Showing 111001 words to 114000 words out of 182919 words

Chapter 38 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

373

jin wani irin zafi a zuciyarta tare da kai idanunta sama tana kallon dakin d’akin tana sake zurfafa tunaninta “ki daina tunanin maryama ki jajurce da addua domin baki da mataimaki sai Allah “ina addau aunty addua nake amman kullum alamarin sake tsamari yake ni har nagaji da addaur aunty , na rasa me zanyi zuciyata kullum muradinsa take ni bama kaina nake ji ba a halin yanzu abinda ke cikina nake tunanin halin da zata shiga idan tazo duniya “ ta qarasa maganar hawaye na gangaro mata akan kuncinta .”wannan kuma ki qyaleshi ko yaki ko yaso abinda yake cikinki nashi ne kuma jininsa ne idan ya ga dama karya amsa mu dai mun amsa kuma muna so .”sannan duk fushi da zai yi na banza ne zai ma sauko ne ni nasan bazai iya cigaba da fushi da abinda ke cikinki ba sai dai idan bata zo duniya ba " maganar aunty tayi mata dadi ke dai ki dage da addua allah yace zai amsawa bayinsa matukar bai kosa ba ki daina cewa adduar kike kinji shiru baa cewa allah anji shiru maryam ki cigaba da yin addua,allah yana jinki kuma yana ganinki kuma zai amsa miki saboda kina da yakinin allah ya ganmu yasan mu kuma yana jinmu ,bawa zai dade yana addua amman yaji shiru har ma yaji tamkar allah bai amsa ba Aa wani lokacin abun ba alkhairi bane wani lokacin kuma Allah yana jaraba bawansa ne .”maryam tayi qasa da kanta tana amsawa da to aunty na gode in sha allahu zan sake jajurcewa ta fad’a haka a fili sai dai abani zuciyarta ta kasa samun nutsuwa .”



Washegarin da misalin qarfe 11 :00 daidai kira ya shigo wayar oga amar alokacin yana zaune a office dinsa ya janyo wayar tare da dubawa ganin wanda ya kiransa ne yasa ya d’aga da hanzari “hello !”daga can bangaren mr ata yace “amar idan kana da time kazo zuwa anjima muje gurin kanin mahaifin maryama shiru oga amar yayi kafin daga baya yace “yanzu kana ganin wannan tsarin da zaka bi daidai ne ?”ko daidai ne ko ba daidai bane ni dai kazo muje kawai “amman jiya jiya nan kace next week ?”na canza shawara .”ya fad’a yana cizan lip’s dinsa na kasa “to shikenna zan zo zuwa anjima yana gama jin abinda ya fad’a ya katse kiran ya cigaba da juyi akan kujera qarfe daya da rabi oga amar ya shigo AGC sai dai bai hau sama ba ya kira mr ata cewar yazo amman zai shiga massalaci yayi sallah “okay nima yanzu nake shirin saukowa .”daga masallaci suka wuce unguwarsu maryama shi da oga amar bayan sun kira baba gali cewar suna son ganinsa suna tafe suna tautaunawa har suka qaraso gidan su maryama lokacin da suka qaraso har baba gali ya gama shinfida ,a bangaren da suke sauke tarbon baki .”



Baba gali ya taresu cikin girmamawa yayinda mr ata sai sunkuyar da kai yake alamar nauyi da jin kunyar abinda ke tafe dashi bayan sun zauna baba gali ya mika masu hannu alamar su gaisa sai dai cike da girmamawa suka ki bashi hannu sai dai daga zaune da suke su ka d’an rusuna abinda ya kara daurewa baba gali kansa kenan “to me ya kawo haka manyan mutune haka masu daraja da arziki zasu rusuna masa lallai akwia babban alamarin daya kawo su .”Bayan sun dan zauna jimm, baba gali ya kalli oga amar yace “wallahi ranka ya dade tunda naji wayar ka na kasa samun natsuwa ina ta zullumi da fargabar ko lafiya?Oga amar ya danyi murmushi yace “lafiya qalau baba daman muna son rokon wata alfarma ce a wajenka “ Alfarma ? Wallahi kunfi karfin komai a gurina yallabai. A yanda nake jin labarinku a gari nan ban taba tabbatar wa ba sai da naga zahiri yadda kazo janaizar sadam ka bamu kudi masu tarin yawa sannna kullum cikinn taimakawa mutane dana kasa daku kukeyi jifa kwanakin baya akan maryama tayi aiki a qargashin yalla’bai kudi masu yawa aka bani a ina ake yin haka ai giramanku ya kai kusa ayi ko babu kosisi ku din na daban ne allah dai ya taimakeku .”baba komai baba mubar maganar nan haka abinda ya kawo mu muna neman Alfarmar auren maryama ne a wajenka “baba gali ya dago kanshi da sauri yana dubansu kafin muryarsa a dan rikice yace “maryama kuma ?”




Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


             Page 32


Ahankali oga amar ya gyad'a masa kai alamun "eh!shiru baba gali yayi zuciyarsa cike da matsanancin mamaki kafin ahankali ya motsa labbansa yace "kada dai in ce kai ne ke son auren maryama  ?"oga amar ya girgiza masa kai yana cewa "a'a bani bane  baba d'an uwana dake zaune agefena ke son maryama da aure kuma yake  son ta zamo uwar 'ya'ya nsa ya qarasa maganar yana nuna masa mr ata dake zaune a gefensa .wani irin tashin hankali baba gali yaji yana shigarsa,yayinda farinciki dake bayyane akan fuskarsa a mintuna data gabata yaji ya d'auke. nan take zuciyar baba gali ta shiga  tsinke wa,lokaci d'aya jikinsa ya kama rawa rawa ya mugun tsurawa mr ata dake zaune shiru idanunshi na kallon had'add'un takalman  dake sanye a qafafawunsa ido cike da tsananin mamaki "Allah mai iko yanzu maryama din ce zata auri mutun kamar wannan shahararren mutun da duniya tasanshi  tasan da zamansa ?" zuba ma mr ata idanu  kawai baba gali yayi yana kallonsa yana jin wani zallar 'bacin rai na ratsashi ,suna cikin tashin hankali shi da matarsa basu fita acikin ba sai ga wani sabon tashin hankali yasan muddin matarsa salma taji wannan labarin sai ta kusan hauka dan duk duniya babu abinda ta tsana kamar maryama da cigabanta .bataki kullum ta ganta cikin damuwa ba ,burinta  taga tozarta ta wulakanta ta rasa mai sonta."



oga amar ya gyara zamansa kana ya cigaba da magana a tsanake "alfarmar da muke nema a wajenka itace ka taimaka mana da aurenta acikin kankanin lokaci sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba muna bukatar aurenta ne batare  da saninta da sanin kowa ba saboda wasu dalilai namu  amman idan komai ya daidaita nan da wani lokaci kad'an zamu bayyyana mata komai "baba gali ya d'auke kwayar idanunshi daga kallon mr ata ya maida kan  oga amar, ido cikin ido  suke kallon juna kafin ahankali yace "wannan wani irin aure ne haka  ?taya za'ayi aure haka batare da saninta ko sanin kowa ba ?”kusani maryama nada mahaifiya ,sannan tana da kani,bayan ni kuma  tana da kannen mahaifin kunga wannan bukatar taku  ba abune mai sauki ba abu ne mai matukar wahala gara dai yaje ya  sameta idan sun daidaita kansu shikenan ni ta wajena mai sauki ne amman babu yadda zanyi mata irin wannan auren ta ina ma zan fara aikata haka ?"daman mutane suna min kallon bana qaunata ai a yanzu zasu sake tabbatar da hakan dan nasan duk runtsi duk wuya sai maganar ta fito wata rana ".




“kayi hakuri baba ka fahimcemu babu wanda zai sani daga mu biyu din nan sai kai "sam ko d'aya bazan amincewar da haka ba nan gaba ake gudu ku nemi wata alfarmar amman banda wannan ". “wannan alfarmar kawai muke bukata a wajenka wallahi  nan da wani lokaci zamu sanar mata zamu sanar da kowa ,idan ma lokaci yayi tsinke bama  so daga gareku sai ita kad'ai ,haka ma maganar hidima zamu  dauke muku nauyin komai kai ma zamu maka duk abinda kake da bukata ka fad'a min ko ya kai nawa zan mallaka maka ,jin haka yasa baba gali yayi shiru yana nazari yayinda kwakwaluwarsa tayi zurfi cikin tunani abun yi ahankali ya dinga filla filla da maganar amar dan yasan baqaramin alkhairi zai samu ba a wajensu matukar ya amince da buqatarsu amman bazai ta’ba yin haka ba lallai yana buqatar yayi magana da salma sai daya numfasa kana yace "Alhamdulilla na  gode  sosai da wannan mutuntaka  domin a gareni mutuntaka ne sai dai ina kan maganr farko kuje ku daidaita da maryama idan kunyi haka  baku da matsala dani .”



ahankali amar ya dinga binsa yana kwadaita masa irin alkhairi da zai samu idan ya amince masu shi kam mr ata tunda oga mar ya soma magana da gali bai tsoma masu baki ba haka zalika bai dago ya kallesu ba sai dai wani irin bugawa zuciyarsa take da qarfin gaske "duk naji maganarka amman ku sani ina da yan uwa mata wadanda suma suna da hakki akan yarinyar nan zan so ka bani lokaci muyi magana dasu sai lokacin mr ata ya dago idanunshi  a natse ya zuba masa tsumammun idanunshi “wato dai zargin da yayi acikin maganganun maryama na ranar farko daya fara kawota gida gaskiya ne akwai wata manakisar da mutanen gidansu suke kulla mata wanda hakan yake da alaqar fasa aurenta da maza ke yi ,kuma a kallon da yake wa baba gali ya fuskanci yana d'aya daga cikin mutanen dake damun rayuwarta ,ba iya hassada suke mata ba har da son rayuwarta ta zamo koma baya “allah sarki maryarsa "ni nasan me nayi going tru arayuwata a yanzu ba aure ko soyayya bane a gabana akwai abubuwan daya kamata nayi kafin aure bare wata aba soyayya .”
 


" batun  yan’uwanka wannan ba komai bane daga baya  zanmu kasance tare dakai nan gaba sai kayi mana jagora mu  gabatar da kamu a wajensu bayan nan sai  mu  aiko da magabatanmu a sake daura aure a zahiri kowa ya sani amman a yanzu baba karka yi tunanin ko gaggawa fadawa kowa dan bama son kowa ya sani mu bar maganar daga mu sai kai .”
baba gali yayi murmushin takaici yana cewa " wallahi bazan iya aikata haka batare dasaninsu ba dan a gaskiya ina tsoron fadawa cikin tashin hankali kada nazo nayi abinda maryama zata zo daga baya ta birkice mun ko mahaifiyarta gara dai kuje  ta amince masa  dan da alamun maryama bazata amince dashi bane yasa yake son aurenta boye"karkayi wannan tunanin dan kai ma kasan babu yadda zaayi maryama taki amincewa dashi kuma ni nayi imani yau adam ya furta yana sonta zata so shi  .”baba yace "nifa wannan duk ba damuwa bace idan dai har ta amince dashi ,bazan duba wani tarin abun duniya da zaa bani ba kawai abinda nake so maryama tazo min da maganarsa "amar tashi muje !” mr ata ya fad'a a zafafe yana mikewa , kai tsaye ya nufi hanyar fita daga d’akin ."ata ka tsaya mana mu gama magana dashi "bazai ta'ba fahimtarka ba ka taso muje kawai yana gama fadar haka ya qarasa ficewa ."



Akan hanyarsu ta dawowa oga amar ya kalli ata
yace "mai yasa komai kai sai kayi gajen hakuri ?"
"kai ma fa kasan wannna al'amari ba abu bane mai saukin samu ,kuma ma ni naji matukar dadi yadda talaucinsa bai sa ya bada auren maryama ta wannna hanyar ba "ba wannna bane acikin zuciyarsa idan zaka kwana kana masa magana akan auren bata lokacinka kawai zakayi ,kai yanzu baka fuskanci duk maganar da yake ba?” kasani ba gaskiyar dake cikin ransa yake fad'a ba auren ne kwatakwata baya da muradin tayi ,ba wai wannna alafarmar ne bazai iya yi ba ,kuma komai zaa bashi bazai yarda ba saboda tsananin bakinciki da hassadar da yake mata .”
sosai mr ata ya dinga nusar da shi abubuwa da dama daya dauka acikin maganganun maryama ."to tunda kasan da haka ka fito a zahiri ka mana ka fahimtar daita .”numfashi ya sauke da qarfi "zanyi qoqarin nifa ba wai ina jin shakkarta ko tsoronta bane yasa kaga zanbi ta wannan hanyar ,idan ina son maryama ta amince dani umarni kawai zan bata kuma dolenta ko tana sona ko bata sona ta amince da aurena .”dole zaka mata kenan ?mr ata yayi shiru yana ciza lip’s dinsa ,”kasani baawa mace dole akan aure kai dai kayi iyakar qoqarinka ku fahimci juna .”




“Wannan yarinyar bazata fahimceni ba saboda soyayyar wannan mataccen mutumin yayi tasiri acikin zuciyarta sannan kuma akwai abinda nake gudar wa rayuwarta dan ga dukkanin alamun rayuwar datai abaya cike take da tashin hankali da qalubali banason na kawota cikin ahlina ta fuskanci wani tashin hankali , shiyasa nake son nabi komai ahankali kafin na killaceta agidan dan bazan yarda kowa ya takata ba haka zalika itama bazan yarda ta taka min yan’uwana ba ,sannu ahankali suna tautaunawa har suka kawo AGC ."bayan direba yayi parking atare suka fito suka tsaya ajikin mota "bayan kamar minti goma oga amar ya qarasa inda yayi parking din motarsa ya shiga ya wuce shi kuma ya nufi ciki ."maryama nã tsaye da madam some suna magana akan ciwon hannunta mr ata ya qaraso da sauri madam some tayi masa sannu da zuwa ya amsa aciki batare daya kalli inda maryama take ba ya nufi kofar office dinsa yana cewa madam some "kawo min coffee."cike da girmamawa tace "okay sir ta juya ta bar maryama tsaye tana kallon bayansa mutun kullum cikin zafin zuciya kamar bashi ne jiya ya gama narke mata cike da tausayawa ba sai gashi yau ko kallon inda take bai yi ba bare ma ya tambayi lafiyar hannuta taja "tsaki tana duban hannu mai ciwo ."



cikin kankanin lokaci madam some ta had'a masa coffe ta nufi office dinsa ta ajiye masa cup din a gabansa tana cewa "ga coffe din sir”.sannan ta ja ta tsaya a gefe guda ya d'ago tsumammun idanunshi ya kalleta yana tsuke bakinsa sannan ya motsa lip's dinsa kamar mai koyon magana yace "zaki iya wucewa ta juya a natse ta fara taku yace" ummm kice maryama tazo nan da 30 minutes "okay sir ta qarasa fita da sauri ."ya kai hannu ya d'auki cup din coffe ya kai bakinsa yana kur’ba ahankali yana lumlumshe tsumammun idanunshi kana yana nazarin abinda ya dace yayi ."mikewa yayi hannunsa rike da cup ya rasa abinda ke masa dadi dan ransa yayi matuqar baci da rashin amincewar baba gali ,sosai kwakwa
Luwarsa ta dinga tunanin neman mafuta dan dole yasan abun yi kafin wani yazo yayi masa shishigi da shigar sauri ,ahankali ya soma zagaya office din “adam dan dole ka nemawa kanka mafuta to mai zan yi yanzu ?”mai zanyi?” dole dai idan ina son mallaka
r maryama sai na sheida mata kamar yadda baba gali yace ,amman taya zan fuskanceta har na iya fad’a mata ina sonta da aure ?”ka bata umarni kawai kenan nace maryama kisoni ki aureni bisa dolenki ?“No no impossible hkn bai yi ba shiru yayi yayinda ya ajiye cup din hannunsa ya shiga d’aya daga cikin dakun nan dake cikin office dinsa ya zauna akan kujera yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudun tsere .”




Jikin baba gali a matukar sanyaye ya shiga bangarensa inda zuciyarsa ke wani irin bugawa da qarfi,yayinda aunty salma dake tsaye tace " ba dai har bakin naka sun wuce ba?"ya gyad'a mata kai tare da cewa "sun wuce salam !.”ya fad'a tare da samun guri ya zauna yana jin kanshi na sarawa bai ta'ba jin wani abu na farinciki ya samu maryama wanda ya haddasawa zuciya da gangar jikinsa shiga rudani da tashin hankali ba sai wannan." ganin yanayinsa yasa jikin aunty salma yayi sanyi ,dan haka ta matsoshi tace "wasu irin baki ne suka zo wajenka ?"kuma me ya kawosu ?”dan naga jikinki yayi wani iri ?dafe goshinsa yayi da hannu d'aya yana ciza labbansa yana sake jin tashin hankalinsa na nunkuwa agaresa .aunty salma taje ta kawo masa ruwa mai sanyi ta mika masa "ka sha ko kadan ka ji sanyi kafin ka sheida min meke faruwa dan lallai akwai abinda ke faruwa dan ban ta'ba ganinka haka ba ,dan ko dakatar da kai da umman sadam tayi banga ka shiga damuwa da tashin hankali irin haka ba."bai mata mutsu ba yasa hannu ya karba ruwa mai sanyi ya sha kad'an ya ajiye kofin din a gabansa ita kuma ta zauna kusa dashi "ina jinka bani labari meke faruwa da kai ?"shiru yayi "dan allah ka fad'a min dan shirunka ya fara sakani jin tashin hankali ."




numfasawa baba gali yayi kana ya cire hannunsa daga goshinsa ya soma bata labarin halin da yake ciki ,suman zaune aunty salma tayi a wajen kamar wacce aka dasata tsabar tashin hankalin data shiga ai baba gali yana gama labarta mata komai tsoro da matsanancin firgici yaga ya bayyana akan fuskar aunty salma wanda babu tantama yasan na tsananin firgita ne daman kuma yasan zai iya ganin fiyye da haka atattare daita muddin taji ".cike da tsnanin tashin hankali ta fashe da kuka tana cewa "nashiga uku wannnan babban mutumin ne ke son auren maryma "?tabbas salma shine kuma wallahi ga dukkanin alamun mutumin nan yana mutuwar sonta ."wani irin bugawa zuciyar aunty salma tayi ta soma kuka wiwi baba gali ya matso kusa daita yana girgiza mata kanshi alamar kartayi kuka hannunsa yasa ya share mata hawaye kuka take sosai har numfashinta ya soma qoqarin tsayawa tace "to kai me kace masu ?"ajiyar zuciya baba gali ya sauke yace "me kuwa zan ce masu daya wuce ban yarda ba kuma ban amince ba, dan tarin dukiyar da zasu bani bazai rage min radadin bakinciki da nake ji ba .

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login