Showing 114001 words to 117000 words out of 182919 words

Chapter 39 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

374

ban barsu sun wuce ba sai dana tabbatar masu bazan masu wannan alfarmar ba,amman ni tsorona kar yaje su daidaita kansu da maryama din.”dan wallahi naga gabad'aya yanayinsa ya sauya alokacin da yayi maganarsa ta qarshe kinga kuma idan yaje ga maryama ta amince bani da uzurin da zan sake basu ."



cikin tsananin tsoro aunty salma ta sauke numfashi tana cewa "dan ubanta bata isa ta amince ba wallahi kuma bata isa ta taka wannan matsayin ba,wallahi muddin kaga maryama tayi aure to bana raye acikin duniyar nan , amman muddin ina raye ya'yana ne zasu rigata taka kowani irin matsayi ,kuji min tsinanniyar yarinyar kamar ita kadai ta kawo kan arziki duniya daga wannan ya wuce sai wannan yazo ?”wallahi salma ni kaina na firgita matuka da jin wannan alamarin da mun sani tun farko kin bar malam yahuza ya aureta mun huta da ganin wannan bakinciki .aunty salma ta share hawayenta tana dubansa karka shiga damusa in dai akan wannan matsalar ne ,ka yarda dani zan sa ayi aikin da duk duniya babu wanda ya isa yaga maryama yace yana sonta bare ma ya aureta, shi kuwa wannan mutumin sai ya dawo yana nuna mata zallar qiyayya daga yau bazai sake takowa zuwa wajenka da wannan zance ba ."aunty salma ta fad'a idanuwanta na kan baba gali dan murmushi yayi wanda yafi na kuka ciwo yace" na yarda dake salma, kiyi duk yadda zakiyi ya manta daita, me malamin nan yace miki akan yusif?"bar dan barouban yaron nan shima da kayan takaici sai aiki yayi kamar zai cisa sai kuma ya karkace ko da yake malam yace “bashi da laifi uwarsa ce take tsaye akansa da addua amman mu zuba ido muna zaune zai kawo kanshi” to to shikenan Allah ya taimakemu maganr dai suka cigaba da tautaunawa a tsakninsu ."




Cikin nutuwarta ta ko yaushe  ta tsaya a gaban kofar office dinsa sai dai bata hangosa ba bare ta nemi izinin shiga dan haka ta juya ta koma office dinsu inda ta baro madam some tace "madam naje banga mr ata acikin office din ba, may be ko ya sake fita ne "no no !! bai fita ba ,ki shiga ki jirasa zai fiyye miki akan ya ganki anan “maryama bata mata mutsu ba ta sake juyawa ta tura qofar office din ta shiga da siririyar sallama tana  hadiye wani yawu sannan  tana gogarin daidaita numfashinta da nutsuwarta dan wani irin qamshin turarensa office din yake mai bugar da zuciya .kusan mintuna shabiyar tana tsaye babu shi babu alamunsa dan haka  ta nufi wata qofar  data gani a bude dan tayi tunanin yana ciki  tayi knocking ahankali sbd sanin bayason hayaniya. Jin shiru yasa ta sake knocking din amma shiru dan haka ta juya ta tsaya tana cigaba da jiransa tare da sunkuyar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta ,kusan minti biyar tana tsaye bai shigo
ba kuma bata ji alamun yana ciki daya daga cikin  dakunan dake cikin office din ba , kai tsaye tayi tunanin qila baya nan ne dan haka ta  harzata
juyawa da zumar barin office din sai taji motsin bude qofar  ta juyo da sauri , ya qarasa fitowa hannunsa d’aya rike da qugunsa yayinda gaban  rigarsa ke bude har tana iya hango fara singlet din da yake sanye ajikinsa .”


a matukar tsorace take kallonsa kwayar  idanuwan
ta ya shiga cikin nasa da sauri ta juya masa baya sakamakon cin karo da tai da qirjinsa duk ilahirin jikinta da muryarta na rawa tace  "madam some wai kana son ganina.” ta qarasa maganar tana duban hannunta mai ciwo bai ce daita  komai ba har lokacin kallonta yake yana jin wani irin zazzafar sonta na fixgarsa ya mugun tsura mata idanunshi yana kallon yadda numfashinta ke fita da garfi .” kujerarsa  ya nufa ya zauna tare da gyara hannun  longsleev din dake sanye ajikinsa  tai shiru tana duban duk abinda yakeyi komai yayi kyau yake masa tana kallonsa ya janyo wayoyinsa guda biyu dake kashe ya  kunna sanin yadda yanayinsa yake tamkar mai  jinin sarauta haka  yake yasa ta matso gabansa a natse tace "sir ko akwai aikin da zanyi maka ?"no !” ya fad'a atakaice yana danna bell ,cikin second biyar madam some ta shigo "miko min ruwa mara sanyi "okay sir !”ta qarasa ta bude fridge ta dauko ruwa marasa sanyi sosai tazo ta ajiye masa "you can leave



"maryama ta d’an d’ago kanta ta kallesa cike da mamaki "yanzu kawai dan ta bashi ruwa ne ya kirata to mai yasa ita bazai ce ta bashi ba ?"kai wannna mutumin akwai izzar tsiya ."alamar ta zauna  yayi mata da tsumammun idanunshi .ba mutsu taja daya daga cikin kujerun dake gabansa ta zauna tare da sunkuyar da kanta tana mai runtse idanunta tana addua allah yasa labari  ya samo mata akan nadia ."
"Cike da jin kai  ya miki ya zagayo cikin  tak'onsa na izza ya tako zuwa inda take zaune , kujerar dake ajiye a gefenta ya janyo ya juyo daita gabanta ya  zauna bata ankara ba taji ya juyo da kujerarta.”
ta juyo suka fuskanci juna har qafafunsu na gogar juna nan take taji qirjinta ya soma bugawar da yake a duk sanda suka samu kusanci da juna tayi saurin runtse idanunta tana sauke numfashi da kyar ahankali taja kujerata baya .”sake matsota yayi yana sauke mata numfashinsa ,ta kame jikinta sosai duk yadda take jin numfashinsa na saukar mata bai sa ta bude kwayar idanunta ba har sanda ya kai lallausar tafin hannusa ya kamo hannunta mai ciwo.”



wani irin zafin yaji ya ratsa nashi tafin hannun ita kam ji tayi kamar ya jona mata wutar lantarki ne
tayi saurin bude idanunta sai dai ta kasa d'agowa ta kallesa .mr ata yayi shiru yana cigaba da kallon hannunta daya d'an kumbura kafin ahankali yace "kinyi aiki da hannu ne "?uhm amm "nayi amman ba wani mai yawa bane ".ta bashi amsa a diririce tana sauke numfashi, bai tsaya iya hannunta ba ya kai hannusa daidai saitin wuyanta yadda yaji wani abu ya tsalga masa a gabad’aya ilahirin jikinsa itama hk taji dan haka da sauri ta d'ago idanunta da suke a shanye  ta tsura masa  oly eyes dinta shima kallonta yake sosai ya tsura mata idanunshi  masu firgitar da mutum “bayan wannan ciwon akwai abinda ke damunki."?yayi mgnr kamar bashi yayi maganar ba  Ikc daya  tayi saurin kawar da kanta gefe kmr tayi kuka tace "babu komai ."kinci abinci?"tai shiru yayinda shi kuma ya cigaba da shafa hannunta mai ciwo ,wani iri ta dinga ji ajikinta har tsigar jikinta na tashi wanda a zahiri yake kallon haka "shima wani irin yaji a jikinsa tamkar an jona masa wutar
electric yayinda sha"awarta ta soma motsa masa .”



Zazzafan numfashi ya sauke kana yayi kasa da muryarsa sosai “kinga abinda ke had’ani dake bazan ta'ba tmbyrki abu ki bani amsa alokacin ba har sai nã maimata kanta " ya qarasa maganar yana furza mata iskan bakinsa muryarta a raunane tace “kayi hakuri banci ba ."wani zazzafan kallo yayi mata mai dauke da nau'ikan soyayya "ko zan iya sanin dalilin da yasa zaki kai har by this time baki ci abinci ba ?” "bana jin ci ne amman da zarar na koma gida zanci bai sake cewa komai ba ya mike ya fita wanda hakan ya bata damar sauke lafiyayyen numfashi dan muddin ya ta sata gaba irin haka bata samun tayi wadataccen numfashi ,bayan second goma sai gashi ya dawo hannunsa rike da cup fari sol da kwalin biscuit super two ya zauna tare da mika mata cup din tea ya rike mata biscuit din a natse tasa hannunta mara ciwo ta kar’ba tana cewa “na gode !”



ahankali ta kai cup din bakinta shi kuma yayi shiru zaune yana dubanta yana mika mata biscuits cike da tausayawa sannan yana tunanin hanyar da zai fito mata da maganar da take ransa sai dai har ta gama shan tea ta ajiye cup bai samu damar cewa komai ba tace "sir lokaci na tafiya idan akwai aikin da zan maka ka bani sai nayi maka a gida ?"babu sai dai ina son na yi miki wata tambaya idan babu damuwa?” da sauri tace "no babu wata damuwa zaka iya .”ta fad’a haka ne saboda tunaninta ko akan nadiya ne "mahaifiyarki tana zaune acikin gidanku ne ?"taji ya jeho mata tambayar da batayi tsamanin ita zai mata ba ta d’an saci kallonsa kafin ahankali ta gyad'a masa kai alamun “Eh! "shi wancan mutumin gali mai aiki a gidan borodi ." maryama tayi tsam da ranta gaban ta na faduwa da sauri sauri ,sosai ta natsu tana jiran taji mai zai fad'a akanshi "wani irin zama kukeyi dashi ?"muryarta a sanyaye tace “normal muna zaman lafiya da kowa ma "kin tabbatar da abinda kika fad’a ?"ta sake gyada masa kai ya sani ko zaa mutu zurfin cikinta bazai barta ta fad'a masa akwai damuwa ba .”ya sake janyo hannunta yana shafawa yace "me kika fuskanta atattare dani .”?


Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 33

Jikin maryama na rawa tace "ban .."ban fahimci komai ba ya d'an yin sama da hannun rigarta kad'an yace "ki natsu sosai maryama ki kalleni ki fad'a min  abinda kika gani "jikinta ya sake d'aukar rawa "ni wallahi ban fahimci komai ba sir  "uhm !"ya fad'a yana sauke numfashi tare da tsurawa  pink lip's dinta idanunsa yana cigaba da shafa saman hannun ta, muryarta na rawa tace "stop sir !"stop what !"? ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi "abinda kake yi ne bana so , “please stop  touching my body". ta fad’a tana danne kwalla dake kokarin zubo mata "ya kwantar da muryarsa sosai yace "bakya son ina ta'ba jikin ki? ya tambayarta yana ‘kara bin jikinta da wani shu'umin  kallo mai gigita zuciya da sauri tace "eh wallahi bana so "ta fad’a tana qoqarin zame hannunta amman ta kasa  dan yayiwa hannun kyakkywan rikon da bazata iya zamewa ba "dan Allah ka sakar min hannu sir  bana son kana ta'ba min jiki "ni kuma ina so"ya fad'a kmr bashi yayi mgnr ba, Ikc ma ya sake riko hannunta sosai  cikin nashi yana furza mata hucin numafshin sa , "shiyasa kikaji nace mai kika fahimta atattare dani kikace babu komai bayan ni nasan kin fahimci komai "ni allah ban fahimci komai ba wIh “ta fada tana fashe masa da kuka dan zuwa yanzu ta fahimci abinda yake nufi daita so yake ya lalata mata rayuwa ya cuceta ."



mamakin saurin kukanta yake , yayi notice dinta  kwatakwata kuka baya yi mata wuya"lumshe tsumammun  idanunshi yayi  yana saisaita nunfashinsa ,dan  buguwar da zuciyarsa take akanta ya wuce kaida  ,shi kad’ai yasan me yake ji a daidai
Ikc nan,  dan ji yake kamar ya fito mata da zuciyarsa taga halin da take ciki akanta ,jin taki daina kukan yasa ya bud'e idanunshi da kyar ya tsura mata kafin ahankali ya motsa lip's dinsa "me ye hk ? ya fad'a yana sake tsareta da tsumammun idanunsa "mai yasa kwatakwata baki jin kunyar kuka?"dole ne nayi kuka nidai dan allah ka daina ta'ba min jiki dan wani iri nake ji " ta qarasa mgn tana turo masa qaramin bakinta gaba, yaji kamar ya kai bakinsa kansu ya fara tsotsa a zahiri ,amman sai ya share yayi murmushin aciki dan shi yasan me take ji ajikinta kuma abinda yake bukata kenan, ta soma jin wani abu akansa shine hanya mafi sauki da zai mallaketa gabad'aya, ya sake shafa skin dinta yana sauke boyayyen ajiyar zuciya ,duk da ya san jikinsa nada tsananin taushi amma sai yaji nata kmr yafi nashi soft kai everything ma ko dan  akwai banbancin halitta ne?akwai abubawa ajikinta  dake mugun d’aukar hklsa a tare daita wanda a duk Ikc da yayi arba dashi ya kan gusar masa da hklnsa  ."



Bai san sanda yayi kusa daita sosai ba yace "fad'a min me kike ji ajikinki "wannan iskanci da kake min wallahi ji nake Kmr kana shafa min wu..."kafin ta qarasa maganarta taga ya tsareta da kwayar idanunshi  yana  jefanta da wani shi'umin kallo mai rikitarwa ,wanda yasa tayi  gaugauwar  yanke maganarta qirjinta na bugawa da sauri sauri .ba zato ba tsammanin zai doke mata baki sai jin saukar hannusa tai a saman lip dinta ya bata bal....wanda yasa tai saurin saka hannuta a daidai gurin saboda zafin da taji ya ratsata ta tsura masa idanunta tana kallonsa hawayenta na cigaba da zuba "wallahi mr ata mugu ne na bugawa a jarida ga azabar da take ji gashi yaki sakar mata hannu "dan Allah ka rabu dani nace bana so bana so kana ta'ba ni " ta fada tana bubbuga kafafuwanta a kasa hade da sakin gunjin kuka"kallo ta kawai yake without saying a word to her lallai ma yarinyar nan kurciya na mugun cinta.”
Inda mata ke nemansa ruwa a jallo idan akwai abinda yafi wanda yake mata ma suna só da zasu samu dama amman ita dan iskanci ta samun damar har kuka take tana danganta hakan da iskanci ."
hannunta ya saki  sannan  ya mike tsaye yayi taku kamar zai fita don ita a tunaninta  fitar zaiyi  sai ganin tayi  ya kashe light din office  din nan take duhu  ya mamaye office din ,nan da nan  kukan da take yi ya tsaya cak. tsoro ya ziyarceta Ikc daya hankalinta ya tashi  shayayyun idanun ta  zaro sosai cike da storo sakamakon ganin yadda yake tattaki zuwa inda take  zaune ."




da sauri ta mike tsaye  tana cewa "sir ni zan wuce gida "karki damu yanzu zamu wuce ."yanzu zamu wuce kuma ?"ta maimaita a fili zuciyarta na luguden bugu "eh zamu kai ki gida ne ko bakya so?" tayi shiru tana tunanin tare da nazarinsa "kin yi shiru ya fad'a yana dawowa gabanta ya tsaya yana kallonta ta d'an d'ago ahankali idanunta sukaci karo da sarkan zinarin wuyansa dake kwance a qirjinsa wani sabon tsoro ya kara dirar mata a zuciya wadda yasa tai  saurin sunkuyar da kanta tana runtse idanunta gam "ko kin fi so ki shiga motar hanya kuna gogayya da maza ?"numfashi kawai ta sauke batare da tace masa komai ba ."ahankali ya juya yana maida maballin rigarsa ya kwashe wayoyinsa ya nufi kofar fita tana tsaye kawai taji alamun baya gabanta dan haka tayi qoqarin bud'e idanunta taga har ya kusan ficewa daga cikin office din, tabi bayansa da kallo tana maida numfashi bata san me take ji adaidai wannan nan lokacin akansa ba .”idan tace tasan abinda take ji ko tasan abinda shi yake tattare dashi tayiwa kanta karya ta dai tasan a duk lokacin da tayi arba dashi ya kan gusar mata da hankalinta bazata ce so bane dan bazata jefa rayuwarta cikin matseefa ba dan ko soyayya ne sai tayi duk yadda tayi takicesa aranta bare ma bashi bane .”



Bazata ta’ba wannan ganganci ba shi kuma tasan yafi qarfin ya sota sai dai idan wata manufa garesa akanta idan ba haka ba ina ita ina shi hanyar jirgi dabam ta mota dabam ta sake numfasawa tana tunanin binsa ,ta bishi ne ko kuwa ta kama gaban ta ?" abu daya ne zai sa ta bishi saboda taimakon da zai mata  akan nadiya if not bazata sake ganganci binsa ba kuma tasan halinsa muddin taki baqaramin aikinsa bane yace ya fasa taimakonta ."ta kusan mintuna a haka bata motsa daga inda take ba kafin ahankali ta soma taku ta fito ta shiga office dinsu inda kusan kowa ya watse ,wasu tsirarrun maakatan sultan ne suke kai kawo ,ta kai hannunta ta d'auki jakarta dake ajiye akan table ta rataya a kafad'anta tana qoqarin fitowa daga office din wayarta ta shiga qara mara sauti,nan take ta tsaya ta ciro wayar daga cikin jakarta tana duba screen din wayar  suannsa ta gani yana yawo ahankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta d’aga "hello sir !"dan Allah malama ki fito karki ‘bata min lokaci .""O.."okay sir.."kafin ta rufe bakinta har ya katse kiran.”



jiki a sanyaye ta qarasa fitowa daga office din tana d'aga qafafuwanta da kyar,  a tsaye ta ganshi ajikin had’addiyar motarsa bmw fara sol hannayensa duka suna  cikin aljuhun won dashi , ganinta yasa ya bud'e mata murfin kofar baya sannan yayi mata alama ta shiga da kwayar idanuwansa,wani yrrr taji  a gaba d'aya ilahirin jikinta ahankali zuciyarta ya dinga bugawa da sauri sauri "wannan shine karo na biyu da yayi mata haka ,kuma a gaban masu tsaronsa da direbansa ,ba ita ba hatta masu tsaronsa da direban sa a ruwa sun dasa ayar tambaya akanshi dan duk tsawon lokacin da suka d’auka tare dashi suna masa aiki babu wanda ya samu wannan matsayin bayan mahaifiyarsa gashi karo na biyu kenan yana bud’e mata murfin mota .”ahankali maryama tayi kasa da  kanta tana d’ora hannunta d’aya akan d’aya tana d’an jujjuya jikinta alokacin da yake sake  mata alamar ta shiga, tai tsam da zuciyarta dake tsinkewa tana sake nazarinsa da kyau."



alamunsa da abubuwan da yake mata suna nuna mata kamar  só ne saboda duk yadda mutun yake sonta tana ganewa  amman kuma shi nashi salon ne yazo dabam shi yasa ta kasa fahimtarsa da kyau
Idan yayi wani abu kamar só sai kuma yayi wani abu kamar sha'wa ,za dai tafi ajiye abun a matsayin shaawa dan ina mutun kamar shi zai sota ?" "me mutun kamarsa zai yi daita ?"wace ce ita ?"waye ubanta a duk fadin kasar nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login