ya fito kai tsaye hanyar da zai hau lifte ya nufa qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi dan bai san irin tarbar da zai samu ba kafin ya fad’a abinda ya kawo shi adduarsa kada ya iske kowa bare ya masa rashin mutunci a gaban wani gara idan daga shi sai shine da sauki .”
tun daga nesa ya ammar ya hangosa yana shan sigari ya sauke wani naunayen ajiyar zuciya ganin babu kowa a office din sai shi kadai ya daura qafafuwansa duka akan table sigari ne a hannunsa yana cigaba da busawa, gabad’aya idanunshi na kansa jikinsa a matukar sanyaye ya isa office din ya zauna agabansa batare da yace masa koami ba sai dai kwayar idanunshi na kallon kyakkyawar fuskarsa yayinda idanun ATA Ke runtse yana sauke numfashi yana sake kai sigari bakinsa kusan 20 minutes ammar yana zaune yana kallonsa cikin kwanaki kad’an har ya fara fita haiyacinsa “lallai kam yasan zai iya aikata komai akan maryama dan ya rigada ya gama kamuwa da matsanancin soyayyarta “ahankali ATA ya bud’e idanunshi sai dai ganin ammar ne yasa ATA mikewa ya d’auki wayarsa ya fad’a d’akin dake cikin office din ammar ma ya mike tsaye da sauri ya biyosa yana kiran sunansa “ATA ka tsaya ka saurareni kaji abinda ke tafe dani “garam kawai ammar yaji ya rufo kofar da karfi yana danna mata key .”
“ya rabbi ammar ya fad’a yana dafe goshinsa da hannunsa d’aya “kafin ahankali ya fice yana kiran layin salim bayan ya dauka ya zayyane masa komai har ya koma office waya suke da salim a qarshe sukai sallama “Qarfe takwas na dare ammar ya shigo cikin gidan mami batare da ya bukaci rakiyan salim ko wani ba, ya shigo ya gaishe da mami sannan ya haura sama zuwa kayataccen falonsa dake upstairs, bai iskesa a parlour’n ba ya wucewa direct zuwa bedroom dinsa jin alamun saukan ruwa ya fahimci wanka yake dan haka ya fito ya dawo zuwa parlour zaman jiransa mintuna fiye da ashirin ya dauka zaune sai gashi ya fito sanye cikin jallabiya milk colour mai azabar kyau, dukkanin ilahirin jikinsa na fidda wani azababban gamshinsa da ya gama kama komi nasa.hannunsa rike da wayoyinsa. kawai yaga mutun zaune yana fuskarshi wani dogon tsaki yaja tare da juyawa alamun komawa yaji sautin muryar ammar “heyy Mr ata sarkin nasara, sarkin zuciya sarkin girman kai ,ba komai yasa kaga ina ta faman bibiyarka ba sai dan na fad’a maka cewar maryama ba matar aure bace, sai ka ajiye wannan girman kan naka ka shiga sawun masu neman aurenta “wani irin waiwayowa ata yayi da sauri qirjinsa na wani irin buguwa da matsanancin karfi Ji yayi jikinsa suna barazanar kasa daukarsa lokaci daya zuciyarta ta nemi ta tarwatse ya dinga bin ammar da wani irin kallo kafin ahankali kuma ya fara taku ya tsaya agaban ammar yana kallonsa kawai batare da yace masa uffan ba duk da harshensa magana yake son yi masa .”
ahankali ammar ya sakar masa murmushin “da gaske abokina maryama rabonka ce ko ma nace matarka ce in sha allahu ammar ya furta yana dukan kafad’ansa ata bai yarda ba saboda ganinsa wasa da hankali kawai yake son yi masa ”“Wallahi wallahi !! kaji na rantse maka maryama bazawara ce zaka iya shiga cikin sawun masu sonta duk da ahalin yanzu babu kowa sai kai kad’ai “dan girman allah ammar karka min wasa da hankali zuciyata tana daf da bugawa “ka jifa na rantse maka duk iskancina bazan rantse maka akan karya ba “Allah ya shiryeka ammar Allah kuma ya yaye maka wannan mugun hali naka kai wato komai sai ka batawa mutun rai wata dariya ce ta subucewa ammar yace “ai