Showing 6001 words to 9000 words out of 182919 words

Chapter 3 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

340

mutun sak wani irin murmushin jin dadi ya bayyana akan fuskar sultana cike da jin dadi tasa hannu ta d'auka tana cigaba da kallon zanen "wannna ai irin zanen da ya adam yake bukata ne sak "tabbas idan yaga wannan zanen zai ji dadi sosai bari na kai masa nace ni na zana "ta juya da sauri ta nufi hanyar office dinsa alokacin da Kunnensa yake manne da waya yana magana da wani abokin kasuwansa ,yayinda hannuwansa duka ke aikin dadddana keyboard gefensa sectary dinsa ce tsaye rike da wani blue file tana dubawa ."



"Yes !muna da fiyye da abinda tunaninka ya baka ,eh !sosai kuwa akwai abubuwa masu mahimanci akan sakon dana tura maka kayi qoqari ka duba" ya fad'a yana cigaba da aiki can bayan kamar minti goma ya mike tsaye rike da system dinsa ya isa inda sectary dinsa take tsaye yana nuna mata wani sako tare da yi mata qarin bayani yadda yake son kasuwancin ya tafi bai gama rufe bakinsa ba yaji ana magana daga bakin kofa "tare da knowking " ko zan iya shigowa ?.Idanuwanshi dake manne da farin glas ya tsurawa kofar shigowa tare da yin shiru na second biyar sannan maganarsa ta biyo baya "yes !ahankali ta tura kofa ta shigo tana rausaya yana ganinta yaja tsaki ya koma kan kujera ya zauna ya dungule hannunsa duka waje d'aya ya d'aura akan table yana ciza lips dinsa na kasa wani irin numfashi ya furzar mai zafi daga bakinsa ya kawar da fuskarsa adaidai lokacin data garaso qefensa ta tsaya tare da ajiye masa farar takarda a gabansa "ko akwai abinda zaka ce akan wannan zanen ?ta gefen idonsa ya soma hango had'ad'd'en zanen ,a natse ya juyo gabad'aya idanuwan shi suka sauka akan zanen " kaga irin zanen sultuna ba?na sha fad'a maka ina da kwarewa sosai akan zane amman kullum gani kake ban iya komai ba to yanzu dai me zaka ce akan wannnan zanen sir ."?


Shiru ATA yayi tare da kallon zanen yana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba mai tsanani na shigarsa kafin a hankali ya d'an yunkura ya mike tsaye still idanuwanshi na kan zanen jikinsa a matukar sanyaye ya kai hannu ya d'auki farar takardar data ajiye a gabansa ya tsurawa design din ido sosai ,numfashi ya sauke da karfin gaske yana cewa "zanen yayi kyau kwarai da gaske sai dai sultuna ...."sai kuma yayi shiru yana dogon nazari akan zanen "ka gani ba yayi maka ba?" ai daman na sha fad'a maka idan kaga wasu zanen da nake zanawa sai kayi mamaki wannan yayi maka ba ?"
"No ...!"
ya fad'a a natse sannan ya cigaba da magana "wannan ba zanenki ba saboda ba wannan bane karo na farko dana ta'ba ganin shrmen zanenki?"sultana tai shiru yayinda jikinta ya d'an soma rawa saboda yanayin kallon da yake mata .yayi taku biyu yayi daf daita yana ciza lip's dinsa muryarsa can kasa yace " ki kace ke kika zana zanen nan ba ?" sosai kuwa sir ni da kaina na zana shi ya gyad'a kai ya koma ya zauna akan kujera yana sake kallon zanen yana jujjuya jikinsa tare da girgiza kai. can ya d'ago ya dubeta da kyau "kikace zanenki ne ?ya sake tmbyrta ta gyada masa kai alamun "eh! gabanta kuwa banda fad'uwa babu abinda yake "shikenan sultuna tunda ke kika zana ina bukatar ki sake zana min exactly irinsa yanzu "cike da tashin hankali ta kai hannu zata kar'bi zanen dake rike ahannunsa "okay kawo na tafi naje na zana ".


Ya janye farar takardar yana girgiza mata kanshi tare da lumshe mata idanuwanshi na second biyu sannan ya bud'esu fés akanta "ki zauna ga guri nan sannan ga kayan aiki nan duk anan kiyi abinda nasakaki ta tsaya cike da matsanancin tsoro da firgici tana dubansa tare da mamakinsa "wannan mutumin fa katon mugun d'an duniya ne wato dai sai yaga karshenta ?ta fad'a haka acikin ranta ."
Ganin ta kasa kwakkwaran motsi tana tsaye tamkar an dasata yasa zuciyarsa ta soma tafarfasa a matukar tsawace yace "zauna mana Kiyi aikinki ai nasan zaki iya tunda kina da tabbacin zanenki ne cike da tsoro tace "yes sir !ya girgiza kai ya zagayo gurin sectry dinsa ya cigaba da yi mata bayanin abubuwan da yake buakta tayi masa yayinda har lokacin sultana na tsaye cikin tsananin tsoro da tashin hankali "wani irin mugun kallo ya d'auketa dashi yana zabga mata harara,da mugun sauri ta samu waje ta zauna akan d'aya daga cikin kujerun dake fuskartasa ta d'auki pencil ta rike tana tunanin ta ina zata fara ?nan da nan ta qara shiga tashin hankali mai tsanani fiyye da wanda take ciki ahankali zufa ya shiga tsatsafo mata a fuska da sansar jikinta kallo d'aya zaka mata ka fahimce a matukar tsorace take ."na shiga uku nah na dibo ruwan dafa kaina “ta ina zan fara ?tayiwa kanta tamabyar hantar cikinta na wani irin kad’awa .”


Sectary dinsa ta d'auko file green ta mika masa ya kar'ba yana cewa sultana "are you done ? batare daya kalli inda take ba" muryarta da jikinta rawa suke gurin cewa "no sir ! ya gyad'a kai "yau zaki gane baki da wayo muddin bakiyi abinda nace ba ya fad’a a kasan ranshi ,wayarsa tayi ringing some ta d'auka da sauri ta mika masa ya amsa yana manna wayar a kunnensa yana cigaba da duba file din hannunsa at the same time yana magana a waya ."Sosai ya fahimci yanayin tashin hankalin da sultana ta shiga ya sauke numfashi ya ajiye wayar ya maida hankalinsa gurin sectary dinsa suka cigaba da tautaunawa har tsawon mintuna talatin sultana na zaune cikin tsananin tashin hankali batare da tayi abinda ya sata ba ."



ya sake yunkurawa ya mike tsaye rike da zanen maryama a hannunsa ya zagayo ya isa inda take zaune jin hucinsa numfashinsa daya sauka a gefen wuyanta yasa ta waigo a gigice jikinta na wani irin kyarma "ai daman nasan bake kikayi zanen nan ba , sam sam wannna ba zanenki bane ko har yanzu kina kan kece kikayi ?ya tambayeta yana ja da baya yayi taku biyu ya tsaya yana jira yaji karyar da zata sake girba masa ya samu damar cin ubanta son ransa." cike da tsoro da in ina tace" eh gaskiya ba nice nayi ba amman kayi hakuri."tayi mgnr duk a rud'e jikinta na rawa tamakr an jona mata wutar lantarki."ai daman ko baki fad'a ba nasani wannan bazai ta'ba zama zanenki ba ya fad'a yana mai sake tsurawa zanen maryama tsumammun idanunshi kafin ahankali ya soma tafiya yana cigaba da kallon zanen yana lumshe idanuwanshi har ya qaraso ya tsaya bayan sultuna nan take ta sake shiga firgici "”mai yasa kika min karya ?tayi shiru ta kasa bashi amsa gabad’aya ilahirin jikinta na sake d’aukar rawa “why did you lie to me ?yayi maganar a tsawace dan girman Allah kayi hakuri “enough !a ina kika samu wannan zanen ko kuma waye ya zana miki shi ?”
“No sir babu wanda ya zana min.”


“Where did you get this desing?” uhmm ammm daman sabuwar staff din da'aka dakatar d'azu mai suna maryama hussein ce ta zana ta barshi akan table a office dinmu."nan take gabansa ya cigaba bugawar da yake fiyye da kaida yana kallon zanen yana jin wani irin shauki a gabad'aya sansar jikinsa da jijiyoyin jikinsa wanda bai ta'ba jin irinsa akan kowace halitta ba sai akanta lumshe tsumammun idanunshi yayi sannan ya motsa lip's dinsa ahankali "daman mutane dakikai irinki ya zasu iya zane kamar haka ? Ke..! ya kirata da haka muryarsa a kausashe ta natsu sosai agabansa ya d'an rage girman idanunshi "ki daina shiga lamarina " ki tsaya amatsayin da kike dashi a wurina wanda ni ban ma d'aukesa da mahimmaci ba kin fahimci abinda nake nufi da hakan ? tai saurin gyad'a masa kai ya d'auke akanta "kenan zumunci dake tsakaninmu "ta sake gyad'a masa kai jikinta na sake d'aukar rawa dan yanayinsa gabdaya ya gama tsoratata" gud oya leave my office .."ai da mugun sauri ta juya ta nufi kofar fita ."


Komawa yayi ya zauna akan kujera qirjinsa na wani irin bugawa da karfin gaske a natse ya dinga kallon zanen ya kasa hakura da kallon zanen wani irin sonta ne Ke taso masa yana sake bin jinin jikinsa "soyayyata qaunata farinciki rayuwata kece komai nawa ya fad'a a fili tare da mikewa ya koma Kan doguwar kujera tare da zanen a hannunsa ya zauna ganin zanen yake tamkar itace a tafin hannunsa kwakkywan fuskarta yake ganin acikin kwayar idanunshi tana masa yawo can Jim kad'an ya mike tsaye yana lumshe idanuwanshi, abun mamaki ji yayi daidai saitin inda zuciyarsa ke makale a qirjinsa yana bugawa da karfi, ya kai hannunsa daidai saitin gurin yana runtse idanunshi "Tabbas yasan lallai idan bai yi wani abu akan lamarinsa da yarinyar nan ba yana daf da kamuwa da mummunar ciwon zuciya ,"amman me zai yi tunda yarinyar nan matar wani ce ?Ahankali ya dinga daga qafafunsa yana tunanin nemawa kansa mafuta "Adam !zuciyarsa ta kira sunansa da karfi "kayi qoqari ka mallaki yarinyar nan ta kowani hali kasa karfinka ka kwaceta kamar yadda ammar ya fad'a maka "kanshi ya girgiza yana cewa ai matar aure ce ,tô shikenan ka dawo daita kusa da kai ganinta kusa da kai zai d'an samar da natsuwa arayuwarka "na koreta da kaina kuma na sake dawo daita da kaina ?ya tambayi kansa "Kai ba zan iya wannan kasadar ba sosai yayi zurfi cikin tunani ya koma mazauninsa yay rewarning d'aukar safe yana kallon tun daga shigowarta har zuwa fitarsu har inda ta mari salim ya tsaya daidai inda suka tsaya acikin office dinsa yana kallo har sanda ta fito zuwa koridoor ta juyo tana kallon office dinsa fuskata kwance da ruwan hawaye ."naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi lokacin daya kawo inda salim ya sake shan wani marin a hannunta "wani sanyayyen murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa ya kai hannu yana shafa sajen fuskarsa yana cigaba da murmushi " daman nasan dole zakiyi rigima princess."


Cike da sanyin jiki ya janyo wayarsa ya kira mataimakiyarsa ringin daya ta d'auko "kizo! ya fad'a ataikaice yana hura hanci ya d'auke idanunshi akan kallon da yake qaramin tv sakamakon knowking din da akai ,umarnin shigowa ya bayar yana sake daukar zanen maryama sectary dinsa ta shigo ta qaraso ta tsaya cike da girmamawa "sir gani !
" wannan zanen maryama né ba ? "Nata ne sir lokacin da kace naje na sallameta na isketa tana zana wannan zanen ina ganin saboda tashin hankali data tsinci kanta ciki yasa ta manta dashi amamn tabbas nata né "lallai wannan yarinyar tana da baiwa tana da kwarewa akan irin ra'ayina amman kuma zuciyata ta koreta "sir ko zamu kirata ne ?ya wani d'ago da sauri ya kalleta a d'age "wai sir saboda cigaban kasuwancinka domin zata baka duk abinda kake so kuma zama daita riba biyu ne garemu ga iya zane ga sanin Kan kasuwanci ."


Shiru kawai yayi yaki kulata duk da abinda ta fada din abinda zuciyarsa da gangar jikinsa suke bukata né amman ya rasa dalilin daya kasa bata umarni."
ta kusan mintuna talatin tsaye a gabansa bai ce mata uhm ba bare umm umm ganin qafafuwanta sun fara sagewa yasa ta bud'e baki cike da tsaro tace "sir ko zan iya wucewa ."?da hannu ya bata dama .
wunin ranar cikin tsananin tunani yayisa duk inda ya motsa yana jinta ajikinsa da zuciyarsa ganinta yau ya qara wutar soyayyarta a cikin zuciyarsa .”kiran d’aya daga cikin yaransa yayi yace akawo masa sigari dan a halin damuwar da yake ciki ita kawai yake bukatar sha cikin kankani lokaci akayi knowking tare da neman izini ya bada izinin shigowa James ya ajiye masa a saman makeken table dinsa sannan ya juya da sauri ya fice .”yadda ATA yake cikin tsananin damuwar abinda yasa akayi ma maryama haka itama maryama ta kasance cikin damuwar maseefar dake bibiyar rayuwata kuka ta yini shiyasa kafin shida na yamman ranar jikinta yayi zafi tamkar garwashin wuta .


umma ce tsaye akanta tana shafe jikinta da jikakken towel byn ta bata magani tasha ta zauna kusa daita ta riko tafin hannunta cike da tausayawa , bata son rasata kamar yadda ta rasa sadam dinta saboda qaunar da take mata yasa idan ta ganta cikin tashin hankali itama take shiga cikin damuwa .”“ta rasa gane meke sa abubuwa suke juya mata baya haka ?dame zataji ?da kiyayyar mutanen gidansu ko kuwa da wannan jarabawan dake bibiyar rayuwarta ? ahankali maryama ta bude kwayar idanunta ta tsurawa umma “sannu kinji maryama allah ya baki lafiya”Ameen “ karki damu komai mai wucewa ne kuma duk abinda Ke faruwa dake da sanin allah,ki qara rike addua duk wanda yace allah to allah zai isar masa in sha allahu bazaki sake fita zuwa koina da sunan neman aiki ko wani abu makamancinsa ba sai dai ya biyoki har gida da azinin allah “Allah ya nuna min wannan lokacin.”tayi maganar muryarta na rawa” sannu kinji maryama zakiyi farinciki arayuwarki “shi kuma mr ata yaje can ya qarata ya rike aikinsa ai da can ba da aikishi kika rayu ba muna nan aiki zai biyoki” naunayen numfashi da ajiyar zuciya maryama ta sauke tana mai runtsa idanunta dan idan akwai abinda ta tsana a halin yanzu shine mai kamfanin creation .”


Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 3


Kira ne ya shigo wayar umma dan haka ahankali ta mike tsaye ta qarasa inda wayarta take ajiye akan qaramin table din dake d’auke da hoton sadam wanda hakan yasa maryama sake bajewa akan katifa tare da sakin wani marayan kuka mai ban tausayi tana toshe bakinta da hannuwanta dan kar umma ta jiyo sautin kukanta “hakika Mr ata bai kyauta mata ba ,bai mata adalci ba meye laifinta data cancanci wulakanci ?idanuwanta ne suka shiga hasko mata kyakkyawar fuskarsa da kwayar idanunshi wanda ita acikin idanunta muninsa take gani da masa kallon mugu azzalumi mara imani da tausayi ,kuka take sosai zuciyarta na mata zafi da quna tana mai sake toshe bakinta dan bata son umma tajiyo sautin kukanta amman ina abinda batasani ba tunin sheshekar kukanta ya kaiwa kunne umma ziyara. Allah Allah take taji wake kiranta dan hankalinta kacokan ya koma ga maryama dan haka sai faman kiran “hello !take amman bata jin sautin komai sai na saukar numfashin mutun “hello !”wai wake magana ne ?tayi maganr a hassale cike da jin haushin wanda ya kirata sannan yayi mata shiru still dai shiru ne ya biyo baya dan haka cike da jin haushi ta katse kiran dif tana mita “sai a kira number mutun kuma ayi shiru aki yin magana “ta fad’a tana mai jan tsaki da dangwarar da wayar akan table ta qaraso inda maryama take ta zauna kusa da tace “wai ke bazaki saurarawa kanki da wannna kukan ba sai wani ciwo ya kamaki kisa mu shiga uku .?”


hawayen tausayin kanta ya sake gangaro mata tace “ummah Kiyi hakuri ta hanyar haka ne kawai zan raqe tarin damuwar dake tattare acikin zuciyata ta fad’a tana cigaba da sheshekar kukanta tare da dafe goshinta lokacin da zuciyarta ta hasko mata irin kallon da mr ata ya kafeta dashi wanda ko alamar kyafta idanunshi ba yayi haka ma mutumin daya kawota garesa mai tsananin kama dashi wanda yake ta qoqrin dakatar daita “duk da haka kukan ya isa haka kusan fiyye da awa biyar kenan kina abu d’aya kalli idanuwanki duk sun kunbura fuskarki tayi jajur maryama ta sunkuyar da kanta qasa tana sauke ajiyar zuciya akai akai .”“sun jima ahaka umma tana rarrashinta kafin ahankali umma ta kai hannu ta d’ago ha’barta tana kallon kyakkyawar fuskarta da ta ‘bata da ruwan hawaye, ta sakar mata murmushi mai ciwo tare da tsura mata ido “hakika duk nmj daya mallketa amatsayin mata shi ya morewa rayuwar duniya ,hakika mijinta zai yi saar samu mata kyakkyawa mai kyakkyawar zuciya da d’abia mai kyau ko waye wannan mai saar ?umam tayiwa kanta tmby tare da sakar mata murmushi kamar wacce ta tuna wani abu maryama ta mike zumbur ta nufi wajen kayanta dake d’akin umma ta zaro babban littafi wanda take rubuta abubuwan da suka shafi rayuwarta na bakinciki da farinciki ta dawo ta zauna kusa da umma “me kuma zaki rubuta “zan rubuta irin kalar wulakanci da’aka min yau a tun tsawon rayuwata wannna shine abinda aka min wanda yafi komai yi min ciwo “har da irin musgunawar da kawunki da matarsa suke miki “?a wajena bai kai wanda mr ata yayi min ba yasa an wulakantani an tozartani kuma ya ganni a gabansa amman hakan bai sa yaji cewar abinda yayi min zalinci bane he didn't even bother akan yayi ba daidai ba umma tsakanina da wannan mutumin allah ya isa nah ta fad'a a fili cikin zafin zuciya sannna ta fara rubuta kwanan wata kana ta soma rubutu tana jin zuciyarta tana mata zafi kamar zata fashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login