Showing 153001 words to 156000 words out of 182919 words

Chapter 52 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

365

umma shi nake sha okay yayi sai kin dawo “ya rab ka taimakeni ban san yadda zanyi na bashi custard din nan ba gashi yau da alamun akwai rashin mutunci atare dashi kar naje ya sauke min ruwan balai tana cikin wannan halin yazo ya tsaya akanta “maryama”! yes sir !”ta amsa da haka tana qoqarin rufe flak’s din gabanta ta mike tsaye “ance kin kawo min wani abu me kika kawo min ?..”


“uhm ..” no sir bani bace daman umma ummata ce .”ki natsu ki yi min magana ta yadda zan fahimta “daman me ..”?daman ummata ce tayi maka tace na kawo maka “.ta fad’a jikinta da zuciyarta na karkarwa hakan yasa tayi saurin tsarke hannu wanta waje d’aya domin taimakawa gangar jikinta samun sausauci idanunshi ya tsura mata ta cikin farin glas din dake manne da kwayar idanunshi yana kallonta kmr zai cinyeta ,kafin ahankali ya ciro hannunsa d’aya cikin aljihun wondonsa yana kallonta yace “me ta baki ki kawo min ?da sauri ta ciro flaks din ta miko masa jikinta na sake d’aukar rawa, ya cire dayan hannunsa dake cikin wondo ya amsa ya bude flaks din data mika masa yayinda ta tsaya a tsorace tana kallonsa tare da jiran rashin mutuncin da zai mata .”


yana gama budewa ya tsaya shiru yana kallon abinda Ke ciki yayinda ta cigaba da kallonsa a matukar tsorace muryarsa a kasalance yace“meye wannan ? ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi masu matukar tsoratarwa” kayi hakuri sir ummana ce tace na kawo maka .”numfashi ya sauke tare da cewa “yakayi tasan ina matukar son fruit custard kallonsa tayi da sauri tana jin wani irin sanyi a zuciyarta wanda bai tsaya iya zuciyarta ba har ganganr jikinta take jinsa wani sanyayen dadi ne ya mamayeta” kana matukar son fruit custard ?”ya gyada mata kai kawai tare da yin shiru ya rufe flaks din ya juya har yayi taku d’aya sai kuma ya tsaya rike da flaks din “kice wa mum na gode sosai” kenan zaka sha? ya juyo tare da lumshe mata tsumammun idanunshi bana shan abun hannun kowa bayan mahaifiyata da some amman zan sha saboda mahaifiyarki ce tace ki kawo min ,”kuma kace nace mata ka gode?” meye damuwarki dan nace na gode ?ya fad’a yana hura mata hanci tace” babu “!


maryama ta waiga waje taga babu mai zuwa dan Allah Allah take ya fita ya barta kar wani ya gansu bare sultana”
”maryama kina mamaki dan na kar’bi abun hannunki” ta gyada masa kai alamun eh “ina mamaki ne sir dan na ma fad’a mata bazaka kar’ba ba saboda behavior’s dinka sai gashi ka kar’ba babu mai saka abu babu mai hanaka babu wanda kake iya yiwa godiya sai gashi kayi wa ummata,kasan wani abun ?”yayi shiru kawai yana kallon bakinta da take magana dashi daga gida har office nasan duk dabi’a daya kake yi dan allah ka canza wannan dabiar taka kowa tsoronka yake ji “.sannan kuma na gode sosai da kace kowa ya goge hotu nanmu hakan ya rage min tarin radadi da nake ji duk da ya zubar min da kimata agurin abokan aikina ,sun zargeni Akan laifin da ban aikata ba kuma suna min kallon banza gabadaya bana cikin sukuni da kwanciyar hankali ina jin kamar na bar aikina domin bazan iya jurar irin kallon kaskanci da tozarcin da suke min ba ta qarasa maganar muryarta na rawa “ban san me zan cigaba da cewa ba amman naji dadi sosai dakasa suka goge ta fad’a tana d’ago idanunta dake cike da ruwan hawaye .”


Shiru sukai daga ita shi kafin ahankali ta d’ago idanunta nan take idanunsu ya tsarke cikin juna ,ido cikin ido suke kallon kwayar idanun juna suna cikin wannan yanayin sai ga sauran ma’akatan sun shigo da sauri maryama ta d’auke kwayar idanunta acikin nashi ta maida wani bangaren turus sukayi suna kallonsu daya bayan daya kallo daya yayi masu kowannen su ya kama gabansa madam some ta shigo itama kallo daya tayi masu ta d’auke idanunta ta wuce a natse ya soma tafiya rike da flaks din hannunsa cike da jin haushin abinda sukai mata yana zance zuci baku sani bane,akanta zan iya korar kowa acikinku, amman zan d’auki mataki akai dan babu wanda ya isa ya tozarta min rayuwata.”



Bayan wasu mintuna ya bude kofar office dinsa da qarfi ya fito yana waya ya isa a gaban madam some tare da cire wayar a kunnensa ya nuna mata hotunansu shi da maryama “ kinsa sun goge hotunan nan ko kuwa ?”yes sir sun goge ya qara taku daya ya isa inda take zaune yana cewa “zan yiwa kowaye ya tura maku hotunmu rashin mutunci domin ba maryama ake son tozarta wa ba ni ake son tozartawa ko ba haba,” haka ne sir wannan abu ba wai da gaske bane nan ya shiga kora mata dalilin da yasa hakan ta faru batare da yasan ma yana mata bayani ba yana dasa aya tace “I will explain everything to them sir “ bana bukatar some amman na rantse da girman allah bazan d’agawa kowaye kafa ba kuma zan yi komai akan duk wanda zai ciwa maryama mutunci acikin ma’aikatar nan ya qarasa fad’ar haka a tsawa ce kallonsa take cike da tsananin tsora da mamaki yana gama fadar ya wuceta ya shiga office dinsu maryama sakamakon hangosu da yayi suna tautaunawa a tsakaninsu sun ware maryama .”



shiru kowannensu yayi alokacin da suka gansa “why everybody quiet?a tsawace ya tambayesu yana had’e rai fiyye yadda yake yi “oh ashe kunyi shiru ne saboda kunsan cewar ni ne shugaba anan ba .”?ai bai kamata kunyi shiru ba ku cigaba da tautaunawa ko bakuna tautaunawar ne akan abinda ya faru tsakanina da maryama ba ? daya bayan daya ya kira sunansu tare da cewa ku cigaba da tautaunawar mana “speak up let me hear you “. “wato kun d’aukemu amatsayin mazinacita ba?shiru sukai gabad’aya sai yusura ce ta samu damar cewar “kayi hakuri sir ai bazamu ta’ba fad’ar abu makamancin haka ba,dan mun san bazaka ta’ba aika haka ba .”taya kuke tunanin bazan iya aikata haka abu makamancin haka da maryama ba ?ai ni mutun bane kamar kowa kuma zan iya “! a matukar tsorace suke kallonsa yayinda mryama ta kasa d’ago idanuta ta kallesa a tun sanda ya soma magana iska mai zafi ya fesar daga bakinsa ya cigaba da magana kusani babu wanda ake jin tsoronsa anan ,saboda daku da ma’aikatan nan abun ikona ne sannan yadda naga dama zanyi daku kuma ko barin aiki kukayi nan sai naga dama zan baku damar yin aiki da kowani ma’aikatan amman bazan nuna maku qarfin ikona ba ,abinda nake son kusani maryama ba mazinaciya bace, ba yar iska bace, hassalima ta fiku kamewa da natsuwa dasanin ya kamata.”


cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa maryama ta d’ago idanunta tana kallonsa tana sauke naunayen ajiyar zuciya zan iya korar kowa acikin kamfanin nan na zauna daita kad’ai ,sannan da zaa tara min duk matan duniya wad’an da zan sheida ita kadai zan cire wani sabon mamaki ya bayyana akan fuskarsu maryama maryama mutuniyar kirki ce and she have especial talent yayi maganar tare da matsowa kusa daita sosai, ban dauka zaku iya mata wannan tunanin ba domin kuwa nayi imani da itace wani acikinku ya samu kanshi cikin halin data tsinci kanta tabbas bazata so taga ya wulakanta ba ,kuma bazaa ta’ba hade kai daita dan a musgunawa wani ba .”
shiru sukai gabad’aya farko tunani ya kamata kuyi mai yasa maryama ta rungumeni mai ya faru daita ba wai ku dauki wannan damar ba dan kuyi mata wulakacin ko kuci mata matunci ko tozarci ba ,kallonsa kawai maryama take babu abinda yake faru haka kawai batare da dalili ba ,kuma nasan kusan haka dan ku ba yara bane ni mai yasa baku canza min ba ,ko dan ita ta kasance mace ne shiyasa kuke jin haushinta har kuje bleming dinta ?ai ni ma yakama kuyi bleming dina kamar yadda kuke bleming dinta . kallosa kawai maryama takeyi har bata son kifta idanunta.”




Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.



Page 44


maryama na kwance lamo duk abun duniya ya isheta ahankali ta soma jiyo sautin magana daga parlour’n umma ta yun kura ta mike tsaye daga kwance da take ta soma taku cike da natsuwa tana kusanto parlour’n tana sake jiyo abinda suke tautaunawa akai “na gode maku sosai da yadda kuka mutuntani ,kuka nuna min cewar ina da darajar da zan nemi alfarma a wajenku kuyi min,na gode sosai allah kuma ya shirya mana zuria ,”
babu komai dan wallahi kin wuce haka a wajenmu dan data shegiyar yarinyar nan ce ko uwarta da wallahi komai za’ayi sai kowa acikin dangi yaga wad’an hotun , bama iya nan kawai zai tsaya ba dan hatta jama’ar unguwar nan sai sun gani , duk wani mai ganinta da kima ya daina ganita dashi amman taci darajarki”.inji cewar aunty hasana “na gode sosai sai dai hasana kisani duk abinda kikawa maryama kasani kanki kika yiwa saboda idan sunan maryama ya lalace dole za’a zageki saboda jininki “a’a aunty karki had’ani da wannan mara kunyar yarinyar da bata san ciwon kanta ba .”a qalla sun d’auki mintuna sama da shabiyar suna tautaunawa.” maryama ta fito gbdy daga d’akinta adaidai lokacin da umma ta kar’bi duka hotunan hannunsu ta had’esu waje d’aya su kuma suka mike suka nufi kofar fita ,inda umma ta shiga kitchen ta d’auko ashana duk maryama tana tsaye tana kallonta ta fito ta nufi hanyar kofar baya da alamun kona hotunan zatayi .”bayan wasu mintunan ta dawo inda tayi turus sakamakon ganin maryama tsaye dan kwanaki uku kenan rabon data sanyata acikin kwayar idanunta bata ce mata komai ba ta sake shigewa kitchen ta soma qoqarin d’aura girki .”



Jin motsin umma yayi yawa a kitchen yasa maryama ta fahimci wani aiki take dan haka ta taka ahankali ta shiga a bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon bayan umma dake wanke tukunya ,numfashi ta sauke ahankali sannan ta soma taku ahankali har ta qaraso cikin kitchen din sosai ta tsaya a gafenta tana cewa “umma sannu da aiki “yauwa !kawai ta amsa mata atakaice kana ta cigaba da abinda take bayan ta gama ta zagaya ta gefenta ta d’aura tukuyar akan gas jikin maryama a sanyaye ta d’auki wuka ta soma yanka mata karas din data gani dan ko bata fad’a mata ba tasan mai zata girka alokacin.”



“ shiru dukkaninsu sukayi sai dai kowannensu zuciyarsa da abinda take tunani ,maryama ta d’an saci kallon umma inda ta fahimci ta d’an soma saukowa daga fushinta, jikinta da muryar ta amatuqar sanyayye ta motsa la’bbanta“umma!maryama ta kira sunanta. umma na jinta amman tayi shiru taki cewa komai duk da tana son amsa mata” umma nah !” ta sake kiran sunanta a tsanake wanan karon sai da tsigar jikin umma suka mike “kiyi hakuri ummah ki yafe min abinda nayi wallahi nayi nadama bazan sake kuskure aikata abinda nayi ba ,nayi miki wannan alqawarin bazan sake ba .”ta qarasa maganar tana danne kukanta tare da juyowa ta fuskanci umma dake tsaye a gabanta bata san sanda ta durkushe kasa bisa gwiwowinta tare da had’e hannuwanta waje d’aya tana kuka tana rokonta “ ki taimaikeni umma bazan iya jurar fushinki gareni ba ,ina jin kamar na kashe kaina bazan iya jurar fushinki ba kina fushi dani haka ma aunty zuciyata tana bani shawarar na kashe kaina kawai ma kowa ya huta da ganina a duniya.“da sauri umma ta fito daga kitchen din dan bata jin zata sauko cikin sauki haka.”a parlour maryama ta isketa kai tsaye ta isa inda alqurani yake ajiye akan abun tv tsand ta d’auka “umma na rantse miki da girman allah da da girman wannan alqurani mai tsarki.. ..”tun kafin ta kai ga fad’ar abinda zata fad’a umma tayi zumbur ta mike ta kwace alquranin a hannunta tana cewa “qul !na sake ganin kin d’auki qurni kinyi rantsuwa dashi .”
nan take maryama ta zube gaban umma tana wani irin kuka mai ta’ba zuciya tana rokon umma ta yafe mata “hakika maryama kinyi kuskure kuma tun tuni ni na yafe miki dan bazan iya cigaba da fushi dake ba, na dai barki ne kisan mahimanci laifinki “kiyi hakuri umma bazan sake ba aikin ma na ajiyesa bazan sake taka qafafuwa na acikin AGC ba “ta fad’a tana sheshekan kuka.


umma ta tsura mata ido kawai tana kallonta kafin ahankali tayi taku biyu ta qaraso gareta ta mikar daita tsaye ta rungumeta tsam ajikinta tana shafa bayanta .maryama kam banda kuka babu abinda take “kukan ya isa haka maryama dan ga jikinki har ya d’auki zafi ta fad’a tana numfasawa “hakika naji bakinciki yanayin danaganki ban san haka nake sonki da kishinki ba wallahi sai dana ga wad’an nan hotunan duk kwanakin nan bana iya runtsawa sai dai banji digo daya daga cikin so da qaunar da nake miki ta ragu ba,wallahi ni kad’ai nasan irin radadin da ciwon da naji a zuciyata ke macece bai dace ace kina biye masa kina zubar da mutuncinki da qimarki a gurinsa ba, idan kuma kuna son juna ne ai gara kuyi aure kamar zai fiyye maku irin wannan rayuwar .”
maryama tayi saurin zare jikinta ajikin umma tana girgiza mata kai “ni babu abinda zanyi dashi kamar yadda nasan shima babu abinda zai yi dani” kece kike ganin haka maryama” Allah umma babu abinda zanyi dashi babu abinda zakiyi dashi mai ya kaiki jikinsa ?wallahi umma tsautsayi ne amman na rantse miki da girman Allah babu abinda ya ta’ba shiga tsakanina dashi ,umma jawo hannunta ta zaunar daita bisa kujera cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da Jin tsoron abinda zata furta ta kalli cikin idanun maryama tare da yin kasa da murya tace “kina nufi wannan mutumin bai ta’ba sanki ‘ya mace ba ?”numfashi kawai maryama ta sauke da ajiyar zuciya sannan tace “umma zaki iya duba jikina idan kina so, nasan zaki iya fahimtar macen data ta’ba sanin d’a nmj da kuma wacce bata sani ba.” ajiyar zuciya umma ta sauke idan kuma baki yarda dani ba wallahi zan iya miki rantsuwa da alqurni .”abinda ya faru a ranar da har ta kai mu ga shiga wannan halin shine “nan ta fara zayyanowa umma komai tun daga farko har qarshe tana kuka.shiru umma tayi tana sauraronta tana mai gamsuwa da maganar maryama “ni dai fatana ayanzu umma ki yafemin kuma ki rokar min aunty da habib su yafemin bazan sake ba.” cike da kulawa umma ta riko hannunta cikin nata tana cewa kukan ya isa haka kije ki bata hakuri da kanki ganin nan zuwa yanzu .”


numfashi maryama ta sauke da qarfi cikin sanyi murya tace “na gode umma ahankali ta fita ta nufi bangaren mahaifiyarta tana kai wa bakin kofar ta tsaya cak ta kasa shiga tana tunanin abinda zata tarar daga masoyi ya, kuma abar qaunarta sai data sanyawa jikinta jarumta sannan ta shiga inda ta iske aunty zaune ta zuba tagumi daga ganin kasan tunani take wanda bata raba dayan biyu nata ne, ta qarasa ta durkusa gabanta ta dafa gwiwar qafafu wanta cikin tsananin sanyin murya tace “aunty kiyi hakuri ki yafe min bazan sake ba nayi nadamar abinda na aikata hakika baki cancanci haka daga gareni ba. sai lokacin aunty ta dawo daga duniyar tunanin data lula. ta tsura mata ido cikin zafin rai kwanaki uku kenan da faruwar abun amman ganinta yanzu sai take jin kamar yanzu abun ya faru “ki taimakeni aunty ki yafe min ki daina fushi dani bazan iya jurar fushinku ba “just shut up! ta fad’a tana janye qafafuwanta daga gareta batare da tace mata uffan ba “dan allah aunty wallahi bazan sake ba”maryama ki tashi ki fita ki bar nan bana son ganinki dan a yadda nake jin zuciyata zan iya aikata miki komai maryama tayi shiru tana duban mahaifiyarta fuskarta da bayananen mamaki “yau itace ta zama haka ga mahaifiya kuma abar sonta ?”mahaifiyar dake qaunarta fiyye da komai arayuwarta ,mahaifiyar data sadaukar da rayuwarta da farin cikinta dan kawai suzo duniya ita kuwa wace irin baqar rana ce yau agareta?” inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta soma furta wa cikin tsananin tashin hankali yayinda gbdy ilahirin jikinta ya d’auki rawa kanta ta soma juya mata “nace ki tashi ki fita anan !aunty ta sake furtawa a matukar tsawace tana haki da sauri maryama ta mike jikinta na rawa tayi hanyar waje da sauri tana daf da fita suka ci karo da umma ta riko hannunta suka juyo zuwa ciki dan taji tsawar da aunty ta buga mata tsaye suka iske aunty tana zariya tana haki dafe da goshinta



Umma ta saki hannun maryama ta dafa kafad’an aunty tana cewa” taho nan bilkisu ki zauna ta janyota zuwa kan kujera inda aunty ta zauna tana goge hawaye da gefen rigarta” “kiyi hakuri bilkisu ki daina kukan nan haka .shiru kawai aunty tayi tana cigaba da goge hawayenta “bilkisu ki kalleni aunty ta d’ago idanunta da kyar ta tsura mata cikin tsannain damuwa “ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru da diyarmu maryama ki bar damuwa haka mutuncinta yana nan har yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login