Showing 168001 words to 171000 words out of 182919 words
ya ratsa shi karon farko yaji asalin shigarta ta baya tayi matuqar burgesa babu abinda ya nuna ajikinta wani zirrr ya dinga ji asansar jikinsa har tsakiyar kanshi kamar ana jona masa shocking ahankali yaji ya fara samu wadatacciyar natsuwa .”
ta kalli inda yake tsaye ganin yadda ya zuba mata ido ko kiftawa ba yayi yasa ta bud’e bakinta da kyar tace “sorry sir good morning “.bai amsa mata ba kuma bai d’auke kwayar idanunshi akanta ba ,sai dai irin kallon da yake mata yafi komai d’aga mata hankali “oh Allah ni mryama wannan kuma wani irin kallo ne haka ?”to ko dan ta ‘bata lokaci ne yasa yake kallonta haka ?”ta fad’a a kasan ranta,dan ita wallahi bata son yadda yake kallonta dan wanan kallon nasa kallo ne mai cike da kwarjini da dagulawa mutun lissafi ne .”
Ahankali ta juya ta soma taku acikin Office din yayinda mr ata bai daina kallonta ba har ta qarasa inda empty chairs suke ta samu waje tayi wa kanta matsugunni ta had’e hannuwanta waje d’aya tana kallon wani gefe dabam .” a natse ya dawo kusa daita ya tsaya ta d’an saci kallonsa sai kuma ta d’auke shayayyun idanunta da sauri ganin ta bar kallon wanan bangaren da yake ya dawo d’ayan bangaren da ta maida fuskarta ya tsaya ya soma mgn“ guys abinda nake son nace shine nan da sati biyu masu zuwa zamu bar kamfanin nan zamu koma sabon kamfani wanda acan zamu cigaba da aiwatar da ayyukan creation dinmu” ahankali ya cigaba da yi masu bayanin irin cigaba da yake son su kawowa kamfani kuma har zuwa wannan lokacin da yake masu bayani bai fad’a masu inda zasu koma da aikin ba
kuma duk yawo su babu wanda yayi qoqarin tambayarsa inda zasu koma din yadda sukai shiru haka mryama tayi tare da tsura masa idanun tana kallon sa tana nazarinsa har sanda ya dasa aya ya qara da cewa “ ina fatan kun fahimceni “.
“yes sir !” suka had’a baki wajen fad’ar haka still babu wanda yayi tunanin tambayesa wanda maryama bata raba dayan biyu tsoro ne “.
“sir mai yasa zamu bar nan din ?kawai ta tsinci bakinta da cewa haka ,shiru yayi mata batare da yace mata uffan ba “naga nan din kamar ..” “keep queit…”ya katseta ta hanyar fad’ar haka yana hura hanci shiru tayi kamar yadda ya bukata yana hukuntata da kwayar idanunshi “maryama what’s this nonsense?”what’s every time if am talking you most disobey me “? nasan kinsan bana son haka but why ?am sorry sir! but nayi tambayar ne saboda musan..”
”maryama ki min shiru banason ki sake cewa komai” tace “okay sir “.!
ta fad’a sai dai tayi kasa da kanta muryarta can kasan makoshi tace “ko me yasa zai daddakemu daga nan ya maidamu wani waje kamar wasu tsuntsaye ?”me kike ce ?ya tambayeta da sauri ta d’ago kanta gabanta na fad’uwa ta zuba masa shayayyun idanunta tare da sanya kwayar idanunta cikin nashi “ba kallona nace Kiyi ba what did you say ?”bance komai ba sir, kawai dai kunnenuwanka ne suka ji kamar nace wani abu.”
“Maryama nasan kince wani abu” tai shiru kawai” ina jinki! “nifa babu abinda nace kawai dan dai kana jin haushina ne yasa kunnuwanka suka jiyo maka kamar nace wani abu “keep quiet bansan me yasa kika rainani over ba ,kisani na d’auki aikina da mahimmanci ban d’aukesa shirme ba sannan idan kinga zaki bimu fine idan kuma zaki cigaba da zama anan gud ya rage naki.” dumm taji gabanta ya fad’i “daman yace tazo aiki ne dan kawai ya samu damar wulakantata kome ?”tayi mugun zuba masa ido tana dubansa ya juya a natse ya fuskanci ma’akatan sa “guys ina fatan zakuyi aiki dani kuma zaku bini duk inda na bukata?”.sure sir okay back to work ”yana gama fad’ar haka ya wuce ya fita ko kallon inda take bai yi ba dan har lokacin haushinta yake ji kamar yadda ta fahimta Itama ko kallonsa batai ba sai dai abinda yayi mata ya dameta matuka idan tai bleming kanta akan saka bakinta cikin maganarsa ko zuwanta aiki sai kuma ta dawo ta bashi laifi wulakancin da yayi mata .”
Jiki a sanyaye ta bude littafi tana duba zane tana zance zuci “ya ma bari mutun yayi magana yaji me mutun zai ce amman yaki ya hau mutun da matsefa ,masefaffe kawai abinda ya kamata yace min me nake qoqarin cewa .?”Ko me yasa zai daddakemu daga nan zuwa wani guri da alamun inda zai maidasu din akwai nisa sosai may be shiyasa yayi masu kyautar mota amman ita ya hanata ko ita uwar wa ta kashe masa da zai bawa kowa ya hanata ?”tayi maganar tana jan tsaki a fili ita dai gasky zata samesa taji inda zasu koma matuqar akwai nisa daga unguwarsu bazataje ba ,gara ta hakura da aikin gabad’aya ta huta tunda daman akwai sharad’i akanta.”
ahankali ta soma qoqarin mikewa tsaye tana gyara zaman hijab dinta sai ga madam some ta shigo “yauwa maryama latest desing na royal palace zaki zana “okay ma ,zuwa yaushe ake bukata ?”eh to ko zuwa gobe da safe haka “okay ma zanyi qoqari in sha allahu .”
Madam some ta juya ta fita ta shiga wani office din ita kuma ta nufi office din mr ata bata tsaya neman izini ba ta fad’a kanshi na sunkuye yana duba wani file din zane sai dai nan take ya fahimci Itace ta shigo masa office babu neman izini,a natse ta qaraso ta tsaya a gabansa tare da goya hannuwanta duka abaya tace “sir !”ya d’ago kanshi ya had’e hannuwansa waje d’aya ya dafe ha’barsa tare da zuba mata ido .”amm daman nazo ne nasan inda zamu koma aiki idan wajen yayi min zan biku .”
“Idan kuma wajen bai miki ba fa ?”zan ajiye aikin gabad’aya”.ta bashi amsa kai tsaye batare da wani shayi ko ‘bata lokacin ba “okay lekki zamu koma”. “lekki!?ta furta a fili tana d’an ware idanunta ya gyad’a mata kai yana lumshe mata ido “ammm gaskiya Ina ganin zan ajiye aiki dan …”sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da magana “uhm Ina jikin dan me ?”dan na samu wanda zan aura mgnarta ta daki kunnuwansa ta wuce har cikin zuciyarsa tamkar ta soka masa mashi haka yaji maganartata a kahon zuciyarsa “yayi shiru kawai yana kallonta wanda kallon nasa yasa ta sunkuyar da kanta kasa dan bata son wannan kallon nasa mai firgitarwa .”
ahankali ya motsa lip’s dinsa yace “daga yaushe zuwa yau she ne har kika samu wanda zaki aura ?yayi mata tambayar kamar zai yi kuka ta d’ago kanta a natse har lokacin ita yake kallo fuskarsa a had’e “daga sunday wani d’an uwa zan aura”ta fad’a masa tana son tabbatar da abinda yake boye wa aransa,ya lamgwabar da kai gefe kamar abun tausayi “me yasa ni bazaki aure ne ba ?”yayi mgnr acikin ransa yana jin wani irin tuttukin bakinciki mara misaltuwa ahankali ya sauke hannunsa ya mike tsaye ya dawo inda take tsaye ya tsaya a gabanta yana lissafin abinda zai yi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya motsa lip’s dinsa “ni me yasa bazaki aure ni ba sai wani dabam “.?
“Saboda baka sona!”.
“Saboda bana sonki ?” yes of course baka sona shi kuma yana sona kai kuma kace taimakona zakayi kaga gara na auri mai sona ba mai taimkona ba ,dan Kai daman kafi qarfin aurena bare km tun kafin aje koina ka fara da taimakona zakayi “naji but shi da yace yana sonki ke kuma kinji aranki kina son shi ko kawai zaki auresa ne dan kina son kiyi aure?” ta gyad’a masa kai tana cewa “eh to bawai ina son shi bane amman zan auresa dan naji ya d’an kwanta min arai nan take moond dinsa ya sake canzawa ya shiga kai kawo a filin office din .”Sosai tai mamaki yadda ya shiga damuwa “kar dai da gaske mr ata sonta yake kamar yadda ta fara tunani kamar yasan tunanin da take kawai taga ya dawo gabanta daf daita ya tsaya yasa hannuwansa ya rike kafad’unta yace “karki ga na shiga wani hali kiyi tunanin Ina yin shishigi ne acikin rayuwarki ,jikina ya bani baki son auren nan kuma banason ki auri wanda baki so kasancewar akwai illa saboda ni nan hakan ta faru dani kuma babu abinda auren ya haifar sai zallar damuwa ki manta da wannan ni ki aureni “
Tayi shiru tana tunani wannan Iko nashi “gaskiya ni dai gara na auresa zai fiyye min kwanciyar hankali akan na aureka shi mutun ne mai sauki hali mai kyakkwan muamula da mutane mutun ne mara girman kai da sanin kimar mutane mutun ne mai…”ai kafin ta qarasa mganrta sai Jin saukar mari tayi akan kuncinta sosai ta firgita ta dafe kuncinta ta tsura masa ido shima ita yake kallo ranshi a matukar’bace hawaye ya zubo mata akan fuska yace “kina hauka ne ko kuma kin fara shaye shaye ne ?”a gabana kike yabon wani katon banza har kike kuranta shi ?bayan ya gama maganar sai kuma yayi shiru ya juya mata baya yana fesar da iska yana duban hannunsa da ya mareta dashi “oh my god why adam ?”me yasa ka mareta?”yana cikin wannan halin yaji motsin takalmanta alamun zata bar office din juyowa yayi da sauri ya rungumeta tsam tsam ajikinsa gabansa na fad’uwa nan take jikinta ya d’auki kyarma amman ta kasa kwacewa yadda yake ji ajikinsa haka take ji ajikinta kamar an jona mata wutar lantarki cikin sanyi murya yake magana “ki fahimceni maryama banason ki aure wani ,ba wai Ina nufin karki yi aure bane a’a banason ki auri wanda bakya so ne .”
Wani haushi da bakinciki ya dinga shigarta yana mamaye ilahirin jikinta domin alokacin tayi tunanin zai ce mata shi yana sonta ne dan tafi son ya furta mata cewar yana sonta ba wai ta auresa batare da tasan matsa yinta ba kuma tayi Imani idan ta auresa a haka duk ranar data bata masa rai kai tsaye zai wulaqantata .wani haushi ya sake kamata sbd bai ce yana sonta ba ya wani rungumeta yana faman sauke ajiyar zuciya tamkar jinjirin daya kwana uku batare daya sha nono ba tana fama da radadin marin da yayi mata da rashin furta mata yana sonta bare ta samu damar aurensa ,ya wani rungumeta yana mata maganar banzar ko ina ruwan shi da zata auri wanda bata so oho ?”
ahankali ta soma mutsu mutsun kwacewa ya juyo daita suka fuskanci juna ya sake matseta yayi mata kyakkywan riko yana cewa“haba maryama me yasa kike jin cewar zaki iya auren wani ki bar ni “zan fi samun natsuwa da kwanciyar hankali ta bashi amsa da haka tana sheshekar kuka “bazaki samu ba maryama bazaki iya rayuwa da wani ba ke har yanzu baki fara Jin alamun cewar kina son adam ba ?”wannan kam gakiya ne ta fara Jin son shi har ma tana jin cewar bazata iya kwanaki dayawa batare datayi magana dashi ba domin duk yadda yake mata kallon tana son shi ashe abun da gaske ne lallai zuciyarta ta tafka mata babban kuskure domin dai son shine kuskure na farko da zatayi arayuwarta.”
“Ya zareta ajikinsa ya riko hannunta cikin nashi yana murzawa ahankali yace “maryama me yasa bakya tausayawa kanki ?”tayi saurin zare hannunta daga nashi tana yarfarwa kamar wanda wuta ta kona saboda wani blood rush da taji ya taso mata daga hannunsa zuwa nata cikin second d’aya ya zagaye duk ilahirin jikinta cikin tsarke war murya tace “me ya sameni da zanji tausayin kaina?”sannan dan nace zan auri wani ne yasa ka mareni ?”ya lumshe mata idanunshi ya bud’e yana kallon yadda take yarfe hannunta tace to “nasan kana da komai da duk wata mace zata so aurenka amman ni maryama bazan aurenka kuma kome zakayi gara na auri wani akan dai na auri mutun irinka “ bai san sanda dariya ya subuce masa ba, ..ya mugun tsareta da ido sannan yace “kamar zaki iya!” ta d’an tsaya tana kallonsa Tana assessing maganarsa yana kallonta with a broad smile akan fuskashi ta d’auke kanta tana lissafi “kamar fa ya gane ta fara son shi idan kuma bai gane ba tabbas cigaba da tsuyuwarta a wajen zai iya tona asirin zuciyarta bugu da qari ga tsayuwa na neman gagararta dan haka ta juya ahankali zata bar masa offie din taji ya riko tsintsiyar hannunta tare da fixgota zuwa jikinsa ya rungumeta yana jin wata irin tsantsar soyayyarta na ratsashi “
“Ina zaki ?”gida zan wuce !”kuma in sha Allahu daga yau bazan sake ta kowa inda kake ba dan baka you’re so wicked shiru yayi yana shafata kafin ahankali ya cigaba da mgn “gobe ne fa asirin wanda ya fitar da hadad’dun hotunamu zai tono ko bakya son kisan ko waye ?”ya fad’a tare da sausauta rikon da yayi mata zuciyarta na matukar zafi ta tsura masa ido tare da alamun son ya mata qarin bayani ajiyar zuciya ya sauke nan ya kwashe yadda akayi bincike komai ya fad’a mata “waye wanda ya fitar da hotunan?”zaki sani a gobe ta sauke numfashi tace “to sakar min jikina kuma dan Allah wannan yazamo karo na qarshe da zaka kai hannuka jikina “ba jikinki ba hatta komai naki nawa ne kuma ke baki isa ki hanani ta’ba wa ba “ni kam wannan abu ya fara damuna idan kana sona ne ka fito ka fad’a min tai mgnr tana harararsa “baza’a fada ba !ya qarasa maganar ahankali yana had’e fuskarsu waje yana qoqarin kamo lip’s dinta, tayi saurin kawar da fuskarsa gefe tana cewa “bana so abinda kake min kana sa Ina cin raina dayawa
Ina jin nadamar aiki a kamfanin AGC wallahi if Ina son naga wanda ya d’auke mu hoto da har abada bazaka sake sanyani acikin idanunka ba
ga ta’ba min jiki da kake yi ga rashin so ga mari.”
sarai ya fahimci abu biyu din nan sun fi bata mata rai ba wai ta’ba mata jiki ba ,rashin bai furta mata yana sonta ba da kuma marin da yayi mata yayi kasa da muryarsa sosai “kina son na furta miki kalmar so ne kafin ki amince ki aureni ?”tayi shiru tana kallonsa ,ya sauke mata numfashinsa a fuska ya cigaba da magana “ko kuwa kina son na baki hakurin marin da na miki ne ?wad’an nan maganganun d’aya fad’a mata ba iya cikin kwakwaluwarta da zuciyarta suka tsaya ba har ilahirin jikinta take jin tafiyarsu zata so ya aikata abu biyu din nan ,furta mata yana sonta da kuma bata hakuri “naga alamun kina bukatar hakan sai dai kuma bazan yi ko d’aya aciki ba idan zaki aureni a yadda nace fine idan bazakiyi na leave my office “ ya fad’a yana sakar mata jiki ya zagayeta ya nufi wajen zamansa.”
Idan ta fahimcesa so yake ya nuna mata qarfin Iko bayn yayi nasarar tursasa zuciyarta da gangar jikinta sun fara jin wani abu akan shi ,ya fara koyar daita soyayyarsa ,to ko dai zata amincewa aurensa ne kamr yadda ya bukata ?kai Ina bazata iya wannan kasadar ba domin auren irinsa babu abinda mutun zai tsinta aciki sai zallar damuwa ta kasa motsa gangar jikinta tana shawara da zuciyarta bata jin zata sake d’aukar dogon lokaci tana aiki dashi yana zaune zai ji ta auri wani irin kallon da take masa ya fahimci kallon mugu azzalamu take masa haka nan yaji babu dadi aransa jiki a sanyaye ta juya ta fice daga office din tana jin tarin damuwa bayanta yabi da kallo yana hura hanci tare da lumshe idanunshi bayan wasu mintuna talatin da fitartata daga office dinsa ya hango fitowarta tana goge idanuta ta nufi hanyar sauka qasa aranshi yace sarkin yan kuka ranshi bai masa dadi ba yaji kamar ya tashi ya bita ya dawo daita sai kuma yaga gara kawai ya barta wuce .”
Tunda maryama ta koma gida ta rasa meke mata dadi ,ka kasa sakewa da zarar ta tuno kamaninsa sai gabanta ya yanke ya fad’i “ya ilahi kanta ta sunkuyar kan daks din daikinta tana addua acikin zuciyarta dan ta rasa me yake mata dadi ,Ina ma batasan shi ba ,Ina ma aiki bai had’ata dashi ba haka dai tayita tunani tana addua kar Allah yasa son shi yayi tasiri a zuciyarta, da adduar Allah ya cire mata tunaninsa cikin zuciyarta suku suku ta qarasa wuni umma ta lura da yanayinta amman ta share ta dan kota tambayeta tasan zatace mata babu komai qarfe takwas da wasu mintuna na dare tana kwance akan katifarta taji shigowar sako wayarta nan take ta soma qoqarin dubawa taga sakon daga mr ata ne da sauri ta shiga ta soma dubawa .”
“Slm how are you doing ?I just want to apologize for what happened today I’m sorry for today I’m not a wicked man has you think and I’m not a bad person I’m so sorry I’m not intention to hurt you please kizo gobe koda shine zai zamo zuwanki na qarshe .”
Wani irin sanyayyen ajiyar zuciya ta sauke tana sake karanta sakon tana jin wani sanyi na ratsa ilahirin jikinta sai dai tayi shiru tana tunanin amsar da zata tura masa ta d’auki sama da wasu mintuna talatin a qarshe ta tura masa “is okay “Tana gama tura masa ya kirata har missed call hudu bata d’aga ba dan bata son ya sake dasa mata abinda zai dameta wanda take ji ma akanshi zatayi iyakar qoqarin ta ta raba kanta dashi bazata ta’ba yarda sonshi tayi tasiri ba .”
*****
Washegari Wanda ya kama ranar laraba da kusan jiya maryama tazo aiki tana zaune tana aikin zane tana daddaga littafai tana dubawa sai ga yusura ta shigo ta qaraso kusa daita ta tsaya tana cewa maryama ina son muyi wata magana dake dan nayi tunanin nazo gida na sameki amman kunyar haka yasa na