Showing 81001 words to 84000 words out of 165545 words
daɗe yana bani mamaki, da safe koda na gaisheta ƙin amsani tayi, nasan ban mata komaiba dan haka na watsar da lamarinta, ita dai hassada ga mai rabo ai takice.
Ita dayake Maman Ama tafita bariki da wayo sai bata nuna ko a fuskaba, amma abun na sassakar mata rai sosai, da tanada dama saita kaɓe shegiyar wayar waran a ƙasa ta kwararratse muga tsiya.
_______________________________
A sati ukun nan da Samina ta ɗauka a gidan Ma'aruff komai ya gama susuce mata, soyayyar da take tunani yay mata tanadi ko alamarta ba gani takeba, ashe Ma'aruff riƙaƙƙen ɗan giyane, sannan kullum dare sai ya fita ta rasa ina yake zuwa?.
Karfe taran dare nayi zai fice daga gidan, bazai dawo ba sai ɗaya, wani lokacinma ɗayan ta wuce yake shigowa, lokuta da dama kuma cikin mayen giyane, yazo yayta mata amai mai wari, yakumace saita gyara, idan tai masa gaddama ya kusanceta da ƙarfin ƙwanji na tsantsar mugunta ya lakaɗa mata duka dole tayi tana kuka.
Idan gari ya waye kuwa yayta bata haƙuri akan shi baisan yayiba, zata zauna tai masa nasiha yay shiru kamar ya ɗauka, cikin kulawar juna zata taimaka masa ya shirya ya wuce office, idan ya dawoma zaka gansa normal, har ya nuna mata ƴar kulawa suyi ɗan soyayyarsu idan yanada buƙatarta ya sauke nauyi, amma taran dare nayi duk wayon dazai mata yabar gidan ya sanshi.
Gaba ɗaya ta rasa a ina matsalar take?, ga mahaifiyarsa ƙiri-ƙiri take nuna bata sonta, hakama ƙannensa, sauƙinta ɗaya sunajin shakkarsa kuma ba zuwa gidanma sukeba sai idan ta kama dole.
Amarya nayin ƙiba itadai rama tayi, sai wani haske take ƙirjinta ya cika yay fam, ga shegen kwaɗayi dake yawan damunta, sauƙinta ma idan tace ya sayo mata abu yakan sayo, sannan bai rageta a ci da shaba ta kowanne fanni, jin daɗi da kayan more rayuwa na cikin gida komai bata rasaba, dolene idan kazo gidanta ka kirata mai sa'a, sai dai matsalar tanaga farin ciki, dan kuwa kaso ɗaya bisa uku kawai take samu, shima wani lokacin batama samun.
Ƙawayenta fa kullum cikin zuwa suke ganin ɗakin amarya kashi-kashi, kowacce tanaji inama itace cikin wannan daular.
Idan suna ma kansu addu'ar samun ya tata saitai ta kallonsu kawai, dan kuwa kallon kitse sukema rogo.
Ƙannenta ma suna zuwa, hakama dangin mama gaje da ƙawayenta, sauran yaran gidansune dai har yau bataga ƙeyar kowaba, hatta da yayarta binta da suke ciki ɗaya batazo mataba.
A koda yaushe mama gaje da inna mari cikin aiko mata da kayan mata da ƴan ƙulle-ƙullensu na wurin malamai suke, kuma duk tana ƙoƙarin yi, amma ta kula Ma'aruff shegen taurin zuciyane dashi, wani lokacin idan tai wani abu sai taga kamar ya kamashi idan yana kwantar mata da kai, har sai ta fara murna sai kuma komai yazo ya burkuce.
Babu abinda ke ɗaga hankalinta irin shan giyar da yakeyi, ta tsani warinta, ga aman da yake mata mai azabar wari, har kasa cin abinci take idan ta tunosa.
Yau ma dai haka ta tashi batajin daɗin jikinta sosai, ta daure da ƙyar ta haɗa masa breakfast duk dan ta sakashi farin ciki, ga kuma maganin da inna Mari tace ta zuba masa wai zai ƙara lalacewa a kanta, duk dai tayi yanda akace tazo ta jere abincin a dani.
Da taimakon dattijuwar mai aikinta ta gyara gidan, dayake ba anan take kwanaba, zatazo da safe ne da yamma sai ta koma gida.
Hakanne ya ƙara kawoma Samina rufin asiri har yanzu babu wanda yasan halin da take ciki na ƙunci game da halayen Ma'aruff, danta daure ko mama gaje bata sanarma ba har yanzu.
Wanka taje tayi tai ƴar kwalliya dan sam batajinta dai-dai, dama dai tunma tana gida ba isashshiyar lafiyarne da itaba, tana daurewane kawai a zatonta zirga-zirgan bikine, to yau dai sosai takejin ciwon a jikinta.
Ɗakin Ma'aruff ta shiga, yana kwance cikin bargo yana kwasar barcin da giya ta haddasa masa, tunda tazo gidan kullum sai ta tashesa da safene yakeyin sallar asuba, to sanda ake sallar shi hankalinsa bai gama dawowa jikinsa ba ta ina zaiyita?.
Yanzunma da ƙyar ta iya tadashi dan kar yayi lattin Office, ya tashi yana mata masifa, da yake harta fara sabawa sai batace komaiba ta taimaka masan dai har bayi inda ta haɗa masa ruwan wanka.
Bayan ya shiga dawowa tai da nufin ta gyara masa ɗakin kamar yanda ta saba amma sai hakan ya gagara saboda jiri dake kwasarta, dole ta duƙa gaban gadon ta kifa kanta kan gadon.
A wannan yanayi Ma'aruff ya fito ya Sameta, kamar zai shareta sai kuma ya matso yana yarfa mata ruwan hannunsa, “K lafiyarki kuwa? Kina zaman miye da baki gyara ɗakinba? kinsa na fito inata taka datti�?.
Samina bata iya bashi amsaba, bakuma ta ɗago ta kallesa ba, shima saiya watsar da ita yay haramar yin sallar asuba, lokacin takwas ma fa ta wuce🤦🏻♀.
Yana cikin yin sallarne Samina tai baya yaraf ta faɗi.
Saurin idarwa yay ya matso yana taɓata, jin ta suma sai abun ya bashi mamaki, ya shiga kiran sunanta yana murza tafin hannunta, amma ina ko motsi bataiba, ruwa ya tashi ya ɗebo a gaggayce ya yayyafa mata, sai lokacin ta kawo numfashi, “Lafiyarki kuwa? Miya sumar dake haka?�?.
Da ƙyar Samina ta buɗe baki tace, “Sweet banda lafiya wlhy�?.
Hannu ya aza bisa wuyanta, yaji zafi sosai, “Tabbas ga jikinki da ɗumi ma, ni saima yanzu na lura kin rame da yawafa, baƙya cin abince halan?�?.
Murmushi kawai Samina tayi tana haɗiye kukan da yake shirin taho mata, shi tunaninsa abincine ke kawo ƙiba kawai babu kwanciyar hankali?.
“Kinmin shiru ina miki magana?�?.
Kallonsa tayi, sai kuma tayi murmushi tana girgiza masa kai, “Inaci mana�?.
“Shikenan bara na shirya muje asibiti, idan kuma bazaki iyaba bara na kira Adam ya dubaki kawai�?.
“Ka kirashi ɗin to kawai�?.
Kamata yay ta koma saman gado ta kwanta, shikuma ya ɗakko wayarsa ya kira abokinsa Adam daya kasance likita.
Kafin Adam yazo ya gama shirinsa na fita, a ɗakin ya barta yaje yaci abincin data shirya a dani ɗin, yana tsaka dacin abincinne Adam ya iso.
Bayan sun gaisa ne yayma Adam ɗin tayin abincin amma sai yace yayi breakfast shi.
Umarnin shiga ɗakinsa kawai ya bashi yaje Samina na can, babu wani alamar nuna kishi koda a fuskarsa, cigaba ma yay dacin abincinsa hankali kwance Adam kuma ya shige ɗakinsa.
Samina na kwance Adam ya shigo mata saƙaƙa babuko sallama, wannan abu ya sosa mata rai, ta kumaji zafin Ma'aruff, domin dai ya nuna bama ya kishinta matsayinta na matarsa ta sunna, tsabar takaici ma saiga Adam zaune ɗane-ɗane a bakin gadon da take kwance, sirrinsu kuma dukda bata taɓa kwana a kansa ta daɗin raiba.
Haushin hakanne ya sakata ita ta sauka ƙasa, amma ko a fuska Adam bai nuna ya damuba, saima tsokanarta da cewar “Amaryarmu kinsha ƙamshi�?.
Murmushin yaƙe kawai tai masa.
Tambayoyi ya shiga mata, yanda take bashi amsane ya sakashi kafeta da idanu, daga ƙarshe ya bata tsinken gwajin ciki yace taje tayi.
Bata musaba taje tayo yanda yace, ta fitone ta iske Ma'aruff ya shigo, yana zaune kusa da Adam suna magana, sai dai ta lura kamar Ma'aruff ɗin a rikice yake, tsinken ta miƙama Adam ta koma kan sofa ta kwanta.......
“My friend da gaske fa akwai cikin nan�?.
Wata zabura Ma'aruff yayi yana faɗin, “Kai bazai yuwuba Adam, duka yaushe akai aurenma da za'ace ta ɗauki ciki?�?.
“Kaga Calm down Please, bara na ɗiba jininta yanzu zanje na dawo�?.
Ma'aruff baice komai Adam ya ɗiba jinin Samina da suka ɗaure mata kai tama kasa cewa komai balle tunanin inda suka dosa.
Tunda Adam ya tafi Ma'aruff ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai kai kawo yake a ɗakin, ita Samina ma barci ya kwasheta a wajen.
Ba jimawa kuwa sai ga Adam ya dawo, tun a yanda Ma'aruff yaga fuskar Adam ɗin ya tabbatar akwai dai cikin.
Adam ya miƙa masa result ɗin, jikinsa har ɓari yake wajen amsa ya duba.
Takardar ya jefar a tsawace yace, “Impossible Adam, cikin wata biyufa!!?�?.
Yanda yay maganar a tsawace ne ya farkar da Samina mai barci, a kunnenta yake faɗin,
“Ai koda cikinnan a gidan nan ta samesa ba'a wajeba wlhy ban shirya haihuwa yanzuba ballema ɗan shege, dolene a zubar dashi yanzun nan�?.
Sosai Samina ta ƙwalalo idanu waje, “Sweet wace irin maganace wannan haka kakeyi? Ni dai to baza'a zubarmin da cikiba inason kayana, tayaya za'ai mu ɗauki laifi biyu bayan na zina kuma ga kisan kai?�?.
Harara ya maka mata yana sake harzuƙowa kamar zai maketa, “Ke dabbar inace da baki fahimtar abinda muke faɗa?, kina tunanin zan bari ki haifa mana ɗan shege ne a cikin zuri'armu ki gurɓatata? To idanma barci kike ki farka wlhy, ɗan halak ɗinma ban shirya amsaba balle na shege, inhar wannan cikin nawane bawani daban yayisaba dolene a zubar dashi....?�?
Da sauri Samina ta katsesa da faɗin, “Kamarya ba wani yayisaba? Bayan kai na taɓa mu'amula da wanine?�?.
“Ubanwama yasani ko kin taɓayi ballagaza, tunda har kika iya bani wanima zaki iya bashi ai, ciki dai ko uwarki mai kwaɗayinan tazo nan bata isa hanashi yabi sokawe ba yau dinnan�?.
Hawaye masu ɗumi suka shiga bin kumatun Samina, ta nuna Ma'aruff itama tace, “Wlhy sai dai uwarka mai baƙar zuciya......�?
Jikake “Tatasss!!�? saukar lafiyayyen mari a kumatun Samina, ta dafe kuncin tana sake fashewa da kuka.
Adam dake kallonsu yay saurin riƙe Ma'aruff dake zaro belt ɗin wandonsa.
“Kaga ku nutsu dan ALLAH karka taɓata�?.
“Adam in bartafa kace?, wannan karuwar gidance har ta isa ta zagarmin uwa dan ubanta?�?.
“Nasan batai dai-daiba, amma dan ALLAH ka barta muyi kawai abinda ya dace, kekuma tunda yace bayason cikin kibari kawai a zubar dan ALLAH a zauna lafiya, lokacin daya shirya na tabbata bazai hana ki haihu ɗinba.......�?
“Dawa zan haihu? Bar wannan saɓon dan ALLAH Adam, ai babu tsarin haɗa zuri'a da wannan ballagazar yarinyar a daga gareni, haka kawai a haifamin ƴaƴa masu bin maza, saboda ƙwaɗayifa tabar saurayin daya gama mata wahalar duniya kuma ɗan uwanta, tokai ta yaya zanyi fatan tazama uwar ƴaƴana a haifamin fanɗararru waɗanda idan nace ga yanda nakeso suce bazasuyiba, saboda haka uwarsu taima ubanta itams�?.
“Ya isa haka dan ALLAH, haba MJ�?.
Shiru Ma'aruff yay yana ƙwafa, ya nuna Samina dake kuka rurus saboda baƙaƙen maganar daya jefa mata yana faɗin, “Garama ki tsaya da arziƙi, dan wlhy inba hakaba dukan mutuwa zan miki kuma a zubar da cikin�?.
“Sai dai ka kasheni, amma bazan yarda a zubarmin da cikib......�?
Maruka biyu ya sauke mata a lokaci ɗaya, nanma sai da Adam ya riƙeshi yana bashi haƙuri sannan.
Adam ya haɗa allurar dazai mata, Samina naji na gani Ma'aruff ya matseta Adam ya danna mata allurar zubda ciki, tana wani kuka mai tsuma ran mai saurare.
Mintuna sha biyar kacal dayin allurarnan jini yaɓalle kuwa.
Tun tana sanin halin da take ciki har ta rasa jinta da ganinta baki ɗaya.............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(27)*
..............Jini sosai ya ɓallema Samina, abinda ya tsorata su Ma'aruff kenan suka ɗauketa zuwa asibiti, gaggawar fara ƙoƙarin shawo matsalar Aliyu ya farayi, da ƙyar aka samu komai ya dai-daita bayan baƙar wahalar da yasha.
Ma'aruff sai jan tagwayen tsaki yakeyi, ya kasa zaune ya kasa tsaye har sai da Adam ya fito sannan.
Kwantar masa da hankali yayi akan an samu dai-daiton komai, yanzu haka zasu kai Samina ɗakin hutune.
Numfashi ya sauke a hankali, sai lokacinne ya tuna da batun aikinsa, waya ya ciro yay kira Mama gaje ya sanar mata akan tazo asibitin ta samesu.
Hankalinta ya tashi sosai, da yake batasan ina zata gano asibitinba saboda private ne sai ta tasa ƙanin Rumana gaba Kamalu suka tafi dan ya rakata, bata sanarma kowaba saboda a ƙofar gida ta gamu da Kamalun ta iza ƙeyarsa suka tafi.
Koda suka iso suna gaisawa da Ma'aruff ya kaita ɗakin da aka kai Samina sai yay mata bayanin ɓari Samina tayi, daga haka yay musu sallama ya tafi akan shi zaije Office ne saiya dawo.
Yanda Samina ta rame ya tadama mama gaje hankali, amma data tuna ɓari akace tayi saita danganta ramar da kwaikwan ciki, sai dai a ƙasan ranta tana mamakin miyasa Samina bata taɓa sanar mata ta samu cikiba koda wasa? Yanzu kuma auren sati uku ne har an samu cikin da zai iya zubewa?.
Batai zurfi a wannan tunaninba ta watsar da shi gefe kawai ta ɗakko wani.
Kamalu shine ya koma gida ya sanar musu Samina na asibiti babu lafiya, kowa yasha mamaki, amma da yake ba biyema shirmen mama gaje sukeba sai sukai shirin zuwa su dubata.
Yayinda yaran gidan suka fara tafiya kaima yayyensu na ma'auri labarin.
Harsu Ayyah sukazo duba Samina asibiti tana barci bata farkaba, kowa yayi mamakin ganin ramar da Samina tayi a sati uku da aure kacal, hakama zancen ɓarewar ciki ya tsayama kowa a rai.
Ammi ce kawai data daɗe da fahimtar Samina nada shigar ciki tun tana gida abun bai bata mamakiba, sai dai tana tausayin mama gaje akan ƙarancin rashin kulawa da saka idanu akan yaranta.
Basu baro asibitinba sai gab da magriba, har zuwa lokacin kuma babu ko ɗaya daga dangin mijin Samina daya leƙo, shima kansa Ma'aruff ɗin bai dawo ba, sai Inna mari da Iya da sukaje, sai ko dangi ɗai-ɗai irin na kusa da labarin yaje musu suma suka ɗan lalleƙo.
Har zuwa lokacin kuma Samina nata barci bata farkaba, su dai sallama sukai musu suka taho akan sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan malaman asibitin sun fara maganar sunyi yawa, da sun tsaya har sai Saminar ta farka suma.
Bayan dawowarsu gidane suma su Baba suka tafi duba Saminar, sun isa babu jimawa ne ta farfaɗo.
Da ihu da fisge-fisge Samina ta farka, sai ambatar sunan Ma'aruff take akan itafa tanason cikinta karsu zubar mata, babu wanda bai shiga ruɗaniba, su sam sunma kasa fahimtar mi Samina ke faɗa.
Dr Adam yace duk su fita daga ɗakin Please.
A daidai wannan lokacinne kuma Ma'aruff ya dawo, daka gansa zaka san hankalinsa kwance, kuma daga gida yake, dan bakayan ɗazun da safe banema a jikinsa, babu tausayi ya wankama Samina dake cikin halin rashin sanin mi takeyi mari,