Showing 90001 words to 93000 words out of 165545 words
Yaune karan farko da zai shigo cikin gidan har ma falonsu, tsararren falone da yaji kayan more rayuwa, dama ya daɗe yana hasashen hakan kuwa.
Iyayen gidan nasa na zaune fuska ɗauke da murmushi, zai zauna a ƙasa sukace ya hau kujera, bai musaba kuwa ya hau ya zauna, yanda suke jera masa godiya tamkar ya musu wani gagarumin abu sai mamaki ya kamashi.
Miye na wani godiya akan Assignment kawai da yayma ƴarsu? Shida suka bashi wajen kwanafa, sannan suke biyansa duk ƙarshen wata dukda aikin nasa iya darene kawai.
Dad ɗin Happy yace, miya karanta ne?.
Ahmad ya faɗa masa.
Sosai mamaki ya sake kamasu, a take kuwa yace inhar yana bukatar aiki ya kawo takardunsa, dan kuwa ƙaninsa babbane a ma'aikatar man fetur ta NNPC zai sa ya nema masa aiki.
Sosai mamaki ya bayyana a fuskar Ahmad, a yau ya yarda da batun mutane da suke cewa Alheri danƙone baya faɗuwa ƙasa banza, sannan da gaske ƙabilun nan basu da baƙin ciki wasunsu.
Da ƙyar Ahmad ya haɗiye yawu yana jinjina kansa, yace, “Mizai hana inhar babu damuwa nanda sati ɗaya yaje ya kawo dan suna gida�?.
Dad ɗin Happy yace babu wata damuwa zai iya zuwa ya kawo, koda nanda sati biyune, sai dai karya wuce hakan.
Godiya sosai Ahmad ya shiga yi musu, sukam sukace karya damu, tunda baiyi baƙin cikin taimakon ƴarsu ba su mizaisa suyi baƙin cikin taimaka masa.
Farin cikin da Ahmad ya tsinci kansa a wannan rana faɗinsa ɓata lokacine, a daren ya kira Nura ya sanar masa, sosai Nura ya tayashi murna da tabbatar masa lallai shikam yazo Porthercout da ƙafar dama.
Tun a washe gari kuwa Ahmad ya fara shiri, dan so yake ya wuce gida nanda kwana biyu, kodan yaje ya samu damar tattara takardunsa waje ɗaya ya juyo da wuri.............✍�?
*_Afuwan! Afuwan!! Afuwan Please, kunjini shiru kwana biyu, kusan jiki da jini an binciko file ɗinane, amma Alhmdllh lafiya ta samu, inama kowa fatan alkairi🥰🥰🥰🥰🙏🏻_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
a: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*_GDW_*
*(29)*
..............Wannan karon ma bai sanarma kowa zuwansa ba, harma baban baisan da zuwan Ahmad ba.
Cikin amincin ALLAH wannan tafiyar da yake tafiyar wuri sukayo sai gasu kusan sha biyu sun sauka.
Yau ɗinma dai gidansu ya fara sauka, ba ƙaramin bazata yay musu ba, yara nata murnar ganinsa, hakama su Ayyah ɗin kansu.
Bayan ya gaggaisa da jama'a Ayyah ta korashi akan yaje gida ya huta, bai musaba kam, dan dama cike yake da zumuɗin son ganin ƴar matarsa, anan ya bar musu tsarabarsu ya ɗauki iya kayansa da tsarabar Rumana ya tafi.
Umm-Rumana kam haka kawai yau bayan tashinsu barcin safe ta tashi da ƙulafucin son cin alala, wakenta ta gyara ta bama Ahmad ya kai mata markaɗe nan makwaftansu, dayake fa'iza sun wuce gida tun ɗazun, yanzu akwai wajen koyan saƙa da suke zuwa sai lokacin islamiyya suke tasowa su biyoma Rumana, duk da yanzu wataranma ita da kanta take cewa bazata jeba batajin daɗi.
Sai da ta kammala ƙulla alalan ta ɗora a wuta sannan ta share ɗakin ta wuce wanka, shigarta babu jimawa Ahmad ya shigo gidan.
Kawai muryarsa ta jiyo yana amsawa maman Ama dake masa sannu da zuwa, cikin mamaki a zuciyarta take faɗin, “Da gaske yaya Ahmad ko dai kunne nane baiji da ƙyau ba?�?.
Sake jiyo muryarsa tai yana ma yaran da suka shigo masa da kaya godiya.
Mamaki ya kuma kamata da wannan bazata tashi, kofa daren jiya sunyi waya, ita kuma sam bataji alamun tafiyar motaba.
Haka dai ta kammala wankanta ta fito tana tunane-tunane da mamakinsa. Da takalmansa ruwan makuba dake ajiye ƙofar ɗakin ta fara cin karo, maman Ama ta fito daga kicin tana faɗin, “Ohni amarya an iya sema ƙunshe dai? To barka ƴan tafiya an sauka lafiya�?.
Murmushi kawai nai mata ina amsawa da ngd, dan nasan ko bayanin bansan da zuwansaba nima nai mata ba fahimtata zataiba, alwala na ɗaura sannan na shiga ɗakin da sallama.
Yah Ahmad dake kwance bisa gado yayi filo da hannayensa ƙafafunsa duka a ƙasa ya ɗan ɗago ido yana kallonta.
Canji ya sake gani a jikin ƙanwar tasa na musamman fiye da waccan dawowar da yayi.
Rumana dake ɗan sisinne kan kuwa tace, “Sannu da zuwa Yayanmu�?.
Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai idonsa a kanta ko ƙyaftawa bayayi, saurin riƙe hijjab ɗin da take ƙoƙarin sakawa yayi saboda daga ita sai ɗaurin ƙirjine da ƙaramin gyale data yafo, bata yarda ta fita tsakar gidansu daga ita sai zani, dan tasan ko yaushe wani zai iya shigowa daga sauran mazan gidan.
Manyan idanunta da suka ƙara wani haske na musamman ta ɗago tana masa kallon mamaki.
Yanda shima ya kafeta da nashi sai ta kasa jurewa tai ƙasa da nata tana murmushi.
Tsaye ya miƙe kawai ya jawota jikinsa ya rungume, a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya kowanne na sake mannema ɗan uwansa.
Ahmad da idanunsa ke a lumshe yace, “I miss you so much Babie R�?.
Murmushi Umm-Rumana tayi har yanajin hucinsa a ƙirjinsa, ta ɗago kanta a hankali ta manna masa sumba a ƙirjinsa.
Ƙankameta ya sakeyi yana sauke numfashi da kyar, dan ba ƙaramin isa saƙon Rumana yayiba a dukkan sassan jikinsa da magudanar jininsa.
Itako dauriya kawai tai wajen aikata hakan, shiyyasa tana yi ta kuma cusa kanta a jikin nasa.
Da ƙyar ta yarda ya ɗago kanta da hannayensa duka biyu, idanunsa ya fara bazawa akan fuskarta yana binta da kallon ƙurulla tamkar yaune ya fara ganinta, itako sam taƙi yarda ta kallesa.
Iska ya hura mata a fuska yay ƙasa da muryarsa tamkar mai raɗa yace, “Lallai Babie R ɗina ta girma da gaske�?.
Da sauri tace “Ni dai ban girmaba�?.
Yanda tai maganar da shagwaɓa ne ya sakashi yin murmushi, ya matsar da bakinsa saitin kunnenta, a hankaki ya furta, “Tunda kika iya ɗaukar nauyin Amadin Ayyah ai kin gama girma�?.
Saurin ƙanƙamesa tai saboda girman maganar tasa da sanin inda ta dosa.
Aiko Ahmad ya ƙyalƙyale da dariya shima yana rungumetan da ƙyau.
Itama dai murmushi taketa zubawa tana jin ƙaunarsa mai zafi na ƙara tasiri a ranta.......
Daga waje maman Ama ta katsesu da fadin, “Amarya abincinki fa na ƙauri�?.
Da ƙyar suka iya rabuwa da jikin juna, ta ɗauki hijjab ɗin daya hanata sakawa ta saka ta fice domin duba abincin.
Babuma wani ƙaurin kirki da yakeyi, tsabar kutsugune irin na maman Ama, dan ruwan data tsumbula ledojin alalarne yake kumfa yana tasowa da ɗiga a rishoɗin, shinefa yake ɗan hayaƙi, hayakin kuma na ƙauri.
Buɗe murfin tai ta duba, ganinma alalar tayi sai kawai ta sauke ta ɗora man da zata soya, ɗakin ta koma ta kaima Ahmad ruwan sha sannan ta dawo ta tsame alalar ta kashe risho ɗin.
Ba tare da ta shiga ɗakinba ta ɗaga labulen ta ɗan leƙa kanta, “Yaya azuba ruwan wanka?�?.
Ahmad ya ajiye ruwan da yasha yana ɗaga mata kai alamar eh.
Sai da takai masa har bayi sannan ta dawo ta sake leƙawa danta sanar masa ta kai ruwan, hannunta kawai yaja ta faɗa ɗakin sosai.
“Wannan dojewar ai nasan inda ta dosa, oya maza cire min kaya, infa ba'a tarairayata kamar ƙwai a cokali kayana zan ƙulle na koma....�?
“Da gaske?�? Rumana ta faɗa cikin waro masa idanu waje.
Hancinta yaja kaɗan yana murmushi da faɗin, “Mizai hana ƴar ƙyaƙyƙyawa ta�?.
Umm-Ruman tai murmushi tana ƙoƙarin cire masa maɓallin shirt din jikinsa, duk yanda yaso haka tai masa, da taimakonta ya cire komai, ta barsa da kayan ciki kawai ta koma ƙoƙarin ɗakko masa jallabiyya a drawer.
Ta juyo zata bashi ya wani tsareta jikin drawer ɗin yana bata fuska, “Kai gidan hayama bai yiba, a yanda na gajinnan wankanma buƙatar aimun nakeyi�?.
Rumana ta ɗora hannunta kan baki tana murmushi.
“Oh dariya ma kikemin ko? Aiko zan manta da kowa kuwa muje dole kiyim ɗin�?.
Sosai ta kwalalo idanu tana faɗin, “Yaya rufamin asiri, aiko to har gidanmu sai matan gidannan sun kai gulma�?.
Ƙaramin tsaki yayi yana amsar rigar da cewa, “Sun daɗe basu kaiba masu kawunan talo-talo�?.
Ita dai Umm-Ruman dariya tayi, shikuma ya fita domin yin wankan.
Dole taje ta sake yo alwala ta dawo ɗaki, aiko sake alwalar nan ba ƙaramin tsone idon maman Ama tayi ba, harda jan tsakinta tana faɗin, “Iya nan kukafi afana daga ke har lusarin mijin naki da baya amfana miki komai�?.
Nace, “Oh su maman Ama problem😹🌚�?.
Koda Umm-Ruman da batasan maman Ama nayiba ta koma ɗaki sai tai azamar fiddo kaya ta saka kafin ya fito, ta shafa mai ta ɗan murza fauda da kwalli harda janbaki kaɗan sannan ta saka turare ta tada salla.
Tana cikin sallar ne Ahmad ya fito, shima botikin ya ajiye ya ɗauka butar data ajiye masa yay alwalar sannan ya shigo.
An riga an idar da salla a massallaci, dan haka yay ƙokarin gabatarwa a ɗakin, lokacin Rumana ta idar sai ta bashi abin sallar ita kuma ta miƙe domin shirya masa abinci.
Yana idar da sallar mai yaɗan shafa ya saka wando iyakar gwiwa da t-shirt mara nauyi mai guntun hannu, zama yay inda ta shirya abincin, da mamaki yake kallon Alalar da keta tashin ƙamshi, yanda yakeson alala yasan duk wanda yay tarraya dashi zaisan haka balle ita da suka tashi a gida ɗaya.
Kallonta yay, “Babie anya bakisan zan dawoba kuwa?�?.
Murmushi Rumana tayi da faɗin, “Yaya baka sanarmin ba yaya zan sani? Amma miyasa kamin wannan tambayar?�?.
Ba tare da yayi magana ba ya nuna mata alalar.
“Nayine kawai saboda na tashi da sha'awar cinta ALLAH�?.
Idanu ya lumshe ya buɗe a kanta, yace, “Hakan ya sake tabbatar min zuciyoyinmu suna fahimtar yaren juna koda basa a ƙarƙashin inuwa ɗaya Ruman�?.
Sosai kalamansa sukai mata daɗi, ta duƙar dakai tana murmushi, shiko ya fara cin abincinsa dake masa tsagwaron daɗi.
Sai da yay lauma kusan biyar sannan ya kai ta shidan bakinta, ta kallesa shi kuma ya ɗaga mata gira alamar ta amsa.
Babu musu ta buɗe bakin ya saka mata, a haka suka cigaba dacin alalar yanaci yana bata har saida sukayi nak sannan, ita tama rigasa ƙoshi.
Taji daɗin yanda yaci sosai kuwa, ya fita ya kuskuro bakinsa yazo ya haye gado yana fadin, “Bara naɗan rage barci kafin la'asar�?.
“A tashi lafiya yayanmu�?.
Harya rufe idanunsa ya buɗe yana kallonta, ”Bazaki tayaniba?�?.
Kanta ta girgiza alamar a'a.
Yaɗan ɗage gira sama kaɗan yana fadin, “Shikenan zan rama�?.
Ita dai Rumana Murmushi kawai tayi batace dashi komaiba, ta tattare kayan da suka gama cin abincin ta fita tsakar gida danta wanke, shiko babu jimawa barcin ya kwashesa dan dama shine fal idonsa.
Daga ita saisu Ahmad a tsakar gidan, mamansu ta fice tun ɗazun, Kausar kuwa tana ɗaki saboda yanzu tayi nauyi, gashi bata da isashiyar lafiya tunda cikin yakai watanni bakwai, yanzu ma inba sune suka lekata ba baka taɓa ganinta tsakar gidan sai alwala ko wanka ko fitsari ya fiddota dole.
Tana ciki. wanke-wanken ne Maman Ama ta shigo, tasan dai daga gidan maman Aysha take gulma, batabi takanta ba taci gaba da aikinta.
Koda ta kammala sai ta koma ɗaki abunta ta zauna tana ƙarema Ahmad dake barci cikin nutsuwa kallo, sosai ya kara canjawa, daka gansa kaga nutsatstsen matashi mai sassanyar ƙwalisa, ya kumayin haske ga ƙibar da yayi jikinsa ya kuma murjewa sosai, hakan saiya ƙara masa kwarjini sosai, ga ƙasunbar daya ajiye tun wancan zuwan ta kuma fidda sirrin kyawunsa kai kace irin ɗan yankin utopia ɗin nanne.
Ajiyar zuciya Rumana ta sauke a hankali, ta ɗauka wayarta ta cire hasken camara ɗin ta lallaɓa ta gabansa tai masa hoto, sosai kuwa hoton yayi ƙyau tamkar ba barci yakeba.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar, a kiran farko da aka ƙwala Ahmad ya buɗe idanunsa.
Barcin dai ba isarsa yayi ba, amma yaji nauyin jikinsa ya ragu Alhmdllh.
Kallon Rumana data fara gƴangƴaɗi yayi yana murmushi, daga gani bata san barcin ya figeta ba, bai tadata ba ya sauka a gadon ya fita yo alwala, sai da ya dawone ya taɓata ta tashi shikuma ya saka jallabiya ya fita masallaci.
Bayan an idar da sallar la'asar ɗinma ya jima bai shigoba, har kusan mintuna ashirin bayan sannan ya shigo.
Sannu tai masa ya amsa yana nufar drawer, kaya ya ciro wando da riga na farin yadi ya saka, ɗinkin ya masa kyau dan iyakarsa cinyarsa, gashi fitet akaima rigar, yana ƙoƙarin saka link ɗin hannun yake fadin, “Ruman bara naje na gaggaisa da mutane, idan na dawo kuma akwai labari mai daɗi�?.
Cikin zumudi Rumana tace, “Yayanmu da gaske?�?.
Sai da ya kama hannunta cikin nasa sannan yace, “Sosai ma kuwa babia na, ke dai ki tanaji goro mai daɗi da saka kunne miƙewa�?.
Tai ɗanyi walai da idanunta cikin salon jan hankaki tace, “Ka ɗauka ka samu Yaya na, mi zan dafa da dare?�?.
Matso da fuskarsa yay kusa da tata ƙasa-ƙasa yace, “Ke kaɗai kin isheni ai�?.
Da sauri ta ƙwace hannunta ta juya masa baya, yay ƴar dariya yana rungumota ta baya da mata abinda ya sake tsundumata a kunyar da tafi ta farko, ga tsigar jikinta da tai wani yarrr.
Shiɗinma ganin zai ɗakkoma kansa dala babu gammone ya sakashi sakinta yana sauke numfashi a harhaɗe ya fice da fadin, “Saina dawo�?.
“Uhum�? ta iya ce masa kawai, hakanne ya sakashi juyowa ya kalleta.
Saurin juyawa tai wani sashin, shi kuma ya fice yana murmushi mai sauti.
__________________________________
Duk da yace kartai komai bata zaunaba, ta diba ayar da take saidawa wadda ba'a soyaba ta fita ta gyara, dama tanada kayan kunun ayarta datai tanadi akan duk randa zai dawo zatai masa sai kuma ya shammaceta.
Abu taima filashin, babu jimawa kuwa ya kirata dan shima yanada ƴar jagwal dinsa, roƙonsa tai akan ya sayo mata kwakwa ƙwallo biyu idan babu tsada ya kawo mata sai ta bashi kuɗin, idan kuma da tsada ya sayo ɗayama zata isheta, sai ƙankara kuma dan ALLAH.
Kafin ta kammala gyaran ayar kuwa sai gashi, ashema yana kusa da anguwar tasu yazo sayen kayan ɗinki.