Showing 81001 words to 84000 words out of 182919 words

Chapter 28 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

390

sultana rashin mutunci yana zaune akan kujera yana amsa waya da d’aya daga cikin wayoyinsa kiran yaya Ibrahim ya shigo ya d'auki wayar ya duba ganin sunansa ne, yayi shiru ya cigaba da magana cikin nishadi kamar zai d'aga ko tunanin me yayi sai ya share ya cigaba da wayarsa dan haka nan jikinsa ya bashi waya ce akan aikinsu shi kuma ko me zai faru sai dai ya faru amman sai ya cima burinsa yana son yaga me zai biyo baya idan yayi ."bangaren yaya Ibrahim kuwa layin mr ata yake nema sai dai kiran na shiga ba'a d'agawa ya kira layin ya kusan sau biyar amman the same thing ne.
ya shiga zagaya office dinsa tsabar tashin hankali kafin ahankali ya koma kiran layin sultan kira d'aya sultan ya d'aga."



Sultan yana d'agawa bai tsaya sun gaisa ba ya soma da tambayarsa halin da'ake ciki ,bangaren sultan yace "tabbas labarin daka ji haka ne sai dai baba ya takawa abun burki babu abinda zai yi "ka tabbatar sultan dan yanzu ina kiran layinsa yaki d'agawa ?"to ai ka rigada kasan halin wannan banzan mai banzar rayuwar ba lallai ya d'aga kiranka ba tunda an hanashi cima burinsa yana can yana bakinciki da bakin rai ,sannan mami ta tabbatarwa baba bazai yi ba ,bayan haka ma tace zai bar mana kamfani gabad'aya ,kaga ai mu gaba ta kai mu, ita kuma wannan yarinyar mai rawar kan zan san abinda zanyi akanta, duk yadda zanyi na rabata dashi dama aikin a qarqashinsa zanyi,dakata! dakata!! sultan ni fa ba batun wannan yarinyar bane agabana ,muyi magana mai bullewa kasani nasani kai kowa ma acikinmu ya san kasancewar ata acikin AGC yana da matukar amfani bazan so ata ya bar kamfani nan ba domin kasancewar sa tare damu akwai alkhairi .”



"wani alkhairi ne akwai ?"sultan ya fad'a haka a zafafe ta hanyar dakatar da yaya Ibrahim dan arayuwarsa yana bakinciki ace mr ata yana da wani qualities ko mahimanci,sai daya ja numfashi ya sauke sannan ya cigaba da mgn "mutumin da yayi mana handama da babakere,mutumin da yake qoqarin yaga bayanmu,mutumin da babu komai aransa sai zallar zalinci da .."dakata sultan ban kiraka dan kayita aibuntashi ba,tunda naji kan magana sai anjima yana gama fad'ar hk ya katse kiran yana sauke numfashi sannan ya soma magana a fili “bansan har sai zuwa yaushe sultan zaka dainawa ata bakinciki ba ,”kasa ganewa kayi amman ata ba sa’anka bane ,ba sa’an karawarka bane ya fad’a yana cigaba da lamuran gabansa da zumar idan ya koma gida zai nemi ata suyi magana ta fahimta dan shi bai yarda da tsarin barinsa kamfani ba "qarfe shida daidai yaya Ibrahim ya dawo gida wanda har lokacin mr ata bai dawo ba yana can zaune a office ."



Ahankali mr ata ya mike daga mazauninsa yana duba lokaci karfe shida da wasu mintuna ya kai kwayar idanunshi saitin office dinsu maryama yaga kowa dai bai gan ita da yusura ba,sauran ma’aikatan ma dake office din shirin tafiya gida suke dan haka yayi tunanin suma sun wuce gida.ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa ya soma shirin wucewa gida ya tattara duk abubuwansa masu amfani kira madam some ya mika mata ta fito ta nufi qasa sannan shima ya fito yana taku cikin isa da jin kai yayinda .”
tun daga nesa ya hangosu tsaye ajikin motar sultan tare da yusura wacce ke tsaye ajikin kofar baya da alamun jiran maryama take yayinda maryama ke tsaye a kusa da sultan rike da yatsun hannunta tana wasa dasu suna magana .nan take qirjinsa yayi wani irin bugawa da karfin gaske har sai da yayi qasa da tsumammun idanunshi ya kalli daidai saitin zuciyarsa sakamakon bugawar daya ji take dum dum!! .”


hankalinsa yayi matukar tashi fiyye da duk wani tunanin mai karatu " meke shirin faruwa anan ?"
“meye had'in maryama da sultan kuma ?tsayuwar ma me take dashi "yayi kanshi wad’an nan tambayoyin ajere yana sake jin wani sabon tashin hankali mai tattare da zazzafan kishi “ya salam !" ya furta a fili sannan ya samu waje ya tsaya ya hard'e hannayensa duka a qirjinsa yayinda kwayar idanunsa akansu .bai san me sultan yake fad'a mata ba amman dai yaga ta bud'e gaban motarsa zata shiga inda qirjinsa ya sake bugawa da matsanancin qarfi nan take zufa ya shiga tsatsafowa a saman gishinsa da karan hancinsa ,maryama tana shirin shiga gaban motar kenan kamar ance ta kalli gefenta mr ata ta gani tsaye ya hard'e hannuwa yana mata wani irin kallo mai bugar da zuciya .ga kuma yanayinsa cikin tsananin tashin hankali ,haka nan taji gabanta ya shiga dukan uku uku cike da tashin hankali bayyane akan fuskarta ta fasa shiga motar ta koma baya kad'an ,shayayyun idanunta masu haske har lokacin suna akansa, shi din ma kallonta yake fuskarsa babu annurin kirki bugu da qari ga wani bayyananne mamaki akan fuskarsa ."


"Ha'a! ya kuma kika fasa shiga ?"shigo mana na saukeku ina son naga gidanku ne kinga daga nan duk sanda zan zo sai dai kawai kiganni ."bata ko kallesa ba ta furta "bazan iya shiga motarka akan idanun mr ata ba kaje kawai ni na hakura "yusura data rigadata shiga motar bata san wainar da'ake toyawa ba ta d'an leko ta side din da maryama ke tsaye tana kallonta "yaya maryama shigo mu tafi mana Kinsan hanyarmu fa ko ba motar zamu bi bane ?"wai ta fasa bina saboda ata ko saurayinta ne ?"ai da sauri yusura ta girgiza masa kai tana fitowa daga cikin motar tare da’ bata fuska "kallo d'aya tayiwa mr ata tana rusunawa alamun girma mawa garesa sannan ta kalli maryama tayi kasa da muryarta sosai ta yadda babu mai jinta sai maryama tace "haba mana qawata dan Allah kizo muje ya ajiyemu gida kinga ai bai kamata yace zai taimake mu ba ace kinki yarda kuma saboda mr ata wanda shi ba taimaka mana zai yi ba .”



maryama tayi shiru tana sake jin wani sabon tashin hankali mai tsanani saboda har lokacin tana jin idanunshi akanta "to ko dai kun fara soyayya ne dashi ?"murmushin gefen baki maryama tayi mata kafin ta bata amsa ta dan kalli inda yake tsaye ai kuwa wata qatuwar harara ya zabga mata wacce tasa hantar cikinta kad'awa ta sake kallonsa sai taga yayi kwafa fuskarsa da alamun gargadin karki sake ki shiga motar nan sarai ta fahimci abinda yake nufi daita ".ganin da sultan yayi bazata bishi ba ya sakar mata murmushi yace "shikenan kiyi hakuri ai ban san d'anuwana ya rigani ba da gsky bazan ma tsaidake ba ,ke kuma ai sai kiyi min bayani tunda nasan kin fahimci abinda nake nufi well ku janye jikinku na wuce da sauri maryama "ta kallesa daman zuwan da zai yi gidansu abinda zai fad'a mata kenan ?"no sir abinda kake tunani ba haka bane”.
ta fad'a tana sake kamo yatsun hannunta tana murzawa "haka ne mana gashi saboda shi kin kasa shiga motata ".


“Allah sir ba haka bane babu komai a tsakanin mu ina ni ina mai gida mr ata ?"ke kike ganin haka amman ai babu lafiyayyen nmj da zai ganki yace baki masa ba ."maryama tayi murmushin jin dadi inda zuciyar mr ata kad’an ya rage bai tarwatse ba zuciyarsa ta dinga tafasa tana quna wani irin tuttukin bakinciki yaji kamar ya qarasa ya rufesu da duka har yusura dan yasan ko menene take fad’a mata haka tana jan raayinta ne "shikenan maryama bari ni na wuce sai gobe kenan mayi magana kanta kawai ta gyd’a masa .yusura tayi kasa da muryarta "malama idan bazaki tafi ba to ni zan shiga ko a qarshen titin nan ne ya ajiyeni sai na samu wata motar ta qarasa dani gida "shikenan yusura zaki iya binsa sai mun had'u gobe tana gama fad'ar haka yusura ta shige gabanta mota "sir please ni bari na bika zan sauka a qarshen layin nan "okay !”ya fad'a tare da d'aga kafad'ansa ya shiga mota yana sakin murmushin jin dadi ahankali yaja motar suka wuce suka bar maryama tsaye ".



suna fita maryama bata juyo ba ta kama hanyar ficewa daga get din ma'aikatan ,madadin tabi dogon layin da sauran ma'aikatan marasa mota irinta suke takawa sai ta karya tabi layin baya doguwar hanya ce da zata fitar da mutun babban titi kamr wancan sai dai mutane basu fiyye binta ba tunda ta hau layin taji wani irin mugun shiru maimakon ta dawo kawai zuciyarta ta ingizata dan haka ta fara tafiya abunta cikin sauri sauri tana yi tana waiwayen bayanta ganin babu kowa sai ita kad'ai yasa ta fara jin tsoro ahankali ta soma jin motsin tahowar mota dan haka ta qara sauri gabanta na faduwa kamar daga sama taga motar ta ja wani wawan burki agabanta, duk da ta d'an razana da ganin motar baka sidik mai bakin glas ta yadda duk nacinka bazaka ga wanda yake ciki ba ,kana kallon yanayinta zaka fahimci tana cikin tashin hankali da tsoro amman hakan bai hanata sake yin jarumta ta damk'e jakarta sosai ta ra’ba ta gefen motar taci gaba da tafiyarta tana mita ."


Tana tafiya motar na cigaba da binta ganin haka yasa
Maryama ta k'ara sauri, yayinda motar ke binta ahankali dan duk saurinta bazata tsere masa ba ko da maryama ta waiwayo taga motar tabbas ita take bi har ta kusa cimmata tuni zuciyarta ta bata shawaran ta arci ta kare.bata ko gama tunaninta ba tace "k'afa me naci ban baki ba" dafe jakarta tayi sosai ta fara falfala gudu da iya k'arfinta,motar ma
haka nan tsere ya kaure tsakanin mota da maryama gudu take cike da matsanancin tsoro gashi gabanta babu wata mota dake tahowa haka zalika bayanta babu sai wannan bakar motar gashi tunda tabiyo layin babu wani mutun d’aya daya biyo sannnan baka jin motsin Komai sai nã qarar injina kamfani wanda ko ihu kayi kafin ajiyoka kaci ubanka motar ta biyota gadan gadan tare da jan wani wawan birki agabanta murfin motar ya tura batare da yayi magana ba, tsayawa tayi zuciyarta na wani irin luguden bugu tana wani irin haki ttmkr ranta zai bar gangar jikknta "mutuwar tsaye tayi a wajen daman shine yayi qoqarin tsorata “? sam batayi tunanin zai biyota ba yadda take kallonsa dafe da qirjinta haka shima kallonta yake kafin ahankali ya motsa lip's dinsa yana jifanta da wani kallo "ki shigo muje .”girgiza masa kai tayi alamun bazata shiga ba "Ke malama ki shigo kina b'atamin lokaci .ya sake mgn yana zabga mata harara .”



"Tana hakin tace "karka damu sir zan qarasa na ma kusa fita a layin ina fita kuma zan samu mota"okay kada Allah ya baki ikon shigowa muje daman kuma wannan layin reping din mata ake , Allah kuma yasa kafin ki qarasa ki had'u dasu suyi watanda dake kinga duk ma abunda aka miki, ke kika jawowa kanki babu ruwana a ciki.?"Jin abunda ya fad'a yasa tayi saurin sake dafe qirjinta tana waigawa tana
kalle kalle,ganin ya rankwafo jikinsa ya kama murfin motar zai rufe tayi saurin rikewa ta fad'a ciki motar .” dariya ce taso kufce masa amma yayi k'ok'arin dakewa, batare daya kalleta ba ya tada motar yana fad in"mara kunyar k'arya kawai, ashe ke din muguwar matsoraciya ce haka ? ai na dauka zaki kafiya ne kamar yadda kika ce da kuwa kinga aiki da cikawa nonsense kawai kome ya kaiki biyo wannan hanyar ."


Maryama bata kula shiba illa ta jingina bayanta da jikin seat din motar ,ruwan data hango a gefenta ta kai hannu ta d'auko harta b'alle murfin ta kaishi bakinta yayi saurin k'wacewa yana hararata "mene hakan.?"me kuma nayi ?"tayi maganr cike da shagwaba kamar zatayi kuka "Kina hauka ne zaki sha ruwa yanzun bayan kinyi gudu.?"to mene ne dan Allah ka bani na sha zuciya zafi dan har murfin zuciyata ya bud'e ,d'an waiwayawa yayi ya kalleta a natse yana cewa "murfin zuciya kuma ?"ta lumshe masa shayayyun idanunta " wani irin zirrrrrrr yaji a gbdy ilahirin jikinsa tmkr an jonasa da wutar lantarki “zuciya tana da murfi ne ?"ni dai ina ji ajikina tana da murfi ."you're not serious "ya fad'a yana jan tsaki .”ta mika masa laulausan tafin hannunta "please sir ka taimakeni wallahi a tsananin buqace nike da ruwa "ke fa matsalarki kenan kin cika kafiya banda rashin hankali an fad'a
miki ruwa ake fara sha idan mutum yayi gudu..?"



"am very sorry sir kanata ce min mahaukaciya ko rashin hankali "wani kallo yayi mata mai tsuma zuciya yace "to me kke son akira dashi idan ba haka ba?"kayi hakuri sir "idan mahaukaciya ce ni ko bani da hankali ai bazaka d'aukeni aiki ba sannan dazu nan fa ka gama cewa nafi sultana hankali yanzu kuma kana ce min mahaukaciya tayi mgn a shagwabe. wani irin sanyi da shauki suka taru suka hade masa suna yawo a gabad'aya ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa jijiyarsa motsawa amman dake shi din miskilin kanshi ne sai ya danne ya zabga mata harara yana jan tsaki dan baqaramin kasada taso yi masa ba ,yaso yaji abinda suka tautauna da sultan amman yana tunanin ta inda zai fara .”
ita kuma tun daga yayi tsaki bata sake yin mgn ba tayi shiru tare da lumshe idanunta yadda taja bakinta tayi shiru haka shima yayi tafiyar ta koma ta kurame, tana kallonsa yana juya stearing mota cike da kwarewa har ya hau Kan titi oshodi tana jiran taji ya tambayeta unguwarsu amamn taji shiru itama kuwa taki ce masa komai tana son taga iya gudun ruwansa ."



tafi tafi dai har suka isa unguwarsu tayi shiru tana kallonsa tana mamakinsa taya yasan unguwarsu ?”
yayinda jama'ar unguwar dake zaune da wadan dake qoqarin fitowa daga massalaci sukawa motar kuri da ido masu cewa woow nayi masu cewa masha Allah nayi har sanda ya samu waje yayi parking batare daya kashe motar ba nan da nan kuma area boy's din unguwar suka shiga zagaye motar suna jiran mai motar ya fito ko zasu samu na abinci naunauyen ajiyar zuciya maryama ta sauke "wannnan mutumin kullum da sabon abun mamaki yake zuwa mata muryata a matukar sanyaye tace "na gode sosai "ta qarasa fad'a batare data waiwayo ta kallesa ba tana kokarin bude murfin kofar motar sai dai ta kasa dan idanunta ma basu gane mata wajen da zata danna dan hk ta koma ta zauna tana jiransa.kusan mintuna shabiyar suna zaune acikin mota sanyin  ac na ratsa su magana take son yi amman tana fargaban abinda zai fad'a mata ba. ta kai dubanta ga agogo "a ranshi yace zaa soma halin ?"kin shirya yin aure ne kamar yadda na shawarceki?"ta waigo a sanyaye tana mai tsura masa idanunta , tana cigaba da kallonsa tana
assessing maganarsa,ta rasa gane masa meye damuwarsa daita ko dai sultan ya hango wani abu ne yasa yace saurayinta ?"kai ina impossible ina ita ina wannan mutumin ai inuwar giginya tayi nesa da kasa ."please maryama Answer ."



"Ranka shi dade ba wai ban d'auki shawarka bane bani da wani tsayayye a yanzu "sultan fa ?"taji tambayar a wani iri ta tsura masa ido kawai "idan aurenki zai yi ki auresa mana "a'a sir bai ma ce ba kuma ni yanzu babu wannan budget din nayi matukar shan wahala arayuwata babu wani gurbi da zan iya sake bawa wani da nmj dan har yanzu hk jinyar zuciyata nake yayi shiru yana tsareta da idanunshi “har mazaje goma Sha nawa kika aura ko kika yi soyayya dasu ?”taji fitowar tambayar wani iri daga bakinsa wanda yasa ta sunkuyar da kanta qasa duk dai maganar ta furgitata amman kuma ta bata dariya “zata so ta fad’a masa gsky amman kuma tasan halinsa yanzu zai canza mata magana a qarshe ma yayi mata bita da kulle ta d’ago shayayyun idanunta aiko karaf idanunsu ya tsarke cikin juna atare zuciyarsu ta buga da qarfi .kuma a kallon da yake mata ta fahimci amsarta yake jira “mutun biyu zuwa uku ne suka nemi aurena amman a qarshe mutun d’aya na aura wanda ya kasance d’anuwana auren gida aka mana sakamakon matsalolin da akayita samu akan aurena .”


Numfashi da ajiyar zuciya ta sauke atare tana kallonsa “bansan ina sonshi ba sai dana rasashi acikin duniyar nan ,na rasa yaya sadam amman na rasa dalilin dayasa a kullum nake jin tamkar yana raye acikin duniyar nan amman Allah yafini sanin daidai kuma na barwa Allah komai ,duk hukuncin da ya yanke akaina daidai ne “gyara zamansa tare da riko laulausan tafin hannunta "yanzu dai babu kowa sai sultan?”wani kallo ta sake binsa dashi mai d’auke da tambayoyi “yaushe ne kuka fara soyayya dashi ?”shi wa kenan ?itama ta aika masa da nata tambayar “karki rainawa kanki hankali mana amsar tambayata kawai zaki bani “ya qarasa mgnr yana matse hannunta cikin nashi wanda yasa ta dan saki qara mara sauti “ouch!” ahankali ta motsa lip’s tana yatsina fuska tace “yau dai muka fara magana “okay kinji zaki iya fara son shi ?ya sake tmbyrta yana jin mummunar faduwar gaba ”babu wannan maganar araina akwai tarin abubuwa dayawa agabana wanda aure ne zai zamo last .”


Wani boyayyen ajiyar zuciya ya sauke yana cewa “Okay Idan kin san baki tashi aure ba a yanzu kar na qara ganin kin kula sultan ,magana ma ta fatar baki kar ya qara shiga tsakaninku dashi ya qarasa mgnr yana mata tafiyar tsutsa a tsakiyar tafin hannunta tayi saurin zare hannuna daga cikin nasa tana yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani blood rush data ji ya taso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login