Showing 150001 words to 153000 words out of 182919 words

Chapter 51 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

362

dan nasan bazai bar abun ya tafi haka ba, ko babu komai dole zai qare mutuncinsa dan haka ki kwantar da hankali ki share karki nuna alamar akwai wata matsla ,maryama ta gyad’a mata kai tana qoqarin saisaita kanta .har suka isa unguwarsu maryama madam some na kwantar mata da hankali .”





“Tunda maryama ta isa gida ta kasa aiwatar da komai duk da tana ta qoqarin kawar da damuwar dake tattare daita sai dai kallo d’aya zaka mata ka tabbatar da bata cikin natsuwa da kwanciyar hankalinta minti minti take sauke naunayen ajiyar zuciya ,kuma irin wanda yake fitowa daga kasan zuciya umma sarai ta fahimceta dan haka ma ta isketa ta tamvayeta amman tsananin zurfin ciki irin na maryama ta kasa cewa daita komai ,ganin tunani zai mata yawa kuma hakan zai iya barin hankalin umma yaki kwanciya yasa ta d’auko littafi ta dawo parlour ta zauna tana dubawa wanda hakan bai rage mata komai daga cikin d’igon damuwar da take cunkushe a zuciyarta ba.”
ahankali take bin littafin tana goge hawayen dake tsiyaya a gefen idanunta ta d’auki kusan mintuna talatin tana zaune tana duba littafin da babu abinda take fahimta aciki idanuwanta sukai mata nauyi sosai saka makon abu biyu da suka had’e mata waje d’aya bacci da kuma damuwarta. anan ta zame ta kwanta akan kujera tare da yin shiru tana zance zuci “ko a wani hali mr ata yake ?”ko me ya iske a gidansu ?”haka nan take jin ya dace ace ya kirata yaji halin da take ciki, ko tana tare da matsala ko akasin hk?” dan tabbas ya kamata ya kirata yaji yata qare ta iske an turo hotunansu gidansu ko kuwa amman ya shareta “wato kowa yaji da damuwarsa.”



sannu ahankali bacci ya d’auketa da tunanin mr ata acikin ranta ,acikin bacci ne taji ana shafata ana mata massagin jikinta ana mata magana cikin wani irin salo.”ahankali ta bud’e idanunta ganin mr ata tayi manne ajikinta,ya d’aura kanta adaidai damtsen hannunsa yayinda bakinta ke daidai nipples dinsa ,ta d’ago kanta zuwa fuskarsa, janyota yayi jikinsa sosai yana cigaba da shafa sansar jikinta “kina dani ki daina damun kanki too much duk wanda ya ta’ba min ke zanji dashi “zare jikinta tayi daga nashi ta tashi zaune tana girgiza masa kai tana share hawaye tace “kai din ba nawa bane taya zan yarda da Kai ?”
ya janyota zuwa jikinsa yayi mata kyakkwan runguma a faffad’an qirjinsa“ki yarda dani“!
ya fad’a yana d’aura lips dinsa akan nata cike da shagwaba tace “ni dai kataimakeni “ya cusa kanshi a qirjinta yana cewa “zanyi komai dan bana son ganinki kina kuka.” ahankali ta dinga jin yana sarrafata cikin mafarki ita dai bata san ya’akayi taje d’akinta ba sai farkawa tayi da misalin qarfe hudu na dare da wasu mintuna ta ganta kwance a d’aki .”


ahankali ta mike zaune bakinta dauke da addaur tashi a bacci tana sauke numfashi ta godewa da mafarki tayi ba gaske bane komawa tayi ta kwanta lamo tana tariyo abubuwan da suka faru acikin mafarkinta tana kwance tana juyi har aka fara kiran sallah ta tashi ta matso kad’an ta zuro qafafuwanta duka qasa sannan gangar jikinta ya biyo baya kai tsaye bayi ta shiga tai wanka ta d’auro alwala ta fito ta sanya doguwar riga da hijab ta qarasa inda daddamar sallarta take shimfide kamar koda yaushe ta soma gabatar da raka’atani fajiri byn ta idar ta mike tai sallah bayan ta idar sallah bata mike ba ta soma azkar sannan ta janyo alqurani ta soma karatu cikin surataul ahraf har zuwa karfe shida daidai sannna ta rufe alqurni ta samu waje ta kwanta a kasa kasance war har lokacin akwai bacci acikin idanunta,nan take wani bacci yayi awon gaba daita kusan yadda baccin safe yake bare ya hade mata da gajiyar zuwa aiki da tarin damuwa bata dade tana bacci ba ta tashi tana miqa tana duba lokaci “takwas da wasu mintuna da sauri ta soma shirin zuwa office bata wani jima ba ta fito kai tsaye falo ta wuce inda ta iske umma zaune .”


Ahankali ta zauna akan hannun kujerar da umma take zaune tana cewa “umma ina kwana !”ta gaishe da umma tana daukar littafinta na jiya .umma ta amsa mata muryarta cikin wani irin yanayi maryama ta dubeta a tsanake qirjinta na bugawa so take ta gano ko akwai wani abu dan haka jikina a matukar sanyaye tace “umma ya naji muryarki tayi wani irin ?”me murya ta tayi maryama ?ta tambayeta tana dubanta “ai umma ji nayi muryarki tayi wani irin ba kamar yadda na saba jinta ba sannan yanayinki kmr kinyi kuka .”ta qarasa maganar tana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba.murmushi umma ta sakar mata tana cewa “ke fa matslarki kenan saurin rud’ewa babu abinda Ke damuna kece ma zance yanayinki kmr kinyi kuka bama kamar bane kinyi kuka dan ga sheida nan a little danunki bata da ja domin ita kanta tasan tabbas a irin kukan datai dole za’a gane ba “tabbas nayi kuka umma amman acikin mafarki .”umma bata mutsa mata ba amman tasan ba’a mafarki bane azahiri tayi kuka amamn tunda ta zabi ta fad’a haka shikenan “na had’a mana tea mai dadi bari naje na kawo miki jirani ina zuwa .”umma ta mike ta nufi kitchen inda maryama tabi bayanta da kallo mai tattare da tsantsar qauna tana zaune umma ta fito ta dawo gabanta ta tsaya tana mika mata cup din tea “ga naki tea tasa hannunta ta kar’ba cike da girmamawa tace “na gode sosai ummata umma ta kai nata cup din baki ta kur’ba tana cewa kai tea din nan yayi dadi sosai hakan yasa maryama ta kai nata cup din bakinta ta soma kur’ba tana lumshe ido “gsky ne umma yayi dadi kuma ya sha bambam da sauran tea “kuma kinga bashi da wata wahalar yi ba idan zaki yi ki samu kanufari,lipton tafarnuwa mint leave da gayen nahna’a shikenan ina son ki koya dan bamu san wani irin mutun zaki aura ba, idan allah yasa mai yawon sha tea ne shikenan sai ki dinga masa irinsa” kai umma duk maganarki bata wuce ta aure nifa ynzu ba aure bane agabana kamar yadda na sha fad’a miki burina a yanzu mu bar gidan nan “nasani amman kibi komai ahankali” umma ta fad’a tana dubanta a natse kafin ahankali ta cigaba da magana ina son ki bani aron hankalinki jin haka yasa zuciyar maryama ta fara tsinkewa ina son nayi miki magana akan wani abu zuciyarta ce ta cigaba da tsinkewa yayinda ilahirin jikinta ya d’auki rawa babu shiri ta ajiye cup din hannunta ta tsura mata ido “muryarta a sanyaye tace “ina sauraronki umma “ina son Kiyi aure maryama bazan so ki cigaba da rayuwa haka ba wani irin ajiyar zuciya ta sauke mai qarfin saka makon ba abinda tayi tunanin bane “ muddin ban baki shawa rar kiyi aure ba lallai ban cika mai adalci ba ,aure yana daraja kuma zai kareki daga dukkanin wata matseefa “in sha allahu zanyi umma amman ba yznu ba dan ahalin yanzu babu wanda yace yana son maryamarki ko da yake kin dai san maryamarki da bakinjini .”ta fad’a tana dan murmushi “.


“ni maryamata bata da wani bakinjini kisa niyya sai Allah ya taimakemu ,shikenan umma naji bari na wuce aiki lokaci na tafiya .”har tayi taku biyu ta kira sunanta “maryama !ta tsaya cak batare data juyo ba ki tsaya bari naje na kawo miki custard lokacin data juya alokacin maryama ta juyo tana duba agogon hannunta, lokaci ya soma tafiya umma bata wani jima ba ta fito hannuta rike da wasu flaks guda biyu kanana
ta miko mata daya maryama ta kar’ba tana murmushin jin dadi “kai gaksy umma kina ji dani shiyasa nake sonki fiyye da komai kamra Kinsan kwana biyu nayi missing custard dinki ai shiyasa nayi miki dan nasan kina so ga naki ,wannan d’aya kuma na mai gidanki “what !”
Maryama ta furta da karfi jikinta har rawa yake tsabar rudewa “umma wa kenan kike magana akai wa custard ?wa kuwa bayan mai gidanki mr ata shi zaki kaiwa nasan bai ta’ba shan custard irinsa ba “what !” wai mr..”mr ata kike nufi ?ta fad’a murayarta na rawa me zai yi da wani custard umma?” ke kike tunanin mai zai yi dashi ke dai ki kai masa ki gani “murmushi maryama tayi tana cewa “amman dai umma da wasa kike ko ?” idan ba haka ba ta yaya zan kai wa mr ata custard?”


“to ke mai yasa kike mamaki ke dai nace ki kai masa kuma kice inji mamanki “no no umma karki damu kanki wallahi baki san waye wannna mutumin ba shiyasa ,mutumin da bashi da bambamci da hawainiya mutunin da zuciyarsa bata da bambamci data dutse kai zuciyarsa tafi ta dutse karfi mutumin da babu abinda yasani sai wulakanci da tozarci shine mutumin da kike tuannin na kaiwa custard?” ina bazan iya ba umma ba,” tsaya maryama ina son ki fahimceni kema na rasa gane kanki wata rana kice mutumin kirki ne wata rana ki canza magana ,ni wanne zan dauka aciki maryama tai shiru kawai cikin tsnanin damuwa dan tasa aiki ja umma take son bata ,duk abinda kike fad’a akansa ni dai abu daya nasani zuciyata tana son shi a haka duk rashin kirkinsa shine yayi nasarar dawo miki da farinciki da walwalarki dan haka ki amsa ki masa idan na isa dake idan kuma ban isa dake ba nasani.” lumshe idanu maryama tayi “.
“na fahimceki umma amman walalhi mutum ne shi mai wuyar shaani”nasani !wallahi umma da wahala ya karba ki fahimceni ba wai ina jayayya dake bane halinsa nasani “nace miki zai amsa ki kar’ba to ni yanzu idan na kai masa mai zance masa ?”
tai maganar tana dafe goshinta umma tace “ bazanki bin umarnina bane ?”babu shiri maryama tasa hannu ta kar’ba “yauwa sai kin dawo Allah ya tsareki “ ahankali ta juya ta bar bangaren da sauri inda ta bar umma tsaye tana kallonta “maryama kenan bazaki gane abinda wannna mutuminn yake nufi dake ba sai nan gaba kin kasa fahimtar mai yasa ya damu dake, me yasa yake yawon fushi akanki ,mai yasa ya damu matukar sai kinyi aiki akarkashinsa ,ni dai nayi imani akwai wani abu acikin ransa akanki, koma dai menene Allah kasa mu dace Allah yayi miki kyakkywan zabi mafi alkairi arayuwarki da addininki.”



Ahankali maryama ta shigo ma’aikatan tana gyara zaman jakar dake kafad’anta tare da rike qaramin jakar da umma ta sako mata flaks ciki duk ilahirin jikinta yayi wani iri yayinda zuciyarta ke cike da tsannain fargaba “maryama ki sanyawa jikinki jarumta sannan ki karkafa zuciyarki, yanayin yadda kike damun kanki akan abinda bai kai ya kawo ba, yanayin ne damuwa zata miki yawa.”
ki samu natsuwa ba dole sai kin bashi sakon umma ba zaki iya bawa wani ya shanye a madadinsa tana tafiya tana zance zuci a natse ta shiga office dinsu ta gaishe da mutanen data iske ,sai dai babu wanda ya amasa mata bare ya kalli inda take, sai yusura kad’ai ta amsa mata sa’banin jiya tana kallonta cike da tsananin tausayi da mamakinta dan har lokacin bata daina mamakin hotunan jiya da’aka tura masu ba .”


Maryama tana tsaye madam some ta shigo ta wuce ta gabanta tana kallonta tana zance zuci tare da nazarin maryma har a wannan lokacin zuciyarta bata bar mamakin mami da dalilin da yasa ta tambayeta tsakanin maryama da mr ata ba ,da kuma dalilin mr ata na cewa lallai ta tabbatar maryama ta shiga motarta kuma lallai ta kaita har unguwar su “amsarki itace mr ata yana tsananin son maryama haka ma mahaifiyarsa ta fahimci irin son da yake mata shi yasa ta kiraki jiya domin ta tabbatar
Numfashi ta sauke adaidai lokacin da maryama tace “good morning ma !” madam some ta amsa mata ,inda maryama ta samu waje ta zauna ta ciro littafinta tana dubawa sai dai bata fahimtar komai “maryama bai kamata kiki bin umarnin umma ba ,meye aciki ki kai masa idan ya kar’ba fine idan bai kar’ba shikenan sai ki bawa wani amamn idan kika ki bashi idan kin koma gida ta rutsaki me zakice mata?” ko idan tace ki rantse me zaki ce ?”.
shiru tai kawai tana tunanin yadda zatayi bayan wasu mintuna ta mike ta nufi office dinsa bata iske madam some a mazauninta ba dan haka ta soma qoqarin shiga ta ajiye masa ta kama gabanta inda ahankali madam some ta kai hannu ta dafata da sauri ta juyo jikinta na wani irin rawa lafiyarki maryama me kikeyi ?sorry ma ta fad’a bakinta da jikinta na rawa kina bukatar wani abu ne ?no ..”no ma .”meye wannan rike a hannunki ?”amm daman mamana ce tayi wa mr ata custard tace na kawo masa .”
nan take gaban madam some ya bada rasa haka ma sultana dake tsaye a bayansu dan tana hankalce da duk wani motsin maryama “kutumar uba can .”sultana ta furta tana cewa” lallai ma yarinyar nan yayinda madam some tace “shikenan kije ki fara aikinki kafin yazo dan har yanzu bai qaraso ba tukun, jiki a sanyaye ta juya bayanta da zumar komawa office tana gama juyawa taga sultana tsaye tana jifanta da wani rikitaccen kallo wanda yasa hantar cikinta kad’awa bata ce mata Uhm ba bare uhm uhm hakan nan yau kallon nata ya saukar mata da mummunar fargaba mai tsanani.”sultana ta cigaba da aika mata da mugayen kallo mai had’e da harara.”




Maryama na tsaye cikin tashin hankali da tsananin fargaba sai gashi ya shigo ya iskesu tsaye “good morning sir”. ta furta da sauri qirjinta na bugawa “morning “!kawai yace tare da kallon inda madam some take yace some kije ki fad,awa duk wanda aka turawa hotunan nan su goge kuma muddin ya fita nayi bincike na gano wanda ya fitar dashi qarshen aikinsa yazo bayan na d’auki mataki akansa” okay sir yana gama fad’ar haka ya shige office dinsa yayinda maryama ta sauke numfashi tana mai Jin farinciki ta koma office da sauri sultana itama ta juya ta shiga wani office ta samu waje ta zauna tana tunanin matakin da zasu d’auka akan maryama.”


Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye acikin office din tana tunanin yadda zatayi ta bashi sakon umma tayi taku d’aya biyu sai kuma ta tsaya gabdaya ma’aikatan dake office din suka bita da kallo sultana da hankalin ta ke kan maryama tai murmu shi yayinda maryama ke sake sake “ naje na bashi yanzu ne ko kuma na bari zuwa anjima na kai masa tana kallonsa ya fito yana kiran sunan some “yes sir “! ta amsa masa dashi yayi mata magana a can kasan makoshi sannnan ya fice da idanu maryama ta bishi dashi tana sauke wani wahallen numfashi ,sultana ta kasa hakuri ta mike ta shigo office din da maryama take ta tsaya adaidai gefenta “ban ta’ba ganin yar talakawar dake shishigi irin naki ba ,wama yasan me aka zuba masa cikin custard din da ake son ya sha dan naga duk hankalinki baya jikinki alamun rashin gasky? .



maryama ta dago kanta ta kalleta da mamaki sai dai bata ce mata komai ba ta maida hankalinta akan aikinta tana zance zuci ,”da Kinsan da yaya na taho da custard din nan da bakice haka ba ,any way ma mai zai sa ayi wa mr ata wani abu mai ake nema agurinsa kawai dai kyatatawa ce irin ta umma ba komai bane”idan kuma son shi kike yi gara kiyi maza ki ciresa aranki dan yafi karfin aurenki ,sai dai ya more kuruciyarki kamar yadda muka gani a hotunan wama yasan me ya faru a tsakaninku dan a yadda nake kallonki zaki iya aikata fiyye da zina “subhallah maryama ta furta a fili tana kallonta da kwayar idanunta da suka soma canza kala tsabar bacin rai “mai yasa sultana zaki fad’a min haka ?”wallahi Allah shine shidata akan hotuna nan kuma nasan duk abinda zan fad’a bazaa ta’ba yarda dani ba amman kije na barki da Allah daman dashi kawai zaki barni dan babu abinda zaki iya min munafuka kawai “dan Allah sultana bana son tashin hankali ki barni naji da damuwata maryama ta fad’a qirjinta na Dylan uku uku gbdy taji sauran natsuwar dake jikinta ta kau mussaman a yanzu tafi Jin bugun zuciyarta yana qaruwa
duk baqaqen maganganun sultana maryama bata tankata ba ta shareta ta cigaba da aikinta sai dai zuciyarta ke mata wani irin zafi kusan mintuna talatin maryama na zaune tana aikinta batare data kalli kowa acikin office dinsu ba haka zalika bata ga dawowar mr ata ba har lokacin break yayi.”
ta ciro flaks dinta ta d’aura akan table ta soma shan custard din tana cikin sha wayarta ta soma vabriting alamun kira ta ciro ta duba sunan umma ta gani yana yawo a scren din wayar ta d’aga tana cewa “hello umma nah daga bangaren umma tace “hello maryamata ya kike ya aiki.”? “alhamdulillah umma!” kin bawa mai gidan custard din kuwa ?”
”amm umm ban bashi ba nasan kunya kike ji da tsoro Kiyi qoqari ki cire tsoron nan ki bashi kinji diyata zan ji dadi idan kika bashi sannan zanyi farinciki idan ya kar’ba ya sha.” “In sha allahu umma zanyi qoqarin na bashi yanzu ma dai baya nan tun dazu daya shigo ya fita banga dawowarsa ba amman da zarar ya dawo zan bashi tana cikin magana sai gashi ya dawo tace “yauwa gashi nan ma amman wallahi umma tsoro nake ji ban san yadda zai dubi abun ba bana son yayi react kamar cutar dashi zanyi .”


“karki damu maryama bana jin zai yi tunanin wani abu kije ki bashi “to umma kin sha naki ne Eh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login