Showing 72001 words to 75000 words out of 165545 words

Chapter 25 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

365

jan tsaki.
Da mamaki Rumana ta kallesa, sai ya galla mata harara yana faɗin, “Da nasan kowanne banza zai nema ɗora idonsa akan matata wlhy da hijjab zaki sawo Mtsoww�?.
Gefe Rumana ta maida kanta tana ƙoƙarin haɗiye dariyar dake neman kufce mata, tofa kishifa kenan? Dan idanunsa harsun kaɗa saboda ɓacin rai.

Kallo bai dawo kansuba ma sai da suka iso ƙofar gidansu, gaba ɗaya mutane sukai musu caa da idanu, abokan Ahmad kam wani ihu suka saki harda masu fito tamkar anci ƙwallo suna haɗa baki wajen ambatar “Sai mai zafin mu!!�?.
Daƙuwa Ahmad yay musu yana cije baki.
Ba tare da yasan mi yayi ba yaja hannun Rumana sukai cikin gida wai duk dan mutane subar gane masa mata.
Murmushi baba ilyasu da Baba Yusha'u dake ƙofar gidan suma sukayi suna girgiza kawunansu, Baba kuwa ai shi harda kunya yaji, dukda yaji daɗin ganin ƴaƴan nasu cikin aminci da kuma kishin Rumana daya hango a fuskar Ahmad ɗin kodan abunda yayi.
Rumana nason tace ya saki mata hannu amma tanajin tsoro, a haka suka shigo har cikin gidan sashensu, inda yake cike da ƴan Shema matan da akazo dasu ɗaurin aure.
Aiko abokan wasa sukai musu caa da sheri, shi saima lokacin ya fahimci tsiyar daya tafka, gashi sunyi ido huɗu da Gwaggo da Ayyah dake tsaye suna magana, gwaggo dai kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta, Ayyah ko saita hau dariya mai nuna tsagwaron farin ciki.
Gasu Yaya Maryam daga gefe suma suna dariyar da kare su Ahmad ɗin daga sherin da abokan wasa suke masa akan ya kamo Rumana kamar yana tsoron kar wani ya ƙwace masa.
Murmushi kawai yayi ya saki mata hannu a hankali, ya sosa gefen wuyansa tare da takawa zuwa ga iyayensu ƴan shema dake wajen.
Rumana kam ai tunda suka tsaya kanta ta sunkuyar kawai ƙasa, jitake inama ƙasa ta tsage ta shige saboda kunya, bata iya ta motsa ba sai da Ayyah tazo ta kama hannunta sannan, amma sai tafiya take a hahharɗe.
Ayyah ta ƙarasa da ita inda Ahmad ke durƙushe yana kwasar gaisuwa da saka albarkar dangin mahaifan nasu, durƙusawa itama Rumana tayi kanta a ƙasa bata yarda ta kalli kowa ba ta shiga gaishesu.
Wata dake matsayin yayar su babansu ce ta jawo hannunta tana faɗin, “Wannan ƴar tawa anya babu ajiyar mijina ko kishiya anan?.
Nanfa kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinsa, Ahmad dai tunda ya saci kallon Rumana saiya miƙe dan yaga su Wasila abokan wasansu ba ɗaga masa ƙafa zasuyiba, shi kuma ba iya maida murtani yakeba dama can.
Wajen Ayyah ya nufa suma ya gaishesu yanata wani soshe-soshen kai, ita Ayyah ma saiya bata dariya.


★★★★★★

Samina na tsakkiyar ƙawayenta ana rangaɗa mata kwalliya wasu ƙawayenta biyu da suka iso kusan tare dasu Rumana suka shigo musu da labarin soyayyar da suka gani a waje na wasu sabbin ango da amarya, dansu basusan Ahmad ɗinba.
Tsigil wata ɗiyar ƙanwarsu mama gaje tace, “Aunty Samina Ahmad nefa da Rumana�?.
Wani irin faɗuwar gaba Samina taji har tana kaɓe hannun mai kwalliyar, tayi kicin-kicin da fuska dan zuciyarta sai zallo take tamkar zata faso ƙirji ta fito, a yanda ƙawayenta ke bada labarin lallai show ɗin ya ƙayatar kuwa, ganin zata sauka a layi Nafy tai saurin ƙwaɓarta.
Duk yanda taso dai-daita kanta saita kasa, dan kuwa ahankali maganar abinda Ahmad ɗin yayi yaketa fitowa daga bakunan mutane, wasu suna ganin yayine dan kawai ya nuna yanzu Samina bata ransa, wasu kuma na faɗin kawai tsantsar ƙaunar dake tsakaninsa da matarsane ya nuna kishinta.
Samina jitake kamar ta fara dannama duk wanda ya ambaci sunan Rumana da Ahmad zagi a wajen............✍�?



_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(24)*


..............Su Rumana dai an shige cikin dangi, kowa sai haba-haba yake da ita, iya kuwa harda guɗa ta callara akan Umm-Rumana, hakan ya jawo kallon Rumana ya ƙara armashi cikin taron, dangin mama gaje da hassada keci sai kusheta suke, ƴan uwanta kuwa dana mahaifiyarta daɗin ganinta cikin shigar kamala duk sai ya lulluɓesu, ko ba komai dai Ahmad ya tabbatarma duniya ya amshi zaɓin ALLAH kuma yabi umarnin iyayensa.
Babu wanda yay tunanin ganinsa cikin taron bikin sai gashi harda matarsa, kuma abin birgewa cikin aminci da cikar haiba aka gansu, ba kamar yanda su mama gaje suke tunanin soyayyar Saminar ta cigaba da wajiga rayuwarsa ba har a wannan lokacin.
Dan bokanta ya tabbatar mata Ahmad tsiya-tsiya zai dawo daga neman kuɗin daya tafi, kuma bazai taɓa shiga gaban Samina ba ita zatai ta kasancewa a samansa, haka Rumana kuwa bazai taɓa ya kusanceta ba sai dai iyayenta su gaji su kashe auren.
Itama Umm-Ruman tun tana sinne-sinnen kunya harta saki jikinta acikinsu, dukda kuwa jitake kamar kowa yasan miya shiga tsakaninta da Ahmad, gashi dama bawani gama jinta tai dai-dai ba, irinsu Ayyah tsoffin mata dasu Iya kallo ɗaya sukaima yanayin tafiyarta suka harbo jirgin.

A ƙofar gidama ga Ahmad dolene abun ya burgeka, harkokin gabansa kawai yake cikin abokansa, sam babu wata damuwa ko kaɗan a saman fuskarsa, shaftarsu sukesha cikin nutsuwa suna kwasar dariya.
Yanda ya nuna halin ko in kula ba ƙaramin burge iyayensa da abokansa yayiba.
Shiko harga ALLAH yanzu Samina bata gabansa, dan ƴan labaran daya samu akanta gameda rayuwar data zaɓama kanta da Ma'aruff ba ƙaramin tsanarta ya cusama ransa ba, balle yanzu da suka zama abu guda shida ƴar ƙanwarsa Umm-Ruman, saima ya kula dama can so yama rufe idanunsa bai kula Rumanan tafi Samina komai ba.

Har aka gama taruwa babu ango babu dalilinsa, hakama waliyansa, ga lokaci yanata ja, an tara mutane dukda sunada uzurorin gabansu, abokan ango dai sun iso, sai kiran wayar Ma'aruff ɗin suke amma tsabar wulaƙanci yaƙi ya ɗaga.
Sai da mutane suka gama ƙuluwa da takaici, wasuma harsun fara miƙewa sannan sai gashi, ko neman afuwar kowa baiyiba kuwa, da yake tare suka iso da waliyan nasa kawai ɗaurin auren akayi.
Kamar mutane akan ƙaya suke ana ɗaurawa suka fara watsewa, shi kansa angon dagashi har abokansa basu zaunaba suka ƙara gaba.
Aiko wannan abu ya zama ƙananun magana sosai a cikin gida, dan irin ƴar gaisuwar iyaye da anguna kanshiga yi su Ma'aruff basuyiba, balle amarya tai tunanin zasu ɗan ɗauki hoton tarihi haryaga kwalliyarsa ita taga tasa ya zamo musu ranar tunawa wata rana a gaba.
Samina ranta ya ɓaci, ta kira Number Ma'aruff amma yaƙi ɗaga mata, daga ƙarshema data jera masa kira kusan baƙwai sai ya kashe wayar gaba ɗayanta.
Wannan abu yaso ɗimauta tunaninta kam, sai dai Nafy na tausarta saboda idon mutane.
A ƙofar gida kam yaran anguwa suka haɗa dj na shaƙiyanci, da waƙar MATAR JAMI'A ta Naziru Ahmad suka fara wadda kowa dai ya fahimci habaicine ga samina, daga nan suka cigaba da saka waƙoƙi kala-kala da dai ke gargaɗi ko magana akan butulci.
Ahmad da abokansa kuwa tuni sunbarma anguwar suma, dan dama sunada wajen zuwa auren kawai suke jira a ɗaura su ƙara gaba.


★★★★★★

Maganar farin ciki dai a wannan buki kam ƙalilanne, dan komai kaga yazo saika samesa a dagule da ɓacin rai, danma dai sunata ƙoƙarin rufe wani abun dan kar a fahimta ai musu dariya.
Da daddare ma sai da rai ya ɓaci akan ƴan ɗaukar amarya kafin abokan ango su iso, tsabar iskanci kuma dukda sun iso a makare sai sukace ƴammatan amarya kawai zasu ɗauka banda tsaffi.
Da ƙyar aka samo wani mai motar hayar taxi a anguwar ya ɗauki wasu a cikin iyayen Saminar tunda bazai yuwu ace ankai amarya babu danginta ko guda ba.
Abinda kuma basu saniba daga nan gidanma bawai gidanta aka nufaba da ita, hotel ɗin da zasuyi dinner abokan ango suka nufa, shiyyasa ashe sukace ƴammata kawai zasu ɗauka.
Ran wasu a cikin iyayen da suka bisu ya ɓaci sosai, dan dangin Ma'aruff ɗin sai kallon banza suke musu.
Ganinfa ana nemam wulaƙantasu suka zaro jikinsu suka fito domin dawowa gida.

Ga Samina kuwa duk ɓacin ran data shirya nunama Ma'aruff tana ganinsa sai taji ta daburce ta kasa ko tari, sai ma damuwa data shiga dangane da shashsharetan da yakeyi.
Har aka tashi wannan dinner bataga fara'arsa ba, sai dai idan abokansa ko danginsa sunzo kusa dasu yin hoto ko magana dashine zataga yana murmushi, amma ita magana ma idan tayi saiya ja lokaci yake bata amsarta, wata kuma ya share abunsa kamar bai jiba.
Ƙarfe ɗaya aka tashi, kowa ya kama gabansa bayan sunma Amarya da ango rakkiya gidansu, dan tsaruwa kam gida ya tsaru, dolene Samina ta kira kanta gwarzuwar shekara a wannan lokaci.
Sai dai suna shiga yaga abokansa sun wuce da ƴan uwansa ya saki hannun Saminar, ɗakinsa ya nufa ya barta a falo tsaye, tun tana tsammanin fitowarsa harta ƙosa ta bishi, tsabar rainin hankali iskesa tai harya shiga wanka, ɗakin ba baƙonta bane, tunda ansha kawota cikinsa a aikata abinda akeso da ita a ciki, sai dai an canja kayan cikinsa, waje ta samu ta zauna tana tsumayen fitowarsa.
Koda ya fito ya ganta kallo guda yay mata ya ɗauke idanunsa, cigaba yay da shirinsa kamarma baisan tana ɗakinba, ita dai Samina mamaki sai kuma ɗaure kanta yake, gani take tamkar ba Ma'aruff ɗinta bane mai sonta da ƙaunarta tare da tattalinta ga komai.
Bayan ya gama shirinsa tsaf yazo ya zauna a bakin gadon yana kunna lap-top, ga kofi daya ciko da fresh milk ya ajiye gefensa.
Kasa jurewa Samina tayi ta miƙe ta koma kusa dashi ta zauna tanata zabga ƙamshi mai daɗi kuwa.
Murya a raunane tace, “Wai lafiya kuwa Sweet?�?.
“Mi kika gani?�? yay tambayar ba tare daya kalleta ba.
Da ƙyar ta haɗiye busashshen yawun bakinta tana zuba masa mayun idanunta irin nasu Ahmad, “Sweet ka canja min, sai kace ba kaiba, kamar baka ɗokin ganina a gidanka matsayin amarya matarka ta sunna? Yanzu wane angone za'a kawoma amarya amma hankalinsa nakan aiki�?.
Wata ƴar dariyar rainin hankali yayi ya juye gaba ɗayansa yana kallonta, yayinda yake kai kofin madararsa a baki yana sha.
“To ke kuwa banda abunki wane zumuɗi kike son ganina a ciki? Babu wani abu baƙon a gareni daga wajenki ai, kokuwa wannan faudar da zanen ƙunshin zan zauna kallo?�? yay maganar yana lakato kwalliyar fuskarta a ɗan yatsa.
Wani mugun tsorone ya kuma dirar mikiya a fuskar Samina, tai galala da baki tana kallonsa ba tare da ta iya furta komai ba.
Bakinsa ya taɓe yana kauda kansa daga kallonta, “Miye abun mamaki a zancena, kema dai kinsan kowane ango yana rawar jikine ga amaryarsa saboda abunda zai amsa mai muhimmanci a gareta, to ni kuma an bani tun a waje ai, mizanma ɗoki kuma yau?�?.
Hawaye masu azabar zafi suka fara gudu bisa fuskar Samina saboda kalaman da Ma'aruff yake gasa mata akan abinda shine yafi ƙarfinta ya amsa ba itace ta bashiba, hasalima tabi duk hanyar da zatabi danta tsare abunta sai irin wannan ranar amma saida ya ruguza mata shirinta.
Tashi tai ta fita da gudu tana kuka, ya bita da kallo yana taɓe baki, sai kuma yaja tsaki yana faɗin “Kajimin wawuyar yarinya, ballaga kawai mtsowww�?.

Samina kuwa ɗakinta ta shiga tunda dama ta sansa, ta faɗa kan gado tana fashewa da wani kuka mai ciwo, farawa da iyawa kenan, daga tarewarta Ma'aruff ya rasa dami zai tarbeta sai wannan rashin mutuncin?.
Kuka tasha bana wasaba, ga maganin matan da aka ɗirka mata sai cizonta yake, har mararta ta fara mata ciwo.
Ganinfa zata halaka kanta kusan biyu na dare ta sake miƙewa ta koma ɗakin Ma'aruff.
Kwance ta iskesa hankalinsa kwance yana barci, cikin sanɗa ta haye gadon tare da ɗaga bargon ta shige cikin jikinsa ta ƙanƙamesa.
Cikin jan tsaki Ma'aruff daya farka yace, “K wane salon iskancine wai haka ina barci zakizo ki tadani?�?.
Banza tai masa ta fara masa salon data san yana saurin ruftawa, da zafin nama ya tureta daga jikinsa.
“K banason rashin mutunci fa, mike damun tunaninkine?�?.
Kuka mai tsuma zuciya Samina ta fashe masa dashi tana roƙonsa ya taimaketa karta mutu, sai faman riƙe mara take tana matse baki, ga hawaye wasu na bin wasu.
Shiko kallonta yakeyi da maɗaukakin mamaki, shi sai yau yake fahimtarma abinda mahaifiyarsa ke faɗa masa akan rashin dacewarsa da wannan yarinyar......
Katse tunaninsa Samina data manne masa a jiki tayi, ya janye jikinsa yana hararta, “Wlhy ki kama kanki, ni na aikeki kisha abinda zai hanaki zaman lafiyar? Can kije kiji da matsalarki ni dai barci nakeji, dan haka tashi kibarmin ɗaki kokuma na fitar dake wlhy�?.
Sabon kuka Samina ta fashe dashi tana durƙusawa a gabansa tana roƙonsa, amma sam yaƙi saurarenta saima faɗi yake ta fitar masa a ɗaki, inba hakaba wlhy zai lakaɗa mata duka, abinda take son shi baida ra'ayinsa yanzun.

DAREN FARKO ya zama DAREN WAHALA, Inji amarya Samina dake neman shiɗewa saboda azabar ziwon da mararta take mata, ruwan sanyi kam harta gaji da sheƙa ma jikinta ta sadaƙar mutuwa zatayi kawai kafin wayewar gari, tayi nadamar biyema su mama gaje da suka dinga ɗirka mata magunguna duk dan ta burge Ma'aruff, kuka kam tayi harma ta rasa hawayen zubarwa, Ahmad ya faɗo mata a rai, yanda yay wani irin murjewa ga wani sheƙi da choco fatarsa keyi, kawai saita shiga kawosa cikin ranta a wani irin yanayin daya sakata kuma fashewa da kuka, dan kuwa tana ƙiyastashi a rantane zuciyarta na hasko mata Ahmad tare da Umm-Ruman.
Jitai tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta lokacin da hakan yazo mata a cikin rai.


___________________________________

Ahmad ma kam baisan tanaiba, dan tun sanda ake dambarwar abokan ango sunce bazasu ɗauki tsoffi a motaba ya shigo gidan ya kaɗa kan matarsa suka ɗauki hanyar gida.
Tana sashensu sunashan hira da Amminta da ƙannen Ammi da sukazo bikin Zainab taje ta sanar mata saƙon kira daga Ahmad akan tazo su wuce gida.
Sam bataso wannan tafiya ba, dama ga tsoro a ranta na abinda ya faru a daren shekaran jiya, Ammi tai mata tsawa ganin taƙi ko motsi balle shirin tafiyar.
Tashi tai tana matsar hawaye ta kimtsa ta fito, a sashensu ta iskesa suna faɗan da suka saba shi da Sakina, tun suna ƙanana idan tace masa ƙaninta sai ya ɓata rai saboda bayaso, to har yanzu da take a gidan aure ga ƴaƴa ba dainawa sukaiba, dan ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login