Showing 180001 words to 182919 words out of 182919 words

Chapter 61 - Mar'adams Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

23 Dec 2024

353

har da mb ba dan meye had'in soja da kasuwanci ."


"kasani ammar! "ata ya fad'a yana kokawa acikin ranshi "kasan dalili kiranku ammar amman kafin nan nasa some ta kira yarinyar nan jiya amman gabad'aya kalamanta sun nuna bazatayi aiki dani ba, amman ni ba wannan bane damwta ." meye damuwarka ata ?"mb ya tambayesa cike da kulawa "sai da ata ya sauke wani naunayen ajiyar zuciya sannan ya motsa lip's dinsa "wai princess dinace tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwar ."yayi maganar cike da tsananin fushi yana zare hannuwansa daga cikin aljihunsa yayi taku d'aya biyu sannan ya tsaya cak atsakiyar office din tare da juya masu baya "gyaran murya salim yayi kana ya fara magana cike da sanyin murya "to meye aciki Adam kowani bawa ai da irin tasa kalar qaddarar "a ina take zaune ne ammar ?"inji cewar mb yayi tmbyr yana duban fuskar ammar ". "tana zaune ne a unguwar gwagulori "ina ne haka kuma ?""wata geto area ce acikin agege local government "cewar ammar "kunji abinda naji kuwa acikin zuciyata kamar ni Adam tariq Abdallah ace matar da nake haukar so ce tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwa wani irin rayuwa ma tayi ?"gidansu ne ko haya suke yi ? Ata yayi masa tamvayar yana dungule hannunsa ya kaiwa bango naushi .da mamaki gabad'ayansu suka mike tsaye cikin tsananin tashin hankali suka qaraso inda yake suka rikesa suna kiran sunansa "what's wrong with you Adam ?" gabad'aya suka had'a baki wajen fad'ar haka."ka natsu mana ."



Shiru yayi kawai yana fesar da numfashi da iska mai zafi daga bakinsa gbdy yanayinsa ya canza zuwa na tsananin damuwa, fixge hannunsa yayi yana shafa daidai qashin hannunsa daya bugu yana watsa ma ammar wani mugun kallo .da sauri ammar ya d'auke idonsa saboda mugun tsoro daya kamasa ya koma ya zauna ."mb ya kallesa cike da tausayawa domin dai ya fahimci tausayi ne mai tattare da tsananin son da yake mata yasa shi shiga damuwa janyosa yayi ya zaunar dashi yana cewa "ka kwantar da hankalinka Adam haka rayuwa take kai a tunaninka zata zamanto diyar wani kamar yadda ka kasance to shi Allah ba haka yake son ganinta ba sannan ba hk tsarinsa yake ba ,ganin damarsa ne ya hada masoya masu wadata waje d'aya haka ganin damarsa ne ya hada talaka da mai arziki ." nasan kasan dukkanin rayuwa rubutaccen lamari ne daga rabbi yadda yaso haka zai yi ,saboda haka kasan duk wannan mai sauki ne a wajen Allah fatan mu yarinyar ta amince da soyayyarka tun da ka rigada ka gano Inda take .”


shiru ata yayi ya fad'a kogin tunani sosai hankalinsa ya bar duniyar da yake ya lula dashi can duniyar maryama inda zuciyarsa ta shiga hasko masa ita tare da wani tana rayuwar aure daahi . wani dogon tsaki yaja yana sake taune gefen bakinsa da qarfi saboda zafin kishin da yake ji hakika idan yace yaji dadin kasancewarta a bazawara yayi wa kanshi karya yaso ace shine mutun na farko da zai fara muamula ta aure daita bawani katon bazan can ba "Adam ka daina zurfafa tunani da yawa akanta tunda already kasan ta ta'ba aure ,tunda ta ta'ba aure kasan dole wani abu zai shiga tsakaninta da wanda ta aura ita kad'anta kake so kuma ko a wani hali take zaka kasance daita ." "jin an dafa kafad'ansa yasanyashi sauke kwayar idanunshi akansu "ba shiga damuwa ko dogon tunanin zaka tsaya ba abinda ya kamata kayi yanzu ka gaugauta aurenta domin ka inganta rayuwata kayi ma iyayenta duk abinda kasan ya dace ."inji cewar mb "Allah kad'ai yasan irin rayuwar datayi acikin wannan banzar unguwar mb ku duba map kuga yanayin tsarin unguwar datai rayuwa aciki inna ilaihi "ya sake furtawa yana yarfe hannu alamun abun na masa ciwo ".kai yanzu meye damuwarka da unguwarsu ? unguwarsu kake so ko ita ?"salim ya tambayesa wani kallo yayi masa yana fesar da huci yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri." rabu dashi salim dan ma bai shiga lungun unguwarsu bane yasa yake fad'ar haka ."wani sabon zufa ne ya karyowa ata yayinda salim ya barke da wata irin dariya yana cewa "ai daidai kenan kamuwa da soyayyar yar talakawa zai sa wasu abubuwa su..."wani mugun kallo ata ya watsa masa wanda yasa salim yayi shiru yana kunshe sauran dariyarsa "ba hararar mutane ya kamata kayi ba kayi maza kayi abinda ya dace ku fahimci juna da yarinya ka aureta kafin wani yazo yayi maka shigar sauri "wannan duk ba matsala bane zan yi duk yadda zanyi ta dawo karkashin ikona . "fatan nasara abokina sun dan jima suna tautau nawa kafin daga baya kowannensu yayi masa sallama ya wuce suna fita yasa a kira masa baba gali "



*******

Cikin sauri sauri maryama ta fito daga bangarensu tana wa Aunty sallama kai tsaye part din umma ta shiga domin tayi mata sallama ta saka mata albarka tana rungumeta ajikinta "fatan alkhairi diyata "na gode umman ,maryama tai murmushi ta qarasa gurin hjy granny " Kiyi min addua kakata "allah ya tsareki maryama allah yasa zaki fara wannan aikin a saa sosai sukai mata addua ta soma kokarin barin parlour'n suna tsaye suna kallon bayanta suna rakata da addaua ."tana daf da kaiwa bakin kofa sai ga sallamar baba gali da aunty hassana tana ganinsu tai saurin durkusawa har kasa ta gaishesu"baba ina kwana aunty hassana ina kwana ? bata gama rufe bakinta ba sai ga mahaifiyarta itama ta shigo adaidai lokacin da yake amsa mata da "lafiya! Atakaice yana qare mata kallonta tare da cewa ina zuwa haka ?zani aiki ne ta bashi amsa jiki a sanyaye."what !? ya furta da karfi ai kuwa gara dana daka sammako ai wannna aikin baza kiyishi ba saboda ke na shigo bangaren nan .a matukar tsorace maryama tabishi da kallo kafin daga baya kalmar "inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun ya dinga fitowa daga cikin bakinta tana maimaitawa nan take jikinta yayi sanyi." "ungu nan ki karanta, emvelop ya mika mata tasa hannu ta karba jikinta na cigaba da rawa a firgice ta dinga bin rubutun sako ne daga AGC compaing wani sabon tashin hankali ta sake shiga mai tsanani tana dafe goshinta ."


"ki karanta a fili so that kowa da kowa yaji babu yadda ta iya ta soma karanta sakon a fili jikinta na wani rawa gabadayansu shiru sukai suna sauraronta zufa ne ya karyo mata sakamakon anyi cancelling sabon aikin data samu sakamakon AGC compaing na bukatarta sai kuma kamfanin gidan burodi wanda yake mallakin umma shima zai tashi domin zaa hana duk wani kamfani dake sarrafa flour bashi kaya jikinta ya cigaba da rawa kafafunta suka kasa daukarta ta sauke takadar tana furta "umma ki rikeni "! da sauri duk suka yi kanta banda mutun biyu baba gali da Aunty hasana "kasancewarki a AGC compaing shi zai sa kasuwancinmu ya cigaba da tafiya akasin haka kuwa kema kinsani sai dai a rufe kanfani mu zauna haka ya qarasa mgnr yana karbar takarda da ya bata ya kalli umma ya kamata kiyi wa wannna yarinyar magana idan ba haka ba zamu rasa komai ."


"Ai wannna galaliyar zataso haka ni ban ta'ba ganin mai kashin tsiya ba irin maryama daga wannan bala'i sai wannnan Ke dai ina ganin babu kashin arziki ajinin jikinki ni wallahi da ma aikin kika rasa gabadaya muka tsira da kafaninmu da zai fi min dadi yar bantar uba mai kashin tsiya ta daga hannu zata kai mata duka.."dakata hasana karki fara cak ta tsaya ."wai bana ce miki karki kara sa bakinki acikin maganr maryama ba muddin dai ba alkhairi zaki fad'a ba cewar granny , duk wani abu da zaa samu kasuwancinmu mutuncin zamu duba wannna kamfanin da suka mata wulakanci ko bashi bane duk suka gyada mata kai "to bazatai aiki dashi ba gara ta sake fita neman wani aiki sanyayye ajiyar zuciya ta sauke ta rarafo ta rike kafafuwan granny tana zubar da hawaye aunty ma kuka take dan baba gali ne ya kirata banci haka da bazata zo taga bacin rai ba "na gode granny dan allah ki taimakeni bana qaunar wannnna kamfanin ."hajiya wai me kke fad'a ne haka da babu dadin ji kin kuwa san adadin amfanin da wannna kamfanin yake mana ?gabdaya idan aka rufeshi to zamu dawo bara ne a bakin titi tayi aiki da AGC compaing mu kuma mu cigaba da kasuwancinmu ".


"Gali kayi hakuri da hukunci hjy ai rayuwar kunci ko da wannna kafanin ko babu idan allah ya ga dama sai yajefa rayuwarka ciki ,amman maryama bata sake komawa wannna kamfanin daaka wulakantata ba ,"maryama ta tsurawa umma idanunta daga ganin yadda take magana kawai dauriya ce da sadaukar da farincikta saboda nata farinciki zamu iya cigaba da rayuwa haka amman wulakanci bazamu dauka ba maryama maza tashi ki koma daki bama zakije koina ba ,"karki damu kinji " baba gali ya bita da kallo."maza taso diyata ta d'agata da kyar tana goge mata hawaye "kama hanya ki koma daki kina zaune wani aiki zaizo ai ke mai saa ce in sha allahu zaki samu wani ."Ahankali ta dinga daga kafafunta ta nufi kofar dakin d umma sai dai ta tsaya jiki a matukar sanyaye ta kasa cigaba da tafiya tana tunanin abinda yake faruwa daita daki daki komai yake dawo mata qirjinta ya buga lokacin data tuna maganr grany da umma hawaye masu zafi suka zubo mata "ni yanzu me ya ka mata nayi hakika idan nayiwa umma haka ban kyuata mata ba na zama silar rabata da abinda ta dogara dashi da kuwa na tabbata mai kashin tsiya idan ma akwai abinda yafishi zaa iya kiranta dashi dan dole nasan abun amman bazai yuwu nayi silar rugujewar kamfanin umma ba ko babu komai umma ta wuce haka a wurina."can kuma maganrsu sectry dinsa ce ta shiga yawo acikin brain dinta ta sake runtse idanunta babu abinda bata tuna ba amman karshe taji bazata iyawa umma haka ba ko ranta tace tana so zata bata bare yin aiki da AGC compaing babu abinda ya kamata tayi daya wuce tai joing din AGC compaing.


Dawowa tayi ta durkusa gaban umma "kiyi hakuri umma ki amince min zanyi aiki da AGC " wani sanyayyar ajiyar zuciya aunty ta sauke tana hamdala acikin ranta "ko kefa maryama sai yau nasan kinsan meye hallici kuma tabbas ke yar halace,karki bari mu rasa kamfaninmu da mukai tsawon shekaru muna amfana dashi "to baba na amince ka fad'a masu zanyi aiki dasu "a'a maryama bafa zan yarda a dinga tozarta min Ke ba dan haka kiyi zamanki da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko da kamfani ko babu zamu rayu "dan allah umma wallahi zan jure koma menene ni dai kawai Kiyi min addua umma tayi shiru ta rarrafa ta koma gaban grany "dan allah kiyiwa umma magana ta amince min tunda su suka nemi ne nasan bazasu tozartani ba kai ni akan martabar gidanmu babu abinda bazanyi ba idan yau mr ata rayuwata yake bukata zan iya bashi akan mu rasa kamfaninmu tana gama fad'ar haka ta sake dawowa gaban umma tana kuka tana rokonta amman umma tayi shiru tare da had'e rai "dan allah aunty kisa baki umma ta amince da kyar granny da aunty sukasa umma ta amince tare da mata fatan alkhairi."



Ahankali ata yake tafiya cikin shiga ta black suit hannusa daya cikin wondonsa yayinda James Ke biye dashi abaya rike da bakar jaka james yayi saurin shan gabansa ya bude masa glass door alokacin marayama na tsaye a office tare da sectary some suna magana akan yadda tautaunawarsu ta kasance akan waya a wancan rabar tare da neman afuwarta yana shigowa sectary tayi saurin gaishesa tana cewa "ga maryama hussein nan sir ."ya tsya cak tare da dan waigowa ya kalleta wani sanyi dadi yaji ya ziyarci jijiya da gangar jikinsa a natse ya juyo gabadayansa ya tsura mata ido itama a natse ta dago fararen idanunta ta tsura masa babu wani alamun tsoronsa atattare daita sai dai take taji qirjinta yayi wani irin bugawa da matsanancin karfi kallon juna suke ido cikin ido tana tuna haduwarsu ta farko duk da lokacin idanunta a rufe suke cikin nikaf shima rayuwar da sukayi a mafarki ne ya shiga dawo masa daki daki ,wanka da yake mata lokacin tana yarinya, wasa daita har zuwa girmanta da komai ya gama bayyana ajikjta da yanayin da yake ta'ba komai na jikinta tare da amincewarta yadda take sarrafa shi duk wani abinda Ke faruwa a tsakninsa daita acikin mafarkinsa babu wanda bai zo masa ba alokacin ."


a natse komai ya cigaba dawo masa boyayyayen ajiyar zuciya ya sauke sam ya manta james da sectary da suke tsaye sun kasa dauke idanu daga kallon juna ko kifta idanu basayi yaji kamar ya janyota jikinsa ya rungumeta yaji dumin jikinta na zahiri amman isa da jin kai bazai barsa ya aikata hakan ba ita kallon mamaki take masa mai ma yasa ya nace lallai sai tayi aiki à karkashinsa byn shine da kansa yasa aka koreta ? "shi kuwa kallon so yake mata yarinyar daya dade yana mutuwar so yarinyar daya dade yana marmarin haduwa daita ,yarinyar da yake muradin ta zamo mallakinsa itace tsaye agabansa a zahiri yana kallonta ba a mafarki ba ."
Bai ce dasu komai ba yana nufi glass door na biyu wanda Ke tsakninsa da sectary dinsa .yana shiga office dinsa ya kasa zama ya daura duka hannayensa akan kujera yana jiran shigowarsu da sauri sectry tayi gaba maryama tabiyota abaya cike da sanyi jiki some tace "kiyi knowking kafin ki shiga batai mata mutsu ba dan gabadaya ta sadaukar da rayuwarta gara kawai tai hakuri tayi aiki karta zauna haka babu aiki sannan kuma babu aure dan bata ga mai qararren kwanan da zai aureta ba bugu da gari kamfanin su."


a hankali tai knowking tana cewa "ko zan iya shigowa ?"Yes ! ya fad'a idanunshi na kan kofar shigowa tun daga kasa ya dauki kallon halittar dayafi qauna akan komai "mamanki ta iya haihuwa maryama ya fad'a acikin ransa tsayawa tayi ta rungume hannuwanta abaya tana hura masa hanci dan kallon da yake mata ya fara damunta sauke hannuwansa yayi ya zuba cikin aljihunsa yana cigaba da tsareta da tsumammun idanubshi masu bugar da zuciya da gangar jiki .Ita kuwa hade rai tayi sosai dan ranta ya soma baci tare da aiyanata wani sabon salon wulakanci zai mata shi kuwa fuskarsa wani annurin murmushi ne kwance amman idan ba mugun kallon kayi masa ba bazaka fahimta ba ya hade rai sosai yana cewa "me kikyi anan ? tayi matukar mamakin jin tambayarsa sai data maimaita kalmar sannan tace "mr ATA ne ya bukacini"ta fad'a har lokacin fuskata a hade ."


Sai data hura masa hancinta sannan ta cigaba da magana "sunana maryama hussein bagoro wannan sabuwar ma'aikaciyar da kuka d'auaka na rana daya sannna kukayi out daita, yanzu kuma kuka sake dawo daita ku kace tazo tayi aiki daku bayan kunsa anyi cancelling aikin data samu tare da barazanar zaa dakatar da kamfaninmu ."ta qarasa maganr tana sake hura masa hanci kamar yadda take masa a mafarkinsa."gabadaya ya mamayeta da tsumammun idanushi yana kallon kyakkyawan lip's dinta da siririn dogon hancinta komai na jikinta daidai ya dan lumshe mata idanunshi saboda dadin muryarta kamr ya fashe da dariya dan ya fahimci ya mugun bata haushi korar da yayi mata amman da yake shin din asalin miskili ne wuceta yayi da sauri ya zauan Kan kujera yasa hannunsa daya yana shafa sajen fuskarsa, can ya dauki wani file yana dubawa batare daya ce mata komai ba har tsawon mintuna shabiyar sannan ya ce "zaki iya tafiya yanzu nayi busy ."ta sake Shaka matuka mutumin nan fa mugun dan rainin hankali ne amman wallahi babu inda zata sai ta amayar da duk abinda Ke ranta ta sake gyara tsayuwa "nasan saboda kwarewata yasa kuka sake nemana domin dai bazaku ta'ba samu wacce zata baku abinda kuke buqa....."shhii karki wani cika wa mutane baki anan dan har yanzu baki da wannan matakin kwarewar , idan kika ga na wasu zaki sha mamaki da kanki zaki kira kanki da miss zero ".


"oh !
"gaskiya ne kam shiysa naga kun bukaci na dawo nayi aiki anan ? ya rufe file din hannusa da sauri yana kallon qaramin bakinta da magan Ke fitowa ta ciki ,kwata kwata babu wani alamar tsoro ko fargaba irin wanda yake hangowa a fuskar mutane dake aiki akarkashinsa idan suna tare dashi ."ni wallahi da an sani an barni alico insurance dina nayi aikina dan ma yafi kwanta min arai ."tayi mgnr tana rausayar masa da kwayar idanunta ."tsaki yaja yana motsa lip's dinsa "kisani duk inda zakije da sunan Kiyi aiki bazai ta'ba kai nan ba saboda aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ..."kayi kuskuren fad'ar hk sir ." ya ware tsumammun idanunshi sosai yana dubanta da mamaki kwamce a fuskarsa "eh haka na fad'a kayi kuskure sir kawai da dai da kun barni acan kawai batare da kun nuna karfin iko ba bare kace me ?mema kace ? "aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ."?"to a wurin wasu kenan yake abun alfahari amman ni dai abinda nayi imani dashi ko wani kamfanin na samu aiki zanji dadinsa sannna zanyi alfahari dashi kuma zanyi masu aiki mai kyau ." kun tursasa mutun yazo yayi aiki daku yanzu kuma kazo kace kayi busy dawa kenan kayi busy kai kai waye ma kai tukun ?ta fad'a a fusace .."


Mmn sudais

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login