Showing 3001 words to 6000 words out of 182919 words
? kaima fa da bakinka kace matar aure ce amman kake son ya shiga hurumin ubangiji ?
a matukar fusace ammar yace "ni kasan iyakar abinda nayi akansa?"kasan laifin dana aikata duk akan ya sameta?"enough ammar ka takaita mgnrka dan bazan iya komai ba kuma karka sake zuwa min da maganar makamanciyar haka idan ba haka ba zan dagargazaka idan ka sake zuwa min da irin wannan maganar acikin alamarina tabbas ina sonta fiyye da komai kuma itace rayuwata amman bazan yi wasa da hakin allah ba ,bazan shiga hurumin aure ba dan haka ka kula idan ba haka ba zamu samu matsala yana gama fad'ar hk ya juya ya soma daga kafafuwansa cikin zafin rai yana cewa "me yasa rayuwarta take shiga rudani ne ?me yasa abubuwa suke faruwa dani ne wannan wani irin tashin hankali ne?me yasa tazo a matsayin matar wani ?"ya Allah! ya furta yana buga table din gabansa da karfi nan take tarin takardun dake ajiye akai suka tarwatse ya runtse idanunshi gam tare da dunkule hannunsa daya ya dauke numfashinsa dan so yake numfashinsa ya bar gangar jikinsa ko ya huta da wannan tashin hankali ,"maganar duniya salim yayi masa amman yaki motsawa haka ma ammar "both of you should leave my office !"sukaji sautin muryarsa cike da karsashi babu wanda yayi yunkurin barin office din illa salim daketa qoqarin kwantar masa da hankali shi kuwa ammar ko a jikinsa dan daman yayi masa haka ne dan yaji wani ciwo akanta "what are you stil doing here ?ya fad'a atakaice batare daya kallesu ba jiki a sanyaye suka soma ja da baya kafin ahankali daya byn daya suka bar office din ."
fitarsu ke da wuya ya sauke wani wahalallen numfashi ."ahankali ya zauna jagwab akan kujera kwakwaluwarsa ce ta shiga caji na neman mafuta dan dole yasan abun yi anya kuwa bazai d'auki shawarar ammar ba ?ya furta hakan a fili zufa na tsatsafo masa a saman goshinsa da karan hancinsa ahankali ya soma magana shi kadai"adam dan dole ka nemawa kanka mafuta dan zuciyarka na tsananin son yarinyar nan akanta kai ba kowa bane ka tuna tun lokacin daka dauka kana dakon soyayyarta tana da tasiri acikin rayuwarka kamar yadda ammar ya fad'a "to mai zanyi ?mai zanyi ?!!yayiwa kanshi tambayar da bashi da mai bashi amsa shiru yayi yayinda ya maida idanunshi ya runtse gam yana jin wani irin zafi mai tarwatsa sansar jiki."yayinda bangaren salim da ammar kuwa tautaunawa suke akan abinda ya faru salim ya dubi ammar dake gefensa hankalinsa a matukar tashe ya cigaba da magana "a zahirin gaskiya ammar baka kyauta ba sam sam bakayi wa adam adalci ba kafa san komai akanshi tun daga tahirin mafarkinsa irin tashin hankalin daya shiga alokacin da zaa aura masa maryam kuma kasan duk akanta ya kasa bawa matan dake mutuwar sonshi dama amman sai kayi masa haka kai da kamata yayi ka d'aukota ka kai masa ita ba sai kayi masa surprise ba "kai dan allah naga ka damu dayawa yarinyar fa bata da aure yanzu amman ta ta'ba yin aure ."yana gama fad'ar haka ya cigaba da tafiya da sauri salim ya biyosa ya sha gabansa yana cewa "da gaske ammar ?murmushi ammar yayi yace "wallahi babu aure yanzu akanta nan dai ya zayyana masa komai daya faru daita bari naje na fad'a masa salim ya juya zai koma ammar ya rikosa "ka barshi tukun zan fad'a masa da kaina amman sai naga karfin soyayyarsa gareta, ba dai yace ya hakura ba ?zan gani da gaske zai iya hakura daita kamar yadda ya saba hakura da komai ." da kallo salim ya bishi dashi fuskarsa dauke da murmushi yana mai qara godiya ga allah daya sa maryama ba matar aure bace ."
a qalla ata ya kusan minti talatin zaune yana nazarin maganar ammar wanda zuciyarsa take son ya dauka ahankali ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa tare da jan qaramin tsaki bai san me zaiyi ba idan yace zai dauki shawarar ammar "me kenan zaiyi ?"me ma yasa zai aikata haka ?duk runtsi duk wuya zai danne abinda yake ji akanta bazai ta'ba shiga gonar wani ba dakace babu auren kowa akanta ne to yana da tabbacin duk wanda yayi yunkurin aurenta to sai dai a bayan ransa amman yanzu bai ga abinda zai yi da wuce hakuri ba, yayi hakurin rashin ganinta abaya a yanzu kuma ya zame masa dole yayi hakuri da sabuwar qaddarar data samesa ,bama zai bari wani mahaluki yasan da zaman wannan labarin ba ". mikewa yayi cikin sanyi jiki zuciyarsa cike da rauni yana jin kamar ya zubar da kwalla ya shiga zagaye office din yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudun tsare kafin ahankali ya shiga yamutsa gashin kanshi sannan ya koma kan kujera ya fara aiki akan system
zaune ata yake yana aiki amman sam tunaninta yaki barinsa ji yayi kwata kwata gara kawai ya cireta gbdy aransa ya huta ."
*****
A matukar jigace maryama ta karaso unguwarsu da kyar qafafuwanta suka qaraso daita cikin haraban gidansu kai tsaye bangaren umma ta nufa tana layi inda ta iske su tare da hajiya grany suna ganinta a yanayin da take suka zabura suka mike cikin tsananin tashin hankali nan kuma suka shiga kallon kallo umma ta kalli hjy itama hjy ta kalleta a karshe suka maida hankalinsu ga maryama da kyar umma ta bud'e baki ta kira sunanta maryama !"da sauri ta qaraso gareta dan sam maryama babu kuzari ajikinta ai kuwa zubewa tayi ajikin umma ta fashe mata da kuka tana kiran sunanta umma .."
"Me..."me kuma ya faru dake maryama "?cike da muryar kuka tace " sun wulakantani umma sun tozartani a qarshe kuma sun koreni a gurin aiki ta qarasa mgnr tana sake rushewa da wani sabon kuka Shikenan na sake rasa aikina ban san meke faruwa dani ba kamar ni kadai ce acikin duniya ,laifin me nayi ?umma ki fad'a min meye laifina "kai kai karki sake cewa haka babu wani laifi da kikayi jarabawa ce ,itama hjy ta qaraso suka sakata a tsakiyarsu gbdy suka rud'e, umma na shafa mata kai hjy na shafa mata bayanta alamun rarrashi "akan wani dalili kenan suka koreki byn sun d'aukeki aiki ?" wai kawai dan nayi rejecting din ayyukansu wannan kawai shine dalilin da yasa suka koreni byn ban yi hakan dan bana so yin aiki dasu bane , nima ina son aikin nan amman alokacin suba'a tafini bukatar shi allah ka gani nayi komai saboda kai ne."
" kun gani ba !shikenan allah ya amsa adduata ba ke uwar yan kankaba yau ga abinda gwaninta ya jawo miki sarkin iya taimako cewar Aunty hasana data fito daga kitchen ".haba hasana haba Hasana !dame kike son yarinyar nan taji ?idan bazaki mata addua ba ai bai dace Ki fad'a mata haka ba." ta kwabe fuska koma dai menene tunda ta rasa aikin ai shikenan bukatata ta biya .ni a gurina wannan jarabawar daga allah ne kuma yana sane da komai bari zanje ma'aikatan da kaina naga mai kamfanin inji cewar umma "a'a umma karkije ,karki wani wahalar da kanki akan zuwa wajensu kawai suje su wulakanki a banza kamar yadda suka wulakantani "a'a bazasu wulakantani ba hakuri zan basu maryama "a'a ban yarda ba kuma wallahi ko kinje bazan qara komawa wannan kamfanin ba da sunan aiki bayan sun gama wulakantani sun tozartani har fa na fara aiki umma suka koreni basu ma tsaya sun fahimceni ba wai da gangan naki aikin dasu , wallahi banason aikin nan kuma kema bazan barki kije koina ba kuma ko zan mutu babu aiki bazan qara zuwa wannan kamfanin ba duk wannan maganar tanayi ne tana kuka har da shesheka "
umma ta rungumeta sosai ajikinta tana rarrashinta "kiyi hakuri maryama in sha allahu zaki samu sausauci ki cigaba da addau lokacin wahalarki ta kusan zuwa karshe da izinin allah Aunty Hasana ta kallesu tana turo masu baki alamun zund'e aranta tace "kwayi kwa gama idan wannan tsinanniyar yarinyar ce mai kashin tsiya ai duk inda arziki yake sai an korota ,sosai umma da hjy suka dinga rarrashinta har hankalinta ya d'an kwanta "yanzu umma kina ganin wata rana zan fita cikin wannan wahalar ?"sosai kuwa maryama zaki fita mana wannan ai duk matakin d'aukaka ne amman fa idan kika d'aure kika d'aina fadar duk abinda yazo bakinki duk maseefar data samu bawa baa son yana yawo fad'ar abinda bai dace ba,abinda ake so mutun ya yawaita furtawa inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ko lallaha illa anta subuhanaka inni kuntun minal zalim, ya hayyu ya qayyum ya zaljalalu wal ikram da sannu allah zai wanke miki zuciyarki da farinciki
."maryama ta share hawayenta ta zauna sosai a tsakiyarsu tana jin damuwarta ta yaye, ta kamo hannu umma cikin nata "wallahi umma bakiga kamfanin ba komai a tsare kuma na dade ina neman aiki a gurin tun alokacin da yaya sadam yaki amincewa da yin aikina dole ce tasa na barwa subai'a wancan aikin "karki damu nayi imani zaki samu aiki wanda yafi wanda kika rasa Ke dai ki rike allah da adduar allah zai bi bayanmu .maryama tayi cikin jikin umma tace "Allah yasa ummah ina sonki mamana murmushi umma tayi tace "nima ina sonki maryama in sha allahu zaki ga haske arayuwarki "ummanki kawai kike so maryama nifa ?hjy ta fad'a tana dungure mata kai lumshe idanunta tayi tana dariya suma dai dariyar sukayi ."
*****
ATA na zaune yana aikin tura sako wayarsa ta dauki ringing ya dauki wayar ya manna a kunnesa yana lumshe ido "yes kuna magana dashi ,okay kuna bukatar kaya new design ok just a second cewar ATA nan take ya kira sunan sectary ,sannan ya cigaba da abinda yake da sauri ta shigo ta tsaya tana cewa "sir ! ya katse kiran byn ta shigo still ya cigaba da daddana system "mutumin dana gama waya dashi sabon customer ne yana bukatar kaya sabbin design dan haka Kiyi kokari ki hada Kan masu fresh design da muke dasu su bamu design masu kyau ayi abinda sabon customer zai ji dadi fatan kin fahimta "yes sir ."ko mu gwada sabbin dauka mugani ? " Eh hakan ma yayi domin muga kwarewarsu " okay sir "ta fita da sauri "maryama hussein ?!ya furta sunan a natse yana danna keyboard din system dinsa da karfi sannan ya cire hannunsa ya jingina jikinsa da kujerar da yake zaune yana jujuya jikinsa "waye mijinta a wani unguwa take ?da gaske dai idan bai dauki shawarar ammar ba ya rasa natsuwa kenan kuma har abada dan ya tabbatar wa kanshi bazai iya rayuwa babu ita ba"waye mijinta a wani unguwa take duk yana bukatar yasani amman dole yabi komai ahankali darajan auren da take dashi ." amman dai zai nemi ammar din dan yana son yasan wani abu a game daita kafin yasan abun yi ."
Cikin kankani lokaci sababbin ma'aikatan suka hallarar a cikin officer dinsa kowannensu rike da takardar zane ya yunkura ya mike da kyar ya zagayo daya bayan daya ya dinga amsa yana dubawa sai dai gabadaya babu wanda yayi masa acikin zanensu . yaja qaramin tsaki ya tsaya ya rike kugunsa yana aika masu da wani mugun kallo mai tattare da abu biyu ,abu na farko damuwar da yake ciki abu na biyu kuma takaicin basu yi masa abinda yake so ba "wannan shine iya kwarewarku?shiru sukai gaba dayansu zuciyarsu cike da matsanancin tsoro kallonsa kawai yana firgita da mutun bare kuma maganarsa cikin zafin rai ko waye kai sai kaji fargaba "ban d'aukeku aiki dan biyaku batare da kun iya komai ba ,na daukeku né saboda kunce kun iya wannan shine karshen iyawarku ?ya sake jefa masu tamabyar data sake gigitasu suka ji kamar su falla da gudu amman babu hali ."wallahi duk na daukeku né saboda best design not nonsense ya fad'a a matukar tsawace ." sannan ya maida idanunshi Kan sactry" some can you see your self ina gwajin da kikace kinyi masu ?"sir duk angwadasu "most of the...."
"Culmdown ata ! aka fada tare da turo kofar office din ,shiru yayi yana dago tsumammun idanunshi zuwa kofar shigowa ganin sultana yasa ransa ya qara baci ,ya lumshe idanunshi yana furzar d iska mai zafi daga bakinsa fuskan natashi babu annuri ko daya sultana ta qaraso har gabansa hannuta rike da farar takarda "nazo da abinda kowa ya kasa kalli nan kaga" ta fada tana jujjuya masa jiki tare da kai takardar gabansa "kalli irin kwarewata nasan wannan ne exactly abinda kake bukata? shiru yayi zuciyarsa na wani irin tuttukin bakinciki "Listing !this is my last warnin karki kara shigo min office batare da kinyi knowking ba sannan idan zaki kirani kisa girmamawa call me with sir ..."yana gama fad'ar hk ya juya da sauri zai barta tai saurin cewa " okay sir !ta fad'a tana masa fari da idanu wanda ko kadan bai girgiza zuciyar ATA ba sai ma qara tsanarta da yayi "my design ! ta furta cikin salon jan hankali tana duban farar takardar dake rike a hannunta a kaikaice ya juyo ya fixge takarda daga hannunta ya tsurawa zanen tsumammun idanunshi dake cike da tashin hankali yana karewa zanen kallo yayinda ta cigaba da juya masa jikinta tana murmushi tana kallonsa sai dai gabanta banda dukan uku uku babu abind yake ."
Wani irin dariya ne yaso kufce masa saboda ganin abinda take takamar ta zana awajensa shi da jagwal gwalo bashi da wani bambamci amman ya danne dan dariya bata kamace masa ba a halin da yake ciki sai dai kana kallon fuskarsa zaka fahimci abun yaso bashi dariya wani irin sanyin dadi ne ya mamaye gabadaya ilahirin jikinta ta sake gyara tsayuwa tana kallonsa tana jiran taji me zaice ."a natse taga ya shiga matsé takardar har ya matseta gabadaya yana mata wani irin mugun kallo sannan ya kalli inda abun zuba shara yake ya cilla takardar aciki ."
sake fuskantata yayi cikin fushi yace "wa kike da suna sultana ko me ,wannan shine sakamakon abinda kike zana yana gama fadar haka ya juya ya soma tafiya zuwa mazauninsa wani irin numfashi ta sauke da karfin gaske tana kiran sunansa "ya Adam !a matukar tsawace yace "me zanyi miki ?wato burinka ka wulakantani a bayyanar nasi ba ?ta sauke numfashi tana furta why ?Kina san kisan ina da ikon wulakantanki ko bani da ?tayi shiru tana dubansa "to ki daina shiga tsabgata ki kama kanki akan komai nawa ki tsaya iya inda aka ajiyeki stay a way from me sultana oya leave ..."ya fad'a yana nuna mata kofa tare da zabga mata harara cike da in ina ta kira sunansa "ya..ya Adam"i saida leave ya sake nuna mata hanyar fita ."
"Some ai na rigada na fad'a miki ki dauki kwararrun masu zane ba muna zane ba gabadayan ni banga na dauka anan ba "ya fad'a yana jan dogon tsaki "sir kayi hakuri kowannensu yana ta qoqarin yaga ya zana abinda zai burgeka "shiiii! "ya fad'a a tsawace "common design sun kasa abinda zai fi ki sallamesu kawai gabadayansu a nemo min wasu "kayi hakuri sir amman me zai hana a nemi maryama hussein nasan zata maka abinda kake ...,"stop ! ya tsadata a tsawace just stop some karki qara kuskure ina wata magana dabam kina sako wannan yarinyar ko kin fahimceni ? tai saurin gyada masa kai "bana bukatar wannan yarinyar kuma bazata sake tako kafarta zuwa cikin wannan kamfanin ba ,bama wannan kafanin ba har kowani kafani da suna aiki ita da yin aiki har qarshen rayuwarta ."
Bayan ya gama mgn ya numfashi yana kallonsu daya bayan "ku saurarani da kyau zan sake baku lokaci "yarinyar ce zaune a lap cike da natsuwa idanunta na Kan farar takarda tana zana doguwar rigar amarya da riga da wondo na ango sosai tayi concentration gaban doguwar rigar tana da shape daga gaba yayinda bayan rigar ta sauko wanda ya hade da dogon gashin mace yana bayani yana kallon maryama cikin kwayar idanunshi cike da matsanancin qaunarta ,lumshe lumtsatsun idanunsa yayi "wannan shine tsarin zanen da nake so ku dinga bin komai daki daki tare da tsare fatan kun fahimceni ?gabadaya suka hada baki "yes sir ."oya maza maza aje ayi daya daga cikinsu ya kallesa yace " kayi hakuri sir inshaallahu zanyi maka abinda kake so "very good ya fad'a yana tare da komawa mazauninsa ya zauna yana jujjuyawa akan kujera sannan ya dauko cup din glass cup dake cike da ruwa ya kai bakinsa ya kurba ya ajiye ya daura hannunsa akan hannun kujera yana cigaba da jujjuyawa."
Bangaren sultuna kuwa office dinsu ta koma ta cike da tsananin tashin hankali da takaicin abinda ATA yayi mata waya ne a kunnenta tana magana da Aunty abida "kinga wulakacin da yayi min kuwa aunty agaban ma'aikatansa bayan ya gama wulakanta zanen dana sha wahala na zana a gaban kowa wallahi bazan dauka ba Aunty bazan jura wannan wulakanci ba" nasan halinsa shegen gaske ne zai iya aikata abinda yafi wannan ki daina damuwa abinda ya kamata kiyi kokarin shine ki fara daukar hankalinsa ...amman Aunty .."No ki tsaya kiji abinda nace Kiyi shi zakiyi karki min mutsu dan duk ina yin wannan abun ne saboda jin dadinki ...."
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 2
Sultana na gama wayar da take idanuwanta suka sauka akan zanen da maryama tayi akan table , shiru tayi rike da wayarta tana duban zanen zanen ne mai Shege kyau da d'aukar hankali. zanen mace ce sanye da kayan weeding gwan sosai maryama ta kwantar da hankali ta zanata had'e da zana gashin kanta har gadon bayanta tamkar dai