Showing 165001 words to 168000 words out of 182919 words
hawaye ya fara zubo mata kan kuncinta ahankali ta fara rera kuka kasa kasa “idan har ya tabbata mr ata sonta yake kuma har ya kasa fitowa ya furta mata kuma yake son ta auresa matuqar ta auresa ba qaramin azaba da matsin rayuwa zata shiga a hannunsa ba koma tace tabani ta lalace dan tun ba’aje koina ba ya fara da taimaka mata zai yi Ina ga ta auresa ?” uwa uba yanayin da take ji akanshi ya bam bamta da sauran mazan “no no !!.” I can’t marry him ya Allah ka ji tausayina ka bani miji daidai dani dan wannan mutumin yafi qrfina kuma koda zuciyata ta kamu da sonshi wallahi sai nasa wuka na raba tsakanimu .”
Ahankali taji an dafa kafad’anta ta baya ,ta jiyo da sauri ganin umma yasa ta sake dafe qirjinta gam tana goge hawayen dake shirin sake gangarowa bisa kuncinta “har mr ata din ya wuce ne ?”ta gyda mata kai da sauri tana cewa”eh ya wuce “ya naga kmr kuka kika yi?numfashi kawai ta sauke dan bazata iya mutsa mata ba tunda tasan kukan take ,umma ta sake tambayarta amman taki bata gamsashiyar amsa “.to akan zuwanki aiki ne kike kuka ko wata magana ya fad’a miki “? still dai girgiza mata kai tayi “to me yasa zaki tsaya kina kuka ?” umma babu komai !”ta fad’a tana shesheka.”numfashi umma ta sauke tare da cewa “ikon allah haka kawai mutun ya zauna yana kuka to Allah ya Kyauta to amman idan kinji har cikin zuciyarki baki son zuwa aikin nan ki hakura babu lallai babu dole dan babu wanda zai takura miki shi yasa ma kikaji nace ya tuntubeki .”tana gama fad’ar haka ta juya ta barta ta shige kitchen tana tunanin me ya sakata kuka ?”Umma ta jima tsaye a kitchen tana qoqarin had’a masu abincin dare koda ta fito bata ganta ba dan haka ta wuce d’akinta .”
Acikin mota mr ata ya iske mb ya shiga ya zauna suka kama hanyar komawa gida mb ya d’an kallesa yace aboki hankalinka ya kwanta zuciya taga abincin ruhinta ”ya qarasa mgnr yana kallon gabansa yana murmurshi “babu laifi hankalina ya d’an kwanta tunda har na d’aura kwayar idanuna akanta “ata kana son maryama..” sosai mb ina sonta ina mata son da idan babu it acikin rayuwata rayuwata zata kare ne cikin garari da tashin hankali amman na rasa dalilin da yasa na kasa fad’a mata kai tsaye kuma wallahi ina son na fito na fad’a mata amman sai naji zuciyata ta kasa “girman kai da rashin son arainaka ne ya hanaka fad’a mata amman dai ya kamata ka d’aure at least tasan irin mutu war son da kake mata tunda ga dama ta samu ance aure za’a mata”friend do something before everything could have mess up to you .”
in sha Allahu i wil try dan ko yanzu nayi mata mgnr ta aureni !”yayi maganar yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa “kai Kai masha Allah mutumina ai an gama magana ,an gama wasan kawai game over sai mu fara shirin shan biki “tsaki ata yaja yana cewa “bata amince ba fa “yayi mgnr muryarsa a sanyaye kamar mai koyon magana” kamar ya bata amince ?” .
“am telling you!” yarinyar nan so take sai taga qarshena hankalinta zai kwanta mb ya saki dry mai qarfi yana cigaba da murza stearing “kar dai tayi wuji wuji da adamcy mami ?”ya qarasa maganar yana sake kwashewa da dariya numfashi kawai mr ata ya sauke tare da kamo lip’s dinsa na kasa yana cizawa a hankali “ka bita a hankali da sannu zata amince kasan ganin abun zatayi wani iri kmr shirin drama ne ace mutun kamarka zaka aureta batare da kuna soyayya ba ”yanzu dai mu ajiye wannna maganar in sha allahu komai zai zo da sauki maryama rabonmu ce da izinin Allah.”Allah yasa”ya amsa masa jiki a sanyaye .”
“ya kukayi daita batun cigaba da zuwanta aiki “ta amince ko kuwa “uhm ai yarinyar nan akwai d’agawa mutun hankali shiyasa wallahi nake jin bazan iya tunkararta da batu na soyayya ba gara kawai na aureta a aikace zata gane son da nake mata”Kai dan Allah kana ganin yarinya kmr mummuna inji cewar m.b “ya fad’a yana masa dariyar mugunta “Ai kana ganinta wallahi muguwar yar rigima ce ta bugawa a jarida.”
“ ai na lura da yadda take girgi zawa iyayenta kai alamun karsu amince” aikuwa zata janyowa kanta sabon tashin hankali domin kuwa bazan barta ba na dinga zuwa kenan Ina d’aga mata hankali har su fahimceni a qarshe su aura min ita kaga shikenan na huta .”mb yasa dariya yana sake dukan stearing motar “wallahi tunda nake ban ta’ba maganin mutun da girman kai da miskilanci mai cutar da kanshi ba kamar kai wai ka fito ka fad’a wa yarinya kana sonta ne abun kunya ko me ?ata ya girgiza masa kai “mb me yasa ka kasa fahimtata ne “ .?
“babu wani na kasa fahimtar ka,kawai kace tsoron yarinyar nan kake ji,kai yanzu a tunanin ka akwai halittar da zanji tsoro? ” gata kuwa na gani tsoron maryama kake ji “mb ba tsoro bane akwai dalilai sannan kuma wannnan yarinyar da kake kallo rikitacciyar yarinya ce shiyasa ma ta kasa fahimtata inda na dosa ko da yake har da kuruciya ke damunta ko nace irin matan nan ne da sai an fito an fad’a masu ana son su suke fahimta if not ko acikin kalamaina ya dace ta fahimceni .”
“Taya kake son ta fahimceka?”kai ma fa da naka kana da son takurawa rai dayawa tsoro ma zai sa ta kasa gane inda ka dosa da wannan tautauna war suka isa abdullahi estate mb ya sauke ata ya wuce gida.”koda ya shigo parlour’n mami babu kowa dan haka ya haye samansa ya kirata ya sheida mata dawowarsa .
bayan sallar Ishai bayan yayi wanka ya sanya Jallabiya brown colour mai gajeren hannu mami ta nufi samansa tare da d’aya daga cikin masu aikinta dake rike da trayn wanda ke d’auke da kayan marmari da hadin salad da qaramin flaks na ruwan zafi abayanta ta same mr ata zaune a parlour’n sa akan kujera hannunsa rike da remut yayi shiru yana kallon tv sai dai hankalinsa baya kan news din daake gabatarwa .har mami ta shigo bai san ta shigo ba mami ta umarci mai aikinta data ajiye trayn ta wuce cike da girmama wa mai aiki taja dan qara min table din glass din dake tsakitar parlour’n ta daura masa akai ta Kama gabanta inda mami ta qaraso inda yake ta girgiza shi sannan ya dawo haiyacinsa .”
Muryarta a sanyaye tace “adamcy me kake tunani haka ?”ya soma in ina yana cewa” babu komai ta zauna kusa dashi tana cewa “kace babu komai ?”ya d’age mata girarsa d’aya yana shafa sumar kanshi “ka fita cikin tsananin farinciki amman kalli yadda ka dawo kamar wani mara lafiya tayi mgnr tana kamo hannunsa cikin nashi inda nan take idanuwanshi suka sauka akan yatsun hannunta masu tsananin Kama dana mahaifiyar mryama “ya ka baro maryama fatan tana lafiya?”tana lafiya!”ya fad’a atakaice tayi shiru tana nazarinsa har tsawon minti biyar ta sake cewa “halan da kaje gidansu maryama wani abu tayi maka ?”ya girgiza mata Kai da sauri sannan ahankali yayi qasa da idanunshi ya zubawa yatsunta na qafa ido ya jima yana kallon yatsun kafafun mami da kuma hannunta yana son yayi mata magana amman yana tunanin yadda zata fahimcesa .”
yana kallonta ta mike ta soma zuba masa abinci tana magana cikin sanyayye yar murya “adamcy banason kana boye min matsalarka dan baka da wacce tafini kuma na jaka ajikina ne don duk lokacin da zaka shiga damuwa ka sanar min kasacewar nasan baka da wani danuwa namiji da zai maye maka gurbin danuwa da kuma mahaifi” ta qarasa mgnr tana tura masa plet din hadin salad gabansa “wai ma me ya kaika gidansu maryama ne kaje ka sanar mata kana sonta ne ko ya !”tmabayar tazo masa wani iri wai me yasa mahaifiyarsa tasan zahirinsa da badinsa?”mami tasan mamakin maganrta yake tace “nasan zakayi mamaki Jin abinda nace amman karka manta nice na kawowa duniya ,yaakayi maryama taki amincewa ko“?yayi shiru kawai yana kallonta yana jin faduwar gaba mai tsanani aranshi “.
“ka fad’a min idan bata amince bane sai na baka shawar yadda zakayi ka shawo kanta cikin sauki ko kuma mu dini zuga muyi gidansu qawwnya tayi maganar cikin tsigar zolaya “bai san sanda murmushin dole ya bayyana Akan fuskashi ba yana cewa “kai sweetheart wallahi kin bari nayi dariyar da ban shirya ba” gyaran murya yayi yace “ba wannan bane wani abu ne ya tsaya min arai har yasa kika ga yanayina haka tace ”meye shi !”?ta tambayesa adaidai lokacin daya fara ci salad tun kafin lokaci ya kure masa sai dai idanunshi na kanta yace “sweetheart yau naga mai irin yatsun qafafunki a gidansu maryama koma nace miki mahaifiyar maryama wallahi yatsunta na hannu dana qafa exactly irin naki ..”
mami tayi shiru tana dubansa cike da mamaki sannan tana duban yatsun hannunta yayinda mr ata ya cigaba da cin hadin salad dinsa dake gabansa “kuma kinsan wani abun sweet Herat “?ta girgiza masa Kai “sai kinganta wallahi sai kinyi mamaki yadda yanayinta yake Kama da aunty nu..”tun kafin ya qarasa kiran sunan ringin din wayarsa ya katse masa maganarsa ya d’auki wayar yana duba wanda ya kirasa ,ganin abokin halkal kasuwancinsa ne yasa ya nemi izini daga wajen mami kanta ta gyad’a masa alamun ya d’aga .”
Ahankali ya soma magana yana cigaba da cin salad ganin wayar tashi mai tsawo ce yasa mami ta yunkura ta mike ta bar parlour’n .”Mr ata ya jima yana tautaunawa da mutumin har kusan sha d’aya da wani Abu sannan sukai sallama ya tashi da kyar ya shiga bedroom dinsa kai tsaye bothroom ya shiga yayi pest yayi alwala ya fito ya zare Jallabiyar jikinsa ya saura daga shi sai gajeren wondo iya cinya ya qara qarfin ac d’akin yayi addua ya kwanta akan katifa yana lullube rabin jikinsa tare da kallon saman d’akin idanunshi ya saisaita kana ya lumshesu ya fara tunanin ko maryama zata bi umarninsa ko kuwa zata masa taurin kan kin zuwa .”
a daddafe yayi weekend dinsa Allah Allah yake Monday tayi .”Ranar monday da wuri ya shirya ya bar gidan dan ko breakfast bai tsaya yayi ba cikin shigar manya kaya yadi ne blue black mai shegen tsaida ,wanda akayiwa dinkin zamani sai dai gaban aljihunsa anyi masa desing da logon din ATA company ,goma daidai a AGC tayi masa sakamakon abu biyu ,abu na farko maryamarsa abu na biyu kuma hira da yan jarida suke so suyi dashi.”
ahankali manya ma’akatansa suka dinga shige da fice a office dinsa wasu magana ce mai mahimmanci wasu kuma saka hannunsa suke bukata har zuwa lokacin da 12:00 dot ta buga yan jarida suka qaraso suka yi abinda ya kawosu suka wuce amman babu alamun maryama tazo aiki ya Kira some bayan ta shigo yace “maryama fa !”?
”maryama kuma sir?ya kalleta a d’age yana karta saman table din gabansa “irin kallon da taga yana mata ne yasa da sauri tace “ai ta kwana biyu rabonta da zuwa aiki kamar yadda kasani .”
shiru yayi kawai yana sauke numfashi tare da hura hanci cike da ‘bacin rai ya kai hannunsa saman goshinsa yana murzawa ahankali ahankali yana tunanin abinda ya kamata yayi mata a qarshe dai wayarsa ya d’auka ya soma qoqarin neman layinta inda madam some ta juya ta koma bakin aikinta kira biyu yayi mata sannan ta d’aga tare da yin sallama “bai tsaya amsa sallamar datai masa ba yace “maryama kina wasa dani ko ?”tai saurin girgiza masa kai alamun a’a tamkar tana gabansa “Ina ganin baki san waye adam ba shi yasa har kike taka masa doka “shiru tayi tana sauke masa hucin numfashin Wanda dole tasa ya d’an lumshe idanunshi yana cewa “na fuskanci maryam kina son ganin iyakar taurin kaina ko“?”kayi hakuri amman ai na fad’a maka bazan ci..”oh my god wai me na fad’a miki ?”banace lallai kizo yau ba “kayi hakuri sir ni aikin ne gbdy ya fice min arai kar na dawo ayita samun matsala dani “da sauri ya mike tsaye tare da dunkule hannunsa ya naushi iska sannan ya dinga Kai kawo a filin office din inda idanun madam some da hankalinta yake kanshi sosai taga ya shiga damuwa maryama kuwa tana can rike da waya tana zance zuci “dokar daya kamata yayi akan matarsa ko damuwar daya kamata yayi akan matarsa ya tsaya yana yin abinda bai shafesa ba on expecting taji saukar muryarsa “karki ga na damu akanki ki d’auka wani dalili ne amman kisani zuwanki aiki gobe shine kwanciyar hankalinki wallahi muddin kuma kika yarda na tako gidanku zan miki abinda zai miki illa.”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
47
“karki ga na damu akanki ki d'auka wani dalili ne amman kisani zuwanki aiki gobe shine kwanciyar hankalinki wallahi muddin kuma kika yarda na tako gidanku zan miki abinda zai miki illa."ta maimaitawa kanta furucinsa tana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba from know where dan zuwa yanzu tasan halin mr ata kamar yunwar cikinta bashi da kyau ta kowane fanni kuma duk abinda yace zai aikata zai aikata shi babu wanda ya isa yasashi kuma babu wanda ya isa ya hanashi ,zai iya aikata fiyye da abinda yace zai mata“.to ma akan me ye zai nemi ya dinga takurawa rayuwarta alhalin ita din ba matarsa bace ba kuma kowa nasa bace ?”.ahankali ta sauke naunauyen ajiyar zuciya batare data sake cewa komai ba.”
“maryama….”!
ya kira sunanta cikin wata irin kasalalliyar muryarsa mai tsananin kashe sansar jiki da tsuma zuciya wanda yasa taji gabad’aya komai ya tsaya mata cak, yayinda ahankali ahankali tsigar jikinta suka dinga mikewa sai dai daga sunanta daya kira bai qara cewa komai ba yayi shiru ya koma ya zagaye table dinsa ya tsaya ya d’aura hannunsa d’aya,jikinsa yayi mugu mugun sanyi dan ya fara Jin alamun bazata zo ba dan haka ya wani dawo kamar wani abun tausayi muryarta a sanyaye tace “sir ka kira sunana kuma kayi shiru ?”tsaki yaja yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa .”“please sir kayi hakuri “zaki zo goben ko zaki tsaya yi min taurin kai?”wani irin mugun tsoronsa ne taji ya shigeta wanda yasa tai saurin cewa”shikenan naji zanzo!”yana gama jin abinda ta fad’a ya katse kiran tare da lumshe tsumammun idanunshi yana jin wani irin farinciki na shigarsa with an unreadable expression akan fuskarsa.”
maryama kam numfashi ta sauke da ajiyar zuciya atare tana sake mamakin qarfin halinsa,mutun kamar wani aljani gabad’aya yana son ya canza mata tsarin rayuwarta da tunaninta koma tace ya canzata completely dan a halin yanzu bata da wani aiki sai fama da tunaninsa ,ahankali ta runtse shayayyun idanunta tana sake tariyo komai nashi most especially yadda yake nanike mata a duk sanda zasu kasance tare wasa wasa dai mr ata so yake lallai sai yayi wa rayuwarta karfa karfa da karan tsaye sai ya dasa mata matsanancin son shi ya ruguza mata rayuwa sannan hankalinsa zai tashi , ta jima zaune tana tunanisa kafin ahankali ta zame ta kwanta a gurin still dai tunaninsa bai bar zuciyarta ya huta ba.”
“ maryama me zai hana ki auresa kawai tunda ya amince zai aureki kuma kema alamu sun nuna kin fara jin wani abu akanshi ?”ta yiwa kanta tambayar tana jin wani abu tun daga tsakiyar kanta har zuwa kasan maranta mai kama da shocking din wutan lantarki “maryama matukar kika auri mutun nan wahala zaki sha a hannunsa ki manta dashi kawai ki samu wani ko kuma ki yiwa Oga amar magana ko akwai wanda ya yarda da natsuwarsa kuma wanda bashi da mata ya had’u su aure kamar hakan zai fiye mata zaman lafiya da samun kwanciyar hankali a rayuwarta “yes yes !!gara kiyi hakan dan auren mr ata ba mafuta bane gareki wahala kawai zaki bawa kanta ga matarsa dan dole kin san yana daita ga kuma baud’adden halinsa.”Juyi tayi ta gyara kwanciyar tana tunani da zance zuci tana jin kamar kartaje aikin gobe sai dai zuciyarta na tsananin jin tsoro dan bata san abinda rashin zuwan nata zai haifar ba .”
Washegari
Da misalin karfe shabiyu saura Mr ata yana tsaye a gaban ma’aikatansa a office dinsu maryama kuma har lokacin bata qaraso ba yayi shiru yana zance zuci sai gata ta shigo a natse bakinta d’auke da sallama cikin shiga ta kamala, sai bayan data shigo office din sannan taga mr ata tsaye .”office din ya d’auki shiru tamkar babu wasu halittu dake numfashi acikinsa duk wad’an da ke zaune acikin office din babu wanda bai juyo ya maida hankalinsa kanta ba sakamakon jin sautin muryarta d’aya byn d’aya take kallonsu kmr yadda suke kallonta kowa na zaune a mazauninsa sai dai bata ga alamun yusura ba .”
mr ata kuwa tun da ya d’aura tsumammun idanunshi akanta bai d’auke ba. dan tuni ya fara cire ransa da zuwanta a yau din duba ga lokaci ya fara tafiya dan har ya shaka ya fara jin haushi jira yake biyu ta buga yayi mata diran makiya kallonta ya cigaba da yi koina na jikinta a lullu’be yake tun daga saman qafarta har zuwa kanta da hijab wani irin sanyi