Showing 123001 words to 126000 words out of 182919 words
zata ganta ba duba da ba'a wannan company take aiki ba , maryama ta soma taku ahankali har ta qaraso kusa daita ta tsaya still kwayar idanun nadiya na cikin nata babu abinda maryamah ke gani alokacin sai tunanin ganinta na farko da taí lokacin da tazo gidansu amatsayin abokiyar aikin sadam yadda komai ke zuwa maryamah haka yake zuwa ma nadiya tunanin maganarta da sadam ne ya shiga dawo mata daki daki alokacin da take bashi labari samun aikinta a ATA company ."
"My heart na samu aiki a ATA company gsky naji dadin samun wannan aikin "ba dadi ya kamata kiji ba ,abun ki tsaya kiyi tunani ne ," me yasa suka kiraki adaidai wannan lokacin cewarsa "idan zaka tuna ai na ta'ba aiki dasu lokacin baya kafin naje kasar Índia kuma naji dadin aiki dasu haka zalika suma sun ji dadin aiki dani ,daman kuma ni bani da wani babban burin da wuce nayi aiki da ATA company yanzu ga dama ta samu sai yanzu nasan na samu aiki mai kyau "babu wani aiki mai kyau da kika samu dan baza kiyi aiki da wannan campany ba". ya fad'a tare da mikewa tsaye ya juya mata baya ,ta kallesa a matukar firgice tana cewa "me kake nufi da bazan yi aiki da wannan kamfanin ba ?ta tambayesa tana dawowa gabansa ta tsaya tana kallonsa ranta a bace "saboda maryama na aiki a d'aya daga cikin kamfanin su " to sai me idan maryaamah na aiki a AGC ? maryama na aiki a AGC ni kuma zanyi aiki a ATA ta ina zan hadu daita ."?
" kaga my heart banason wani rigima yanzu ."
kai yanzu ba kamata yayi kayi murna ba zan samu aiki da zamu ji dadin rayuwarmu kafin ka samu naka aikin ba ?"ya matsota sosai tamkar zai shige jikinta dan har masoyan suna iya shakar numfashin juna sannan ya kai hannuwansa duka ya riko kafad'unta tare da kwantar da murya "ina son ki samu aiki mana amman me yasa bazaki fahimceni ba idan ya kasance plan aka had'a miki fa taya zaki kubutar da kanki ?lokacin data kawo nan qirjinta ya dinga bugawa fiyye da kaida ."kafafuwanta suka kama rawa "tabbas zargin sadam ya tabbata plan akan shirya mata gashi kuma tana tsakiyarsa tsundum .
ta sake tuna maganar sadam ta karshe " ban amince kije ba amman idan kince lallai sai kinje duk abinda ya biyo baya babu ruwana kuma bazan saka kaina cikin rigimar ba sannan zaki nemini ki rasa rashi na har abada ".duk wannan sharad'in daya gindaya mata da zata fito sai da yayi qoqarin hanata hasalima shine dalilin da yasa bata zo akan lokaci ba dan rigima sukai sosai da kyar ta samu ta fito ."
"I hope that you recognize my face ?" maryamah ta tambayeta tana tsareta da kwayar idanunta masu matukar haske ." muryar nadiya na rawa da zuciyar ta tace "uhmm .." eh na gane ki sosai amman ban yi tunanin zanganki anan ba ." eh dole kiyi mamaki ganina tunda Kinsan abinda kikayi ,amman ni duk wannan bai dameni ba ,akwai tamabayoyin da nake son zan miki a halin yanzu,tambaya ta farko "me yasa kikazo gidanmu amatsayin abokiyar aikin sadam ? nan take gaban nadiya yayi wani irin mummunar fad'uwar kafin daga bisani ya shiga dukan tara tara, zuciyarta banda tsinkewa babu abinda take wani irin tsoro da matsanancin firgice suka mamayeta alakaci d'aya ta nemi dukkanin wata natsuwarta ta rasa kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin kwanciyar hankali da natsuwarta ."
"sai tambaya ta gaba me yasa kika bawa wani number wayata ya kirani a tsakar dare nazo aiki da wuri ?"nan ma gabanta ya ba da dammm hantar cikinta ta kad'a "bayan kin rasa wayarki na samu wayarki a hannun wani bayan haka kika kirani domin kiji wayar tana hannun waye da kika ji muryata kikayi discounting din kira me kike nema atare dani ?duk me yasa kika min wad'an abubuwan da kika min ?nadiya tayi shiru ta kasa kwakwaran motsi yayinda jikinta ya cigaba da rawa "ta rasa wace amsa zata bata domin gamsar daita yadda nadiya ke kallon maryama cikin rashin sanin me za tace mata haka mr ata yake binsu da kallo yana mamakin qarfin halin maryama ,yar yarinya daita amman akwai kwarewa da qarfin hali da rashin jin tsoron fuskantar duk wanda zatai magana dashi sai a yanzu ya sake gasgata qarfin halinta ba iya akanshi kad'ai take yi ba ,kuma yayi imani bashi ba duk wanda yayi mata ba daidai ba sai ta saisaitashi tare da yi masa karan tsaye arayuwarsa kamar yadda take qoqarin yiwa nadiya a yanzu "
gabad'aya nadiya ta rasa abun yi domin tana cikin wani irin gigita da tashin hankali wanda bata ta'ba shiga irinsa ba ,ahankali mr ata ya maida kwayar idanunshi sosai ya zubawa maryama kamar yadda nadiya tayi kafin ya juye fuskarsa ya sake had'eta tamau kamar yadda ya saba zuwa yanayi na kamewa da rashin d'aukar raini sannan ya kalli inda nadiya take tsaye cikin tsananin gigita ya bud'e baki ya fara magana "ke... ya kikayi shiru ki bud'e baki ki bata amsar tambayoyinta, dan matsawar baki ba bata amsar tambayoyinta ba lallai bazaki bar office din nan ba idan kuma ya zama lallai sai kin barsa to ki tabbatar a hannun hukuma zaki kasance ."ya qarasa maganar yana kallonta à kaskance "ta waigo da sauri inda yake tana kallonsa a matukar tsorace "yes me yasa kike bibiyar rayuwarta tare da caza mata kwakwaluwa?.bana bibiyar rayuwarta amman a wasu lukuta yana da kyau mu bar wasu abu saboda sirrin dake ciki dan ..."sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa maganarta "ko babu komai bazata fad'a masu abinda zai yi sanadiyyar rasa sadam arayuwarta ba domin shi din muradin ranta ne da soyayyarsa aka halicci zuciyarta kuma tayi imani sadam na matsanancin sonta ."
"me kike kokarin kice nadiya ?kinga karya bata da wani mahimanci arayuwar d'an adam bana bukatar kiyi min karya dan girman allah idan Kinsan wani abu akan yaya sadam ki fad'a min bare ma ni jikina yana bani kina tare dashi "what !"yes abinda kika ji shine abinda na fad'a "sadam fa kika ce ?"!nadiya ta furta sunansa tana duban maryama ?shifa fa ?"inji cewar maryamah "idan har sadam yana tare dani ai da tun tuni na kawo muku shi koda kuwa acikin halin hauka yake ko wani abu makanmanci haka idan kuma akan muryar da kika ji ne a waya kisani wannan muryar ba muryar sadam bane muryar sabon saurayina ne da zan aura ne ta fad'a tana saisaita natsuwarta tare da hura mata hanci amman dai zan fad'a miki wani abu domin nasan sadam bazai ta'ba fad'a miki tsakaninmu dashi ba ."nida sadam mun kasance masoyan juna ne mun had'u dashi a shekarun baya a makaranta ."
"abubuwa dayawa sun shiga tsakanina dashi tare da alqawarin aure byn nayi tafiya zuwa kasar india na samu labarin aurensa da mutuwarsa nayi matukar gigita da jin aurensa kuma naso da zarar na dawo kasar na maka shi a kotu .nan take maryam ta shiga wani sabon tashin hankali mai tsanani ta koma ta jingina jikinta da glas wanda shine madadin bango acikin office din tana cigaba da kallon nadiya cike da tsananin tashin hankali "."Ina ta qoqarin shirya yadda zan maka shi a kotu domin kwatarwa kaina hakina kwatsam sai kuma naji labarin mutuwarsa tsayawa fad'a miki irin tashin hankalin dana shiga maryama bata lokacin ne saboda ina mutuwar son sadam son da bazan iya bar ma wata halitta ba"
"actually akwai wasu hotunan da mukayi dashi kafin na bar kasar nan ,idanun maryamah ya cika da ruwan hawaye shi kuwa mr ATA jira yake nadiya ta gama maganarta ."nayi imani wadan nan hotunan suna cikin dakinsa kuma duk da baya raye zaa iya ganosu cikin sauki shine ma dalilin da yasa na dawo saboda banason kuga munin hotunan da mukayi dashi dan ya sha bani labarin yadda kuka yarda dashi kuka aminta dashi muddin kuka ga hotunan mu tare cikin wani yanayi kwarin gwiwarku akanshi zatai sanyi."hawaye masu zafi suka zubo akan kuncin maryama lokaci data ta tuna ranar data kamasa yana amsa wayar mace "banyi niyyar fad'a miki ba saboda nasan zakiji ciwo sosai acikin ranki amman wallahi wannan shine dalilin zuwana gidanku har na bukaci nabiki dakinsa sai dai a ranar ban samu naga hotunanmu ba shiyasa nayi tunanin sake dawo da daddare . lura da nayi idanunki biyu kina aiki yasa na kiraki tare da canza murya ni kaina lokacin zuciyata a tsorace take saboda banason kiga private pictures dinmu shiyasa nayi duk abinda nayi na kwashesu dan allah kiyi kokarin ki fahimceni amman fa kisani mijinki sadam ya yaudareni matukar yaudara ."
"maryamah sadam yaci amanata na yarda dashi na mika masa ragamar rayuwata amman ya watsar da yardar da nayi masa saboda bai fad'a min cewar zai yi aure ya barni ba ."na tafi kasar india da zumar idan na dawo zamuyi aure dashi amman sai labarin aurensa kawai naji yayi aure intakaice miki ana gobe zaa daura aurenku munyi waya dashi daace zaa ga wayarsa to da kin tabbatar da duk abinda na fad'a miki wata killa da zuciyarki ta buga sakamakon abinda zaki gani domin abubuwan dake tsakanina dashi ko Ke da kike matsayin matarsa bana tunanin kunyi irinsa dashi ."Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryama ta dinga furtawa acikin ranta hawaye na zuba akan kuncinta masu radadi da ciwo."
Yayinda zuciyarta ta dinga mamakin maganganun nadiya akan halittar data yi imani bazai ta'ba aikata hakan ba domin itama ta yarda dashi "maryama ki daina mamakin ,bazan ta'ba daina mamaki ba nadiya har sai naga sheida akan hakan yanzu ga wayarki a hannunki nayi imani idan har zaa samu hotunanku a wayarsa ko katin hotunanku to lallai zaa iya samu a wayarki tunda kuna tsananin son juna bai zama lallai ku iya rabuwa da hotunan juna ba "wannan haka ne maryama nadiya ta fad'a tana goge nata hawayen sannan tana qoqarin bude wayarta domin tabbatar mata da gaskiyar data bukata hotuna guda biyar ta nuna mata kuma duk suna tare da sadam babu kayan kirki ajikinsu cikin yanayi na tsananin soyayya "kadan ne wannan maryama ,kinga bazai yuwu na bar wayata a hannunki ba duk da nasan ganin wadan hotuna zasu miki wuya allah dai ya jikan sadam kawai ni zan wuce ta d'auki jakarta ta rataya ta fice daga office din ."
wani yanayi mai tsarkakkiya da wuyar misaltuwa maryamah ta tsinci kanta ciki rawar da jikinta yake yasa ta kasa tsayuwa sosai tasa duka hannuwanta ta dafe hannun kujera dan karta kai ga fad'uwa kasa da sauri mr ATA ya kamota ya zaunar daita akan kujera domin ya fahimci zata iya zubewa kasa, ya rike yatsun hannunta gam yana kallonta yana jin wani irin yanayi mara misaltuwa na shigarsa duk da yaso yayi ma nadiya nashi tambayar amman ganin tashin hankali da maryama ta shiga ya bar nashi amman lallai sai ya cigaba da bibiyi rayuwar nadiya domin akwai wata gaskiyar da yake tunanin ta boye wa maryama ".ahankali mrs ata ya sakar mata yatsun hannunta dake cikin nashi tare da mikewa tsaye yayinda maryama tai shiru dafe da kanta cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa."
"sosai tayi zurfi cikin tunanin rayuwa "a she haka yaya sadam yake cin amanar yardar da sukai masa ?"a she daman baya sonta ya amince da aurenta?"a she daman yana cin amanarta ne ?"hawaye ne kawai yake turereniyar zuba daga cikin kwarnin idanunta yayinda tsumammun kwayar idanun mr ata yake kanta yana kallonta tare da nazarinta kafin ahankali ya cire yar saman suit dinsa yana cigaba da kallonta tare da tura hannuwansa duka cikin aljihun wondon sa still idanunshi na kanta gabad'aya sai yaji damuwarta ta mamaye kowace gaba dake jikinsa."cikin takun nan nasa ya qarasa ya bud'e qaramin frdge ya d'auki goran ruwa ya rufe ya dawo inda take zaune tana kuka sai dai kukan nata ba mai sauti bane domin kuka take da zuciyarta ."
A natse ya bud'e murfin goran tare da mika mata "take some water "batare data kallesa ba haka zalika bata kar'ba goran ruwan ba tace "no ..!thank you." ta fad'a cikin wata irin sanyayyar murya mai tattare da tarin damu wa da tashin hankali "Ala hakikanin gaskiya ta dade bata shiga gigitaccen yanayi irin na wannan lokacin ba, ko zata kwatan tashi da wani abu sai dai ta kwatantashi da irin radadin da taji alokacin da taji tarihin rayuwar da iyayenta sukai kafin aure ,zuciyarta tayi matukar gigitata " iya tashin hankali ta shiga a zaunen da take "hakika yaya sadam ya cutar da umma ,sannan yaci amanar yardar da tai masa kuma yaci amanar tarbiyar datai masa da umma zata ga hotun sadam dinta cikin wannan yanayi da'aka kirasa da soyayya tabbas da take zuciyarta zata buga "why yaya sadam me yasa ka zabi irin wannan rayuwar ?"mai yasa kayi mana haka ?"duk wad'an story din da yarinyar nan ta bayar yanzu shi sadam din ya ta'ba fad'a miki ?."
yanayin da take ciki bazata iya bashi amsar tambayarsa zai fi ya barta taji da tashin hankali daya tsinci kanta ciki ,numfashi kawai take janyowa da kyar tana fitarwa "wannan shine matsalarki ana magana kiyiwa shiru ,okay but now this is your problem tunda kinsan komai akan mutumin da kika yarda dashi ,daman kuma matsalarku kenan mata kuna da saurin yarda da mutun kalli irin abinda ya saka miki dashi, yasan bai sonki mai yasa zai amshi aurenki har yayi nasarar dasa soyayyarsa acikin zuciyarki ?"is better to forget him in your life ki manta ko kuma nace ki goge wannan yarda da kika masa coz you trust him so many "
"bani kad'ai ba gabad'ayanmu ne ,mun yarda dashi mun aminta dashi shi din jigo ne acikin rayuwar ahlinmu kamar yadda mahaifinsa ya kasance alokacin da yake raye "sai dai mun yarda da yaya sadam dayawa batare da tunanin zai ta'ba mana haka ba ,we trusted him blind ,idan wani yace min yaya sadam zai aikata haka agare mu bazan ta'ba yarda ba duk da na ta'ba kamashi yana waya da mace amman siffa ta nagarta da kamala yaya sadam ya had'asu bazakace zai iya rungume wata mace da ba muharamrsa ba bare har ya kasance cikin irin wannan yanayin dana gansu tare da nadiya ba "I trusted yaya sadam without thinking ."ta qarasa maganar tana zubar da hawaye" I trusted him without thinking because I don't believe that yarda dashi din zai zame min qalubali arayuwata ."shiru ne ya ziyarci office din kafin ahankali ta cigaba da magana cikin muryar kuka "shikenan yanzu babu wanda zaka iya yarda dashi ?" ta fad'a wasu hawayen masu zafi da ciwo suka zubo mata "
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 36
Daga inda mr ATA yake tsaye yayi shiru tare da zuba mata tsumammun idanunshi yana kallonta yana jin wani irin zallar 'bacin rai na ratsashi saka makon jin sautin kukanta da kuma ganin yadda hawaye ke turereniyar gangarowa bisa kuncinta."
sosai kukanta ke ratsa kunnuwansa da zuciyarsa dake bugawa da matsanamcin qarfin gaske ."nan take yaji zuciyarsa na qoqarin motsawa sai dai ganin yanayin halin da take ciki alokacin yasa ya dinga kwantar da zuciyarsa yana qarfafata dan kar yayi misbehaved ."ahankali ya dinga danne matsa nancin kishin da yaji yana taso masa yana kai kawo acikin zuciyarsa dama gangar jikinsa ."naunauyen ajiyar zuciya ya sauke yana mai kwantar da murya cikin salo na kwantar da hankali ya soma magana a natse "maryama look at me!"ya fad'a kwayar idanunshi na kanta ,bata d'ago ta kallesa ba kamar yadda ya bukata sai dai hakan bai hanashi fad'ar abinda yayi niyya ba ,dan haka ya cigaba da magana "maryama dan ka yarda da mutun bai zama kuskure ba ko wani laifi ba ,kamar ka yarda da mutun as ending yaci amanar ka."ya qarasa maganar tare da yin shiru yana sauke numfashi yayinda ita kuwa sai faman sheshekan kuka take da sauke numfashi da qarfi tamkar wacce tayi gudun tsere tana sake jin mamakin irin rayuwar da yaya sadam dinta yayi da nadiya ,"
"yarda da mutun maryama ba kuskure bane amman dai yana da kyau kisan wani abu "shi wannan mutumin ya amince da aurenki ne alhalin zuciyarsa tana ga wata ."idan kuma har ya kasance yana sonki tô kisani da ya rayu zaki sha mugun wahala a hannunsa kasamcewar zuciyarsa tana tare da wata dabam, zuciyarsa tayi miki karya da yawa maryma sannan wannna mutumin baya miki soyayyar gaskiya ,domin kuwa duk abinda kake so tsakanin da Allah duk runtsi duk wuya kana qoqarin fad'a masa sirrin dake cikin zuciyarka ,ya so ya saka yaudara cikin lamarinsa koma nace ya saka yaudara.
A tashin farko da'aka bashi aurenki ya kamata ya fad'a cewar yana da wacce yayiwa alqawarin aure amman sai yaja bakinsa yayi shiru yaki fad'ar gsky kinga ko anan ma yaci amanar mutanen dayawa amanar nadiya amanarki da kuma amanar mahaifiyarsa ."abu na gaba da bai mutu ba da bazaki ta'ba sanin yaso nadiya ba kuma dole kuna tare zai koma gareta wala ya aureta wala kuma su cigaba da soyayyarsu ."mutumin nan ya cuceki dayawa dan ya dasa miki sonshi alhalin shi a zuciyarsa ba haka bane ,yayinda ke kuma kika d'aukesa a matsayin abun sonki da yardarki ,har kika d'aukesa matsayin masoyi kika yarda dashi kika mallaka masa ragamar rayuwarki you know this is your biggest mistake maryama domin kuwa kin so wanda bai dace da rayuwarki