Showing 66001 words to 69000 words out of 182919 words

Chapter 23 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

355

ba ,sai dai duk runtsi bazai d'auki raini daga gareta ba farar takadar ya janyo ya ajiye mata sannan ya janyo wata roba da kayan zane yake ciki shima ya ajiye mata "ki zanani ahaka .
"what ?" !
ta furta à matukar razane tare da d'ago fuskarta ta tsura masa yana rike da sigari yana zuga muryarta a raunane tace "sir kayi hakuri bazan iya zanaka kana shan sigari ba ka canza min da wani aikin na yarda "okay ! zana min mata da miji rungume da junansu suna kissing din juna a bakin kofa "oh my goodness god ya rabbi ka taimakeni akan wannan mutunin ta furta a can qasan makoshinta sannna ta sake tsura masa idanunta gbdy ta rasa natsuwarta ji take kamar zuciyarta zata buga haka ne ma yasa ta cigaba da kallonsa ko dai a buge yake ne ?sai dai tsaf yake abunsa idan ma baa a gabanka yake shan sigari ba bazaka ta'ba cewar shi din dan sigari bane dan babu abinda ya nuna ko ya sauya ajikinsa "Kina 'batawa kanki lokaci domin kuwa babu inda zaki har  sai kinyi abinda nake bukata."




Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 19



Zuciyar maryama cunkushe da haushi had’e da takaicin mr ata ta zari pencil din zane ta soma aikin daya sakata wanda tai masa laqabi da aikin mugunta tana zane bakincikinsa na sake ninkuwa a kasan ranta, yayinda zuciyarta ke wani irin zafi da suya .
ina ma zata iya murje idanunta tare da cire d’an burbushin tsoronsa dake ranta ai wallahi data zage kunjinta ta zabga masa rashin mutunci fiyye da wanda ya iya .amman ina bazata iya ba ,bazata iya karawa da mr ata ba ,dan ko a yanzu ya gano wani abu daga cikin rauninta domin kuwa ya fahimci aikinta yana da matukar mahimanci arayuwarta.
cikin kankanin lokaci ta zana namiji sanye da kaya wondo da riga tare da jacket sannan ta zana mace tana rungume da namiji sanye da dogon riga kanta lullu’be da mayafi,ta gama amman tsabar ‘bacin ran sigarin da yaketa faman bankawa cikinsa yana busa mata hayaki ya hanata d’agowa ta kallesa bare ta sheida masa ta gama.”shi kuwa mr ata zuba mata ido yayi ganin yadda ta gama amman tana jin wani abu aranta yasa ya sake ware qafafuwansa ya kunna wani sigari a ransa yayi murmushi ,shi ko kwana zasuyi a hk daidai ne.”



“ ganin muddin bata yi managa ba zasu kwana a haka ba damuwarsa bane dan ta tabbrwa kanta miskilancisa da jin kansa bazai barshi yayi magana ba , dan haka cike da tsinkewar zuciya da kyarma jiki ta d’ago fuskarta inda yake karaf idanunsu ya tsarke cikin juna ,ganin haka yasa maryama sake had’e ranta tamau dan bata son ya kawo mata wani sabon rainin hankali ko rainin wayo tare da d’aga masa farar takardar hannunta tana nuna masa alamun ta gama .” kina son ki zamo matsalata?” yayi mata tambayar yana tsareta da tsumammun idanunshi ahankali ta girgiza masa kai tana cewa “bazan ta’ba son na zamo matsalar kowa ba ,abinda kasani kenan sir , kuma wannan shine iya abinda zan iya yi . shiru yayi kawai yana ajiye qarshen bakin sigari acikin wani dan qaramin kwanon tangaran .”sannan ya cigaba da dubanta tare da cewa “tsarin yanayi rungumar bai min ba kasancewar babu remotic .“
ta kalleshi da tarin mamaki akan fuskarta lip’s dinta take matsawa alamun magana take son tayi masa sai dai ta kasa furta komai dan zuwa yanzu gaba d’aya a firgice take dashi .”


Yanayin zamansa ,yanayin kallonsa ,yanayin maganarsa duk sun canza dan hatta kwayar idanunshi sun canza kala yayinda shirunta ya
bashi damar kallonta son ranshi dan ko son kifta
ido ba yayi ,ga wani kalar murmushi da yake wanda shi karon kanshi bai san yana yi ba sosai itama ta shagala da kallonsa amman ita kallo ne dake tattare da tashin hankali da tsoro ,ahankali ya matso kusa daita ya hura mata iskar bakinsa da sauri tayi kasa da kanta tana jin wata irin fargaba yayinda gabad’aya ilahirin jikinta rawa yake .zuciyarta ta cika fal da matsanancin tsoronsa ,jigun sukayi daga shi har ita barin maryama wacce komai ya tsaya mata cak ,yadda bai sake yin mgn ba itama bata ko motsa ba daga inda take zaune sai dai kowannen su da abinda zuciyarsa ke saqawa acikin zuciyarsa .”
zurfa goshinta ta share tana kallon mr ata tace “sir ko zan iya wucewa “?numfashi ya sauke da kyar yana soka yatsan hannunsa a gefen bakinsa.”



“ kamar yace mata “a’a sai kuma yayi mata alama da hannunsa dan ya tabbatar muddin yace zai yi taurin kai zata maimata masa abinda tasaba ,dan yana ji kuma yana gani zata wuce abunta ta barshi zaune ” ahankali ta mike ta biyo ta raba gefensa zata wuce har jikinta na zozon jikinsa saurin d’auke numfashi yayi yana jin kamar ta jona masa wutar lantarki ne
ta juya a natse ta soma daga qafafuwanta da kyar gyara zama yayi tare da ware qafafuwansa yana bin every step of her tafiyarta kad’ai aka bar mutun dashi wani abu ne mai tsayawa arai bare akai ga samunta gabad’aya .”ahankali ya dinga bin kugunta da wani mayataccen kallo cikin salon magana yace “wannnan kugun zai sha wuya a hannuna domin kuwa bazan ta’ba saurara masa ba haka zalika wannna bakin rashin kunyar zai sha kissing har sai yayi kukan neman sausauci.”sai bayan la’asar maryama ta soma shirin tafiya gida taso kwarai ta sake yi masa magana akan sabon aikinsu amman sai taga gara kawai ta rabu dashi idan ranar ta kusa zata sake nemansa da maganar wata killa zuwa lokacin ya amince suyi .” wucewa tayi abunta tana tunani hali irin na mr ata “tsarin yanayi rungumar bai min ba kasancewar babu remotic girgiza kai tayi tana murmushi.”

******

Da daddadre da misalin karfe takwai yana zaune atsakiyar gadonsa hannusa rike da remut ya canza channel zuwa breaking news yana kallo sai dai hankalinsa baya wajen kallon labarai  yana gurin tunanin  yadda zai mallaki maryama ne cikin sauki har sanda mami ta shigo hannunta rike da cup din coffee'nsa bai sani ba ta tsaya shiru tana kallonsa tana nazarinsa kafin ahankali ta kira sunansa "adamcy "! yayi firgigib ya dawo haiyacinsa yana kallonta  "kar’bi !" ta mika masa cup tana cewa "wai meye matsalarka madadin naga lapto agabanka kana Kan aiki  amamn kayi busy kallo kana tunani ".
"na gaji ne sweetheart !"ba maganar ka gaji bane what's wrong with you?" ta tmbyesa tana kallonsa " me kake tunani yanzu  koda yaushe cikin tunani kake , meye matslarka"?  babu !"ya fad'a atakaice yana kai cup bakinsa "akwai gskyar ko damuwar da zaka iya boye min duk yadda mami tayi dashi yaki fad'a mata damuwarsa abinda bai saba mata ba Kenan  ya ajiye cup din hannunsa ya koma Kan kujera ya zauna ya dafe goshinsa."



ta dawo kusa dashi ta zauna" abinda kake min wani lokaci yana damuna "ya d’ago ya kalleta kawai kuma zai iya kashe ne tun kwanakina basu kai ba .”ta fad'a tana dubansa shi fa duk saboda wannna yarinyar maryam ne  yasa baya jin zai iya fad'a mata damuwarsa domin dai ya fad'a yaga mafarkinsa a yanzu zai iya janyo masa damuwa bugu da qari shi karon kansa bai san takamaiman makomarsa ba ta yaya zai fito da damuwarsa yana cikin zance zuci ya cigaba da jin maganarta "idan  ka kamu da soyayyar yarinyar nan dake aiki a qarqashinka fine let me know?"  ya sake d'agowa ya kalleta atsanake amman still bai ce mata  komai ba dan ba maganar kamuwa bane magana ce tsananin qauna kuma jin zai iya hakura daita duk runtsi duk wuya sai ya mallaketa kuma acikin wannan lokaci zai organizing wasu mutane dabam su nema masa aurenta ."



“Adamcy boye abu acikin zuciya yana saurin cutar da dan Adam,sannnan boye abu shi da kyau a zuciya yana da kyau mu samu wadan da zamu dinga sharing secret dinmu dasu. wannna shine karo na farko da ka boye min damuwarka .dan haka zaka iya tsintata cikin damuwar datafi taka .sam baya ma jin maganr da mami take masa dan hankalinsa gabaday baya ga mami yana ga yadda zai mallaki maryama ne, tunanin hanyar da zai bi ya bayyana mata matsayinta da kuma su wa ya kamata ya saka zuwa neman aurenta da yake bukata arayuwarsa yake .
Mami ta kallesa taga hankalinsa da natsuwarsa baya gurinta shima wannan ne karo na farko da take masa magana hankalinsa baya gareta ba dan haka ta mike ta fito daga d’akinsa sai dai zuciyarta ta tsayu ne akan danta ya kamu da son wannan bazawarar yarinyar ita ko zata so tagansu tare domin kasancewarsu waje d’aya zai tabbatar mata da zarginta “bazawara!”zuciyarta ta furta hakan a fili .”



Yau ma kamar jiya maryama bata qaraso gida ba sai daf da sallar isha’i a gajiye ta shiga bangaren ummah tayi mata sannu da gida “sannu maryama ya aiki ?”naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana cewa “ummah aiki da mr ata sam babu dadi amamn a haka zamuyita lalla’bawa ,ta fad’a tare da shigewa d’akinta murmushi umma tayi tace “ke dai da wannan mutun allah ya d’auraki akanshi idan ba haka ba bazaki ji dadin aiki dashi ba “maryama tana shiga daki ta fad’a bayi tayi wanka tare da dauro alwala ta fito daure da towel orange tana goge sansar jikinta byn ta gama ta d’auki terry dream’s ta feshe ilahirin jikinta sannna ta zura doguwar riga baka ta gabatar da magrib da isha’i dan zuwa lokacin an kira sallah byn tayi sallama ta ‘daga hannuwanta zuwa sama ta soma addua ta kira allah da sunan daake kiransa yake amsawa, kuma idan an rokesa dashi yake amsawa “allahumma as alukal bi anna lakal hamda laila ailla anta ,wahdaka lasharika laka ,al mannan ya badi’us-samawati wal ardi ya zal jalalu wal ikram ya hayyu ya qayum inni as alukal janna wa auzubika Minan nar har da mr ata tasanya cikin adduarta allah ya shiga tsakaninta dashi .”



Bayan ta kammala ta mike tare da daddumar sallah tana nadewa ta fito zuwa parlour inda umma take zaune ta d’auki jakar aikinta tana cewa “umma zan shiga wajen aunty idan goma tayi baki ganni ba ki rufe gida “to shikenan abinci fa bazaki ci ba ?ko zaki turo habib ya kar’ba miki ?”ko da yake ba abincin da kike so nayi yau ba .maryama tayi murmushi tana tambayarta “umma me kika dafa ?”tuwon samoviter ne da miyar kuka nan take maryama ta kwa’be fuska dan gaskiya bata qaunar tuwo da duk wani abu daya zamo loma bata só sai dai tsananin yunwa tasa taci dole “umma bari naje Allah yasa aunty ba tuwon tayi ba itama ”to shikenan yasa ki samu abincin da yayi miki idan itama tuwon tayi ki aiko habib ko ki kirani sai na dafa miki ko indomi ce “shikenan umma nah na gode .”tasa kai ta fito ta wuce part din mahaifiyarta inda ta samu abinda take so .”



Jollof din rice and beans aunty tayi wanda yaji busashen kifi da vegetable taci sosai kasancewar tana matukar so duk wani abu da zaa sarrafashi da wake bayan ta gama cin suka shiga hira da aunty da habib tana aiki habib ya dameta sosai da tambaya “daman kusan hayaniyarsa ke hanata zama a bangresu idan tana da aiki dan baya barinta tayi “heartbeat dan Allah ki bar aikin nan muyi hirarmu ta tsaida abinda take ta zuba masa ido “ance wannan mai kamfanin AGC din yana matukar takura miki dayawa ?Injiwa yace maka yana takura min ?yayi murmushi yana shafa fuskarsa “abakin lancin kanin yusura naji maryama tayi murmushi dan tasan tabbas a bakin yusura yaji “dan Allah ki bari naje naci miki ubansa mana ?yayi maganar cike da zolaya maryama ta zaro waje duk da tasan da wasa ya fad’a,can kuma kwashe da dariya “ai kuwa daga ranar na daina aiki dashi bayan yasa anci masa ubanmu,after dad ai wannan mutumin ya wuce da tunaninka shegen kanshi ne duk abinda mutun yake ji dashi zai sauke masa shi cikin isa da miskilanci shiyasa yanzu har cikin addua nake saka shi .”



“Ai kuwa kin kyautawa kanki gara ki dinga hadawa da addua kuma ki dinga binsa ahankali banson a cutar min dake “inji cewar aunty wacce ta mike ta nufi hanyar d’akinta ta barsu suka cigaba da hirarsu maryama lumshe idanunta ta soma tattara takardun zanen dake  watsewa  akan kujera ta mike tsaye tana cewa “gara na tattara na koma inda na fito dan bazaka barni nayi aiki ba ta leka dakin aunty tana cewa "aunty zan wuce part din umma "a can zaki kwana mu kulle gida ?eh ! aunty a can zan kwana halan habib ya hanaki aiki? maryama ta rausayar da kwayar idanunta kawai “to shikenan allah ya tashemu lafiya Ameen ta fad'a tana juyawa tare da kiran habib yazo ya rufe gida  ta wuce part din umma,ta iske kofa a bude dan haka turawa tayi kawai ta shiga inda iske umma tana massaging kafafunta tana runtse ido da sauri ta qaraso ta ajiye jakarta ta karbin man aboniki dake rike a hannunta tana cewa”ummah sannu bari nayi miki “to maryama nã gode allah yayi miki albarka “Ameen umma maryama ta fad’a tana mai tsananin jin tausayin umma aranta kuma tana tsanani qaunarta kuma zata kasance daita muddin rai zata maye mata gurbin komai arayuwa .”



Ahankali ta dinga massaging qafafunta tana mata sannu umma tayi shiru tana jin tsananin qaunar maryama aranta amman wani lokacin sai ta dinga jin tamakar zata juya mata baya wata rana ,domin d’an wani da uwar wani sai Allah duk da dai tana mata kyakkyawan zato haihuwa na dadi amman haihuwar da tafi kowace dadi itace haihuwar diya mace tasan koda sadam dinta yana raye watan wata rana sai taji kewar rashin haihuwar diya mace sheshekan kukan umma ne yasa maryama ta bar abinda take ta dago a gigice tana cewa “umma lafiya ?” ai sai umma ta fashe mata da kuka hankalin maryama yayi matukar tashi duk ta rude ta sake bajewa daga tsugunon da take a gaban umma ta riko hannunta cikin nata itama idanunta sun cika da hawaye dan haka kawai bata ta’ba ganin umma tana zubar da hawaye ba lallai duk abinda ya sakata zubar da hawaye abu ne mai girma “dan girman allah umma kiyi hakuri ki daina kukan “ko kin tuna da yaya sadam ne ?”



Umma ta sauke wani ajiyar zuciya tana damke hannun maryama cikin nata cikin muryar kuka ta soma magana “ba akan sadam bane maryama”to akan menene haka umma kike min asarar hawayenki ?”ina jin araina kamar wata rana zaki gujeni alhalin bani da kowa daga Allah sai ke maryama zuciyata tana tsananin qaunarki maryama rashin sadam ya tabani matuka amman rashin ki shi zai fi komai damuna “numfashi da naunayen ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan ta yunkura ta mike ta zauna kusa da umma tana goge mata hawaye tana cewa “a gsky umma baki ta’ba min abinda ya ‘bata min rai ba irin wannnan lokacin ba domin baki d’aukeni kamar yadda na d’aukeki ba nan take umma ta soma girgiza mata kai “umma nifa yar halak ce kuma nasan hallaci kuma zuciyata tana qaunarki fiyye da tunaninki bana tunanin akwai wata ranar da ni maryama zan juya miki baya ba duk runtse duk wuya umma nah tare ban ta’ba jin cewar bakece kika kawoni duniya ba zan kasance dake muddin rai mutuwa ce kawai zata rabamu dan Allah ki daina wannan tunanin ki daina tunanin zan gujeki ni amarki ce haka kema amanata ce ta qarasa maganar tana zubar da hawaye .”



Umma ta rungume maryama ajikinta umma kuka maryama kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani acikinsu sai dai har ga allah umma ta samu natsuwar zuciya domin bata son abinda zai nisantata da maryama idan ba aure bane .kuma a kullum tana mata fatan samun miji na gari sun d’auki sama da mintuna talatin suna kuka sannna umma ta soma shafa bayanta tana cewa “kukan ya isa haka maryama kiyi min afuwa yau ummanki ta sakaki kuka sheahekan kuka kawai maryama take tana narkewa ajikin umma “dan allah umma ki daina wannan tunanin aranki “in sha allahu maryama bazan sake ba kuma na gode matuka da qaunarki allah ya barmu tare allah yayiwa rayuwarki albarka Allah ya azurtaki da samun miji na gari wanda zai kular min dake ya kuma rike minke amana addua sosai umma tayita mata tana shafa bayanta har maryama ta samu natsuwa .”



Parlour’n ya d’auki shiru har na tsawon minti goma sannna umma tace “tashi muje ki kwanta gobe zaki office ta fad’a tana mikewa tare daita ajikinta ta d’aukar mata jakar aikinta da d’ayan hannunta suka nufi d’akin maryama umma na sake kwantar wa maryama da hankali ,ta ajiye mata jakar akan table sannna ta kwantar daita akan katifa ta zauna a gefenta tana tofe mata jiki da addaua tana cigaba da shafa bayanta tamakar wata yarinya qarama maryama tace, umma kije ki kwanta ki huta kema “to maryama sai da safe, Allah ya tashemu lafiya ta mike ta fito ta shiga dakinta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login