Showing 54001 words to 57000 words out of 182919 words
tafi da zuciyarta da rayuwarta gabad’aya soyayyarta ta mutu akanshi ba lallai ta fahimcesa ba bare ta fahimci irin tarin qaunar da yake mata .”
gbdy idanunsa sun sauya kala fuskar maryama kawai yake gani ko a wani hali take ciki a inda ya barota numfasawa yayi yana dafe goshinsa yace “anya kuwa banyi kasadar barinta a wajen nan ba ?“anya kuwa bazan tura a ruwa ya koma ya dauketa ya kaita gida ba ?”wannan tunani yasa shi ya mike yayi taku zuwa inda wayoyinsa suke akan mirrow ya dauki d’aya daga ciki ya soma kiran layin aruwa bayan ya d’aga ya bashi umarni abinda yake son yayi sannan ya katse kiran ya koma ya zauna yana fidda numfashi sama sama.” bai sauko ya cin komai ba ya kwanta yana runtse tsumammun idanunshi tare da rungume hannuwansa duka aqirjnsa yana jin yadda soyayyarta ke fixgarsa .”
Bangaren maryama kuwa da kyar ta yunkura ta mike ta nufi gidan cikin tashin hankali wuni daya amman idan kaganta ta fita haiyacinta ta rame da kyar take daga qafafunta tana shiga gidansu bangaren umma ta nufa a falo ta sameta ita kad’ai umma tana ganin yanayin maryama ta mike da sauri ta tarbota ai kuwa ta zube ajiknta tana kuka “Lafiya maryama meke faruwa dake naganki kamar baa haiyacinki kike ba?umma …”sai kuma ta fashe da kuka ta kasa qarasa mgn nan fa hankalin umma ya sake tashi ta mike taje ta kawo mata ruwa a glass cup ta kai bakinta “sha ruwa kiji sanyi .”ta kurbi kad’an tana sauke naunayen ajiyar zuciya .”
umma ta sake tmbyarta bata boyewa umma komai ba ,ta zayyane mata duk abinda ya faru “wannan laifinki ne maryama shiru tayi tana duban umman bazaki fahimci yadda mutun yake shiga idan yayi alkawarin cika aiki ba “umma nima ban so haka ba nayi kokarin nayi masa aikinsa koma dai menene wannan laifinki né d’an ya kamata ki qarasa masa aikinsa ki kai masa albashi daga baya sai ki nemi excuse ki tafi duk inda zaki “shiru maryama ta sake yi tana tunanin maganganunsa “babu wani mutun da ya isa ya fadawa adam tariq abdullah magana akan aiki amman yau anyi ,and it happened because of you “gsky umma nayi kuskure amman idan kikaga yadda mr ATA ya zageni gabadaya ya hanani cewa komai “.ai duk ya faru ne saboda kuskurenki ko haka kawai zai fada miki magana “?
“Kinsan irin asarar da kikasani wai Ke dame kike takama ya tsaidaita ?”Kinsan yadda kasuwancina yake da matukar mahimanci agurina gabaday na daura raina akan designs dinki nasaka raina nayiwa wanda zaizo yagani alkwari amman sai kika ki zuwa kuma idan na kiraki sai Kiyi rijecting din kirana me ma kike yi anan ki bani amsa .”?maganarsa ta shiga yawo acikin brain dinta” idan kinje office gobe ki tabbatar kin bashi hakuri ki nuna masa kinyi Kuskure gyad’awa umma kai kawai tayi .”alamu taji .
*****
Daren ranar daga maryama har mr ATA babu wanda ya runtsa kwana sukayi cikin tunanin juna da maganganun juna ta mike zaune akan gado ta jingina bayanta tare da daga idanunta sama “wai a haka kike son ki zama profetional a ma’aikatan mu?Kinawa mutane iskanci da kika ga dama saboda kina daukar wai dan kin iya designed yasa kike samun aiki cikin sauki ? gabadaya zagin da yayi mata babu wanda ta manta yadda take zaune haka shima bai tsaya iya daki ba har kasa falon mami ya sauko ya dinga tafiya tamkar wanda bai da laka ajikinsa ya wuce ya karya kwana zuwa parlour’nta na biyu tun saukowarsa maryam taji ajikinta dan daman baccin nata rabi da rabi né .sad’af sad’af ta fito ta gansa zaune akan kujera yayi shiru cikin tsananin tunani shiru tayi tana qare masa kallon taso ta qarasa garesa ta tambayesa damuwarsa amman tasan halinsa komai zatayi bazai ma saurareta ba ta jima tsaye kafin daga baya ta juya tana masa fatan sausauci duk da batasan abinda ke damunsa ba .”
Ya dinga jin kamar ya kirata yaji muryarta ko hankalinsa ya dan kwanta tunda a ruwa ya tabbatar masa da yaje bai sameta a wajen ba .”
Washegari daga maryam har mr ATA babu wanda
yayi kokarin zuwa aiki kwamciyata tayi dan tasan tana zuwa zai korata idan taci saa ma bai hada mata da zagi da tozarci ba, sam ransa bai iya baci ba idan ransa ya baci baya control din kansa “numfashi ta sauke tana cewa “wallahi matarka tana dan katoton matsala ta fada gabanta fadawa bangarensa shima zama yayi adaki bayan yayi wanka ya sauya kaya yana zaune mami tashigo kamar daren jiya tmbyrsa ta soma yi stil yace babu komai “idan zaka boyewa kowa damuwarka adamcy banda mahaifiya yadda bazaka yadani ba nima haka né bani da kamarka damuwarka damuwatace “sweetheart maryama ce !”ya furta yana jin bugun zuciyarsa na qaruwa .”wacece ma haka ?ta tambayesa tana tattara gabad’aya natsuwarta garesa .”
Ya d’auki minti goma sannan ya motsa labbansa yace “wannan sabuwar maaikaciyar dana d’auka ce “
ya fad’a yana sauke numfashi “ me tayi maka wanda har ya hana rayuwarka sukuni?”yayi shiru ya kasa magana “ fadawa sweetheart dinka abinda tayi maka still shiru yayi yana tunanin ta ina zai fara mata bayani ta tsura masa idanunta sosai tana karantarsa tare da nazarinsa daman kuma maryam ta fad’a mata daren jiya bai yi bacci ba gashi yayi sanadiyar daya zauna gida bashi da niyyar fita office
“Adamcy!
Ya d’ago tsumammun idanunshi ya zuba mata dan mgn wahala take masa a tsakanin jiya da yau “ko dai sabuwar ma’aikaciyar nan ta sace maka zuciya né ?da sauri ya furta “kai sweetheart, kai sweetheart ko gsky shiru yayi kawai qirjinsa na dukan uku uku “tambayarka nayi ka bani amsa kana sonta ne dan wannan damuwar tayi yawa tunda ka fara aiki daita kake cikin damuwa “haka nan ya tsinci kanshi da girgiza mata kai alamun a’a “sweetheart babu wani so “ ya fad’a mata haka ne saboda maryama bai kafa kansa a wajenta ba taya zai fad’a mata shi da yake da qatotuwar matsala a gabansa gara yasan matsayinsa tukun koda zai shigo mata da maganar soyayyarsa “adamcy idan bashi bane me zai sa ka dinga zama always busy thinking kuma nasan akanta ne ?” ta kamo hannunsa cikin nata” ina sauraronka fad’a min damuwarka bai boye mahaifiyarsa ba ya koro mata duk abinda ya faru da dalilin dayasa taki zuwa ta kawo masa aikinsa sai dai har lokacin yaki fadawa mahaifiyarsa cewar itace yarinyar mafarkinsa ce .”
“lallai wannan yarinya tayiwa shalelena Kuskuren da baa masa ya dauka ,ina kyautata zaton da wata ce da yanzu kasa an sallameta “yanzu ma tunanina kenan sweetheart gara na sallameta na huta da matsalolinta “a’a karkayi haka ita rayuwa tattare take da qalubali sannan yarinyar abar tausayi ce wata killa ma ita ce Ke dauke da dawainiyar gidansu sakamakon yadda rayuwar nan tayi tsanani sannan kai ma kace ga dalilinta na kin zuwa “ tunda mami ta soma magana bai ce uhm ba bare uhm uhm “adamcy karka koreta na rokar mata wannan alfarma ka bata wata damar kuma ina da tabbacin bazata sake aikata Kuskurenta ba.”ta cigaba da magana “ adamcy ya kamata ka daina sauran daukar zafi akan komai ka koyi hakuri da juriya sannan ita wannan yarinyar Kmr yadda ka fada zuciyarta na tattare da damuwa mai tsanani ,da ciwo a zuciya ba kowa bane zai iya dauriyar abinda ya faru daita .”dan ka dinga mata hakuri kana tausaya mata mutuwar miji fa bakaramin ciwo bane .”
yayi shiru yana sauraran mami yana tunainn lokacin da yake mata balain tana bashi hakuri akan ya tsaya ya saurareta” yau ta wuce na zuwa aiki amman gobe idan kaje office ka nemeta ka bata hakurin tozarcin da kayi mata” tana gama fadar haka ta bar dakin dan ya d’an ya samu ya huta tana fita ya mike tsaye yana tafiya yana tunanin maryama yana tunani maganr mami shi gabadaya yanzu ba rasa aikin bane damuwarsa yadda zuciyarta ta mace akan matacce shine babban tashin hankali sa washegari da sanyi jiki ya tashi ya shiga bathroom ya jima a bathtub cikin ruwa kafin ya fito ya goge jikinsa ya feshe ilahirin jikinsa da turarensa REED Kmr koda yaushe ya shirya cikin suit black and milk colour bai daura yar saman suit dinsa ba ya qarasa gaban mirrow ya dauki curm yana taje sumar kansa ya ajiye curm ya dauki agogon ya daura atsintsiyar hannunsa duk jikinsa ya sanyaye yake komai ya manne medical glas dinsa duk abinda yake tana makale aransa ya rasa wani irin zazzafan so yake mata .”
“ina maseefar sonki maryama” ya furta a fili bayan ya gama shirinsa ya tsaya cak yana kallon kansa ta cikin mirrow maryama ya gani tsaye ta cikin mirrow sanye da doguwar riga ja tayi rolling kanta da bakin mayafi fuskarta babu alamun annuri haka zalika babu alamun murmushin nan nata , yayi shiru yana kallonta tayi masa kyau sosai bai san lokacin daya kai hannunsa yana shafa fuskarta ta cikin mirrow zuwa lip’s dinta ba .”nan take ta sakar masa laulausan murmushinta .kokuwa ya shiga yi da numfashinsa ya juya da sauri zuciyarsa na rawa byn Kmr second ya juyo yaga wayam yaga babu ita babu alamunta ya lumshe tsumammun idanunshi “it was imagenation .”ya furta yana sakin numfashi da qarfi “zatazo aiki yau dan jiya an tabbatar masa bata je ba amman yau kam yana ji ajikinsa zataje “? Idan kuma taki fa ? ya tmbyi kanshi “to karita mana kace mata taje aiki kai ma kasan irin haukan daakayi mata zataji tsoron zuwa .”should I called her or not ?ya sake tmbyr zuciyarsa “a’a bazan kirata ba ya furta yana lumshe idanunshi yayi shiru yana zagaye dakin.”
bangaren maryama itama shirin zuwa aiki take saboda umma tun daren jiya ta matsamata lallai taje aiki tunda itace tayi masa laifi bugu da qari ba korarta yayi ba .ta shirya tsab cikin daguwar riga kamar koda yaushe exactly yadda ya ganta a tunaninsa haka shirin nata ya kasance cikin doguwar Riga ja mayafi baki haka baby shoes din da take sanye dashi baki ne agogon hannunta baki ne ta qarasa ta dauki takardan zanenta ta rufe ta saka cikin jakar aikinta ta rataya sai dai ta tsaya shiru tana jin tsoron fuskartasa “ko ya zamu qare yau da mr ATA ? Kinsan irin asarar da kikasani wai Ke dame kike takama ya tsaidaita Kinsan yadda kasuwancina yake da matukar mahimanci agurina gabaday na daura raina akan designs dinki na saka raina nayiwa wanda zaizo yagani alkwari amman sai kika ki zuwa kuma idan na kiraki sai Kiyi rijecting din kirana me ma kike yi anan ki bani amsa .” ?maganarsa ta shiga dawo mata kamar alokacin abun ya faru ta dan ciza harshenta tana jin wani iri ajikinta kamar karta tafi “wannan mutumin yana ban tsoro ta furta a fili .”
“Hakika baka kyauta ba abinda kayi ka kirata ka bata hakuri tun kafin kaje office,no!!akan me kenan zaka bata hakuri bayan itace tayi maka laifi ,aa adam kai ma ka fada mata abubuwa dayawa tô na bata hakuri nace ma me ?kawai sai nace maryama kiyi hakuri akan …”no impossible I can’t gbdy ya rasa yadda zai fuskanceta da wannan kalmar dan tunda yake bai ta’ba bawa wani mutun hakuri ba sai mahaifinsa da mahaifiyarsa saboda me ita zai bata capital NO no !dan haka yayi cilli da wayar akan gado yana duban wayar ai itace tayi min laifi to dan me zan kirata?Kyakkyawar zuciyarsa tace sai me ai ba wani abu bane karka tsaya girman kai akanta ka dai san irin wahalar daka sha tsawon shekaru kana nemanta alhalin tana raye kuma a kusa da kai ma dan ina gra apapa ina agege is not far kai ya kamata ace ka fahimci kayi kuskure dan haka ka kirata nan take wata zuciyar tace “saboda me zaka kirata ai tama fika laifi ita data hada maka Zafi biyu ,ita yakamata ta nemi yafiyarka .”
“Idan mai hankali ce kuma tana bukatar aiki dani ai ya kamata ace ta kirani since tayi apologize abinda tayi amman taki saboda tana tunanin bata aikata kuskure ba. dan haka she’s the one who wil apologize she must apologize” ya furta a fili kuma idan ma taki zan sata dole tayi apologize da wannan shawarar zuciyarsa ta samu natsuwa .”yana tsaye mami ta shigo tana kiran sunansa “Adamcy Nah !kallonta yayi tare da cewa “good morning sweetheart morning my dear fatan ka tashi lafiya lumshe tsumammun idanuwansa yayi ya zagayo ya tsaya kusa daita ta dauki yar saman suit dinsa ta saka masa tana cewa “ kayi aure da ban huta ba ,shima yanzu ban huta ba har sai yashe zaka bar mahaifiyarka ta huta ?sai randa mafarkina ta bayyana ya bata amsa da haka yana kallonta .”
Murmushin mami tayi “wannan mafarki da gskiya ne da zanji dadi kadan “idan ta tabbata gsky ce sweetheart zaki sota kamar yadda kike sona ?” ya fad’a yana cigaba da kallonta yana son yaji amsar da zata bashi “ zan sota mana amman kadan tunda kai ma baka so zabina ba ,son 50 50 zan mata mur mushi ya bayyana akan labbansa “sai abu na gaba “karka manta idan kaje office ka kira yarinyar nan ka bata hakuri ka nuna mata shima Adam mai kuskure ne ka nemi yafiyarta yace “uhm alamun yaji idan ka gama ka sauko kasa abincinka yayi ready .shiru yayi kawai yana tunanin ta ina hakan zai faru “kabi umarnin mahaifitarka zai zame maka alkhairi ki rata tun kana gida kyakkyawar zuciyarsa ta bashi kwarin gwiwa , jiki a sanyaye ya dauki wayarsa ya soma neman layinta tare da tsurawa sunanta idanunshi .”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 16
Fuskar wayar yake kallo tare da raya abubuwa da dama acikin zuciyarsa ,wani irin abu yake ji yana tsarga masa a gbdy sansar jikinsa, sai wayar ta kusan shiga sai ya katse ,yayi haka ya kai sau uku yana katsewa cike da fargaba ya rike wayar a hannunsa yana tafiya acikin d'akin yana tunani ." maganar mahaifiyarsa ta shiga dawo masa "zuciyarta na tattare da damuwa mai tsanani ,da ciwo a zuciya ba kowa bane zai iya dauriyar abinda ya faru daita .
“Dan hk ka dinga mata hakuri kana tausaya mata mutuwar miji fa baqaramin ciwo bane ," runtse idanuwanshi yayi sosai yana kiran sunan Allah a lokacin da ya tuna yadda hawayenta ya dinga zuba akan wani matacce .”wani dogon tsaki yaja ya sake cilla wayar akan gado yana sake jan tsaki tare da kai hannu ya dafe goshinsa ahankali ya bud'e idanunshi wad'an da suka kad'a sukayi jajur saboda tuno abinda ya faru jiya. kukanta da damuwarta akan wani namiji wanda bashi ba ."wannan abu yayi matuqar masa ciwo ,qirjinsa na wani quna ya juya wa wayar baya kamar itace tayi masa laifi ."
Ya kamo lip's dinsa na qasa gabad'aya ya dinga taunewa da karfi gashi dai zafi yake ji amman zafin kishin maryama ya zarta zafin da yake ji acikin zuciyarsa ,byn kmr second goma ya sake juyowa da sauri yana kallon wayar kmr zaiyi kuka ,"bazan ta'ba bayyana miki soyayyata a yanzu ba dan nasan ko na bayyana miki a acikin wannan halin bazaki ta'ba sona ba amman zan san abunyi ," ya furta a fili yana sauke wani naunayen ajiyar zuciya ya sake d'aukar wayar stil numberta ya shiga kira yana tunanin mgnr da zai fad'a mata da zai sa tazo aiki dan yayi imani tunda bata zo jiya ba tabbas yau din ma bazata zo ba "to idan ina kirata ta d’aga me zance mata ?” ya sake tambayar kanshi yana sake danne lip's dinsa da hakori "idan ta d'auka kace mata tazo aiki amman karta zo maka da past dinta , ta bar komai a gida baka buqata that's all ."
sai dai wayar na daf da shiga ya sake ya katse wa yana sauke zazzafan numfashi ."maryama ta tsaya shiru acikin haraban ma'aikatan tana tunanin hawa sama ,kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin fargaba, ita ba wai tsoronsa take ji haka nan ba kamar yadda sauran ma'aikatan suke rawar jiki idan sun gashi disgi da tozarcinsa ne bata so kuma shi babu ruwansa ko gaban uban waye shuka rashin mutuncinsa yake kuma kamar bai d'auki hakan a wani abu ba ."da kyar ta tattare jarumta ta sanya ajikinta ta nufi kofar shiga lift byn ta shiga ta shiga, mutane da dama sun shiga a natse ta danna number inda zata sauka sannan ta ra'be jikinta waje d'aya tana jin mummunar fad’uwar gaba ,kofar na gama rufewa wani sabon fargaba yayi mata diran makiya gabanta ya dinga luguden bugu har sanda kofar ta bud'e , sai da kowa ya fita ya barta kamar ta koma kasa amman wata zuciyar ta dinga karfafa mata gwiwa.”
Ahankali ta fito zuciyarta na bata kwarin gwiwa "haba maryam kowa tsoronsa yake ,ya kamata ki zama zaka acikinsu ba wai ki masa taurin kai ba aa ki zama jaruma ."kai tsaye ki shiga office dinsa ko kuma ki kirasa “ta zaro wayarta ta rike tana tunanin abinda zata ce masa idan ta kirasa "sir kayi hakuri nayi realize din mistakes dina bazan sake aikata wannan kuskure ba shikenan kina yin hk zai yafe miki ."tana cikin tunanin kawai taji wayarta ta d'auki qara a matukar tsorace ta duba sunanshi ta gani yana yawo a scren din wayar nan take bugawar da zuciyarta take ta qaru yayinda sansar jikinta ya kama kyarma ,amman tayi karfin halin ta daidaita natsuwarta ta d'aga kiran cikin sanyayyar muryarta mai sanyi da bugar da zuciya duk wanda ya saurara "assalamu alaikum "