Showing 6001 words to 9000 words out of 165545 words

Chapter 3 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

355

kuɗin ankonsa. Ada bata kula kowane saurayi sai Ahmad, amma zuwa yanzu kam ai samari babu iyaka take kulawa, dataga kazo da ƴar kalar manyan mutane babu wani jan aji take miƙa kanta.
Tun Ahmad na zuba mata idanu akan ƙananun sabbin ɗabi'unta harya kasa haƙuri ya tuhumeta akan bilicin data fara, ya tabbatar masa shi bama ya ra'ayin farar mace, yafisonta da kalar fatarta choco color, alokaci haƙuri tabasa, ta shirya masa ƙaryar ba bilicin baneba, kayan gyaran jikine irin namu na gida take amfani dashi.
Cayay kosu ɗinne tabar amfani dasu sai sunyi aure ya yarda da ingancinsu.
Ta amsa masa da to, amma tana bama su Nafy labari sai suka zugata akan ai ba aurenta yakeba, taci gaba da abinta, gashinan harta fara zama big girl shine zata wani biye masa, inharfa bazata cire tsoron Ahmad a rantaba to bazata taɓa wayewaba ta zama cikakkiyar ƴar jami'a balle shima ta maidoshi kan hanya su shinfiɗa ƙyaƙyƙyawan rayuwa irinta jaruman littafi🤦🏻‍♀.............✍�?








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*




*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(3)*

...........Da waɗannan shawarwarin dukkan ginin Ahmad ya fara rushewa ga tarbiyyar Samina, ta fara biyema ruɗin su Nafy, idonta ya fara buɗewa da rayuwa ta manyan yara masu aji, duk wani dandalin wayewa suna wajen matsayin manyan baƙi masu lokaci, wannan damar samarin jami'a ƴan ƙwalisa da lectures suka samu wajen shiga jikin su Samina, sai ga ƴaƴan manya masu abin magana a aljihu sun fara kutso kai cikin rayuwarsu.
Tunanin Samina ya fara bata cewar lallai Ahmad bazai zama dai-dai da burinta na rayuwar Jaruman novels ba, saboda har lokacin dai ana nan jiya iyau, buga-bugar sana'a ce dai kawai a samu na yau na gobe sai an fita nemansa, suturar kirki wannan ta shiga taro Ahmad bashi da ita, gaba ɗaya kayan nasa duk yadin (Tashi sama sallau) ne, idan ƙananun kaya ka gansa dasu ma dai na gwanjone ba sabbi ba, ƙyawune kawai Ahmad ɗin zai iya mata burga dashi.
A samarinta kuma na yanzuma akwai waɗanda zasu iya linkashi ƙyawun, ga kuɗi na gaske suna mata wasa dasu, wanda suka fara lulluɓe zuciyarta dana mahaifiyarta wajen mance alkairin Ahmad a garesu.
Duk tsiyar da Samina ke aikatawa mama gaje ta sani sarai, kwaɗayin abinda Samina ke kawo musu na ciye-ciye ne ya lulluɓe idanunta ruf.
Idan cikin samarin Samina wani yace zaizo bata kawoshi gidansu, sai dai ta kaisa can gidan kakanninta da suka haifi mama gaje.
Hakan yasa Ahmad baisan mi Samina ke aikatawa ba, dan bai taɓa kawoma ransa zata kula wani saurayi bayan shiba, musamman da yasan akwai alƙawarin aure a kansu da ƙaunar juna mai ƙarfin gaske.


_________________________

A yanzu haka Saminar na gidan kakarsu, taima Ahmad ƙarya Inna mari bata da lafiya dan kawai tasamu taje wani bikin ƙawarta da za'ayi.
Sai dai tsoron kar wani yakai masa gulma yasata kiransa a waya ta sanar masa cewar zataje wajen kamun bikin ƙawarta.
Bai musa mataba ya barta, amma yace ta jirasa yazo da mashin ɗin Sufyan zai kaita.
Hakan ba ƙaramin haushi ya bataba, amma yaya ta iya dashi.

Shiri take da sauri-sauri gudun kar Ahmad yazo ya sameta a gidan...... Dan tafison su tafi tare dasu Nafy, kiran da taji Iya kishiyar kakarta Inna mari na ƙwala mata daga waje yasa gabanta faɗuwa, tasan dai yanzu haka Ahmad ne yazo.

“Samina!, Samina!!, Wai Samina baƙya jinane kokuwa lalatar takice ta motsa ne?�?.
Ta sake jiyo muryar iya daga tsakar gida.
Cikin cuno baki ta fito daga ɗakin dake can cikin wani lungu tana gyara ɗaurin ɗankwalinta ture kaga tsiya tana kumbura fuska.
“Kai Iya, irin wannan kira haka saikace na mafarauta, ɗan kwalifa nake ɗaurawa saboda su Nafy zasuzo yanzu mu wuce, mi kuma zan miki?�?.
Baki iya dake tsaye bakin murhu tana ƙokarin hura wuta ta riƙe, “Samina anya wannan rayuwar ta dace dake kuwa? Baƙya ganin kinason wuce gona da iri? Yanzu nan kodan yaron nan Ahmad ai ƙyaɗan sassauta wani abun, wlhy kibar biyema lalatattun yarancan su Nafisa karsu kaiki su baro�?.
Baki Samina ta ɗan taɓe tana gyara zaman gyalen kafaɗarta, “Iya nifa wlhy banajin daɗin irin maganganun nan naki, ni mi nakeyi mara ƙyau a rayuwata dan ALLAH?�?.
“Ba nace kina wani abu mara ƙyau bane ba Samina, Inason dai ki tsaya matsayinki kodan Yaronnan da ya gama wahalar duniya a kanki, karsuje su hure miki kunne akan ɗabi'u mara amfani�?.
“A'a Atine, anface ka fadi alkairi ko kai shiru, dan Ahmadu yaymata wahala sai akace bazata mori ƙuruciyarta ba? Naga ba aure aka ɗaura musu ba alƙawarin auren ne kawai ko?�?.
Wata dattijuwar tsohuwa mace dake fitowa daga bandaki ta faɗa tana ƙokarin ajiye butar hannunta.
Su duka kallonta sukayi.
Iya tace, “Amma dai Mari ai kowa yasan dama ALLAH shine yake yanda yaso ga mutum, amma kinsan ta yaro ƙyau take bata ƙarko, tunda har da alƙawarin auren, wataranama ɗaurawa za'ayi kamar yanda muke fata
“Uhm Atine, mubar wannan batunma dan ALLAH, dan yanzu ba lokacin yinsa bane, ni dai abinda nasani kawai shine bazamuyima yarinya auren doleba, idan tace Ahmad takeso zamu bata, idanko ta kawo waninsa shima zamu bata�?.
“Hakane Mari�?.
Iya ta faɗa tana ɗauke kanta daga garesu ta koma ƙoƙarin hura wutar data fara.
Daga Samina har inna Mari kakarta harar Iya dake duke sukayi.
Samina ta maida kallonta ga kakar tata tana murmushi, “inna mari bara naje karsu Nafy suyita jirana, kinsan za'a fara kamun ƙarfe uku na yammane�?.
“To Samina ALLAH ya tsare, a dai dunga kula saboda ƴan saka ido, kana rayuwarka baka damu da kowaba saikiga anata ƙokarin taɗo ƙafarka da harshe, bayan ko MANZON ALLAH ma yace mu kiyayi harsunanmu�?.
“Humm Inna ai mutanen duniya ba'a iya musu, sunfi son kullum su ganka jiya iyau, kuma idan arziƙin kayi sune zasu fara zakalkalewar kai nasune�?.
“Maganarki na kan hanya wlhy ƴar albarka, kedai jeki karki makara�?.
“Okey my sweet kakus bye�?.
“Duk da ban iya turancinba Samina, nima bye�?.
Ficewa Samina tayi tana dariyar zancen kakar tata.
Itama inna mari ta shige ɗakinta tana ƙyalkyata dariyar sake ƙular da kishiyarta iya Atine.
Murmushi kawai Iya tayi, tasan duk ita akema habaicin, ta girgiza kanta tana nemawa abokiyar zaman nata da jikarta shiriyar ALLAH, tare da fatan ganewa kafin guri ya ƙure musu.

Kamar an saita Samina na fitowa daga ƙozajjen soron gidan kakanninta da Ahmad ta fara cin karo zaune bisa ɗan dandamalin dakalin dake ƙofar gidan maƙwafcinsu.
Ta tsaya tsam tana ƙarema kwalliyarsa kallo, tabbas Ahmad ƙyaƙykyawane, shiyyasa duk rashin tsadar kaya sukan zauna masa a ƙyaƙyƙyawar surarsa suyi ɗas.
Ba wani kayane mai tsada a jikinsaba, hularsa ƙube da ita kaɗai ta iya saninsa dashi ta ƙarshen gayunsa ya saka, ta zauna ɗas akansa, inda daga bayan ƙeyarsa kwantacciyar sumarsa ta jinin fulanin rumawan asalin katsinawa ta bayyana, sai yadi mai ƙarancin kuɗi mai kama dana ƴan makaranta kalar ruwan shanshan bale, takalmansa ƴan saƙe suma masu ƙarancin kuɗi, sai agogon fatar da itace ta saya masashi naira ɗari huɗu ɗaure a hannunsa da zoben azurfa a yatsansa, kayan sun ɗauki guga, dan haka suka kwanta luff tare da ɓoyewar tsufan da suka fara a idon mai kallonsa, ƙamshin turarensa yake mai ƙarancin kuɗi, amma akwai daɗi ga hancin mai shaƙa.
Ganinta ya sakashi miƙewa yana ƙawata nutsatstsiyar fuskarsa da murmushi na musamman.
“Barka da fitowa tauraruwar mata ma'abociyar haske da walwali�?.
Samina ta kallesa a wani yatsine tana cuna baki gaba, ba tare data amsa masa kalmomin yabonsa ba ta maida murtani da faɗin, “Kai yaya, dama zakazo ɗin amma kaki kirana ka sanarmin kuma? Gashi nacema su Nafy su jirani a gidansu saimu tafi tare�?.
Murmushi yaɗanyi duk da yanda tai masan ya bashi mamaki, “Yi haƙuri Samie na, banzo danna hanaki ƙyautata zaman tareba, nazone dama na kaiki basai kinsha wahalar jiran abin hawaba�?.
Yanzu kam sosai ta juyi ta kallesa, cikin waro masa manyan idanunta tace, “Ka kaini kuma yah Ahmad? Da wane motan?�?.
Huci yaɗan fidda mai ɗaci, dan ta fara ƙokarin janyo fusatarsa da wannan salon rainin wayon data ɗakko, amma kasancewarsa sonta na ɗawainiya dashi saiya sauke numfashi da ƙokarin hadiye dukkan fusatar tasa ya saki murmushi a karo na babu adadi.
“Banda abunki Samina ina naga mota, wannanma mashin ɗin Sufiyanu ne na aro danna sauƙaƙa miki wahala�?.
“Tofa, to ALLAH yay mana maganinta ita wahalar, karka damu na hutar dakai, kaje kawai zamu tafine dasu Nafyn tunda kaga na musu alƙawarin binsu dan ALLAH�?.
Wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi, sam baya ƙaunar alakar Samina da su Nafyn gidan ɗan-majillisa, amma ya kula yanzu dukkan hankalinta yana ga mu'amulantarsu. Ganin zata tafi yay saurin tsaidata ta hanyar faɗin,
“Okey to babu damuwa tunda kin samu abokan tafiya, ga wannan kozaki buƙaci wani abu a wajen�?.
Har tayi niyyar wucewarta saita dawo baya jin ya ambaci kuɗi, babu kunya tazo ta amshe kuɗin dayake miƙomata canzazzu ƴan hamsin-hamsin rabin bandir ɗaya.
Godiya tai masa cikin ladabi, ta tura kuɗin a jakarta tare da sakar masa murmushi duk dan dai hankalinsa ya kwanta da barinta ta wuce ita kaɗai.
Ta ɗaga masa yatsun hannunta guda biyu alamar bye cike da wani salo.

Da kallo kawai ya iya binta tamkar wani soko, ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya yana nufar roba-roba mashin ɗin dayazo dashi kalar jaa, hawa kawai yay ya zauna yana kallonta harta ɓacema ganinsa, yanda take tafiyarta cikin yauƙi da yanga sai sonta ya kuma nunkuwa a ransa, yanason Samina so irin mai tsanani ɗinnan, dankuwa dashi ya girma a zuciya tun baima gama sanin ma'anar SO ɗinba.
Ya ɗauki kusan mintuna talatin a wajen kafin ya hau mashin ɗin yabar anguwar da tunanin ina ya dace ace yaje, dan shidai a yanzu ya koma majalisar abokansa dariya zasuyi masa, yanda ya fito yana ɓare-ɓaren jiki zaije yakai Samina, sai gashi Samina ta watsa masa ƙasa a ido, bayan kuma dama kullum abokansa na nuna masa yanzu Samina ta canja, ta fara fin ƙarfinsa amma sam yaƙi fahimtarsu balle ya yarda da batunsu.
Yawo yaytayi a gari, sai da ya fahimci man ciki yayi ƙasa kafin ya koma gida.
Ya iske abokansa na hada-hadar shiga sallar magriba a massallaci, dan haka shima yay haramar yin alwala domin samun jam'i.
Bayan an idar duk suka fito ɗai-ɗai zuwa majalisarsu da suka kafa a ƙofar gidan su Yakubu abokinsu, saboda baranda dake wajen, shikuma yakubu yanada shagon littatafan hausane da yake bada rancin da saidawa.
Hannu suka shiga bama juna suna gaisuwa, Ahmad ya miƙama Sufyanu key ɗin mashin ɗin yana faɗin, “Broth nagode, ALLAH ya bada ladan zuminci�?.
Amin suka faɗa a tare, yayinda Sufiyanu dake amsar key ɗin ke faɗin Sharukhan ɗinmu nazata fa sai dare zamu ganka ALLAH, Amma kunyi saurin dawowa kaida gimbiyar taka�?.
Murmushin yaƙe Ahmad yayi kawai, ya kishingiɗa kusa da Musa yana bama Sufiyanu amsa da, “Ai ba yaune ainahin bikinba fa, kamu sukayi yau shiyyasa, sai jibinema ɗaurin auren, kasan mata da shegen son bidi'a, shiyyasa a kullum ake ƙara nisanta talaka da samun aure cikin sauƙi�?.
Cikin damuwa Rabilu yace, “Maganarka gaskiyane wlhy Ahmad, ba gamunanba, acikinmu nan wanene bai isa aurenba, kuma duk munada ƴammata amma babu kuɗin yin auren, to wai muma fa kenan dakeda sana'oi munkuma ɗanyi karatun, inaga waɗanda basuda sana'ar babu karatun kumafa�?.
Salisu daya zabga tagumi ya wani marairaice fuska yana harɗe kafafunsa dake lilo a ƙasan benci, “Abokai wlhy bidi'oin biki suna taka rawar gani wajen ɗora mata a burin auren mai hannu da shuni, tana kuma jefa rayuwarsu a garari harma da ƙara yawaitar fyaɗe, yanzu irina masu ƙarfin sha'awa idan baka danne zuciyarkaba ai tuni zaka afkama ƴar wani ka jefa kanka a halaka da ƴan uwanka a damuwa ko�?.
Lumshe idanu Ahmad yayi a hankali, dan maganar Salisu ta sosa masa inda ke masa ƙaikayi, yace “Uhumm�? kawai ba tare da ya ƙara komaiba.
Hakane ya saka Sufiyanu da Yakubu dake kusa dashi kallonsa.
“Sharukhan yaya dai?�?.
Ameenu da tun ɗazun baice komaiba ya faɗa yana kallon Ahmad ɗin shima.
Buɗe ido Ahmad yay da suka canja launi zuwa jaa, yay murmushi kawai yana girgiza kansa.
Hakanne yasaka su cigaba da hirarsu akan matsalolin aure da burikan da mazan da ƴammata ke dorawa saboda son gasa da masu kuɗi keyi lokacin bikinsu.

Sallar isha'ice ta tadasu a majalissar, dukansu suka dunguma zuwa massalaci, akabar waɗanda zasu sake alwala irinsu Ahmad.
Bayan sun idar da salla zama sukai islamiyyar da suka tsarama kansu kamar yadda suka saba a kowanne dare, malam Sulaiman ne malaminsu, wato limamin massalacin, bayan ƙarin karatu yay musu nasiha kamar yanda ya saba.
Ƙarfe tara da rabi dai-dai suka fito, kowa daga nan gida ya shiga domin cin abinci.

Tsakanin gidansu Ahmad da majalissarsu gida biyar ne, hakan yasakashi takawa a hankali suna tafiya shida Salisu da shima gidansu ke maƙwaftaka da nasu Ahmad, suna isowa kowa ya shige.

Gidansu Ahmad gidane na talakawa irin masu ƙaramin ƙarfinnan sosai kamar yanda kukaji tun a farkon labarin, ginine irin na zamanin daya shuɗe, duk da dai yana mulmule da suminti har jikin bango, amma kallo ɗaya zakaima gidan ka fahimci ingantaccen ginin daya samune yasaka sumintin daɗewa bai zabtareba, saika shiga soro biyu kafin ka iso ainahin tsakar gidansu, amma a shiga farkon gidan zakaci karo da turken awakine da mahaifansu mata ke kiwo, sai kejin kaji daga gefe wanda baida nisa sosai da ƙofar banɗakinsu.
A shiga farkon gidan ɗakunan kakanninsu da aka zagaye da katanga zaka fara iskewa, sai sashen Baba Iliyasu daga bangon gabas, sai sashen Baba Yusha'u mahaifin Samina daga can Bangon arewa, suna kallon sashin kakanninsu, sai sashen iyayen Ahmad a bangon yamma suna kallon sashensu baba Iliyasu.
Tsakar gida zaka fara tararwa, sannan kabi siririyar hanyar da zata sadaka da ainahin sashen da matan Baba Hamza mahaifin su Ahmad suke.
Ya shafa kan tunkiyar daketa ɓara kuka saboda rashin ganin ɗanta kusa da ita, “K dan ALLAH ki rage ihunan, tunkiyarnan sam baki da hankali akan ƴaƴa, inama ya shiga shima uban ɓarnar�? Ahmad ya ƙare maganar yana leƙa ƙasan kejin kajinsu kozai gano ɗan jaririn ragon tunkiyar.
Can kuwa ya hangoshi kwance, dan haka yasa hannu ya zaƙulosa ya kai gabanta ya ajiye kafin ya shige ainahin cikin gidan da sallama.
Mahaifiyarsa da ƴar kunya ke tsakaninsu saboda shine na fari a gabanta ya fara cin karo tana ɗibar ruwa a tulun dake ƙasan barandar ɗakunansu cikin kofin silba.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tamkar batama gansaba, sai ƙannensa dake zaune a tabarma da fitila a gabansu sun baza littatafaine suka amsa masa, sai kuma Ayyah matar babansu ta farko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login