Showing 36001 words to 39000 words out of 182919 words

Chapter 13 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

360

A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 10


Maryama tayi shiru tana kallonsa da bayyanane mamaki a saman fuskarta yayinda qirjinta ke wani irin dokawa da sauri sakamakon bakincikin da yayi wa zuciyarta diran makiya ,ahankali ta soma nazarin maganarsa babu abinda yazo cikin kwakwaluwarta sai tozarci so yake ya tozartata baya ga haka babu wanda zai ga zanen data zana bai sa albarka ba had’iye bakincikinta tayi ta d’an saki fuska still kwayar idanunta na kanshi tare da sakin kasalallen murmushi wanda dole tasa mr ata ya lumshe tsumammun idanunshi wad’an da suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da wanda yake jin bacci .cikin sanyayyar muryarta mai taushi tace “idan na fahimceka kana son na sake wani kenan?”fuskarsa babu walwala ya lumshe mata ido tare da jinjina mata kai .still shiru tayi tana dubansa shima kallonta yake da kwayar idanunshi yadda yake kallonta ne ke sake d’aga mata hankali domin kallo ne da bata ta’ba cin karo da irinsa ba a tun tsawon rayuwarta.”




“ take tsoron yanayin yadda yake kallonta ya mamaye zuciyarta da gangar jikinta wanda ta rasa a muhallin da zata saka, kallon ne na gargadi ko kuwa na rashin mutunci ne ?”dan baza tace kallon soyayya bane dan matsayi da darajanta basu kai wannan matakin ba a wajen mutun kamarshi “wacece ita ?za dai tafi ajiyesa a muhalin gargadi ne .”tsaki yaja kafin a hankali ya kalli agogon dake d’aure asintsiyar hannunsa yace “mintuna talatin na baki kacal ki canza min “wani ta kalleshi kawai sannan ta motsa lip’s dinta “okay sir !”ta soma taku a natse har ta qaraso kusa dashi bai yi alamun bata hanya ba dan haka muryarta a sanyaye tace”sir ko zan iya wucewa ?”no ! ya bata amsa adake yana had’iye duk wani emotion din da yake ji a gabad’aya ilahirin jikinsa. “fuskarsa babu annuri ya sake sanya kwayar idanunshi cikin nata yana mai nuna mata wajen zama da d’an yatsan hannunsa “ki zauna kiyi anan .”“mamakinsa ya sake kamata .ahankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya cike da girmamawa tace “sir kayi hakuri na koma office nayi acan zan fi samun natsuwa “me zai cinyeki anan ?”ya watsa mata tambaya yana mai tsareta da idanunshi”.



Shiru tayi tana nazarin maganarsa komai zai yi cike da gadara da nuna isa yake kamar ba aiki suke akarkashinsa ba shi ya haliccesu , cike da fargaba ta rausayar masa da kwayar idanunta sannan tace “babu kawai banason nayi anan ne “to anan din zakiyi kiyi maza ki fara yana gama fad’ar haka ya soma taku.”dogon hancinta ta d’an hura tana jan tsaki a ranta bata jin zata iya kasancewa daga ita shi ,wannan firgitaccen kallon nasa kad’ai ya isa yasa ta kasa aiwatar da komai dan haka cike da danne tsoronsa ta kai hannunta zata tura kofa fita a matukar tsawace ta jiyo sautin muryarsa “ke bana son iskanci da rainin hankali ko ni saanki ne ?”yayi maganar tamkar bashi yayi ba .”


Jikinta a sanyaye ta juyo tana kallon bayansa kafin ta sadaukar ranta dan bata da yadda zatayi yanayinsa na yau babu sausauci komai zai iya faruwa daita idan tayi masa taurin kai ,gara tayi masa abinda ya bukata kawai ta kama gabanta,ahankali ta soma takowa cikin natsuwa a natse ta qaraso ta zauna akan kujerar daya nuna mata ta zauna tare da zabga tagumi, tana kallonsa ya zaro farar takarda guda d’aya ya d’auki roban da pencil gbdy yake jere aciki ya nufi inda take zaune ya ajiye akan table din gabanta “start!” ya fad’a a dakile sannan ya juya ya wuce ya koma mazauninsa tare da juyar da kanshi gefe yayi kamar bai san da wata halitta zaune ba .”



kallonsa kawai take tana mamakinsa yayinda zuciyarta ke cike da rauni tana jin kamar ta rusa masa kuka, kwatakwata bashi da imani bare tausayi ta kai dubanta ga farar takardar da ajiye mata sannan ta zari pencil d’aya ta rike tare da yin shiru tana tunanin ta inda zata fara ta d’auki tsawon minti goma sannan ta fara ,lokacin daya ga ta maida hankalinta kan aikin daya sakata ne ya juyo da hankalinsa gareta yana kallonta yana jujjuya jikinsa yana jin soyayarta na fixgarsa, domin ji yake matukar bayi saurin killaceta a gidansa ba zai iya rasa ransa akanta sam baya jin dadin yadda yake mata amman yarinyar ce ya fahimci tana da raini shi kuma duk son da yake mata bazai yarda ya d’auki raini ba zai sota hakazalika zai hukuntata idan tayi masa ba daidai ba ” .



bayan kamar minti goma ya mike tsaye maryama taga tahowarsa amman bata d’ago kanta ba dan kwata kwata bata son ko kallonsa a yanzu dan kallonsa zai haddasa mata jin mummunar tsanarsa acikin ranta ,har ya iso inda take zaune ya tsaya akanta yayinda ta tattara dukkanin natsuwarta kan zane da take bata d’ago ba ,har sanda ya janyo kujera gabanta ya zauna tare da ware qafafunsa still bata bar abinda take yi ba .ahankali ya gyara zamansa ya duko da kanshi daidai kanta yana kallon zanen. numfashi ta sauke ta bar abinda take tana jin yadda qirjinta Ke bugawa da karfin gaske sakamakon dab da junan da sukai wanda da zai matso da kujerar kad’an zasu iya had’ewa da juna “ki cigaba da aikinki kada ki ‘bata min lokaci kisa nayi asara .”ya furta cikin wani irin salo da sautin murya hucin bakinsa da numfashinsa na shiga hancinta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa “.



“sir ko zaka ..” bata kai ga yin magana suka ji an turo kofar glass din office din an shigo .”sautin muryar ammar dake d’auke da sallama yasa mr ata ya waigo bayansa ido cikin ido suke kallon juna da ammar . ganin ammar bai sa mr ata ya mike ko gyara zamansa a gaban maryama ba illa ma ya cigaba da mata bayanin yadda yake son tayi masa zane da kallo ammar ya bisu yayinda maryama bata masa ba sai gyad’a masa kai tayi tana jin kamar ta fashe da kuka amman ta danne dan muddin ya gane hawayenta shine rauninta ta kad’e a hannunsa “so take ta d’ago su gaisa da oga ammar amman ta kasa dan wata irin faduwar gaba take ji saka makon kusancinta da mr ata gashi yaki mikewa bare ya barta ta samu natsuwa .”


ammar ya koma jikin window office din ya d’an zuge labule kad’an yana hango haraban ma’aikatan dan yasan ko yayiwa ata magana ba lallai ya sauraresa ba .sai da mr ata yayi raayin tashi dan kashi sannan ya mike ya tura hannuwansa duka cikin aljihunsa ya qaraso inda ammar yake tsaye batare da yace masa komai ba “mutumina kana shaa’aninka har kun fara soyayyar ne ?“oh my god sai ka bari taji? ya furta a can qasan makoshi ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimci abinda yace ba .”
murmushi ya kwace a saman fuskar ammar “kar dai ka tsaya ‘bata lokaci ?ammar kayi kasa da muryarka mana “okay amman mutumina kayi zafi zafi fa karkaje garin neman gira ka rasa ido kar wani yayi maka shigar sauri a ma’aikatar nan “babu wannan mahalukin a yanzu idan ka ganta da wani to ni ne idan zata só wani to ni ne .”ammar yayi murmushi yana kallon inda maryama take kamar tasan kallonta yake ta d’ago idanunta da suke ta tara hawaye tana dannesu ta saukesu akanshi tana qoqarin motsa bakinta domin gaishe da ammar yayinda ammar din tuni har yayi taku d’aya ya jiyo muryar ata cikin rad’a yana cewa “karkaje !ammar ya tsaya cak yana fuskatarshi “ko me yasa ?”gaisawa kawai zamuyi daita “bana bukata dan nasan halinka byn gaisawa har da rayuwata zaka shiga .”


sanyayyar murmushi ya subuce masa sanda yake hango kishinsa a fili “me kake tunani akaina ?amman dai tunaninka kar yaudareka kasan bazan sota ba ?”ata yayi shiru adaidai lokacin da wayar mr ata ta soma ringing yaja qaramin tsaki yana jin haushi “mutanen nan suna son d’aga min hankali wani tsakin ya sake ja sannan ya kalli inda maryama take yace “Ke ..”tana jinsa tayi masa banza tamkar bataji shi ba “am talking to you ina magana kina jina “.a sheke ta d’ago ta kallesa kwayar idanunta cike da rauni da ‘bacin rai “karki ‘bata min lokaci kin gama “?kamar tayi masa banza sai kuma ta tsinci kanta da ce masa “sauran kad’an na gama ,oga ammar ina kwana ?kina lafiya maryama ya fama da wannan abokin nawa ?numfashi kawai ta fesar “.tana ta’be bakinta ina ruwanta dashi bare tayi fama dashi ta maida kanta ta cigaba da aikinta.”


Ammar ya juya kan ata wanda ya koma mazauninsa shima kujerar dake fuskarsa yaja ya zauna “kai mutumina kabi yarinyar nan ahankali fa “wani abu kaga nayi mata ne da zaka zo min da wata magna ?” ji yadda kake mata magana, kana kallonta kasan bata jin dadin aiki da kai “kar Allah yasa taji ,kana ganin yarinyar nan muguwar yar rainin sense ce kai kaga rashin mutuncin da ta min jiya ace ba ita bace wata ce dabam da yanzu na koreta “me ye tayi maka ?amman bana tunanin maryama tana da matsala nayi aiki daita “nan mr ata ya shiga magana kasa kasa yana koro masa abinda ya faru ai kuwa ammar yayi dariya kamar me “wallahi tayi min daidai haba ai kai din ne baka da kyau shine ka wani tasa diyar mutane gaba kana son firgita masu yarinyar Allah zan fad’a mata ta cigaba da jajurcewa
“tashi mu bar office din nan karka ballo min ruwa .”tare suka mike ata ya zagayo suka fita wanda hakan ya bawa maryama damar aiwatar da aikinta a tsanake .”


Bayan minti goma ya dawo shi kad’ai ya zauna a mazauninsa ya tsarke hannuwansa duka cikin juna ya rike ha’barsa dashi yana kallon zara zaran yatsun hannunta dake kwance tana zane, komai nata dabam ne bai ta’ba ganin halittar data shiga zuciyarsa kamarta ba “kin sace zuciyata ya Allah ka shigar dani zuciyarta da rayuwarta domin na zama abokin rayuwarta na har abada ita dai maryama bata san halin da yake ciki ba ta dukufa kan aikinta.”bayan kamar minti shabiyar ta gama ahankali ta d’ago kanta karaf idanunshi ya tsarke cikin juna wani irin bugawa da karfi qirjinsu yayi take yayi saurin wayancewa “kin gama ne ?”jikinta a sanyaye gabanta na faduwa tayi saurin gyad’a masa kai .”ya mike tsam ya d’auki zanen data fara zanawa ya tako har inda take.”


tana ganin tahowarsa tai saurin mikewa tsaye ta mika masa takardar cike da girmamawa ya kar’ba ya soma dubawa yana taku ahankali ahankali acikin office din yana duba dayan zanen da tayi .gani tayi ya ajiye zanen farko da tayi a daren jiya sannan ya kai d’ayan hannusa ga zanen da tayi yanzu yayi kuci kuci da takardar ya watsa mata “shima wannan bai min ba har gara na farkon zaki iya tafiya sannan ki godewa allah zuwanki ma’aikatan nan ya gyara rayuwata yayi sanadiyyar sauyawata da wani labarin akeyi ba wannan ba akan iskancin da kike min jiya .”ya qarasa fad’a yana tsareta da tsumammun idanunshi ,bata bari ya qara magana ba ta ra’ba ta gefensa har jikinta na gogan nashi sbd kusanci ta wuce zuciyarta tamkar zata kama da wuta kuka ne ke qoqarin kufce mata amman ta danne saboda ganin idanun mutane gabad’aya taji aiki akarkashinsa ya fita ranta tana shiga office dinsu ta zauna tana sauke numfashi.”


maganganunsa suka soma dawo mata wanda ta kasa fahimtar inda suka dosa me yake nufi tana bukatar tasan me yake nufi “ki godewa allah zuwanki ma’aikatan nan ya gyara rayuwata yayi sanadiyyar sauyawata da wani labarin akeyi ba wannan ba akan iskanci da kika min jiya “kamar yaya kenan yake nufi ?wani mummunar abu yake yi mara kyau wanda zuwanta yayi sanadiyyar sauyawarsa ko me ?” to ita a wa kenan data sauyasa ganin kwakwaluwarta na neman daurewa yasa ta kad’a kai tare da yin watsi da maganarsa maimakon cigaba da tunani sai ta janyo jakarta ta fito da kayan aikinta ta fara wani aikin wanda some ta ajiye mata .”

******
Washegari

11:00 dot a office dinsa tayi masa gbdy ma’aikatansa suka dinga shiga office dinsa domin gaishesa a dakike ya dinga amsa masu kwayar idanunshi maryama kawai take son ganin sai dai har lokacin da karfe shabiyu ta buga babu maryama babu alamunta a office dinsa kamar yadda sauran ma’akatansa suka saba shigowa byn sun yi gaisuwa idan akwai aikin da yake bukata ayi masa sai yasa some ta basu mikewa yayi rike da wasu file guda biyu ya fita ya ajiyewa some sannan ya shiga office din da take aiki .”hangota yayi zaune tana aiki ahankali ya zarce inda take yace ta biyosa sannan ya juya ya fice daga office din ya koma office dinsa .”kamar maryama bazata tashi ba amman sai fahimci idanun sultana suna kanta dan haka tá mike ta shiga office dinsa ta samu waje ta tsaya a gabansa fuskarta a had’e tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa .”


gabansa ne yayi wata mummunar fad’uwar ya tsura mata ido ta bala’i qara shiga ranshi haka yake son mace jajitacciya mai natsuwa da kamewa “manyan ma’aikatana sun shigo domin gaisheni ke me yasa baki shigo ba ko kinfi karfin kizo ki gaishe dani ne ?”ta tsura masa ido kamar tace masa siyanta yayi ko ita bawarsa ce amman sai tace “shigowa gaisheka yana cikin kaidodin aiki a karkashinka ne ?”baya ciki ikona ne yasa hk “okay !ta fad’a tana gyara tsayu warta tana ciza gefen lips dinta alamun bazatayi ba .”
yaji kamar ya fixgota yayi mata muguwar matsar da zai sa ta shiga hankalinta ,ya tsura mata ido kawai har kusan mintuna talatin sannan yace ta dauki file din gabansa “ta kai hannunta ta dauka ta soma dubawa “ kije ki duba page 9 da 10 irin zanen da nake bukatar ne ki natsu Kiyi min aiki mai kyau “amman sir da ka kira wadan da suka fini kwarewa zaka fi samun abinda kake bukata kar nazo nayi maka kace bai maka ba .”ta qarasa fad’a tare da maida file din inda ta d’auka yayi murmushi aciki ranshi yarinyar nan tana son na koya mata hankali tana son nayi mata abinda banyi niyya ba “ki dauka kije kiyi abinda nake so taki d’auka ta cigaba da tsayuwa.”



a tsawace yace “take it and leave me my office”numfashi ta sauke tana yatsunsa fuska ta juya har ta kai bakin kofa yace “ke!” ta tsya batare data juyu ba “awa uku kawai na baki “ta qarasa ficew tana cewa “aikin banza ai dakasani ka bawa wasu sun maka kaga aikin shirme duk wannan abun akan idon some ya faru ta cika da mamaki karo na biyu kenan maryama ke sainsa da mr ata .”Ahankali sultana ta mike zata bar office din sai ga some ta shigo tace “ ina zuwa ?”tayi mata banza “at least ki zauna ki d’an yi wani aiki mana tunda kika zo yau bakiyi aikin komai ba.” sultana ta kalleta a wulakance sannan ta soma magana cikin tsananin fushi “kina hauka ne ? “aiki sai naga dama zanyi dan bama fama da yunwa da tallauci aikin nan ra’ayi ne ko nayi aiki ko kar nayi dole kuma abiyani saboda mahaifiyata tanada karfin iko acikin wannna kamfanin dan haka daga yau ido ne naki akaina dan ko mr ATA bai isa ya koreni daga wannan ma’aikatanr ba dan banyi aiki ba okay.”



Some bata ce mata komai ba har sultana ta qarasa inda maryama take zaune ”uhm Ke dai bagajiya da aiki kamar ba d’azu kikayi wani aikin yanzu kuma kin dukufa yin wani “me ya kawo ni ?”ai aikin ya kawoni kinga dole nayi”sultana tayi shiru can ta cigaba da mgn “duk aikin da mr ATA ya kawo bakya sallakewa ?”taya zan tsallake me ya kawoni idan ba aiki ba kuma dai ai shi din mai gidana ne dole nayi masa duk aiki daya sakani sultana ta cigaba da surutu mara ma’ana “maryama tace “kinga sultana kin dameni ni fa ina son aikina “ ko ma dai menen bazaki ta’ba burge mr ATA ba “banzo dan na burge kowa ba nazo dan nayi aiki ne oky sultana taja tsaki da numfashi sannan ta fita “.


Some ta tsaya akan maryama !tana kiran sunanta “yes ma ta tsaya kusa daita rungume da file “duk cikin masu aiki a kamfanin nan daga manya har kana babu wanda Ke iya maidawa sir magana saboda tsoro amman naga ko kad’an bakijin tsoron komai kina iya mutsu dashi kina iya magana dashi kai tsaye tun shekaranjiya hankalina a tashe yake sai gashi naga sir yayi shiru bai ce komai ba “Eh ! nima nayi tunanin zai ce wani abu sai naga bai ce ba sai abu na gaba nima ina jin tsoronsa kamar kowa “really!?” yes ma !ta fad’a tana sakar mata murmushi “na danne nawa tsoron ko nace so nake na cire tsoronsa dan naga alamar kowa najin tsoronsa shine nake son na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login