Showing 99001 words to 102000 words out of 165545 words

Chapter 34 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

378

“Rumana kiringa samun ko cingam ne ko wata alewa haka kina sakawa a bakin, zai rage miki tara yawun kinji�?.
Rumana da bata fahimci al-amarinba tace, “To Umma, ni wlhy nama rasa miya kawo hakan, sam ban iya haɗiye yawun yanzu, idanma nai kuskuren haɗiyewa sainaji kamar zanyi amai ko zuciyata taita tashi�?.
Su dai iyayen da suka fahimci tsagwaron wautar Rumana duk sai sukai murmushi, sai su Yaya Raheenatu ne suke mata dariya sosai.

Ahmad na zaune suna magana da Doctor Samina ta shigo ko neman izini babu, kallo ɗaya Ahmad yay mata ya ɗauke kansa yana sake shan toka, zama tai a kujerar dake kallon tasa, hakanne ya saka Ahmad miƙewa yana bama Doctor hannu sukai musabaha yana masa godiya.
Ya tsallakota zai fice ba tareda yama nuna yasan ƙurar data kwasota ba, gudun kar taji kunya yasata tasowa da sauri tabiyosa, nanma baiko dubeta ba dukda yana jin takunta gab da shi, kusan a tare suka iso wajen, aiko Rumana da ganinsu tare ya sosa ranta karaf sai suka haɗa ido da Ahmad.
Yanda ta juya idanun ta ɗauke daga kansane ya bashi mamaki, dan tsagwaron kishi ya hango a cikinsu, saima yaga ta miƙe ta fita.
Ayyah da duk ta kula da abinda ke faruwa tai dariya a zuciyarta, kallon Ahmad ɗin tai tana faɗin, “Ɗan albarka ya kamata a samowa Umm-Ruman wani ɗan abu ta saka a bakinta koda alewane ko cigam, wannan zubda yawun baida daɗi, ta kasa zama waje guda ta huta�?.
Da kallo yabi Rumanan data dawo yanzu ta zauna, shi kansa abin ya fara basa mamaki, yace, “To Ayyah bara na samo mata, zama muje taga likitane, ni kaina narasa mike damunta�?.
“Allazi an ƙara kenan�? cewar Sakina tana dariya.
Harararta Ahmad yay dan dama tunda ya shigo basuyi faɗan da suka saban ba.
“Allazi an ƙara me? Kekuma?�?.
Sakina tace, “Haba ɗan ƙanina miye na fusatar?�?.
Hannu ya kai zai ranƙwasheta ta matsa tana faɗin, “ALLAH kana taɓani akan matarka zan rama, a maganata dai ai ban ambaci sunkaba ka tsargune kawai�?.
Dariya kowa ke musu, dan babu wanda baisan wannan ƴar tsamar dake tsakanin Ahmad da Sakina ba, inhar suka haɗu faɗa sau goma su shirya yamusu kaɗan.
Shi yaƙi yarda ta girmesa, ita kuma bazata fasa faɗar shi ƙaninta bane🤣.
Ƙwafa yay zai bar wajen, tace, “Iye kaga su Amadi masu mata, saboda nace zan rama a kantane ka haƙura kenan, a lallai soyayya ruwan zuma�?.
Wucewarsa yay bai tanka mataba, ya saki lallausan murmushi saboda iya shegen da Sakina ke masa har yanzu shida Rumana.
Babu abinda zuciyar Samina keyi sai zallo, adai fahimtarta suna nufin Rumana ciki ne da ita, cikinma na Ahmad ɗinta.
Wata irin tsuma jikinta keyi, numfashinta kuwa da ƙyar take fusgarsa wajen fitarwa.
Ana cikin haka sai ga Ahmad ya dawo da leda mai ɗan girma, har gaban Rumana yaje ya miƙa mata ledar, ta amsa kanta aƙasa saboda nauyin iyayensu da yayenta, shiko ta kula koma ajikinsa, kansa tsaye yake komai.
Saboda neman magana irin na Sakina ta amshe ledar daga hannun Rumana tana dubawa, “Iye kwali-kwali fa ya siyo, Amadi bara na raba nima naɗan ɗib.....�?
Ai bata ƙarasaba taji saukar rankwashi mai zafi a kanta, ya kuma fisge ledar yana fadin, “Ko kece ƙwalan ta kankia bazaki lashi ko ledar abu ɗayaba�?.
Aiko mi za'ai inba dariyaba, Sakina kuma ta dafe kanta kamar zatai kuka, tace, “Kam balastin, aiko ka jama matarka, kanta zan rama�?.
Sake juyowa yay ya kama hannun Rumana yace, “Basai idan ta zauna inda kikeba zaki raman�?.
Rumana duk da kunyar da ta nema halakata tanaji tana gani Ahmad yaja hannunta suka bar wajen.
Sakina tace, “Matsoraci kawai�?.
Gwalo ya juyo yay mata yace, “Oho dai�?.
Basu Ayyah ba hatta dasu Baba sai da sukai dariyar wannan rikici na Sakina da Ahmad.
Samina kuwa tsaki tayi zuciyarta na mata zafi da turiri, wannan itace ƙauna da soyayya da riritawar datai tsammanin samu daga Ma'aruff, amma sai gashi tana ganinta wajen wanda takema kallon gara, faƙiri.
Ta haɗiye wani yawu mai kauri tana binsu Ahmad dake ƙoƙarin shiga Office ɗin doctor da kallo, kuma har suka shige bai saki hannun Umm-Ruman ba, jitai wata irin tsanar yarinyar na ƙara mamaye duk illahirin zuciyarta.
Mama gaje tsaki tayi, sosai maganar cikin nan na Rumana ya tokare maƙoshinta, a ganinta Samina ta cancanci wannan cikin, babu wanda yabi ta kansu dan bama asan sunaiba.

Su Umm-Ruman kuwa a office ɗin Dr suka yada zango, dama bayanin da Ahmad yaje ɗazun yay masa kenan, bayan sun zauna Rumana ta gaida likitan ya amsa da ƴar fara'a yana tambayarta yaya jikin.
Sai da ta kalli Ahmad sannan tace, “Nifa banajin wani ciwo a jikina Yaya�?.
Murmushi Doctor ɗin yayi, danshi tun shigowarsu ya fahimci Rumana nada ƙaramin ciki.
Shine ya katse musu kallon da sukema juna, Ahmad na harara-harara, Rumana na kallonsa a tsoro-tsoro.....
“Hajiya ai dama bamuce muma wani abu na damunki ba, jininki kawai zan ɗan ɗiba yanzu.
Dole ta amsa da to, saboda yanda Ahmad ya tsuke fuska.
Kiran waya Doctor yayi, babu jimawa wata Nurse ta shigo, ita yasa ta ɗiba jinin Rumana ta fita dashi zuwa lab.
Tashi sukai suka koma wajensu Ayyah, dan Doctor yace sai nan da kamar awa ɗaya zai basu bayani idan result ɗin ya fita.
Ahmad bai zaunaba suka wuce massalaci dasu baba, Rumana kuwa tazo ta zauna wajenta nada.
Tun tana sauraren hirar yayun nata har itama ta fara saka baki, Samina ce dai ta koma gefe ta tsume taƙi shiga cikinsu, a ganinta ta wuce da ajinsu, gefe kuma mugun haushin Umm-Ruman takeji dama su kansu ɗin da suke tarairayarta.
A haka su Ahmad suka dawo, baba yace su tashi duk su wuce gida hakanan anbar yara su kaɗai, su zasu zauna har malam ɗin ya farko.
Rumana sai addu'a take ALLAH yasa Ahmad yace ta bisu, tanata satar kallonsa amma shi yaƙi kallon inda take sai faman latsa wayama yakeyi, a bazata baba yace Samina da Rumanan suma suje can idan mazajen nasu sun tashi sa biya su ɗaukesu.
Dama ita Samina can zata koma, Rumana ce ke a cikin ƙila wakala, shiyyasa baba na faɗa wani daɗi ya ratsa ranta da zuciyarta.
Aiko tana ɗago ido ta tsinci na Yah Ahmad dake antaya mata harara.
Fuskewa tai ta ɗauke kanta kamar ma bata ganshiba, takobi su Ayyahn.
Tun a wajen asibitin Mama gaje da Samina suka raba hanya dasu Ayyah, dansu daga nan wajen malaminsu suka nufa Inna mari nacan na jiransu dama tun ɗazun.
Babu wanda ya damu da lamarinsu kuwa, dan suma su Sakina ayarin ƴan gidan nasu sukabi kowa nason ƙarasa yininsa a gida, hakama bintu yayar Samina gida tabi ƴan uwanta tanama mahaifiyarsu da ƴar uwarta fatan shiriya a wannan rayuwa.

★★★★★★

Ba ƙaramin daɗi Rumana ta tsinci kantaba na ganinta a gida cikin ƴan uwanta, su Fa'iza harda mata sherin wai akuyar ɗaure ta samu sake.
Daƙƙuwa kawai tai musu tana dariya.
Abinda ya tsayama Rumana a rai yanda kowa ke mata magana akan ta kula da kanta sosai, sannan tabar zama babu wani abu a bakinta saboda hanama kanta zubda yawu. Ɗan tsarguwa ta farayi a ranta jin Yaya Bintu na faɗin, “ALLAH dai ya raba lafiya wannan ɗan gatan dangi ya fito duniya musha shagalinmu�?.
Rumana tai kasaƙe tana tunani, idanfa har zata ɗora maganganunsu a mizani kamarfa suna dangantata da cikine na haihuwa? To amma haka ake cikin dama babu wani wahala? Ita dai bayan ciwon kai dataita fama dashi kwanaki batajin wani ciwo a jikinta sai na rashin jin daɗin jikinta, tanajin komai na sauya mata a jiki kam sai wannan zubar da yawun shima baifi kwana biyu kenanba ya fara addaba mata.
Kauda zancen tai kawai a ranta da yaƙinin ba haka bane, ta cigaba da hidimarta hankali kwance............✍🏻�?



_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

https://youtu.be/N2nbw8zn9Jk


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/HFjVgQVnmn0


*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(32)*


............Bayan tafiyar su Rumana Doctor yake sanarma su Ahmad sakamakon gwajin da akai mata, ya tabbatar musu tana ɗauke da ƙaramin ciki ɗan watanni uku.
Daga su Baba har Ahmad bayyana farin cikin da suka tsinci kansuma a ciki ɓata lokacine, bakin kowa ya kasa rufuwa, wannan aure da suka haɗa yayi riba, dan sun sake tabbatar da ƴaƴansu sun amshi ƙaddarar UBANGIJI da hannu biyu.
Ahmad sai sinne kai yake yana murmushi, shi adole kunyar su baba yakeji, Su Mudan ne dai suketa shirmensu shi da Abu da sauran ƙannensu.
A wannan yanayin farin cikin abokan Ahmad suka iskesu, suma sunzo duba Malam.
Aiko sunajin abinda ke faruwa suka tasa Ahmad da sheri, baiko ɗaga musu ƙafaba ya shiga ramawa.
Gaba ɗaya Ahmad ya kasa daina mamakin abun a ransa, wai shine yau da ɗa, Umm-Rumana zata haifa masa ƴa ko ɗa mallakinsa.
Ya lumshe ido yana haɗiyar wani tsinkakken yawu da sauri-sauri, taɓasan da Sufyan yayine ya sakashi buɗe ido yana kallonsa.
Sufyan yay murmushi tare da faɗin, “Kai Alhaji duk murnarce? Badanma ka tsaya jamana ajiba ai da wannan watanne watan haihuwa�?.
Ƙaramin naushi Ahmad ya kaima Sufyan, da sauri Sufyan ya kauce yana dariya, Ahmad ya faɗaɗa murmushin sa yana harar Sufyan ɗin, “Ɗan sa ido kawai, nakula ka fara lalacewa kaje kai aure?�?.
Rabi'u yace, “Iye kaji masu aure, mikakeci na baka na zuba, muma muna nan tafe insha ALLAH, dan da yawanmu bazamu wuce shekarar nanba�?.
“Da nayi farin ciki kuwa, ko yaya nasamu sauƙi daga iskancinku�? Ahmad ya faɗa yana hararsu.
Nanma dariyar suka ɗanyi kaɗan.

Suna a asibitin har kusan tara na dare, a lokacinne kuma cikin amincin ALLAH malam ya farka, kowa yaji daɗin yanda ya farka daɗan ƙarfinsa, kuma a hayyacinsa, dama can Malam bayason asibiti, hakanne yasaka shi yanzuma ya tijare musu akan bazai kwana ba su maidashi gida, da a hayyacinsa yakema bazai yarda a kawosa nanba.
Duk yanda su Ahmad da abokansa sukaso lallaɓa tsohon nan sam yaƙi harda shirin musu kuka yake.
Babu shiri Doctor ya basu sallama akan zai dinga zuwa da safe yana dubashi insha ALLAHU.
Sunji daɗin karamcin wannan likita, dan haka suka nufi gida da ƙwarin gwiwa.


★★★★★★�?

Lokacin da suka iso gidanma Rumana ita har tayi barci a ɗakin Amminta, ta kwantane da fatan ALLAH yasa karsu Ahmad su dawo da wuri yau ta kwana gida, koba komai ta huta da fitinarsa ma.
Sai dai kam addu'arta bataci ba, dan su Ahmad suna kai malam ɗaki yaga komai ya dai-daita sashensu ya shiga.
Ayyah da Gwaggo sukai masa sannu da zuwa.
Amsawa yay yana zama kan dutsin dake kusa da kwatanniyar ruwan agwaginsa, gaishesu yayi suma, suka ƙara masa ya mai jiki, yace Alhmdllh, dan kuwa kowa yaga malam yanzu bazaice shine aka fita dashi shataf ba ɗazun da safe.
Ayyah tace, “Ɗan albarka a kawo tuwo ko?�?.
“Ayyah anya kuwa zanci tuwon nan yau?, gaba ɗaya a gajiye nake kwanciya kawai nake buƙata yanzu, ko ma yunwar banaji sam�?.
“Sannu kaji, zirga-zirgace wlhy, jiki da jini ai yana buƙatar hutu, to inko bazaka ciba kuzo ku wuce gida dare nayi, dan itama wannan yanayin nata bai buƙatar yawace-yawacen daren nan kodan shaiɗanu, tunda baikai ƙwariba har yanzun�?.
Murmushi kawai Ahmad yayi, dan ya lura dai iyayensa mata su dukma sun gama fahimtar yayi ajiya ashe.
Gwaggo dai duk na zaune ta kunna redio tana sauraren taskar labarai, tana kuma jinsu sarai, amma yanda ta ɗauke kanta saika ɗauka batasan hidimar da akeyiba.
Sadiya ya ƙwalama kira, ta amsa daga ɗakinsu tana fitowa, da alama ma harta kwanta ya tasota.
“Jeki ki kira min Ruman mu wuce gida�?.
Da “to�? Sadiya ta amsa tana wucewa.
Shi kuma ya miƙe ya ɗauki buta ya shiga bayi.
Dai-dai nan baba ya shigo shima, daga Ayyah har gwaggo sannu sukai masa, ya amsa yana faɗin, “Su Amadu sun wuce dai ko?�?.
“A'a yanzu dai suke shirin wucewar, yana bayi�? Ayyah ta bama Baba amsa.
Baice komaiba ya shige sashensa.

Ahmad na fitowa Rumana da Sadiya suka shigo suma, sai kumbura fuska Rumana take saboda barcin data fara aka taso ta, ji take tamkar ta fasa ihu.
Ahmad ya sauke idanunsa a kanta, ta ɗan hasken farin watan daya gota sha biyar, hakan ya saka ƙyawunta kuma bayyana masa a cikin ido, ya sauke ajiyar zuciya kaɗan yana maida idonsa gasu gwaggo da Ayyah.
“Tom bara mu wuce sai da safen ku�?.
Ayyah tace, “To ALLAH ya huta gajiya ɗan albarka, Umm-Ruman ALLAH ya ƙara lafiya kinji, aita addu'a dai ALLAH ya inganta mana ya kuma raba lafiya�?.
Sadiya ce kaɗai ta amsa, Ahmad da Rumana kunya ta hanasu cewa komai, hakama Gwaggo da tunda aka fara zancen cikin bata tofa nata ba, tana dai cikin tsantsar farin ciki a cikin ranta.
Itama Rumana tai musu sallama tabi bayan Ahmad da yay gaba.
Sai da sukaje soro ne ya juyo, hannunta ya riƙo ba tare daya ce komaiba, dan ya lura kamar barcin data fara bai saketa ba.
A ƙofar gida sukaci karo da motar Ma'aruff yazo ɗaukar Samina, amma sai masifa yake mata akan tun ɗazun yazo kusan mintuna talatin yana jiranta, itako sai faman lallaɓashi take dan karya ɗaga murya ƴan majalissar abokan su Ahmad su ji.
Fitowar su Ahmad ne ta saka ma'aruff yin shiru yana kafe Umm-Ruman da ido tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa, suko koma kallonsu basuyiba duk da su Ahmad ɗin sunji jarabar da yakema Saminar, sun gittasu Ahmad yajiyo warin giya ya buso, mamaki ya kamashi warin giya daga ina haka? Yasan dai mu al'ummar arewa kasantuwarmu mafi yawa musulmai bamu cika huɗɗa da giyaba musamman yankinmu da Hausawa sukafi yawa, sannan shi baima taɓa jin warin giyaba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login