Showing 159001 words to 162000 words out of 182919 words

Chapter 54 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

359

kasan bazanki rakaka gurin gimbiya kuma sarauniyar mata ba ,muje ko !”ya fad’a yana mika masa hannu bayan sun gaisa mb yace” muje masaalaci muyi sallah tukun sai muje dan lokaci sallah ya kusa tsaki mr ata yaja yace “ai kai wallahi baka da mutunci sai ka gama batawa mutun rai ka dawo kana bashi hakuri “naji dai ai gara ni tunda zan iya bada hakuri muje amamn fa abokina kayi kyau sosai wannan sai kasa maryama ta furta kalmar só batere data sani ba .”

wani irin kallon iskan yayi masa “allah baqaramin kyau kayi ba wallahi duk inda muka bi dole sai an kalleka saboda uban wanka turaren da kayi ko mace sai haka nifa ina ganin kamar har da hoda ka shafa ko ?shi dai mr ata bai tanka masa ba har suka isa massalaci yana koda kyawun da adamcyn mami yayi wanda shi bai ce masa komai ba qarshe dai yayi shiru yana cigaba da sauraronsa .”


Mmn sudais
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


45


Daga masallaci basu tsaya koina ba sai akan titin unguwar su maryama, bayan sun samu guri sunyi parking suka fito ahankali inda m.b ya tsaya shiru yana karewa yanayin tsarin unguwar kallo ,”titin unguwar tasu babu laifi sai dai cike take da jama’a ‘yan cirani da ‘yan sikiraf “mr ata tsab ya fahimci inda hankalin m.b ya dosa dan haka tun kafin yace masa wani abu ya tsosa keyarsa yace “kaga malam ban son gulma da iskanci muje!”.wallahi wannan yarinyar bancin a mafarki ka fara ganinta da nace asiri ta maka, dan irin wannan unguwar sai dai aikin asiri ne kawai zai kawo mutun .”
a natse mr ata ya wucesa ya d’auki hanyar dogon lungun da zai shigar da mutun zuwa kofar gidansu maryama.ganin haka yasa m.b ya biyosa da d’an sauri suka jera suna tafiya acikin lungun mamakin m.b ya sake qaruwa dan duk yadda ata ya fad’a masa yanayin unguwarsu geto area ne bai d’auka haka yake ba dan har gara kan titi akan wannan lungun da suka shigo. m.b dai ya kasa hakuri yace “lallai wani abu sai aikin syya idan ba soyayya ba mai zai kawo mutun irin wanan ungu war ?”ko da yake wannan shine abinda yafi dacewa ga attajirai irinku masu jin kai soyayyarku ta qare akan yaran talakawa wanda ba kome bane.”madadin mr ata yaji zafin maganarsa sai ma yace“ashe dai kana da raunin imani kasani nasani babu wani abu da zai gagari Allah kawai zai fi kyau kace qaddarar aurena tana cikin wannan unguwar kuma ban isa na gujewa qaddarata ba ko tazo ta sameni a inda nake ko kuma ni na biyota inda take kamar dai yadda ya faru sai dai in sha Allahu da zarar na d’auke maryama daga unguwar nan daga ni har ita mun bar shigowa cikinsa”mr ata yana gama fad’ar haka ya ciro wayarsa ya soma neman layin maryama domin ya sanar mata isowarsa da kuma katse duk wata magan da zata fito daga bakin m.b sai dai akayi rashin sa’a layin nata a kashe yake .”




Har suka qaraso kofar gidan kiran bai shiga kira biyar yayi mata anace masa layin switch off yayi shiru yana tunani yayinda nan take moon dinsa ya sauya zuwa damuwa.”mb ya kallesa yace “ya’akayi ne mutumina naji kayi shiru ko akwai matsala ne?layinta ne wai akashe “okay sake kira may be matsalar network ne kasan yanayin network din yanzu bai fiyye kyau ba bare a irin wad’an nan unguwannin,sake kira idan bai shiga ba sai mu samu yaro mu tura cikin gidansu take yabi shawarar m.b ya sake kira layin cikin sa’a layin ya soma ringing sai dai bata d’aga ba sai da yayi kira biyu a karo na uku ne ta d’aga tare da yin shiru taki cewa komai illa numfashin data dinga sauke masa acikin kunnensa wanda ya haddasa masa shiga cikin wani yanayi mai tsarkakkiya da wuyar musaltuwa wani iri naunayen ajiyar zuciya mr ata ya sauke da qarfi shima .”
kamar yadda maryama tayi shiru haka shima yayi shiru har kusan mintuna sha takwas babu wanda ya cewa d’anuwansa uffan.” maryama ta sauke wayar daga kunnenta ta duba ko ya sauka akan layin ne sai dai gani tayi har lokacin yana kan layi magana ne dai bazai ba ta kalli inda umma ke zaune a kusa daita wacce ta kasa kunne domin sauraron abinda zata ce .”



da kyar maryama ta sanyawa jikinta jarumta tace “ina wuni sir….” “fito gani a kofar gidanku!” ya fad’a atakaice “what ?!ta furta a d’an firgice tana sake kallon umma kafin ahankali ta daidaita natsuwarta “ko ba zaki fito bane ? kwantar da murya tayi sosai tace “sannu da zuwa gani nan fitowa “.ta fad’a tana sauke numfashi tare da zubawa umma ido ,gabadaya duk sai yanayinta ya canza daga d’an farinciki data fara samu zuwa bakinciki ,dan a yanzu bata qaunar duk wani abinda zai zame mata damuwa arayuwar ta .“kallon tsanake umma tayi mata kafin ahankali ta motsa bakinta tace “bako kikayi ne ?cike da damuwa ta gyd’a mata Kai tare da cewa “mr ata ne yazo” mr ata sai yanzu zai nemeki ?” umma ta furta hakan
dan batayi tsamanin zai d’auki lokaci har haka batare daya kawo kansa ba dan har ta fara cire ranta akan son maryama yake .maryama tayi mamakin jin furucin umma “to yanzu mai km ya kawosa ?nima bansani ba amman may be ayyukan daya bani ne yazo kar’ba ganin kwana biyu banje aiki ba haka nan ta tsinci kanta da shara rawa umma karya “inda umma tace “ai shikenan sai kije ki samesa kiji abinda ya kawosa bata mike tsaye alokacin ba sai data d’auki kusan minti biyar zaune har sai da umma tace” ki tashi ki shirya kije mana kin bar mutun tsaye sannan ta mike da kyar ta shiga d,akinta .”



A can kofar gidan kuwa tun daga nesa baba gali ya hango tsayuwar mutane biyu a kofar gidansu cikin shiga ta alfarma tun bai qaraso ba yaji gabansa yana wani irin bugun tara tara ahankali ahankali ya dinga taku har ya kusan qarasowa inda suke tsaye , nan idanunshi ya tabbatar masa da ko waye tsaye, a fili ya sauke ajiyar zuciya had’e da kare masu kallon tsab cike da mamakin ganinsa yace “duk lalata da kayi a wajen aiki bai maka ba har sai ka biyota gida ai kuwa bazata sa’bu ba bindiga acikin ruwa nan take baba gali ya soma tunanin irin qalar wulaqancin da masu sai dai yana qarasowa gabansu yanayin yadda yaga fuskar gogan naku babu wasa bare alamun d’aukar nonsense yasa baba gali ya had’e abinda ke cikin ransa, ya ‘bige da yar gyaran murya kana yace “ashe kaina tsaye ?”m.b ya kalli baba gali sannan ya kalli mr ata sannan ya gaishesa .”baba gali ya amsa yana washe masa baki yace “sannuku da zuwa .”
”yauwa !”inji cewar mb shi kam mr ata sai da ya d’auki lokaci kafin yace masa “ina yini!” kuma daga nan bai qara ba sai ma sake had’e fuskarsa da yayi yana kallon wani banngare dabam “ku shigo daga ciki mana “ba wajenka muka zo ba ata ya fad’a yana fesar da iska mai zaki daga bakinsa jiki baba gali a sanyaye ya nufi cikin gida yana wai wayensu sauran ka d’an ya tuntsura da hannu mb ya nuna baba yana cewa ”halan waye wannan mutumin?”ban san shi ba “mr ata ya fad’a atakaice shiru m.b yayi kafin ahankali ya cigaba da magana “baka san shi ba amman kuma shi da alamun yasanka “kai ma kasan sanina ba abu ne mai wahala ba acikin kasar nan mb yaja bakinsa yayi shiru .”



Maryama ta d’aura after dress akan kayan jikinta tayi rolling mayafin after dress din ta dauki turarenta mai sanyin qamshi ta feshe ilahirin jikinta sosai tayi kyau ta fito zuwa parlour qamshin turarenta yasa umma ta waigo inda take tsaye tana qoqarin saka takalmi umma tai shiru kawai tana kallonta ,sai kace mai zuwa zance ko wani biki amman dai tayi kyau sosai Allah yasa mr ata ya furta mana yana sonta dan hakan nan take ji mutumin son maryamarta yake ,maryama ta qaraso ahankali ta tsaya kusa da umma tana cewa “sai na dawo umma” adawo lafiya amman kinyi kyau sosai maryama ta d’an murmusa tana cewa” na gode umma nah sannan tasa kai ta fice .”
ahankali take taku kamar bata son taka qasa yayinda zuciyarta ke wani irin tsinkewa tana tunanin abinda ya kawosa gidansu, har ta fito zuwa kofar gidansu ta tsaya inda idanunta suka sauka akan mr ata nata da kuma wani da bata san ko waye ba .”wani abu taji yana shigarta wanda take yawon jinsa ailahirin jikinta a duk sanda zata d’aura kwayar idanunta akanshi sai dai ta rasa gane komenene wannan abun dake shiga jikinta yana yawo acikin jini da tsokar.”
sosai taga yayi mata kyau acikin shigar da yayi looking extra ordinary mr ata ba dai kyau ba his nose is so pointed har baki ga gashin fuskarshi baki sitik kamar an ratsa golden brown aciki sai shining yake yi kamar ya zuba oil gashin yana cikin abinda yake mugun qara masa kyau ,”masha Allah ta furta ahankali.”



Numfashi da ajiyar zuciya ta sauke atare sannan a natse ta cigaba d’aga qafafunta.” tun daga nesa mr ata ya d’auki kallonta har ta qaraso ta tsaya a gabansu tana masu sannu da zuwa “sannuku da zuwa”! mb ne kawai ya amsa mata cike da kulawa shi kuwa mr ata yayi gum da bakinsa ya cigaba da kallonta wanda yasa tayi kasa da kanta ta kamo yatsun hannunta ta tsarke cikin juna tana wasa dasu.gabad’aya sai ta jita a takure sakamakon tsumammun danunshi dake yawo a sansar jikinta “bayan kamar minti biyar ta d’ago nan take kwayar idanusu ya tsarke cikin juna ,wani irin yanayi mai bugar da zuciya ya farmakesu atare ,da sauri maryama ta janye idanunta daga cikin nashi tana gaishesa “ina yini !?”har sai da dimple dinta ya lotsa kmr an saka nail da hammer anyi nailing cheeks dinsu norma normal ko bata tayi magana ba ana ganin alamun lotsawarsu still mr ata bai amsa mata ba ya cigaba da kallonta yana hukuntata da kwayar idanunshi masu firgitarwa tare da qara d’aure fuska tmkr wani zaki .”
mb yayi kusa dashi sosai tare da yin kasa da muryarshi yace “kayi mata magana mana ko za’a bamu izinin shiga ciki “still shiru yayi yaki cewa komai har sai da maryama ta sake d’ago idanunta, sosai ta tsorata da ganin yanayin yadda ya d’aure fuska yake kallonta,muryata na rawa tace” mu shiga daga ciki”still shiru yayi yaki motsawa har sai da ta sake yin magana “kayi hakuri ka shigo baza kuji dadin tsayuwa anan ba.” tana gama fad’ar haka ta juya .



Wani irin naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da qarfi “kaga malam ka saki fuska mu da muka zo zance da ban hakuri zaka wani had’e wannan fuska tare da takure yarinyar mutane wannan fuskar zakin taka ai sai ka firgitata .” iska ya fesar mai zafi daga bakinsa sannan ya soma taku ya biyo bayanta shima mb ya biyosu sosai mr ata yake kare mata kallo yana furta masha Allah yarinyar ba dai diri ba she has the best figure kyawunta sirri ne ya godewa Allah da zai mallaketa ,kusan atare suka shiga gidan a haraban gidan suka tsaya mr ata yaki yin magana haka zalika maryama da mb babu wanda yace komai gabdaya marayam ta rasa meke mata dadi “wanna shirun nasa yasa zuciyarta Ke tsananin bugawa da qarfi ”
Cike da tsinkewar zuciya tace “please sir kayi hakuri nasan nayi maka ba daidai ba na ajiye aiki da nayi batare da sanar maka ba, dan rashin maganarka a yanzu ya fara d’aga min hankli matuka fiyye da tashin hankali dana shiga.”ta fad’a tare da yin shiru stil qirjinta na dokawa .”



baba gali dake tsaye aharaban bangarensa ya janyo hannun aunty salma suka la’be duk zufa ta rufesa “salma matso kiga ikon Allah “aiko karaf idanunta ya sauka akan mryma da ata tsaye “me zan gani kamar wancan mutumin da ya rungumeta a hoto ko ?”shine kuma shine dai wannan mutmin daya zo neman aurenta a boye na hanashi“anya salma malam bai fara girba miki karya ba?“Anya ma kuwa kinsa a farraka tsakaninsu domin muddin mukayi sakacin da maryama ta auresa mun tafka babban kuskuren da bamu ta’ba yi ba a rayuwarmu “ka yarda dani ba zan ta’ba barin muyi wannan kuskuren ba,ina ganin an samu kuskuren aiki ne amman tabbas malamina ya tabbatar min bazai aureta ba sai dai su qare rayuwarsu a neman juna.”




Maryama tayi kasa da kanta sosai tace “kayi hakuri dan Allah nasan nayi maka laifi gashi na sakaka wahalar zuwa unguwarmu ”ta qarasa maganar muryarta na rawa “mryama you should know me by now mai yasa rashin magana ta zata d’aga miki hankali ?shiru tayi tana kallonsa up & down.”
shi kuwa gogan hannu ya kai yana shafa qirjinsa yana jin wani irin sanyin dadi a ilahirin jikinsa “well yanzu ma ba saboda ke nazo ba nazo ne naga ummanki ki shiga ki sanar daita zuwana .”shiru tayi tana kallonsa cike da tsannain mamakinsa “ki shiga mana kin wani tsareni da wad’an nan idanuwan naki kmr na mage “.jiki a sanyaye ta juya tana taku ahankali tamkar kazar da kwai ya fashe acikinta .”
iskar bakinsa ya furzar yana bin every step of her “Adamcy kana mugun son yarinyar nan over wallahi mb so ba kad’an ba yanzu haka ganin da nayi mata wani irin yanayi mai tsarkakkiya da wuyar misaltuwa ke shigana da ana bud’e sansar jikin mutu nasan ana bud’e nawa tsananin soyayyar maryama da qaunarta kawai zaa gani yana yawo aciki ji nake na zarta duk mazan duniya shan wahalar soyayya amaman na godewa allah da zai mallakamin ita.”
“ karka cika baki ka fara sheida mata matsayinka tukun kafin wani yazo yayi maka shigar sauri dan irin wad’an nan matan Allah ba’a sakaci dasu itama dan tana cikin lugun ne da waje take wallahi da yanzu matar wani ce.”wani murmushin yake mr ata yayi yana shafa qirjinsa cikin kankanin lokaci ya hango tahowarta tana gama qarasowa tace “muje!” tana gaba suna biye daita har bangaren umma .”



basu iske umma parlour’n ba maryama ta kallesu tace “ga guri ku zauna yanzu zata fito.” mb ne ya soma zama akan kujera mai zaman mutun daya yayinda ata sai daya kalli maryama sannan ya zauna a natse yana gyara wuyan rigarsa bayan ya zauna ya d’an kalleta a tsanake yaga duk tayi wani iri kamar a firgice take ya d’an motsa lip’s dinsa “ya naga duk kin birkice?”ta girgiza masa kai”to ki zauna!”ya nuna mata kusa dashi tayi saurin girgiza masa kanta tana sake damke yatsun hannunta .”suna nan zaune har sanda idanun mr ata ya sauka akan hoton sadam dake manne a bangon parlour’n sosai ya tsurawa hoton ido yana kallonsa kafin ahankali yace “wannna shine sadam ?da sauri ta gyad’a masa kai tana cewa “shine sadam dina sir.” wani mugun kallo yayi mata yana sauke numafshi tare da jinjina kai yana jan tsaki adaidai lokacin da umma ta fito tana masu sannu da zuwa.”
Cike da girmamawa suka rusunar da kansu suka gaisheta ta amsa masu da kulawa tana murmushi ta kalli maryama dake tsaye “ya zaki bar bakinki haka batare da kin kawo masu komai ba?” akwia sobo da nayi d’azu da safe sannan akwia cinci a fridge maza je ki kawo masu “okay !” har ta juya taji mb yace “no a koshe muke wallahi mun gode sosai ya fad’a yana murmushi amman duk da haka sai data maryama taje ta kawo a gaban mb ta ajiye ta samu waje ta tsaya tana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba .”mb yayi gyaran murya sannan ya fara magana a tsanake cike da kamala “amm daman abinda ya kawo mu akan abinda ya faru ne atsakanin maryama da adam “.


Umma ta jinjina kai sannan tace “ai nayi mamakin ma da sai yanzu biyo sawunta “mr ata najin haka yayi kasa da kanshi “kuyi hakuri da abinda ya faru
“Ala hakika gaskiya gabadayanmu bamuji dadin faruwar wannan alamarin ba kuskure aka samu daga gyara matsala abun ya dawo matsala domin shi yayi qoqrin yaga ya rabata da damuwar dake damunta ne ba wai da wata manufa hakan ta faru ba “.
“ba wai dan adamcy yana nawa ba wallahil azim shi din mutu min kirki ne .”umma ta kalli maryama tace “maryama maza kije ki kira aunty ayi komai a gabanta ahkli maryama ta juya ta fita yayinda mb ya cigaba da zayyanowa umma komai kamar yadda maryama ta fad’a mata yana rufe bakinsa aunty da maryama suka shigo bakin aunty d’auke da sallama cikin shiga ta kamala “yauwa ga mahaifiyarta nan” a sukwane mr ata ya juyo ya kalleta adaidai lokacin da take qoqarin zama kusa da umma, yayi shiru tare da tsura mata ido yana kallonta ta banga ren fuska ba tayi kama da maryamarsa ba dai dai ta yanayin jiki kasancewarta ba wata mai kiba bace duk da cikin hijab take amman yanayin ta ya nuna masa bata da kiba, yayi kasa da kanshi sosai inda idanunsa ya sauka akan yatsun qafafuwanta abun mamaki da d’aure kai irin yatsun sweet heart dinsa sak gareta ya d’ago kanshi kad’an zuwa yatsun hannunta nan ma irin yatsun maminsa ne gareta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login