Showing 171001 words to 174000 words out of 182919 words
kasa zuwa maryama ta bar abinda take tare da mikewa tsaye tana fuskartata ina jinki yusura
“dan Allah Kiyi hakuri” hakuri kuma wani hakuri ai tunda mr ata yace kubani hakuri km kin bani hakuri komai ya wuce araina ,nasani ina sake baki hakuri ne saboda ban kyauta ba domin idan kowa yayi zarginki ni bai kamata ba kasamcewar tare muka taso ki yafe min karki tsaneni dan Allah “kai haba yusura wallahi babu komai nasan qauna ce tasa haka duk mai sonka shine zai ga kayi wani abun batancin ya nuna damuwarsa wallahi babu komai komai ya wuce ni dake qawaye ne kuma wannan matsalar bazata rabamu ba ,”haka ne maryama ta fad’a tana rungumota jikinta ta sausata rungumar datai mata tana cewa amman idan bazaki damu ba mai yasa kukayi wannan hotunan?” mukayi ko akayi mana?” to waye wanda ya iya munafurci haka ?”wallahi yusura ban sani ba kuma har yanzu nan da nake tsaye a gabanki ina wannan tunanin amman mr ata jiya ya tabbatar min an gama bincike” nifa tunanin yan gidanku dan wallahi idan gidanku suka gani akwai damuwa gara duk ma’aikatan kowa yasani akan mutanen gidanku .”
“ai tunin an wuce gurin dan sun gani shine ma dalilin rashin zuwana aiki kwana biyu sai da mr ata da wani abokinsa kukaje gida suka bada hakuri sukai masu bayani dalilin da yasa hakan ta faru yanzu dai komai ya wuce yanzu haka ban jima da fitowa daga office dinsa ba kuma yace zuwa anjima za’a kar’bi wayar kowa dake office din nan ,duk maganar da maryama take acikin kunnen sultana tayisa daga office dinsa ya hango maryama tana magana da yusura abayansu kuma sultana ce tsaye tana sauraronsu tana zance zuci “ina ai bazan bari ya duba wyata ba kafin ma ya duba na goge komai , sosai yake kallonsu ta cikin glass sai dai idanunshi kyam akan sultana yake yana nazarinta yana kallonta ta juya da sauri yayinda shi kuma ya cigaba da juyi akan kujera kai tsaye wani office dabam sultana ta shiga ta fad’a bayi jikinta na rawa ta shiga photos dinta tana cikin neman hotunan taji ya fixge wayar a hannunta yana cewa “me kikeyi anan ?
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
48
saurin d’auke numfashi sultana tayi tana dubansa fuskarta da bayyananen tsoro tace “uhmm amm babu komai kawai ina son goge wasu tsofafin hotuna ne acikin wayata “tsuma mmun idanunshi ya zuba mata yana mata wani irin wulakantaccen kallo mai razanarwa”lallai ma yarinyar nan tana da matuqar rainin hankali kenan har yanzu bata ma san waye shi ba ?“tsofaffin hotunanki zaki goge ?”ya fad’a yana kallon wayarta dake rike a hannunsa“eh tsofafin hotuna nake son na goge dan wayar tana hanging da alamun hotuna ne suka masa yawa.“
“kin tabbatar?”tayi saurin gyad’a masa kai alamun “eh!”jikinta na wani irin shaking alamun rashin gasky tana jin kamar ta fixge wayar daga hannunsa sai dai babu dama aikata hakan dan ko giyar meye akanta bata isa ba,bama zata fara gwadawa ba “.
“maryama !”
Ya kira sunanta tare da lasar lip’s dinsa na qasa “yes sir !”ta amsa masa cike da girmamawa tana kallonsa” ungo wayar nan ki duba min hotunan dake cikin har recently deleted ”yayi taku biyu ya qaraso inda maryama take tsaye ya mika mata wayar .”maryama tasa hannunta ta amsa ta shiga daddanawa tana dubawa ,shi kuma yayi shiru tsaye yana kallon sultana wacce hankalinta yayi matukar tashi fiyye da tunanin mai karatu”.
muryar maryama na rawa tace “ga..”gasu nan sir! “ga hotunanmu nan acikin wayar sultana wanda ke nuna alamun da wannan wayar aka fara d’aukarmu “nan take gaban sultana ya bada wani irin dum jikinta ya cigaba da kyarmar da yake mr ata ya kar’bi wayar a hannun maryama yana duba wa” ai nasani nasan itace.”
maryama ta d’ago kanta da sauri ta kallesa “na dade da sanin itace nayi haka ne kawai dan na kamata da hujja “.yayi maganar yana dawo wa kusa da sultana ya tsaya ji kake tass tass!! ya d’auketa da wasu gigitattun mari har biyu ajere wanda yayi sanadiyyar da numfashin maryama ya tsayawa cak, ya daina bugawa tare da dafe kuncinta tamkar itace ta sha marin dan tasan zafin marinsa yaso qara mata wani marin sai dai ganin maryama na shirin fad’uwa ne ya rikota cikin zafin nama ya makaleta da jikinsa hankalin maryama yayi mugun tashi ta kwanta lamo ajikinsa tana kyarma numfashi ya fesar ta hancinsa sannan ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta yana mata magana .”
halin da sultana ta shiga kafin ta dawo haiyacinta kuwa Allah ne kad’ai masani , ta wani zuba masu ido ganin yadda yanayin adamcy ya canza duk ya wani susuce akanta yana shafa kanta zuwa bayanta kamar wata jinjira yayinda bakinta yake motsawa ahankali ahankali “kayi hakuri karka sake marinta “tayi magan cikin tsananin tashin hankali ,bakinciki ne ya tokare ma sultana kahon zuciya wanda yasa hawaye ya fara zuba daga idanunta tunda take arayuwarta ba’a ta’ba tozartata irin na yau ba“mari kuma agaban maryama?mr ata ya maida kallonsa ga sultana yana hura hanci “this is your last warning sultan if I ever seen you do something like this wallahi zan kasheki da hanuna dan babu wanda zai min irin wannan tozarcin na kyalesa.”
“Kuma karki d’auka dangantakar dake tsakaninmu na duba”no ban duba wannnan halakar ba, kuma daman Kinsan bazan ta’ba duba wannan danganta kar ba, abinda na duba ke ma’aikaciya ce acikin wannan kamfanin kuma dokar ma’aikata shine idan an kama mutun da laifi za’a fara bashi warning tare da dakatarwa “.
yana gama fad’ar haka ya mika mata wayar ya tsaida idanushi akan maryama wacce ke kwance ajikinsa ya sake kai bakinsa daidai saitin kunnenta“malama ai sai ki tashi ko dan kin lafe.”
ya fad’a tare da qoqarin d’agota daga yadda ta kwanta ajikinsa da sauri ta qarasa barin jikinsa ta koma gefe guda ta tsaya tana cewa “ I’m very sorry sir bansan ya’akayi na kwanta ajikinka ba .”sultana kuwa ranta a matukar ‘bace take kallonta batasan adadin tsanar da takewa maryama ba ita dai tasan tsanace irin wacce take jin zata iya rabata da duniyar gabad’aya.”
“Ya adam you slapped me in front of this useless girl “?zaki ‘bace anan ne ko sai na qara miki nonsense kawai and kuma na dakatar dake zuwa aiki karki kuskura na d’aura kwayar idanuna akanki da sunan kinzo “ maryama muje ya tasa maryama gaba suka fice daga office din suka bar sultana tsaye cikin quna rai da ‘bacin rai .”kai tsaye office dinsa ya shige inda maryama take biye dashi abaya ya zauna a mazauninsa tare da tsura mata ido yana kallonta”.muryarta a sanyaye tace “na gode sosai sir duk da nasan kai din mutun ne da baka son ana yawon maka godiya akan abu amman dai dole zan gode maka thank you so much mr ATA ban cin kai ni nasan bazan ta’ba gano wannan gaskiyar ba a karo na biyu ka sake zama silar yaye duk wata damuwata” .”
Tunda ta soma magana ya tsurawa bakinta ido yana kallo yana Jin kamar ya Kai bakinsa ya tsosa ,sai dai har tai shiru na second goma bai iya aikata komai ba ta cigaba da magana “dan Allah sir kayi hakuri da sultana ka barta ta cigaba da zuwa aikinta dan ni na yafe mata coz I think she’ll not do it again in sha allahu .”haushi yaji har cikin zuciyarsa ”.bai sanda yayi magana a harzuke ba“Idan ke sha sha ce ni bashi bane idan ke sallamamiyar zuciya gareki ni ba itace dani ba nasan me nakeyi kuma nasan ciwon abinda aka min okay “.duk naji abinda kace amman kayi hakuri dan Allah dogon tsaki taja yana watsa mata harara yace “kin wani damu kanki ita datai laifi kinji ta bud’e baki ta bada hakuri !?“ya tambayeta yana sake jan tsaki “idan ta baka hakuri zaka hakura ?dan nasan dai dole zata ..”!
”shiiiiiii !”
Yayi mata alamar tayi masa shiru nan take tayi tsit ta shiga taitayinta tun kafin itama ta samu nata marin sai daya numfasa kana yace “idan kina da abunyi je kiyi dan ni bani da lokacin ‘bata wa akan wannan nonsense girl din” ya fad’a tare da mikewa tsaye ya shige d’akin dake cikin Office dinsa .”
ahankali tabi bayansa da kallo dole bata yadda ta iya ta fito anan suka ci karo da madam some ta qarasa kusa daita tana gaisheta tare da fad’a mata an gano wanda ya d’aukesu hoto sai dai bata fad’a mata ko wacece ba “kai marayama amamn gaskiya naji dadi sosai da’aka gano ko waye ,wallahi mr ata yayi min qoqari sosai banida abinda zance masa dan allah ki tayani masa godiya” ai ke din tabance a zuciyarsa sau nawa zan fad’a miki matsyainki a wajensa ?mutane nawa ne sukai aiki dashi amman ban ta’ba ganin wacce ya damu da damuwarta ba kamarki wanda hakan ke nuna alamun yana matukar sonki ne “haka dai kike fad’a amamn ni walalhi bazan ta’ba yarda ba, dan maganarki ma mamaki take bani ta yaya hakan ma zai kasance gara ma idan kince tausayina yake ji zan fi yarda da hakan amman batu na maganar so kam babu alamunsa saboda shi kulkum yayi min wani taimako cewa yake akan baya son ya samu matsala ne da aikinsa sai dai ban ta’ba jin ya burgeni ba kamar yau dan ya kwantar min da hanakali sosai .”
“da fari yasa naji zan iya cigaba da rayuwata ko babu kowa ,yasa na daina kwana ina kuka akan damuwa .” “ke dai kinyi sa’a ko babu so kinsamu matsayin kulawa a wajensa wannan ma kawai abun godiya ne bare kuma mu musan akwai so wanda kema kinsan da zaman haka mryama tayi murmushi ta juya tana cewa “a’a ni dai gaskiya bansan da zaman komai ba tana daf da shigewa office dinsu madam some ta biyota “maryama waye ya d’auke hotunan?.”maryama tai shiru na second goma sannan tace “gaskiya ban so na fad’a ko waye ba dan duk wanda ya rufa wani danuwansa asiri ,to fa asirin kansa ya rufa kawai Abar magana kamar zai fi “okay shikenan amman jikina ya bani kamar sultana ce amman Allah ya Kyauta ta fad’a tare da juyawa ta koma mazauninta .”
Mr ata na zaune yana amsa waya sultana ta shigo Office din kamar wacce aka jeho kai tsaye ta soma magana cikin wata irin murya mai karfi wanda yasa mr ata yace “excuse me just give me fiver second, disconecting din kiran yayi tare da had’e hannuwansa waje d’aya ya rike ha’barsa dashi tare da zubawa sarautar Allah ido “ban san me na kashe maka ba arayuwar nan “baka san abinda kayi a yau din nan ba sake qara min tsanar maryama kawai kayi a zuciyata .”
“amman kasani zan baka mamaki kuma lallai kasa hankalinka da kyau akanta duk abinda zai faru ,dan duk abinda ya samu maryama kasani kai ne sila ,kuma ka sawa ranka nice nan sultana na aikata ,wallahi wallahi maryama ce zata d’auki zazzafan hukuncin abinda kayi min .”
jin ta ambaci sunan maryama ce zata d’auki hukunci yaji gabansa yayi mummunar fad’uwa a sukwane ya mike tsaye yana taku yana mata wani mugun kallo mai tarwatsa zuciya kafin a natse ya motsa lip’s dinsa “look sultan bazan ce karki yi duk abinda kike so ba ,kiyi komai kike so but kisani ni ne na wulakantaki idan abinda nayi miki wulaqanci ne ba maryama ba why not ni kiyi facing dina ni da nayi miki hukunci “.
“okay saboda kinsan ni ba abokin karawarki bane shine zaki huce akan maryama we’ll go and head dan girman Allah karki fasa ki tabbatar kinyi abinda kike son kiyi karki fasa amman kasani duk abinda kike ji dashi nafiki iyashi ya fad’a a tsawace yana nuna mata kofar fita da yatsan hannunsa “leave my office.”””
da sauri ta juya ta nufi kofar fita tana wani irin haki ,kamar wata zautacciyar mahaukaciya ta sauka zuwa qasa ta nufi inda motarta take da kyar ta lalaba ta shiga motarta ta zauna ta kifa kanta akan sitiyarin mota wani irin kuka ne ya kufce mata ba dan taso ba , tayita kuka sosai dan haka ne kawai zai iya sanyaya mata zuciyarta sai datai kukan mai isarta ba mai rarrashinta tukun tayi shiru taja motarta ta wuce gida sai dai aranta ta kudurta duk runtse duk wuya sai taga bayan maryama sai tayi mata abinda har ta mutu bazata manta daita arayuwarta ba .”tana isa gida ta zayyanewa aunty abida komai daya faru a Office jin abinda tace ta fadawa ata yasa gabanta yayi wani irin mummunar fad’uwa hankalinta ya tashi sosai tace “kinga babu kyau ire item wad’an nan maganganun wani Abu yaje ya sameta ace kece maganganunki sunyi tsauri dayawa me yasa baki kirani ba ?ko me yasa bayan yaga hotunan a wayarki baki dawo gida ba ?.”
kinga irin taurin kanki tunda kika tura wa wad’an da kike bukatar suga hotunan nace ki goge kika ki ban san meye amfanin zamansa a wayar ki ba gashi kin ruguza komai dan damar data rage mana kinsa ta subuce mana tayi shiru tana jan tsaki tare da neman mafuta dan dole su samo mafuta kafin komai ya rincabe masu mikewa tayi tsaye ta shiga Kai kawo acikin parlour’n tana Neman mafuta can ya tsaya cak tace “dole ki bashi hakuri .”wa kenan zan bawa hakuri ?”adam zaki bawa hakuri “I can’t aunty duk wannan wulakacin da yayi min kuma na bashi hakuri ?”mari har biyu fa yayi a gaban wannan tsinanniyar yarinyar wallahi idan ban kashe yarinyar nan ba hankalina bazai ta’ba kwanta wa ba..”Kinga sultana dole fa yanzu ki ajiye komai ki nemi adam ki bashi hakuri dan nasan halinsa mahaukaci ne na bugawa a jarida zai iya sakawa ‘batar dake kuma babu abinda za’ayi .”
Sultana tayi shiru tana dubanta tana mamaki “kinyi shiru kina kallonta sanin halinsa ne danayi dan ga hindu nan ta isheni misali tunda aka ne metà aka rasa da kyar uwarsa tasa ya fad’i gaskyr inda take kuma duk da haka baa bada belinta ba ana kan bincike akanta dan haka ki kirasa ki bashi hakuri tun wuri ki kuma janye kalamanki kar wani abu yaje ya samu yarinyar yace kece kinga kin sakamu cikin damuwa .”
Bana tunanin aikata hakan ,bana tunanin zan iya bashi hakuri “ni dai ki tabbatar anjima idan ya dawo kije ki bashi hakuri idan ba haka duk abinda yabiyo baya babu hannuna”ban gane hausar babu hannunki ba ?ai kece kuwa mai hannu dumu dumu aciki ma kuwa dan Ina zaman zamana kika janyoni cikin matseefar da bansan ranar fitata acikinsa ba “sultana daga abun arziki ?ina arzikin yake ?tunda nazo wani kwanciyar hankali na samu ?”kullum daga wannan matsalar sai wannan I can’t take any more kuma zance naje na bashi hakuri bazanje na bashi hakuri komai ba bare na janye wata magana da nayi duk abinda zai faru ya faru am ready to die “ta fad’a da qarfi har sai da gidan ya amsa sannan ta fashe da kuka .”
Ganin ta fita haiyacinta yasa aunty abida ta rungumeta zuww jikinta tana rarrashinta “kiyi hakuri sultana Nima bansan abun zai zama haka ba, nayi tunanin zai amince da aurenki cikin sauki , amman kiyi hakuri “aunty Ina tsananin son ya adam akan na rasashi wallahi gara na mutu “subhanallah!”ki daina fad’ar haka bama zaki mutu ba muryarta da sheshekar kuka tace “to kiyi wani abu ko kiyi abinda zaki cire min son shi ko kuma kiyi abinda zai aureni “ki kwantar da hankalinki sultana muddin Ina raye zaki auresa ko ya aureki da girma da arziki ko kuma ya aureki da tsiya amman wannna auren babu fashi sultana sai kin auresa wani irin naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana sake rungume yaruwarta ajiki aunty abida tai shiru kwakwaluwarta na tunanin abun yi .”
Wunin ranar cikin farinciki maryama tayi sa cike da farinciki ta koma gida tana shiga bangaren umma ta shige tana cewa” umma nah na dawo ta fad’a tare da zama a kusa da umma ta ajiye jakarta “sannu da zuwa ya aiki”?” wayyo allah umma na gaji sosai kaina ciwo yake amman kuma alamun sun nuna kina cikin farinciki ?”
“sosai kuwa ammn wallahi kaina ciwo yake bari naje na kawo miki magani ki sha umma ta mike ta shige dakin bata jima ba ta fito rike da magani “ungo ki sha zaki ji daidai ta kai maganin bakinta saurin runtse idanunta tayi dan ta tsani shan magani umma ta dafa bayanata tana shafawa
da kyar ta amince ta sha “sannu kinji !”yauwa bari naje na kawo miki abinci umma me kika dafa ne mutuminki na dafa” shinkafa !? sosai kuwa shinkafa da miyar dayen kifi nayi “wow umma wallahi naji dadi sosai amman bari nayi fresh up nayi sallah ta mike ta shige d’akinta bayan ta gama komai ta fito adaidai lokacin da tuni umma ta kawo mata abincin ta d’aura akan qaramin table tana zaune tana jiran fitowarta.”
ahankali ta zauna kusa da umma ta soma cin abinci suna hira da umma “amm ummah ina son na tambayeki wani abu ?”ina jinki misali mutun ne yake da zafin rai sosai sai dai yana da kulawa da duk wani damuwarka, idan kana cikin damuwa shima yana tsintar kanshi ciki kuma bai ta’ba cewa yana sonka ba hassalima idan magana zata had’aku dashi