Showing 63001 words to 66000 words out of 182919 words
."a natse ya soma masu bayani aikin da yake so yana zagaye makeken table din da suke zaune yana cigaba da kallonta zuciyarsa na sake narkewa akan soyayyarta." ita din daban ce acikin zuciyarsa kuma yayi imani tunda Allah ya hallata zuciyarsa ya sanyata aciki ,kamata yayi ya mallaketa cikin sauki batare da saninta ba, ahankali sai ya dinga shigar da soyayyarsa dan a yanzu soayyar wannan mataccen mutumin bazai bar zuciyarta ta amshesa ba ."
" taya zaka sameta cikin sauki "?ya tambayi kanshi samunta shi yafi komai sauki da yuwuwa agaresa tunda kawunta gali yana raye yasan bazai ta'ba bashi matsala ba "ya bawa zuciyarsa amsa da haka sama da awa daya yana bayani kuma duk hankalinsa da natsuwarsa suna kanta duk sanda ta d'ago kanta dole zata kallesa dan idanunshi na kanta bayan ya gama bayani ya basu lokacin da zasu yi submitting aikin sannna ya sallami kowa har ta mike kasance war itace last person din da zata fita yace "tsaya .”
tana kallonsa ta koma ta zauna tana jin wata irin mummunar fad'uwar gaba mai tsanani sam bata son wannna mayataccen kallon da yake mata yana saka zuciyarta jin wani irin firgici." mr ata ya samu waje ya jigina jikinsa da bangon d'akin tare da rungume duka hannuwansa a qirjinsa yana cigaba da dubanta cike da tsananin qaunarta.”
wani abu ya gani kamar hawaye yana diga a saman hannunta .bai san lokacin da yayi taku ya qarasa inda take zaune ba, ya zauna a gefen table din da hannunta ke kai ya duko da kanshi daidai fuskarta qirjinta ne yayi wani irin tsalle sakamakon sanyayyen kamshin turarensa daya ziyarci hancinta tayi saurin runtse idanunta tana sake jin fad'a uwar gaba ."hannunsa ya kai ya d'ago ha'barta agigice ta bud'e idanunta dake runtse ta zuba masa nan yaga hawaye cike da idanunta suna siyayya bai ce mata komai ba ya sanya kwayar idanusnhi cikin naya sannan ya ciro handkerchief a gaban aljihun rigarsa mai azababben kamshin turaren red ya soma goge mata hawaye . inda maryama take binsa da wani irin firgitaccen kallo kafin ahankali ta kawar da idanunta gefe tana mai danne hawayenta Itafa gaskiya ya fara takura mata da kallon nan shi na babu gaira babu dalili ,dan idan akwai abinda ta tsana arayuwarta daga nmj to bai wuce yawon kallo ba sam bata són shi kuma ta rasa dalili da koda yaushe idanunshi na kanta ."
"maryama !"
Taji ya kira sunanta muryarsa a raunane kamar mai shirin yin kuka ta waigo ta kallesa a natse idonsa cikin nata , ya matsota sosai tare da riko laulausan tafin hannunta cikin nashi yana murzawa wani irin yanayi suka tsinci kansu ciki mai wuyar misaltuwa nan take jikinta ya kama rawa alamun rashin sabo "ina son zan miki tambaya biyu .yayi maganar fuskarsa a had'e kamar ko yaushe bai tsaya jin amsarta ba ya soma magana ."me yasa kike yawon kallona ?"ta d'an ware idanunta sosai cikin nashi tana mamakinsa "ita ya kamata ta tmbyesa amman dan rainin wayo da karfin hali irin nasa shine zai ambayeta ?tayi mgnr a qasan ranta tana lumshe masa shayayyun idanunta tare da sauke naunayen ajiyar zuciya "ki bani amsa kafin na shigo da tambayata ta biyu ."
still shiru tayi dan idan tace zatayi magana to bakar magana zata fad'a masa wanda hakan zai iya dagula komai ."okay tunda baza kiyi magana ba bari naje tamvayata ta biyu ta natsu sosai tana jiran taji tambayar rainin hankalin da zai sake mata "me ya sakaki kuka yanzu ?"shiru tayi kawai tana kallonsa dan bata da abinda zata fad'a masa a zahiri , amman zuciyarta cewa tayi kwayar idanunka ne suka sakani kuka bana son yawon kallonka ."ya tsuke bakinsa yana duban cikin kwayar idanunta batare da yace mata uffan ba ."tayi qoqarin ta cire tafin hannunta cikin nashi sakamakon wani salon da yake mata mai fitar da mutun haiyacinsa amman taji ya rike yatsun hannunta gam ji tayi wani sanyin dadi na ratsa sansar jikinta har tsigar jikinta na mikewa abinda bata ta’ba ji ba kenan a iya tsawon rayuwarta akan wani d'a namiji sai akanshi ."
Allah ya taimaketa rigar dake sanye a jikinta mai dogon hannu ce tasan data shiga uku idan ya gani dan tayi imani sai ya tamvayeta dalilin mikewar gashin dake kwance ajikinta ."ya sake had'e fuska sosai tamkar zaki kana yace "ko kina kukan tsohon mijinki ne ?"shiru tayi kafin ahankali ta tsinci kanta da ce masa" eh ! rashinsa yasa bana jin dadin rayuwata .tayi maganar idanunta na cikin nashi "zafi nake ji sosai a qirjina "ta sake mgn cike da dakiya ai gama fad'ar haka da tayi keda wuya taji ya sakar mata hannun tare da mikewa tsaye ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ya juya ya fita daga d'akin zuwa office dinsa zuciyarsa nã qauna da tafasa zariya ya soma acikin office din yana zance zuci ".shikenan rayuwarsa tana cikin uku bala'i yana mutuwar sonta ita kuma tana mutuwar son matacce ya zai yi kenan ?" shirin mallakarta da yake son yi bashi da wani amfani kenan ?"ya fad'a a fili tare da dungule hannunsa ya d'aura akan table "shikenan wahalarsa ta tsawon shekaru ta tashi a banza ?"no no!! it can be possible "dole ne nayi duk abinda zanyi na cire shaukin soyayyar acikin tunaninta ."
Ahankali ya samu waje ya zauna yana sauke numfashi tare da dafe goshinsa yana jan tsaki inda zuciyar maryama ta cika da tsananin mamakinsa wannan shine karo na biyu da yake nuna damuwarsa akan mijinta to me haka yake nufi ?”ta tambayi kanta ganin ta kasa gano dalilinsa kuma kamar matsawa kanta da son gano dalili tamkar bawa kanta wahala ta tarkata komai ta watsar ta mike ta fito ta koma office dinsu .mr ata ya jima zaune ahaka yana saka da warwara ahmed yaronsa na Z&A ya shigo cike da girmamawa ya gaishesa sannan yaja kujerar dake fuskantarsa ya zauna ya ajiye masa file a gabansa "sir ana bukatar saka hannunka anan da anan ya fad'a tare da zaro biro a gaban rigarsa ya mika masa ya karbi biron yayi sign sannan suka fara tautaunawa akan kasuwanci sun d'auki sama da awa d'aya sannan yayi masa sallama ya wuce yana fita James ya shigo ya ajiye masa cup din coffee wanda ya za me masa jiki sannan ya ya juya fice .”
ahankali ya d'auki cup din ya kai bakinsa kamar ance ya kalli office dinsu maryama wani maaikaci mai suna ema ya hango duke a gabanta suna magana fuskarsu d'auke da annashuwa duk da bai san maganar me suke yi ba amman fuskokinsu ya nuna alamar maganar tana masu dadi sosai .”anatse ya ajiye cup din hannunsa ya zagayo hannuwansa duka cikin aljihunsa yana taku zuciyarsa na tsinkewa yana shiga office din bai ce masu uffan ba sai ji ema yayi mr ata ya zagaye wuyansa da hannunsa yayi hanyar waje dashi a gigice yake kallonsa yana biye dashi ,haka ma maryama a gigice tabi bayansu da kallo ahankali ta maida kanta ga aikin da take kafin ya gama dashi ya dawo kanta "kai tsaye office dinsa ya nufa dashi tare da hankad'a keyarsa ."fuskarsa a hade tamkar kumurci macijin dake neman abinci yace " zance me kuke yi ?"yayi masa tambayar yana juya masa baya ".
“kayi hakuri sir muna magana ne akan wannan sabon aikin dakayi mana bayani akanshi d'azu na banjana company shi muke sake tautaunawa akai domin yana bukatar nazari sosai "bayan shi kuma?”
”amm sai kuma dan naga sabuwar zuwa ce ita shine nake son na koya mata wasu abubuwa "mr ata ya juyo a natse fuskashi babu annuri yace "waye yace maka bata iya abubuwa ba ?ema yayi shiru sai dai à matukar firgice yake da irin kallon da mr ata yake jifansa dashi ".wannan da kake gani tafika fikira sannan tafika kwarewa akan komai zai fi kyau ka tsaya iya inda aka ajiyeka aiki ba yawon shiga cikin rayuwar wasu ba "wannan gsky ne sir dan yadda take magana ma kawai ya isa yasa mutun ya manta tarin ayyukan dake gabansa dan tana magana ne cike da shauki "what .?"mr ata ya furta acikin ransa qirjinsa na wani irin luguden bugawa sannan yana aikawa da ema da kallo mai hargitsa tunanin mutun da saka mutun shiga uku ."
Ya tsaita kallonsa sosai ga ema sannan ya cigaba da magana "yadda take magana da kai haka take magana da karnuka da kuma aladu da jakuna dan kasan ba wai matsayinka ne yasa take magana da kai haka ba ,ka tattara ka koma office din qasa kwata kwata "ema ya zaro idanu waje da sauri yana dubansa a marairaice "kana ‘ batawa kanka lokaci maza kaje ka tattara ka koma inda nace "ayi hakuri sir ban san cewar matsayinta ya .."leave my office kafin nasa a dakatar da kai gabad'aya ai da wani mugun sauri ya juya har ya kusan kai bakin kofa ya jiyo sautin mr ata cak yaja ya tsaya da girmamawa “bance ka fad'awa kowa dalili ba muddin kuma naji wani to kasan ka kori kanka da kanka aiki da sauri ya qarasa ficewa ya shiga office na tsakiya wanda ya kasance anan yake aiki ya dauki bakar jakarsa ya saba a kafad'ansa sannan ya d'auki laptop dinsa ya rungume yana kallon sauran abokan aikinsa yusura tace "ema ina zuwa haka "?an maidani office na qasa gabad'aya "what ?"ta mike tsaye hankalinta a matukar tashe alokacin da shi tuni ya fito.”
ta biyosa tana tambayarsa dalili amman bakinciki ya hanashi yi mata bayani haka ta juyo jikinta a sanyaye ta koma office cike da kewarsa dan gskiya ema yasan kan aikinsa gashi da sauki kai ,dan duk lokacin da ya gama aikinsa zai kar’bi nasu yayi.."
Yau Kamar abun had'in baki kusan hankalin mazan dake aiki tare da maryama duk yayi kanta bini bini zasuje inda take ita kuma cike da sakin fuska take sauransu suyi abinda zasu yi su koma mazauninsa wanda hakan keta faman baqanta ran mr ata hatta masu shiga da fite dan duk wanda ya shigo sai dai idan bai daura kwayar idanunshi akanta ba amman sai hankalinsa ya tsayu akanta wannan alamari fa ya daga hankalin mr ata matuqa sosai yasanya ido akanta ".Mr ata na zaune tare da wasu abokon business dinsa mutun uku alhj deeni ,alhj farooq alhj bb ya tsinkayo muryar maryama tana neman izinin shigowa.”
muryarsa a tsarke ya bata izini a natse ta shigo tunda ta shigo wad’an nan mutun nan suka tattara hankalinsu gareta,cike da girmamawa ta gaisheku
Sannan ahankali ta qaraso gaban mr ata ta ajiye masa file din da zanen datai ." ya tsurawa zanen ido na second goma kafin ahankali ya motsa labbansa yace "you can go back to your work ."har tayi taku biyu yace "ke.."ta juya a natse idanunshi na kanta kamar yadda idanun bakinsa ke kallonta kamar zai cinyeta wanda hakan ya haddasa mata jin wani mummunar faduwar gaba "shiru yayi kafin yace d'auki cup din can ki samu some ta nuna miki yadda ake had'a min coffe "okay sir “. ta furta cikin sanyayyar muryarta yayinda jikinta ke rawa rawa
ya d’auke kanshi ya maida kan bakinsa daya lura sunata kallonta amman sai ya share .”
Ta qarasa inda cup din yake ta dauka ta soma tafiya kamar wace aka hankada aiko qafafunta suka hard'e tayo kansu mr ata bai san sanda ya mike tsaye ya shiga tsakaninsu ba ta fad'a saman faffad'an qirjinsa tayi masauki atare suka dinga sauke ajiyar zuciya "ki dinga bi ahankali kada ki jima kanki ciwo kija ma kanki asara.” ya furta cikin wani salo da sautin murya mai sanyi yayinda hucin bakinsa dana numfashinsa na dukan wuyanta da fuskarta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa yrrrrr".
"Kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta dinga furtawa ahankali ahankali sakamakon yanayin data tsinci kanta .”ya riko tafin hannunta ya zaunar daita akan kujera qirjinta na bugawa fat fat kamar zata fasa qirjinta tayo waje . ta had’e yatsun hannunta waje daya tana murzawa shi kuma ya janyo wata kujera ya ajiye adaidai saitin bayanta ya zauna yana kallon inda su alhj deeni ,alhj farooq ,alhj suke zaune sun zubawa ma iyalinsa idanunsu kowa da abinda yake sakawa a ransa,a hankali mr ata ya lumshe idanunsa tare da sanya hannunsa a saitin kirjinsa yana murza dai-dai indai zucyarsa take beating vry fast,su kuwa cigaba da kallonsa suke
suna kallon sarautar Allah "dan babu tan tama mai kamfanin AGC ya kamu da mummunar qaunar yarinyar nan qauna kuma mai girma qauna ce da ma basu ta'ba ganin irinsa ba ".
tsumammun danunsa ya ware sosai akansu yana cewa "mintuna goma kacal sun isa ku tattara duk wasu kalamanku masu mahimanci." sarai sun fahimci inda ya dosa dan haka suka taikaita maganarsu kamar yadda ya bugata suka kama gabansa tun kafin yace ya fasa halqallar kasuwanci dasu ."bayan tafiyar bakinsa ya mike tsam ya janyo kujera zuwa gabanta ya zauna tare da ware qafafunsa ,sunyi mugun yin daf da juna ta dan ja kujerar baya kad’an amman hakan bazai hana idan ya sauke numfashinsa taji ba. ganin yadda idanunshi ke yawo ajikinta yasa tayi saurin sunkuyar da kanta qasa natse alokacin daya soma magana a tsanake amamn idan mutun ya natsu sosai zai fahimci cikin tsananin fushi yake "anya kuwa kwakwaluwarki tana da cikakkiyar lafiya kuwa ?" ta d'ago kanta a gigice tana kallonsa "yes !dole na tambayeki dan kin wani tsareni da idanu "ya qarasa maganar yana lumshe mata ido .”
“Ko me ya gani atattare daita yasa zai had’a da wannan mummunar ciwo ?” tabi jikinta da kallo na second goma sannan ta d’ago ta zuba masa idanunta “me yasa zaki fad'a kan mutane ?" Muryarta na rawa tace “wallahi ban sani bane ni ma haka kawai naji jikina ya kama rawa.” taso ta fad'a masa idanunsu ne yayi mata yawa amman sai ta tsinci kanta da kasa fad'ar haka dan batasan me hakan zai haifar ba tunda ta rigada tasan halinsa abu kad’an ke hassalashi "idanun maza yayi miki yawa kina gani bai kamata kiyi aure anan kusa ki huta ba "?tayi shiru tana cigaba da kallonsa yayinda qararrawar zuciyarta na kad'awa da sauri sauri sakamakon kusancin da suka samu na haifar mata da shiga cikin wani yanayi "ya dai kamata kiyi tunani ko sanin cewar ke matar aure ce zai saukaka miki wasu abubuwan ."numafshi ta janyo ta sauke da kyar tana sake sunkuyar da kanta gabdaya ta sake neman natsuwarta ta rasa rawar da jikinta keyi ta qaru ".
“Maryama ki tsaida miji kiyi aure zai fiye miki kina aure kina aikinki , dan bai dace ki dinga kula kowani kare alade da jaki ba "idan dai kema din ba irin hallitarsu gareki ba ."ya qarasa mgnr yana jan tsaki tabi shi da wani irin kallo zuciyarta na tsinkewa idan ta fahimcesa da kyau" idan halittartata ba irin ta jaki kare da alade bace ta daina kula kowa kallonsa take fuskarta da bayananen mamaki “to shi da yake kulata take kulasa fa ?”kenan shima ya kasance d’aya daga cikin abinda ya lissafa kare da alade da jaki ne ?”tayi maganar a can kasan makoshinta ta yadda ko shi da yake zaune a gabanta bazai iya fahimtar komai .ya juya ya d'auki kwalin sigari ya bud’e ya zari d’aya ya kai bakinsa ya kai hannu ya dauki abun kunnawa tana ganin haka ta zabura ta mike ranta a matukar bace ta nufi kofar fita tana jan tsaki da kallo yabi bayanta yana ta'be fuska "abinda zaki qarasa tsawon rayuwarki daita itace abar gudu ai gara ki fara sabawa daita sannna ya lumshe idanunshi lokacin guda kuma ya budesu yana cewa "ke dawo ki zauna ."!
Maryama taki tsayawa bare ta dawo kamar yadda ya bukata "idan kika kuskura kika bar office din nan ki tabbatarwa kanki kin tafi kenan har abada bazaki sake da aiki a AGC ba ".cak taja qafafuwanta ta tsaya tana sauke wani wahalallen numfashi daga inda yake zaune yana kallon yadda kafad’unta suke d’agawa sama alamun tana kokuwa da numfashinta Ahankali ta juyo tare da sunkuyar da kanta kasa dan bazata iya cigaba da kallonsa a yanayin da yake ba saboda yayi mugun tsareta da ido yana kallonta tana takowa ahankali har sanda ta qaraso ta tsaya "set "! ya fad'a yana kunna sigarinsa muryarta sanyaye tace "sir kayi hakuri ka kashe wannan abar bana son warinta "daga yau ki koyi son warinta set !ya sake maimaitawa" inna ilaihi ita kam ta shiga ukunta da wannan mutumin ta sake yin kasa da muryarta sosai kmr zatayi kuka "sir kada kamin haka dan Allah "me nayi miki ?"ya tambayeta yana dage mata girarsa d’aya “sigari ce fa kawai ?meye illarta?" set and don't let me repeat my seif again ".
babu yadda maryama ta iya da rayuwarta haka tayi shiru ta toshe hancinta da hannunta d'aya dayan hannun kuma taja kujerar baya kad'an domin rage kusancinsu ta zauna sai dai duk a rud'e take .
tunda ta zauna bata d'ago kanta ba yayinda shi kuma kwayar idanunshi ke kanta yana zugar sigari yana zance zuci "ta d'ara duk matan duniya a idanunsa ita kadai zuciyarsa take so ,kuma bazai ta'ba son wata bayanta