Showing 30001 words to 33000 words out of 165545 words

Chapter 11 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

361

niko nayi biyayya na haƙura har a ɗaura a kawomin ke babie�?.
“Oh ni kana bani kunya, gara dai kayi haƙuri harnazo, dan saboda na faranta makane ma nai duk abinda ya dace kar wancan shashashan ya sameni, dan kaɗan daga aikinsa ya kwata cikin ƙarfi, niko kai kaɗai nake burin cikama alƙawarin kawo maka budurcina har gida�?.
“Nagode ta wajena, shiyyasa nake ƙara jin sonki na ƙaruwa a raina a kowacce daƙiƙa, dolene nazo na samu su baba ayi komai da wuri, insha ALLAHU nanda karshen wata kina nan kwance a ƙirjina�?.
Yanda yay maganar da wani irin salone yasaka tsigar jikin Samina tashi, ta sauke nannauyan numfashi daya sake haukatar da Ma'aruff daga can, hakan yasashi kuma manne karuwarsa dake barci a jikinsa, dan saida ya gama holewarsa ne ma ya kira Samina ɗin.
“Sai da Safe�?
Samina ta faɗa a sanyaye saboda kasalar da ya sakar mata da kalamansa.
Shima da “Uhmm�? kawai ya iya amsa mata ya yanke wayar yana sake maida karuwarsa a network.

Haka Samina tai barci da ɗunbin begen abokin hakittarta, dolene ma tai yadda zatai ai aurensu da Ma'aruff a nan kusa, koba komai ta samu nauyin shekaru dake gallabarta ya fita. A shekarun da suka shuɗe Ahmad kawai take iya suffantawa da wannan yanayin, amma zuwa yanzu sam ba haka bane.
Wani gefe na zuciyarta yace yanama can yana hutawa da kanwarki amaryarsa kuma Rumana.
Baki ta taɓe tana jan tsaki, sai kuma ɗayan gefen zuciyarta ke shaida mata sam Ahmad bazaiyi hakanba, dan tafi kowa sanin halinsa idan ka ɗebe iyayensa, dan ko ƴan uwansa tafisu sanin wanene Ahmad akan abinda yake so, tasan kafin Rumana ta samu gane kan Ahmad za'a yara, dan soyayyarta ta riga ta masa ƙullin yaɗon wake a gona, kafin zuciyarsa ta fara kallon Rumana matsayin mace sai anyi babban dagama...............✍�?








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*a: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(11)*



............Kiran sallar farko Ahmad ya farka, zazzaɓin ya sauka masa, sai dai akwai ciwon kai kaɗan-kaɗan, sai nauyin jiki da yakeji.
Ƙamshin sabon fenti dana katako ne ya tuna masa da inda yake, ya janye bargon da yake a ciki a hankali yana yunƙurawa ya tashi zaune, babu haske a ɗakin, dan Rumana ta saba idan zasu kwanta sai Ammi tace su kashe fitila, shiyyasa jiya da zata kwanta bayan ta gama shan kukanta sai ta kashe ta ajiye kusa da ita, a tunaninta ai zata riga Ahmad tashi da asuba.
Ahmad ya ɗan laluba ko zaiji wayarsa a jikinsa, sai dai babu, ya tura hannunsa ƙasan filon da ya tashi nanma babu.
Iska ya huro ƙaɗan a bakinsa yana janye bargon baki ɗaya, da lalube ƙafarsa takai ga bakin gadon, ya zurasu gaba ɗaya yana ambaton ALLAH a kan laɓɓansa.
Da sauri yay ƙoƙarin janyewa saboda jin ya ɗora akan mutum, sai dai nan ɗinma sake ɗorasu yay akan jikin nata.
Zafin da Rumana taji a ƙirjinta ne ya sakata farkawa tana faɗin “wayyo ALLAH Kadija zaki kasheni, bakicewa na haska miki fitila, ji yanda kike takani a ƙirji..�?
Yanda tai maganar cikin yanayin barci da sanyin murya irin ta wanda yaji zafi sai da tsigar jikin Ahmad ta tashi, bai kawo a ransa tana wajen kwance ba, duk da ma dai zai iya cewa ya manta da ita a ɗikin.
Yana ƙoƙarin janye ƙafafun nasa Rumana ta kunna fitila ɗakin ya gauraye da haske.
Ba ƙaramin faɗuwa gabanta yayi ba ganin Ahmad zaune, sam ta manta inda takema ita, tai saurin jan gyalenta ta rufe jikinta saboda da daddare takura mata rigarta tayi shine ta zuge zif ɗin ya koma ƙasa sosai.
Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa, ya sake ziro ƙafafunsa ƙasan batare da yace mata komaiba.
Itama dai ko motsi bata sakeba harya ɗauki buta ɗaya cikin guda biyu da aka zubama ruwa aka ajiye farkon ƙofar ɗakin.
Hannu yasa ya zare sakatar ɗakin da ta saka ya fice, yanda iskar asuba ke kaɗawa a hankali ce ta sakashi buɗe hanci ya zuƙa sosai sannan ya fesota ta baki yana lumshe idanu.

Rumana dai kasa motsawa tai, sai kalmomin data faɗane ke mata kaikawo a rai, takai hannu saman ƙirjinta daya taka kunya na sake kamata, dukda ba nauyi ya sakiba taji zafi, kuma tana ɗanji har yanzu kaɗan, maida zif ɗinta tayi ta miƙe jiki duk babu ƙwari, ta ɗauke filon data kwanta tare da naɗe tabarmar.
Yanda fitilar tasu taɗan hasko waje tana hangenshi yana alwala a ƙofar ɗakin, da yake gidan bawani girmane da shiba, babu wani isashshen tsakar gida sam....
Ya katse mata tunani yayinda yake ɗaga labulen ya ajiye butar, kamar zai tafi sai kuma ya dawo da baya ya shigo ɗakin.
Ta gabanta yabi zuwa gaban gadon, ya ɗaga filo yana sake duba wayarsa, ganindai babu ita saiya maida kallonsa ga Rumana dake tsaye jikin Wadrobe kanta a sunkuye tana kallonsa gefen ido.
“Sufyan bai bada wata bane?�?.
Da farko bata fahimci tambayar tasa ba, dan haka taɗan ɗago ido ta kalleshi, ganin ya tsareta da idanu tai saurin janye nata, cikin in ina tace, “A'a, ƙila ya manta ne�?.
Baice komaiba yazo ya sake raɓata ya fice.
Tana jiyoshi ya buɗe gida ya fita, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya itama ta ɗauki fitila ta fita duk da tana ɗanjin tsoro.
Tana cikin alwala mijin ɗayar matar gidan ya fito, ganinsa da ga shi sai gajeren wando yasa Rumana saurin duƙawa tana wanke ƙafa, bata ce masa komaiba shima baice mata ba ya shige bayi, itama tai saurin faɗawa ɗaki.

★★★★�?

Ana idar da salla Ahmad ya shigo, kasancewar massalacin a ƙofar gidan yake, Rumana na zaune saman abin salla tana azkar.
Yanda yay sallama ciki-ciki haka ita ta amsa masa a hankaki, baice mata komaiba yazo ya sake hayewa gadon ya kwanta.
Rumana ta ƙarasa azkar ɗinta sannan tace, “Ina kwana�?.
Kamar bazai amsa mataba sai kuma taji ya amsa da “Lafiya�?.
Daurewa tai ta sake cewa “Ya jikin?�?.
Nanma dai shirun yayi, harma sai da ta fidda tsammanin zai amsa sai kuma yace, “Alhmdullh�?.
Daga haka kowa yay shiru, shi dai barcine ya sake kwasheshi, saboda maganin bai gama sakinshi ba.
Itako duniyar tunani ta faɗa, a ranta sai ƙara girmama hukuncin ALLAH takeyi, yanzu nan Yah Ahmad matsayin miji yake a gareta? Wata zuciya tace, “To gashi ma kun kwana a ɗaki ɗaya�?.
Nannauyan numfashi ta sauke, wanda har Ahmad ya jiyota sama-sama a ɗan barcin da ya figesa.

Umm-Rumana na zaune a wajen har gari ya fara haske, ɗakin kawai take bi da kallo daki-daki, Ahmad dai nata barcinsa, wanda daga inda take tana iya jiyo saukar numfashinsa a hankali.
Sama-sama ta fara jiyo motsin matar gidan da yarinyarta dake kuka, sai kuma zuwa can tajiyo maganar mijin shima suna fira.
Idanu ta lumshe tana tuno gidansu, yanzu tasan gidan nacan da hayaniyar yara daga kowanne sashe, musamman ma sashensu da ke da ƙananun yara da sashen baba ilyasu.
Barcine ya sake saceta a kan abin sallar itama.

Sallamar Zainab ce ta farkar da Ahmad, ya buɗe idanunsa kafin ya tashi zaune yana amsawa, yakai idonsa kan Rumana da ko motsi bataiba, janyewa yay ya bama Zainab ɗin izinin shigowa.
Sai da ta sake yin sallama sannan ta shigo, ta sauke tiren kanta da aka ɗora kofin silba babba da kwanon silba guda biyu akai.
“Yaya ina kwana�? ta faɗa lokacin da take kaiwa ƙasa durƙushe.
Amsa mata yay yana ƙoƙarin sakko da ƙafafunsa ƙasa.
Tace, “Gashi inji Ayyah, tace yaya jikinka? Idan kaci abinci dan ALLAH kasha magani, idan kasha zataji a zuciyarta kasha, idan kuma bakashaba ma zataji bakashaba�?.
Guntun murmushi yayi badan ya shiryaba, a ransa yana kuma jin ƙaunar Ayyah sosai.
A hankali ya furta, “Kice mata zansha insha ALLAHU�?.
“To yaya zan faɗa�? Zainab ta amsa tana taɓa ƙafar Umm-Rumana yanda Ahmad bazai luraba.
Shi baima san tanaiba, ƙoƙarin sakkowa yake daga gadon.
Dai-dai nan Rumana ta buɗe idanunta.
Zainab ta matsa kusa da ita tana ƴar dariya, Ahmad kam buta ya ɗauka ya fita ya barsu suna gaisawa.


Bayan tafiyar Zainab da Rumana taita roƙon ta zauna taƙi, acewarta ance karta daɗe.
Rumana tahau gyaran ɗakin dan Ahmad bai dawo ba, sai da ta gama shara ne ta fito danta share waje sai taga butar a jiye, kenan nan ya ajiye ya juya ya fita.
Share tsakar gidan tayi gaba ɗaya, tana ƙoƙarin wanke banɗaki matar gidan ta fito ɗauke da kwanikan da suka karya.
“A'a amaryace dayin shara da safen nan? Harda su wankin bayi?�?.
Murmushi Rumana tayi, cikin girmamawa tace, “Ina kwana�?.
“Lafiya lau amarsu, ya amarci da angon naki?�?.
Kasa amsawa Rumana tayi, saboda jin kunya, matarma tayi dariya kawai tana ajiye kwankan bakin rijiyar dake gidan.
Rumana ma ta fito daga bayin riƙe da botiki, gaban rijiyar ta ajiye tana faɗin, “Rijiyar akwai ruwa kenan�?.
“Eh akwai ruwa Amarya, sai dai babu guga wlhy, jiya da safe Ahmad ya jefashi cikin rijiyar saboda tsabar rashin jinsa�?.
Kallon rashin fahimta Rumana tai mata, jin ta ambaci sunan Ahmad.
Matar data farga da kallon sai tayi dariya, “Au yi haƙuri, na manta sunan mai gidanki kenan Ahmad, bashi nake nufiba, yaron wajena shima sunansa kenan, sai ƙaramar Faɗima muna kiranta Amatullahi�?.
Rumana tai murmushin jin kunya tana cewa, “ALLAH ya raya mana su akan sunna�?.
“Amin ya rabbi Amarya, amma ke yaya sunanki? Ni sunana Husna, amma yanzu dai anan anguwar anfi sanin maman Ahmad�?.
“ALLAH sarki, ni Umm-Rumana, sai dai ni zanke ce miki Maman Amatullah to�?.
“To babu damuwa Umm-Rumana amaryarmu, ai dole a ɓoye sunan mai gida, kije ga ruwa can a banbuna ki ɗiba kafin Abban Ahmad yazo ya ɗakko gugan�?.
“Nagode sosai�?
Umm-Rumana ta faɗa tana nufar Banbun ruwan kalar ganye dake ƙofar ɗakin Maman Ahmad.

Wanka tayo da ruwan data ɗiba, tayi alwalar walha kamar yanda ta saba ma kanta tun tana gida.
Kayanta da aka jera cikin Wadrobe ta buɗe ta ɗauki zani da riga na leshi ta saka, sama-sama ta shafa mai saboda zafi da aka fara, batai wani kwalliya ba sai fauda data shafa da kwalli a idonta.
Ta fara jin yunwa, dan haka ta matsa gaban tire ɗin da zainab ta kawo ta buɗe, Fankasu ne da yay luhu-luhu a kwanon silban farko, sai miya a ɗayan kwanon tana ta ƙamshin manshanu, kofin kuwa kunune na tsamiya shima sai ƙamshin kayan yaji yake, tana rufewa Ahmad na shigowa da sallama, kanta a ƙasa tai masa sannu.
Ya ajiye ledar hannunsa da kofin roba mai murfi madai daici yana amsawa.
Zama yay a bakin gadon idonsa akan kwanikan data gama buɗewa yace, “Miye wannan a ciki?�?.
“Fankansu ne da kunu�?.
Baikai ga amsawa ba wayarsa tai ring, fiddota yay daga aljihun jallabiyarsa ya duba.
“Manyan ƙasane haka suka tuna damu?�? yay maganar wayarsa a kunne.
Daga can Zaheedah tai dariya tana maida masa amsa da “Ai kune manyan ƙasa Shema, yanzu gudun namu da akeyi har takai ai bikinka babu gayyata?�?.
Murmushi yayi mai sauti, wanda har ya saka Umm-Rumana satar kallonsa da mamaki, ta daɗe bataga Murmushi a fuskarsa ba, duk da dama can itadai bayi mata yakeba sai da taga yanayi a majalissar abokansa ko idan yana tare da Samina, maganarsa ta sata sake maida hankalinta garesa batare da tasan dalilin hakanba.
“Bani da bakin kare kaina kam, amma dai ina roƙon amin uziri, nasan dai Sufyan ne ya sanar miki, kuma inada tabbacin bazai gaza miki bayani ba�?.
“hhh hakane kam ango, ai banyi fushiba, yanzu ma dai taya murna na kira nayi, ALLAH ya sanya alkairi, yasa nanda wata tara muzo suna tunda ba ai biki da muba�?.
Sai da ya saci kallon Rumana dake wasa da yatsun hannunta kanta duƙe ya lumshe ido, sannan yace, “Humm, kina lafiya? Ya mutan gida?�?.
“Lafiya lau kowa da komai yake�? Zaheedah ta amsa duk da taso ya bata amsar maganarta ta farko.
Sun ɗan taɓa hira kaɗan, a cikin hirar take faɗa masa sai tazo ganin amarya.

Bayan ya ajiye wayar ya kalli Rumana da har yanzu kanta ke a ƙasa, “Zubamin kaɗan, sai ki haɗamin shayin nan, anjima nasha kunun�?.
Da to ta amsa tana miƙewa, ƙaton banbun ruwanta da aka zuba kwanikan amfani ciki ta buɗe ta ɗauki filet da cokali da kofi, dukda a wanke suke fes sai da ta sake ɗaurayewa sannan ta dawo inda take, sai faman gyara gyalenta dake zamewa take harta kammala haɗa masa shayin, ta zuba fankasu uku yace,
“ya isa haka, zuba miyar a kai kawai�?.
Da “to�? ta amsa.
Bayan ta gama taɗan kallesa, a ɗarare tace, “Ko a saka Sallaya a ƙasa�?.
Kai ya ɗaga mata yana cigaba da danne-dannensa a waya.

Ganin zai fara cin abincin sai ta miƙe zata fita.
“Kefa?�?
Yay maganar ba tare da ya kalleta ba.
“In....in..ba banajin yunwa�? tai maganar cikin in ina tana sosa gefen kunne.
Manyan idanunsa ya ɗago ya kalle, hakan yasata saurin maida nata ta risinar.
“Dawo ki zauna ki karya ko ranki ya ɓaci�?.
Dawowa tai tabi Umarninsa, zata zuba wani fankasun yay mata nuni da wanda ta zuba masa.
Duk jikinta tsuma yake, itace yau zataci abinci kwano ɗaya da Yah Ahmad?.
Yanda ta takure kanta duk yana kula, amma sai yay kamar baisan tanayiba, yaci gaba dacin abincinsa duk da baya masa daɗi sosai a harshe saboda zazzaɓin da yayi, ga damuwar Samina tana nan daram a ransa babu abinda ya ragu a ciki.
Bai sake tanka mata ba har suka cinye ukun data zuba masa, wanda shine ya cinye kaso mafi yawa a ciki, buɗe kwanikan yay ya ƙara wasu ukun ya saka miya, Rumana dai na kallonsa batako motsaba, gabanta ya tura filet ɗin ba tare da yace uffanba.
Ta kallesa da sauri suka haɗa ido, yanda ya sake tsuke fuska ya sata maida kanta ƙasa da sauri ƙirjinta na lugude, tadai fahinci itace zata cinye wannan kenan?.
Yanda bai sake bi takansa ba itama ta kasa kallonsa, ya ajiye kofin tea ɗin da ɗan saura a ciki alamar dai ya ƙoshi, miya tuna kuma oho masa, sai taga ya jawo ledar da madara ke ciki ya fasa ɗayan sacet ɗin ya zuba a kofin da sukari sai nescafe, ya zuba sauran ruwan zafin kofin ya motsa, gabanta ya ajiye ya miƙe nanma bai tanka ɗinba dai.
Da kallo ta bisa har ya ɗakko ledojin jiya ya ajiye inda ya tashi, ya buɗe banbun da kwanika ke ciki ya ɗauki kofi, sannan ya buɗe ƙaramin banbun danya ɗeba ruwa amma wayam babu komai.
Miƙewa Rumana tayi tana faɗin, “Babu ruwa ai, naje zan ɗiba a rijiya wai gugan ta faɗa jiya, bara nasamo maka wajen maman Amatullah�?.
Baice komai ba ya miƙa mata kofin.
Bata jimaba ta dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login