Showing 48001 words to 51000 words out of 182919 words
kin saka kulafucinsa aranki ne yasa kike jin kamar yana raye banda abunki mutumin da’aka binne agabanki “amman kuma umma ai babu abinda Allah bazai iya ba “to shikenan tunda kince haka Allah yasa yana raye amman yana raye me yasa bazai dawo garemu ba ?”ta qarasa maganar tana fesar da wani numfashi mai zafi kana ta samu waje ta zauna ta zabga tagumi tare da lumshe idanunta .”maryama tayi wani juyi tana sake lulawa duniyar tunani .”
“idan tayi tunanin rayuwarta da irin kalubalin data fuskanta arayuwarta sai ta dawo tunanin mr ata duk dai ta dan samu natsuwa kadan dan yusura ta sheida mata bai je office yau ba “ko dai taje aiki gobe ne ko zai share bazai ce mata komai ba ?Aa maryama karki je aikin nan gobe?tayiwa kanta gargadi “ karkiyi kuskure zuwa domin kuwa ba qaramin aikinsa bane ya tozartaki kamar yadda saba tozarta duk wanda yaso, ahankali ta sauke numfashi tana kallon inda kayan aikinta yake .”nan ta soma tunanin ko zatayi wani abu koda na awa biyu ne idan ma baza taje aiki gobe ba ta kaiwa yusra da safe kamar yadda tayi yau alabashi sai ta bawa madam some ta bashi.” idan ya nemeta sai taje idan kuma bai nemeta ba shikenan sai ta hakura ta cigaba da zama a gida “.
Bangaren mrs ata ahankali ya cigaba da aikinsa kafin ahankali ya janyo d’aya daga cikin wayoyinsa ya soma neman layin some kira d’aya ta dauka cike da girmamawa tace”barka da dare sir ?”barka ya fad’a tare da yin shiru yana kallon screen din system ya d’auki second goma sannan ya cigaba da motsa lips dinsa “yarinyar nan kuwa ta kammala da ayyukan jiya ?”some tayi shiru cike da jin tsoron sheida masa cewar maryama bata zo aiki ba dan tasan ransa zai yi mugun baci idan yaji amman rashin sheida masa shima zai sa ita kanta ta janyowa kanta gagarumin matsala dan haka gara ta sheida masa muryarta na rawa tace “sir maryama bata zo aiki yau ba amman ta aiko da zane guda uku an kawo “what !? ya furta da d’an karfi nan take zuciyarsa ta fara tafarfasa “wani irin batazo aiki ba ?”batazo ba sir sai dai bansan dalilin rashin zuwanta ba kafin ta sake cewa wani abu taji kit yayi disconnecting din kira ya soma neman layin maryama .”
Maryama na kwance ta soma jin qarar wayarta wanda shine ya dawo daita daga tunanin da take,ta mika hannu ta daga ta kara a kunnenta ba tare data damu da duba mai kiran ba"Assalamu alaikum warahmatullah" muryar nan nata mai daraja da qima a wajensa, muryar nan da yake bawa girma muryar nan da babu tamkarta acikin zuciyarsa
itace ta ratsa dodon kunnensa ji yayi tamkar an cire masa duk wata laka dake jikinsa ta cire wayar a kunnenta ta duba ganin sunansa sai da qirjinta ya buga ta sauke numfashi ta maida wayar ta sake yin wata sallamar tare da yin shiru tana jiran taji yanayin da zai amsa mata sallamarta .sai dai madadin taji ya dawo mata fatan amincin data masa sai taji maganarsa cike da gadara ”ke ni ne na zama abun wulakantawa wajenki ?”
Da sauri ta mike zaune tana cewa no !no sir !! ba haka bane wallalhi bana cikin natsuwa ne shekaranjiya kayi hakuri sir “ba hakuri na kira ki bani “mai ya hanaki zuwa aiki yau ?”shiru tayi zuciyarta cike da tsoro “kaji mutumin da bai je aiki ba ko ina ruwansa da rashin zuwanta ?”am talking to you?”amm uhm “sai kuma tayi shiru ta kasa cewa komai “saboda kin rainani shiyasa kike yin abinda kika ga dama “?ta sake kwantar da muryar da ladabi tamkar tana gabanshi tace “sir ba haka bane ai tsakanina da kai babu raini yau din ne na tashi da matsanancin ciwon kai ko kwayar idanuna bana iya budewa amman kayi hakuri” ta qarasa maganar cikin muryar kasaka kwalla na cika mata idanunta alamun kuka.”
nan take yaji zuciyarsa ta karye idanunshi ya lumshe sannan yace “Allah ya baki lafiya karki manta da sauran aikin dana baki gobe ne za’a zo kar’ba kiyi qoqari kiyi da kyau karki bari a samu wata matsala ko kuskure.” tace “in sha allahu sir gobe karfe tara daidai dashi zaka soma cin karo a office dinka ta fad’a “kiyi make sure bakiyi bacci ba dan ki gama komai kafin 5:30 “ok sir zanyi duk yadda kace “ very good .”wani farinciki ya mamayeta cike da jin dadi tace “thank sir …”yayi shiru yana jin yadda take farinciki wanda yayi sanadiyyar shima ya tsinci kanshi cikin farinciki ya maida jikinsa ya jingina da abun gado ya janyo pillow ya matse a faffad’an qirjinsa yana jin tamkar itace rungume a qirjinsa “.“mr ata !ta kirasa cikin kasalalliyar muryarta mai tsananin kashe jiki da zuciya “tasan bazai amsa mata ba dan haka ta cigaba da magana “nayi maka sallama irin ta addinin muslinci har sau biyu amman baka amsa ba “still shiru yayi mata yana sauke mata numfashinsa a kunnenta “.
“dan allah ka amsa min nima kamin fatan amincin Allah ya tabbata agareni shiru ne ya sake biyowa baya har na tsawon second biyar har ta fitar da rai zai ce wani abu sai ta jiyo sautin sanyayyar muryarsa “wa alaikumussala wa rahmatullah “.ya amsa mata bayan ya sauke ajiyar zuciya. idanunta ta lumshe daga can yana duban kanshi a madubi sai yaga gabadaya ya sauya tamkar bashi ba dan shi kansa ya san baya abubuwa irin na mutane “na gode mr ata na gode da kamin fatan samun amincin Allah agare…” jiya tayi ya katse kiran tun bai ji mai zata qarasa cewa ba .”numfashi ta sauke tana godewa allah daya d’aurata akanshi dan bata d’auka zai sauko haka ba bama ta d’auka zai nemeta ba ta d’auka shikenan sai dai taji an koreta daga aiki .” ta ajiye wayarta akan gado, nan da nan ta duro ta d’auko wata katuwar takardar zane tana dubawa ahankali ta soma aiki har kusan karfe biyun dare tana aikinta .”
yadda batayi bacci ba haka shima bai runtsa ba bini bini zai kirata yaji ko idanunta biyu .”gyangyadi tasoma na alamun bacci da sauri ta dawo haiyacinta “kai bacci ka barni bazanyi ka ba har sai na kammala da ayyukan gabana babu abinda take sai Hamma , bacci ne sosai acikin kwayar idanunta amman haka ta cigaba da zane amman bacci ba’a cin bashinsa sai daya d’auketa bata farka ba sai karfe uku da rabi na dare agigice ta kai idanunta kan agogo ta sauke numfashi tana hamma “wallahi bacci nake ji ta furta cikin muryar bacci tana lumshe kwayar idanunta sannan ta bud’e tana kallon tarin takardun data baje akan gadonta ,dole sai na gama aikin nan kafin na kwanta idan ba haka ba zan had’u da tashin hankali gobe.”
ta mike ta tattara kayan aikinta ta dawo parlour’ ta d’auki remut ta kunna tv wai dan kar bacci ya d’auketa ta cigaba da aikinta amman ina bacci fa yace bai san hakuri ba ai kuwa ya kwasheta akan kujera batare data qarasa aikin ba.”shima bangaren mr ATA kwana yayi yana aiki batare daya runtsa ba haka mami bata runtsa ba, ta shigo ta kawo masa coffee ya amsa batare daya ce komai ba ta juya ta fita ya kai bakinsa yana kur’ba a hankali ya d’auki wayarsa yana neman layinta sai dai wayar na ringing baa d’auka wanda maryama na can tayi nisa cikin baccinta ganin haka ya mike tsaye ya ture system din gabanshi ya shiga zariya hannunsa daya cikin aljihunsa yayinda kunnensa ke manne da waya yana neman layinta “maryama ki d’aga wayar mana amman shiru bata d’auka ba allah dai yasa ba bacci yarinyar nan tayi ba.”?
Tana tsaka da baccinta taga yaya sadam sanye da riga baki yana tafiya a hankali ,yayinda hannunsa daya ke rike da waya dayan hannunsa kuma rike da wata kyakkyawar budurwa suna tafiya cike da annashuwa da farinciki har suka qaraso farm center dake ikeja a long suka tsaya daidai wajen wani katanfarin gidan abinci wanda babu abinda babu naci acikinsa budurwa ta kwanto jikinsa sosai tana zuba masa shagwaba tana nuna masa restaurant kai tsaye suka shiga suka samu waje a vip suka zauna inda ma’aikatan wajen suka qaraso suka mika masu wata takarda da jerin abinci da suke dashi yake zane acikinsa budurwa nan tayi shiru tana kallon hadin salad wanda yaji nama da cocomba ta sake kwantowa jikin yaya sadam ta nuna masa abinda take bukata murmushi ya sakar mata tare da shafa gefen fuskarta ya nunawa maaikacin dake tsaye nan ya tambayesu zasu ci anan ne ko zasu yi takeway .”
Ya sadam ya kalleta tace “zasu wuce dashi dan haha maaikacin ya juya cikin lokacin kankani ya dawo rike da farar leda ya ajiye masu akan table din gabansu yaya sadam ya ciro kudi agaban aljihunsa ya mikawa mutumin sannan ya kalli budurwa da yake tare daita ya kai bakinsa daidai nata zai yi kissing dinta nan maryama ta farka a matukar gigice tana kiran sunansa wanda hakan yasa umma ta farka daga nata baccin ta fito da sauri ta nufi d’akinta sai dai bata ganta ba dan haka ta fito zuwa falo tana kiran sunanta “maryama! maryama !! Kukanta yasa ta qaraso da sauri ta rungumeta tsam ajikinta tana cewa “lafiyaki meke faruwa?”ummah mafarki nayi da yaya sadam tare da wata budurwa allah umma ina ji ajikina yaya sadam bai mutu ba yana raye .”
Umma ta kwantar da kanta a jikinta tana cewa “ idan bai mutu ba maryama mai zai hanashi dawowa gida ?idan bai dawo danke ba ai ya dawo saboda ni mahaifiyarsa dana rage masa a duniya ki cire wannan tunanin cewar bai mutu ba aranki d’an mutuwa kam sadam ya mutu sai dai muyi masa fatan allah ya hada fuskokinmu a aljanna .”shiru maryama tayi tana nazarin maganarta da kuma tunanin yarinyar data zo jiya a matsayin abokiyar aikinsa sannan kuma da sautin muryar dataji irin nasa anya kuwa sadam ya mutu kamar yadda mutane suke tunani?” ita dai tana ji ajikinta bai mutu ba amman zatayi kokari taje farm center gobe .”maza tashi muje ki kwanta ki bar aikin nan haka kya qarasa gobe idan allah ya kai mu mikewa tayi jikinta a matukar sanyaye umma ta tattara duk kayan aikinta suka nufi dakinta ta kwantar daita akan gado itama ta hau ta kwanta tana shafa sumar kanta .”
kasa komawa bacci tayi saboda da zarar ta runtsa idanunta sadam dinta take gani har asuba babu wani baccin daya dauketa .”Kiraye kirayen sallah ta soma ji daga masalatai mabam bamta dan hk ta sauko daga kan gado ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta isa inda sallaya yake ta d’auka ta shimfida ta soma gabatar da nafil fili haka ma umma washegari qarfe takwas daidai ta shirya cikin doguwar riga yellow ta fito ta bar gida kai tsaye farm certer ta nufa inda ta shiga gidan sai da abincin data gani ta samu waje ta tsaya tana dube dube komai da ta gani a mafarkinta haka tagani azahiri sai dai wurin babu mutane sosai tana tsaye har karfe tara tana zagaya wurin ko Allah zai sa ta gansa sai dai babu shi .”
Jiki a sanyaye ta fito tana dube dube duk inda taga gidan abinci sai ta tsaya ta nuna hotonsa ko sun gansa a wurin jiya sai dai har karfe goma bata samu wanda yace mata yaga koda mai kama dashi ba amman haka ta cigaba da nemansa yayinda mr ATA ke faman kiranta a waya tana danna masa rejecting .”tsaye yake a office yana zariya domin kuwa dai lokacin da masu kar’ban zane yayi kusa gabadaya an gama arrangement din komai maryama kawai ake jira ya sake kiranta adaidai lokacin data nunawa wani mutun hoton sadam yace “zaki dauki kiran ne ko zaki bari naga hoton da kyau ?”sorry please ta fad’a tana saka wayar a flay mood ta mika masa wayar.”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 14
Mutumin data mikawa wayar shima dai cewa yayi bai gansa ba hasalima bai ma ta'ba ganin mai kama dashi ba" yana gama fad'ar haka ya mika mata wayar ya shige ya barta tsaye cikin tsananin tashin hankali ita kanta tasan mafarki ba gaskiya bane amman mai yasa zata damu kanta akan mafarki ?"saboda zuciyarki ta kasa hakura da cewar yaya sadam ya mutu ne"ta bawa kanta amsa da haka tana dafe foring head dinta tana cire wayarta a flight mode ." Inda mr ata yake can cikin tsananin damuwa sosai ,a natse ya fito daga office dinsa rike da wayar da yake ta faman neman layin maryama yana bin kowa da wani iri kallo, yayinda kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewar baya cikin nutsuwa da walwalarsa duk da daman ba mai sakin fuska bane amman na yau din yafi na sauran lokuta nunawa ."yana cikin wannan halin ya samu kiran gaugawa daga Z&A dan haka ya kalli agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa shabiyu daidai yanzu ta buga bai koma office dinsa ba ya zarce zuwa qasa direbansa a ruwa da escout dinsa suna ganin fitowarsa duk suka zabura suka mike da sauri aka bud'e masa gidan baya ya shiga ya zauna yana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba hannunsa ya kai gwiwar qafarsa yana kad'a qafarsa d'aya yana tunaninta."
tafiyar mintuna ta kawosu Z&A" sanda direba escort dinsa yayi parking atare escout dinsa suka firfito gbdyansu rike da bindiga suka zagayesa inda direbansa a ruwa ya fito da sauri ya bud'e masa kofa ya fito ya nufi ciki har anan ma an fahimci tsananin damuwar da yake ciki ."har yaje ya dawo damuwarsa na nan sai ma ninkuwa da tayi ko cikin kamafanin ranar kowa yasan lallai akwai abinda ke damunsa dan haka kowa ya qara shiga hankalin sa, tun daya hawo saman bai ga alamun maryama ba gabansa ya cigaba dukan tara tara amman ya dake ya samu waje ya zauna ya soma gabatar da ayyukan dake zube akan makeken table dinsa yana mamakin rashin ganinta ."bayan kamar awa biyu da shigowarsa office ya sake duba agogon hannunsa yaga lokaci ya soma tafiya amman babu alamun shigowarta ."
ahankali ya mike ya tura hannunsa d'aya cikin aljihun wondonsa yana taku acikin office din duk wani motsi da zai ji sai ya saita idanushi kan glass door kasancewar ana iya hango duk wanda ya shigo amman sai yaga ba ita bace ,nan fa natsuwarsa ta qara barin gangar jikinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake daga cikin office dinsa zuwa wajen office dinsa zuwa office dinsu maryama kunnensa manne da waya yana faman neman numberta tare da sake duba ogagon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa sauran mintuna talatin wad'an da zasu zo suga representaition dinsu su qaraso ."
daga sectary dinsa har sauran abokan aikin maryama hankalinsu a matukar tashe yake sakamakon yanayin da mr ATA yake ciki ,".yana tsaye sectary ta qaraso da hanzarinta ta tsaya kusa dashi cike da girmamawa idanunshi ya tsura mata yana son yaji mai zatace masa "sir har yanzu bata qaraso ba dan allah kayi hakuri sir gashi Ina ta kiranta bata d'aga kiran ya lumshe tsumammun idanunshi dan shima layinta yake kira tana shiga bata d'agawa fuskarshi a had'e ya tsare some da kwayar idanunshi kafin a hankali ya motsa labbansa "ina yarinyar data bawa zanen jiya ?" da sauri some tayi baya kad'an ta soma kiran yusura batare da 'bata lokaci ba yusura ta fito daga office dinsu ta bayyana a gabansu cike da girmamawa tana gaishesu idanuwansa masu matuqar tsoratarwa suka sauka akanta gabad'aya yusura ta rud'e "kinyi waya da maryama yau ?"no sir !ta bashi amsa a rude ".
"kirata ko zata d'auka jikinta na rawa ta soma neman layinta"kisa wayar a handsfree "okay sir tayi kamar yadda ya buqata sai dai tana kira ta d'aga muryarta a tsarke tace "yusura !" maryama kina ina ?"da sauri mr ata ya fixge wayar ya soma magana cikin zafin rai "ke kina ne ?"kit yaji ta kashe wayar gbdy "oh shit ya furta yana dafe goshinsa yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa yana jan tsaki byn second biyar ya sake tsare yusura da ido "akwai wanda zaki kira a gidansu yanzu domin muji halin da take ciki ?"tayi saurin gyad'a masa kai alamun eh !zufa na karyo mata "ok call !ya fad'a atakaice yana juya bayansa nan da nan ta soma kiran layin umma kira d'aya biyu umma ta d'aga byn sun gaisa ta tmbyeta maryama fa "?ai ta fita tun da sassafe lafiya yusura?"babu komai har yanzu bata qaraso office ba "zata qaraso in sha allahu dan tun sassafe ta bar gidan nan "okay to .ta fad'a tana gyad'a kai cike da tashin hankali ya wucesu zuwa cikin office dinsa da niyyar zama sai dai ya kasa zama bai sani ba tashin hankalin na meye haka na wanda zai zo ne ko kuwa na bai san dalilin rashin zuwan maryama aiki bane ko yace mai tsaidaita ?."
sectary ta biyo shi tana kwantar masa da hankali akan zata zo may be hodop ne ya riketa tunda ance tun da sassafe ta bar gida ya kalli agogon hannunsa a d'age yana cewa " wani irin hodop ne wannan har biyu saura ?yayiwa