Showing 33001 words to 36000 words out of 182919 words

Chapter 12 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

349

tabbatar mata bazata iya haifa da kanta ba ,yanzu shikenan idan ta rasa ranta wajen haifa masa baby bashi da asara babyn ce kawai zatayi rashin mahaifiya ya kamata maryama ki qarfafa zuciyarki ,ki manta dashi ki rayu ko dan abinda yake cikinki domin Ita kad’ai ce gantaki itace zata zama abokiyar adawa ga rayuwar adamcy”


ko cikakken mintuna goma mr ata bai yi da fita ba sai ga mami ta fito da sauri ta qaraso inda take zaune tana kallon kofar fita had’e da kiran sunanta “maryam lafiya ?”meke damunki?”ta fad’a tare da zama kusa daita ta riko tafin hannunta cikin nata .”hawaye kawai take zubarwa saboda tasan me zai iya faruwa idan mami taji damuwarta ita kad’ai tasan yadda take jin cikin jikinta baqaramin tokare mata qirji da mara yayi ba “kiyi min magana maryam meke damunki ?still shiru tayi ta kasa cewa komai sai sheshekan kuka take “kun had’u da adamcy ne ?”ahankali ta gyad’a mata kai alamun “eh! “wani abu yayi miki ne kike kuka ?ta girgiza mata kai alamun babu “to kukan me kikeyi haka ?”still kai ta girgiza mata bugun zuciyarta na qaruwa .”


shiru mami tayi tana rike da hannunta tana nazarinta “ki dinga tausayawa kanki maryam ,ki duba halin da kike ciki komai zai iya faruwa dake “ina tausayawa kaina mami bansan me yasa na kasa cire damuwar nan araina ba.” ta fad’a jikinta na d’aukar rawa “dan allah maryam ki ciresa gabad’aya aranki saboda muna tsananin bukatarki da abinda ke cikinki a raye “mami yaya baya sona baya son cikin da nake d’auke dashi na d’auka zai d’an sauko ko dan cikin jikina “shine ya fad’a miki haka ko kuwa hasashenki ne ya fad’a miki haka ?cike da sheshekan kuka tace “mami yanayinsa ne ya nuna min haka “ki rabu dashi ke dai kiyi fatan ki rabu da cikin lafiya “ta kalli mami ido cikin ido tace “mami ina ji ajikina mutuwa zanyi “gaban mami yayi wata irin fad’uwa tana sake damke hannunta cikin nata tace “in sha allahu mryam bazaki mutu yanzu ba kima cire wannan zance aranki nasiha da kwantar da hankali mami tayita mata tana karfafa mata gwiwa har taji zuciyarta ta d’an yi sanyi .”


Cike da natsuwa mr ata ya dawo parlour’n yana cincin magani har lokacin maryam na zaune tare da mami inda mami ta tsiyaya mata sobo a cup ta mika mata ko kallon inda suke bai yi ba kai tsaye hanyar step ya nufa har yayi taku uku ya jiyo sautin muryar mami ta doke dodon kunnensa “adamcy !”cak yaja ya tsaya batare daya juyo ba, kusan second biyar yana tsaye har sai daya sake jiyo murya mami “kana jina fa ka wani tsaya ni zanzo na sameka ko me kake nufi ?”ahankali ya juyo ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa ya soma takowa zuwa inda suke batare daya kalli inda mrym take zaune tana dubansa ba “ka samu waje ka zauna .”ta nuna masa opposite din kujerar da take zaune babu mutsu ya zauna yana duban yatsun hannunsa “.


Parlour’n ya d’auki shiru baka jin motsin komai sai na tv da ac dake aiki acikinsa sai kuma saukar numfashin mrym dake fita da karfi tana kallonsa tana jin tsantsar soyayyarsa na sake hud’a zuciyarta bayan soyayyarsa da take ji har da tsananin shaawarsa kamar taje ta kwanta ajikinsa ta rungumesa tsam tsam ajikinta “adamcy baka ga maryam bane ?”uhm na ganta sweetheart !amman shine kayi uwar watsi daita ?“to me zanyi mata sweetheart ?”ni kake tmby me zaka mata ?”kai bakasan abinda zaka mata ba ?”mace na d’auke da cikinka tsawon wattani yau lafiya gobe babu amman ka ganta kayi kamar baka ganta ba ko bazaka ce mata komai ba ai ko dan cikinka dake jikinta ka …”no sweetheart ! yayi saurin katse mami cikin ‘bacin rai “ sai daya furzar da numfashi mai zafi kana ya cigaba da magana cikin zafin rai “ba cikina take dauke dashi ba sai dai cikinta “ya fad’a yana tsaida kallonsa ga maryam din “.


maganarsa ta daki kunnuwan mrym sannan ta wuce har cikin zuciyarta wanda ya sake kunno mata damuwarta da take ta qoqarin dannewa acikin zuciyarta “bance ina son na haihu daita ba shiyasa bana bukatar wani ciki daga gareta wannan cikin ba nawa bane nãta ne har abada kar wanda ya sake dangantani da cikinta “sharrrr…”sai ga wasu hawaye masu zafi sun zubo mata akan kuncinta ahankali ta fara rera kuka mai ban tausayi fuskarshi ya daure sosai “ban san ma me yasa ta kwaso jiki tazo ba “kana hauka ne ?to wallahi bari kaji baka isa ka hana mrym zuwa inda muke ba dole mrym ta shigo cikin gidan nan “well tazo wannan ba damuwata bace da zuwanta da rashinsa duk d’aya ne a wajena maganganu marasa dadi ya dinga fad’awa mrym mami dai a qarshe tayi hakuri ta danne zuciyarta tasa masa ido batare data qara cewa komai ba amman adame take sosai game da lamarin adamcy mutun Kmr sheid’an bai da yafiya kuma abu baya wucewa a wajensa .”


mrym ta sake kallonsa taga har lokacin ita yake kallo yana sake murtuke fuskasa byn ya gama ya mike ya nufi hanyar step yana cewa “sweetheart sai da safe .”
Mami tayi masa banza tana qoqarin gogewa maryam hawaye . sauka maryam tayi daga kan kujerar da take zaune zata zauna kasa kan tayis mami tayi saurin rikota”a’a maryam muje d’akina taja hannunta suka nufi d’akinta tana rarrashinta ahankali mami ta zaunar daita akan gado tana shafa bayanta tana mata sannu amman ita bata wannan take ba kukan tausayin kanta kawai take da abinda Ke cikinta mami ta janyo pillow tasa mata abayanta tana sake rarrashinta sai data ga sautin kukanta ya ragu sannan ta fice daga d’akin zuwa na ata byn fitar mami maryam tayi kuka sosai tmkr ranta zai bar gangar jikinta .”


Tana zauna shiru tana kallon saman d’akin kukan abinda ata yayi mata a yanzu ne ko kuma na tashin hankali da zata shiga anan gaba ne idan ta haihu take yi batasani ba ?tayi bitar maganganun ata tana son tayi placing dinsa a scale daidai da rashin daidai a iya fahimtarta tun suna yara tasan yana da mugun kafiya da muguwar zuciya sune ma manya flaws dinsa kuma har yanzu da girma yake zuwan masa bai rage komai ba .”tasan tunda yace bai son cikin tasan komai zaayi ko sama da kasa zasu had’e bazai qaunaci cikin ba .ita kuwa me tayiwa rayuwarta haka?“ta cutar da kanta da abinda Ke cikinta da tasan zata kasance a cikin wannan tsaka mai wuya din data hakura bata kusamcesa ba ”


Bangaren ata kuwa yana zaune a d’akinsa ya natsu acikin kogin revenge ,yadda har yana qoqarin yayi lossing kansa “bazan ta’ba karbar cikin jikinki ba wannan shine hukuncin da zan miki ta yadda a gaba idan an sake halittoki a duniya bazaki sake reaping din wani ba .”da sauri ya kalli kofar shigowa mami ce ta shigo ranta a matukar’bace ganin itace ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana ciza gefen lips dinsa ta nunasa da babban d’an yatsanta “adamcy ka kashe ka huta gbdy tunda kafin bukatar haka “ ya d’ago idanunshi ya kalleta kawai “eh gara ka kasheni kafin naga mutuwar mrym “to ni sweetheart meye laifina ne ?duk abinda nayi akan gskyta nake yarinyar nan nace banso kin matsa na hakura na rungumeta as ending tayi raping dina har yau ina kan shan magani sanadiyyar pills din datayi min amfani dashi” bayan shi dumu dumu na kamata da tukunyar tsafi yau datayi nasara akaina me zaki ce ?mami tayi shiru tana dubansa “ tabbas ya fita gsky .”dan ita kanta taji ciwon abun bare shi to amman yane zatayi maryam dolenta ce bata da yadda zatayi daita .”?



Zazzafan numfashi ya fesar “taya zan iya yafe mata sweetheart bare naso abinda tayi ta’adanci wajen samunsa ?”wallahi sweetheart matukar na riga wannan yarinyar mutuwa bazan yafe mata ba ,gara ma kiyi mata fatan mutuwa watakilla zan iya yafe mata idan bata duniya.” jikin mami yayi mugu mugun sanyi “hankalinta yayi matukar tashi cike da tashin hankali ta cigaba da mgn “babu wanda ya wuce qaddara adamcy wannan alamarin yana cikin qaddaearku .sannan kowani dan adam mai laifi ne “haba sweetheart me yasa wasu lokutan kike kin gsky ne ?wannan qaddara ne ko tsabar iskanci ko son rai ?”qaddara ne adamcy “no no!! sweetheart iskanci ne kawai “ta matso kusa dashi ta zauna tare da kamo hannunsa cikin nashi “munji munyi laifi ka zama mai yafiya domin Allah da kanshi yana son bayinsa masu hakuri ni kuma ina son adamcy nah ya kasance acikin jerin mutane da allah yake so dan Allah ka yafe mata kodan halin da take ciki .”


numfashi ya sauke sannan yace naji zanyi tunani akai daga hk bai sake cewa komai ba ya runtse idanunshi .”na kawo maka abincin nan ne ?”anya sweetheart abincin nan zai samu shiga ? bari naje na kawo maka ko kad’an kaci bai ce mata uhm ba bare uhm har ta fice byn wasu mintuna ta dawo d’akin daya daga cikin masu aikinta na biye daita mai aikin ta ajiye tray ta qara gaba yayinda mami ta zuba masa abinci sai da mami ta matsa masa sannan ya fara ci bawani abinci kirki yaci ba ya ture plet din gefe ahankali ya maida bayansa ya jingina da kujera da yake zaune akai tare da zamowa kad’an yana duban maminsa itama mami shi take kallo “ba dai har ka koshi ba adamcy ?”ya d’age mata girasa d’aya “ko na hado maka tea ne ?dakin ya dauki shiru har tsawon minti goma batare yayi ko tari ba sai da mami ta sake yin mgn yace mata baya bukata gajiya mami tayi da zaman ta fito ta koma dakinta ta cigaba da rarrashin mrym .”



Ranar kwana marym tayi batayi bacci tana juyi da tunanin matsayar rayuwarta yayinda maganganun mr ata yake barin kunnuwanta da zuciyarta su huta “bance ina son na haihu daita ba shiyasa bana bukatar wani ciki daga gareta wannan cikin ba nawa bane nãta ne har abada kar wanda ya sake dangantani da cikinta tayi wani irin juyi da karfi wanda yayi sanadiyyar da yar cikinta ta qara tokare mata qirjinta ta runtse idanunta gam .”haka ma mami bata runtsa ba da zarar taji motsinta zata mike ta tamvayeta ko akwai abinda take bukata ko akwai inda ke mata ciwo .”washegari tun da sassafe mr ata ya fice daga gidan ya wuce office wanda sai lokacin maryam ta samu damar runtsawa . bai jima da fita ba sai ga yaran mami gbdy tare da nana hauwa’u sun taho daita gida daga hospital kai tsaye d’akinsu aka wuce daita wanda ya sha gyara sannan suka dawo parlour’n mami inda mami take sheida masu abinda adamcy ya fad’a mata akan mrym daren jiya “kalmarsa sunyi tsauri dayawa akan mrym yace “bazai yafe mata ba nasani mrym tayi kuskure amman yayi hakuri mana haka .”


“A halin yanzu zuciyata zafi take min banason na mutu na bar baya da kura na rasa yadda zanyi da adamcy hayaniyarsu da koke kokensu yasa mrym farkawa daga baccinta ta yunkura da kyar ta mike ta zauna tana murza idanunta sannan ta zura silipa ta fito nan ta iske mami tana kuka ita da yaranta wad’an da suka had’a kai suna nasu kukan daga can gefe ta hango wacce batayi tunanin ganinta ba wato nana hauwa’u dan a tunaninta gidanta zaa wuce daita , itama kuka take sosai rungume da babynta ta qaraso wajensu tana qare masu kallo d’aya bayan daya bayan ta gama jin duk tautaunawarsu sannan ta kira sunansu daya byn daya da sauri suka d’ago suka zuba mata ido.” murmushi ta sakar masu tana mai cewa “mai yasa kuke kuka ?atare suka mike suka kamota suka zaunar daita a tsakiyarsu “.


“muna kukan abinda adamcy yayi miki ne ta sunkuyar da kanta kasa tana lissafin fingers dinta “karki daga hankalinki mrym mu muna qaunarki kuma muna qaunar abinda zaki haifa mana ta sakar masu murmushin karfin hali wanda kana ganin kasan na dole ne dan tayi dan ta kwantar masu da hankali “me zaki haifa mrym mace ko nmj ?duk scan din da nayi mace yake nunawa“ masha Allah zaa haifa mana beautiful “ta tsura masu ido kawai suma duk ita suke kallo cike da kulawa “me zaa kawo miki kici ,tayi shiru tana tunani kafin ahankali tace na gode sosai yan’uwana , kunata qoqarin kuga kun fitar dani cikin damuwar da nake ciki,dole ne mrym damuwarki itace damuwarmu.”


ta sake numfasawa ta kai hannunta ta kamo hannuwansu gbdy ta d’aura akan cinyarta “duk naji tautauwarku ina neman taimakonku ,nasan nayiwa yaya laifuka masu girma tabbass na cancanci ya d’auki kowani irin mataki akaina ,na d’auki laifina “. “karki damu komai ya wuce in sha allahu zamuyi convincing din adamcy ya yafe miki “murmushi tayi tace “ko amafarki bazai yi ba mutumin da yake son ganin bayana ta yaya kuke expecting zai yafe min ?sukai shiru dan su kansu basusan ta inda zasu bullo masa ba amman zasuyi iyakar qoqarinsu ya yafe mata “ki kwantar da hankalinki zamu masa mgn kuma zai yafe miki ,da kuwa naji dadi sosai bugu da qari kuma ya maidake gidansa ku cigaba da rayuwa mrym tayi murmushi “kai da dai kun barmu haka kowa yayi rayuwarsa idan na haihu lafiya nayi aurena, shima yayi nashi ai kuwa zamu taru mu rusa auren da zai yi ai tunda bakiji dadinsa ba shima babu wacce zai kawo taji dadinmu gbdy suka saka dry har mami mrym ta karbi babyn nana hauwa’u mai tsananin kama da yaya hisham babu abinda ya bari nashi har yanayin fasalin kanshi na ubansa nan suka cigaba da hira a tsakaninsu .”


*****
Zaune mr ata yake a office dinsa yana rubuce rubuce dake gabansa yaji anyi knowking din glass door tare da cewa “sir ko zan iya shigowa ?”ko baa fad’a masa ba yasan muryar mai neman izinin shigowa dan hk kansa na duke ya bada izinin shigowa batare daya d’ago kanshi ba,a natse maryama ta shigo cikin office cike da matsanancin faduwar gaba jikinta sanye da doguwar rigar material tayi rolling kanta da mayafi muryarta can kasa tayi masa sallama. a ciki ya amsa mata batare daya d’ago ba ya cigaba da abinda yake “good morning sir !yana jinta yayi mata banza tmkr ba dashi take ba ganin haka yasa maryama ta ajiye masa takarda data shigo dashi ta dan ja baya kad’an ta sunkuyar da kanta kasa tana kallon zara zaran yatsun qafafuwanta masu matukar kyau da gaske.”



kusan mintuna shabiyar tayi tsaye bai ce mata ba haka zalika batace masa ba ganin fa idan batace wani abu ba haka zasu saura dan haka ta soma takowa ahankali zuwa bakin makeken table dinsa da yake zaune muryarta a matukar sanyaye tace “sir ga aikin na kammala.”ya d’ago kanshi a natse bai sauke kwayar idanunshi akoina ba sai acikin nata nan take kwayar idanunsu ya tsarke cikin juna wani irin yanayi mai sarkakiya da wuyar faasarawa ya ziyarci zuciya dama gangar jikin maryama da ata .”
a bangaren ata tsantsar soyayya da kaunar maryamarsa ne yake bin dukkan sassa jikinshi ji yake kamar ya zarta dukkan mazan duniya sa'a da Allah yasa ya ganta ,fatan shi Allah ya mallaka masa ita da zuciyarta domin ya samu damar nuna mata menene so tayi mashi so mai zafi wanda ya zarta wanda yayi mata idan kuwa hkn ta faru lallai zai nunkaya da'ita wata duniya wadda ma'abota so da shauki ne kadai sukasan zakinta,yanason
yarinyar kamar ranshi shi kanshi yana mamakin zazzafar soyayyr da yake ma maryama mai tafiya da dukkan wani motsi da bugun numfashinsa. “


a yayinda soyayya ke kutimemeniya da ata itakam maryama tsoro ne da kuma tarin fad’uwar gaban irin kallon da yake mata ya mamayeta “why mr ata yake mata irin wannan kallon haka? “Uhm sir ko zanen yayi maka idan bai yi ba sai naje na canza wani dan har yanzu muna da sauran lokaci ?firgigib yayi ya dawo haiyacinsa yana sauke wani boyayyen ajiyar zuciya sai dai bai ce mata uffan ba. takardar data ajiye a gabansa ya dauka ya fara dubawa yana cizan gefen lip’s dinsa har dimples dinsa ya lotsa tsantsar kyawunsa ya sake bayyana ya numfasa kana ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune yana kallon zanen yana jujjuya jikinsa “abinda kike son nace zanen yayi ko ba haka ba ?


Ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi masu dauke da mayakan yakin soyaya wanda sausauyi yasa ya kalli cikinsu sunanshi sorry saurin cire idanunta cikin nashi tayi tana batare data bashi amsa ba illa qoqarin sanyawa jikinta natsuwa da tayi dan kallonsa na sakata jin wani iri mummunar fad’uwar haba wanda batasan dalili ba ”ke..” ya kirata da haka Kmr bai san sunanta ba ta d’ago ta sake sanya kwayar idanunta cikinsa sai da yaji wani abu ya caki zuciyarsa lumshe mata tsumammun idanunshi yayi na second biyu ya bude fess akanta “kina son nace zanen yayi kyau ba ?”cike da girmamawa ta rausayar masa da kwayar idanunta wanda sauran kadan mr ata ya qarasa ficewa daga hankalisa “sai daya ja numfashi ya sauke ya mike tsaye ya soma taku yana duba farar takardar zanen bai tsaya akoina ba sai a jikin kofar fita daga office din ya tokare kafarsa daya da glass door tare da tsareta da tsumammun idanunshi ya soma motsa lips dinsa ahankali “kamar dai jiya ne zanen bai min ba …”



Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login