Showing 156001 words to 159000 words out of 165545 words
mazan aurensu, haka aka ɗaura auren babu wani shagalin biki sam, aka mimmiƙasu ɗakunansu tamakar auren dole.
Suka shiga gidan auren kuma kowacce tai gamo da sabuwar rayuwa mai ban tsoro, tsangwamar dangin miji data kishiyoyi, harma da rayuwar da ba'ai sabo da itaba🤦🏻♀�?.
A yanzu haka dai Ma'aruff shi kaɗaine a gidansu tamkar wani maye, ga ciwo ga kaɗaici, ga rashin abinci, wani lokacinma sai ya fita ya barato abinda zaici, sai kuma maƙwaftan da sukaga ALLAH suka tausaya masa suka kawo masa saura idan sun rage dan karsu zubar.
Haka zai amsa ya cinye tamkar wani maye, wanu lokacinma yanaci yana kuka.
Duk yawan abokansa baya ganin kowa, duk yawan ƴammatansa baya ganin kowa, ma'aikatan da ke ƙarƙashinsa baya ganin kowa, danginsu na wajen uwa dana uba da abaya suke nane dasu yanzu baya ganin kowa.
Yanzu ya sake tabbatar da lallai al'ummar wannan ƙarnin dukiya suke mutuntawa da darajawa ba ɗan adama ɗan uwansuba, idan kanada dukiya zaka taka kowa ya taku, hakama idan kanada mulki, amma daga lokacin da akace kaiba kowan kowa bane zance kuma ya ɓaci kenan, kowanma mantawa yake dakai a sha'aninsa🤦🏻♀️�?.
“Ya rabbi kasa mufi ƙarfin zukatanmu, ka rabamu da mummunar ƙaddara, ka yafe mana kurakuranmu, ka saka duniya a tafin hannunmu karka sakata a zukatanmu😭😭🙏🏻�?.
_________________________________
Kowa yabar gida gida ya barsa, wannan itace kalmar da Ahmad ya ayyana yayinda yake zuƙar iskar ƙasarsa ta Najeriya abar alfaharinsa, ƙasar da bashi da kamarta duk duniya, yana son ƙasarsa, yana kuma burin ganin ya dawo rayuwa a cikinta.
Ya shafa bayan Abu-Turab dake kwance a kafaɗarsa yana barci, tare da sake damƙe hannun Haysam dake cikin nasa.
Umm-Ruman da Zainab na biye dashi a baya, sai Abu-Talib da shima yake tare da Zainab ɗin.
Kowa yasan da dawowarsu a wannan rana, sai dai gudun karsu wahal da kansu wajen zuwa tarbarsune ya saka Ahmad yin gum da bakinsa bai faɗi ainahin lokacin da zasu sauka ba, Mudanseer da Abubakar ne kawai suka sani, shima Abu ɗin yazo gidane saboda dawowar su Ahmad ɗin, amma har yanzu yana porthercout abinsa, zamu ma iya cewa shikam yazama ɗan can.
Rumana ce ta fara hango su Mudanseer dake ta kalle-kallen neman inda zasu hangosu, duk da sun canja mata matuƙa dan dukansu sun sake girma da ƙiba, ga gayu irin na samarin zamani, tai murmushi tana faɗin, “Abu-Haysam ai gasu Yah Mudan can ma�?.
Inda ta nuna ya kalla shi da Zainab, aiko suma sai idonsu akan su Abu ɗin waɗanda sufa har yanzu basu gansuba sam.
Zainab ce ta gwargwaɗama Abu-Talib magana a kunnensa, dan haka ya ƙirƙira da gudunsa zuwa gasu Mudan.
Ahmad da baisan abinda Zee ta faɗama Abu-Talib ba ya shiga ƙwala masa kira, amma sam yaron nan ko juyowa yaƙi yayi, sai ca yake “Abbu ka jirani ina zuwa�?.
Rumana ta dafe kanta da faɗin, “Ni Umm-Ruman! Rabbi ka shirya Abu-Talib, yaro kamar ana kaɗashi da ruwan hanji?�?.
Zainab dake dariya tace, “Nicefa na aikesa.......�?
Bata gama rufe bakiba Abu-Talib ya isa inda su Mudan suke.
Ji kawai Mudan yay an rungume masa ƙafafu ana faɗin, “Yauwa na Aunty Zee na kama mikishi har kizo�?.
Da sauri Mudan da Abu suka kallesa, dan yayi maganarne da larabci, sunan Zainab da ya ambata kawai sukaji su dai.
Ɗunbin mamaki ya kamasu, saboda kama da yaron yakeyi da su, Mudan ya kama hannun Abu-Talib ɗin, “Yaro daga ina?�?.
Abu-Talib da dama dai yanajin hausa, duk da dai bazata kai kamar ace ya tashi cikin ƙasarsa da ake yaren a koda yaushe ba, ya ƙurama Mudan idanu saboda ganinsa tamkar Abbunsa.
Hakan yasa Mudan duƙawa gabansa ya daidaita tsahonsu, Abu-Talib ya kai hannu ya shafa fuskar Mudan yana faɗin, “Lah Aunty Zee zo kiga Abbu biyu.....�?
Kafin Mudan ya samu ta cewa da lamarin Abu-Talib Abubakar yace, “Kai Yah Mudanseer, kodai yaron Yah Ahmad ne.....?
Shima bai samu amsa ba, saboda kwace hannu da Abu-Talib ɗin yayi daga Mudan ya juya da gudu yana ambatar, “Ummie kema zo kiga Abbu biyu�?.
Dariya Zainab ta ƙyalƙyale da shi, yayinda Ahmad yake murmushi saboda jin shirmen Abu-Talib, ya sake kai dubansa gasu Abu da suma yanzu nan idanunsu suka sauka akan Yayan nasu da Ahalinsa.
Ai nan take bakunansu suka washe, suka nufosu cikin matuƙar ɗoki, nan take suka kaure da matuƙar murnan ganin juna.
Mudan dake dariya yana basu labarin abinda Abu-Talib yaje yay musu ya kamo hannun Haysam da shima dai kallonsu kawai yakeyi, shi da yake yayi ɗan wayo dai yasan ba Abbunsu bane ya zama uku kamar yanda Abu-Talib ya koma faɗa yanzu saboda sake kallon Abubakar da yayi yaga shima dai kamarsa ɗaya da Abbun nasu.
Abu ya amshi Abu-Turab dake a kafaɗar Ahmad yana barci suna dariyar shirmen Abu-Talib ɗin.
Basu wani ɓata lokaciba suka rankaya ga motar da sukazo da ita, shi dai Ahmad bai tambayi ina suka samo motaba, amma a ransa yana mamaki kam, baya ya shiga shi da Rumana da Zainab, Mudan ya zauna a mazaunin driver tare da Haysam a cinyarsa tamkar zasuyi tuƙin tare ne, Abu-Turab kam da har yanzu ke barcinsa yana tare da Abu.
Abu-Talib dake baya jikin Zainab ya tubure shima bazai zauna a baya ba sai an sakashi inda aka saka Haysam sunyi tuƙin tare, Zainab nata lallaɓashi amma yaƙi sai turje-turje yake yana bibbige Rumana.
Tun suna masa dariya da cewar yay haƙuri shima zaiyi bayan Haysam yayi tunda shine yaya amma yaƙi, Rumana ta daina tat dariyar ta zuba masa harara tare da daka masa tsawa.
Babu shiri ya nutsu kuwa yana mannewa jikin Zainab, Rumana tai tsaki tana ɗauke kanta da faɗin, “Wlhy ka cigaba dan jikinka ne zai tsami�?.
Abubakar ne yay magana Abu-Talib ya dawo wajensa, shi kuma ya miƙa musu Abu-Turab tunda barci yakeyi, dan da idonsa biyuma ba yarda zaiyiba shi ɗinnan da shegen rashin yarda da mutane.
Hakan da akayine ya kawo zaman lafiya, Ahmad yace, “ALLAH dai ya shiryaka Abu-Talib, ko ina saika nuna hali�?.
Abu-Talib yace, “Abbu aito Na shiryu, kuma ka tambayi Aunty Zee nayi addu'a da mukaje makkah�?.
Dariya su Mudan suka sanya harda Zee, Rumana dai banza tai da su ita da Ahmad, dan ita bama jin daɗin jikinta takeba, tana dauriyane kawai.
Sun isa gida inda suka samu ƙyaƙyƙyawar tarba ta musamman, dan motarsu na tsayawa Abu ya shige gida ɗauke da Abu-Talib ya gwargwaɗa musu sun iso.
Take gidan ya kaure da murna, wasu kasa haƙuri sukai sukayo waje, dan su yaya Maryam duk suna gidan sunzo tarbarsu, duk da basu san taka maimai lokacin isowar tasuba.
Tuni gidan ya rikice, babu maijin zancen wani, kowa na mamakin canjawar kowa, musamman ma Ahmad da yazam babban mutum da ita kanta Umm-Ruman, Zainab kam sai tsiya suke mata wai aure takeso shiyyasa ta zangame da tsaho.
Saboda zafin da akeyine Ahmad yace ma Ayyah a saka musu tabarma a waje kawai, hakan kuwa akayi.............✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_GUDU DA WAIWAYE......_*
_(Shi ke kawo mugun zato)_
*_ƘARHE_*
*Kuma babu editin🥱, aradun ALLAH nagaji😜😂*⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀�?
...........Yanda gidan ya kaure da hayaniya saika ɗauka biki akeyi, maƙwafta sai zuwa suke kallon ƴan Saudiyya, Abu-Talib kuwa yanda ya sake da mutane saika rantse dama a cikinsu ya tashi, Haysam sai laɓe-laɓe yake, yana dai kallonsu ɗai-ɗai, haka yasa mutane keta faɗin saikace Abu-Talib aka haifa anan ba Haysam ɗinba.
Abu-Turab kuwa koda ya tashi shi ai baima aminta da kowaba shima, da an miƙo hannu za'a ɗaukesa sai ya maƙalƙale Ahmad ko Zainab, dan ita Rumana daya raɓeta turesa take saboda takanta takeyi.
Da ƙyar aka samu mutane suka lafa, shima sai da Ayyah ta sakasu suka shige ɗaki dan su samu suci abinci, kuma ta lura Umm-Ruman batajin daɗi, dan da alama dai ba ita kaɗai bace ba.
Zainab kam nacan mamuƙe da Gwaggonta, hakan yasa Abu-Turab binta, ganin Aunty Zee ɗinsa a jikin Gwaggo shima sai ya yarda da Gwaggo ta ɗaukesa ta saka a cinya, amma sai faman kallonta yake.
Gwaggo tace, “Auta wannan ɗan naki kuwa yanajin hausa? Ya zubamin ido kamar yaga kuɗi�?.
Dariya Zainab tayi tana kallon Abu-Turab dake zaune a cinyar Gwaggo, tace, “Sunajin hausa Gwaggo, ai duk muna musu yaya baya bari, dan yace idan ba'a musu mukazo gida da wane yaren zasu shiga ahalinsu, sai dai da yake bazai zam sujita tamkar suna anan da zasuyi cuɗanya da yara ƴan uwansu ba�?.
Gwaggo dake murmushi ta shafa kan Abu-Turab tana faɗin, “Kunyi dabara kam, tunda mudai nan ba larabcin muke jiba�?.
Zainab ta sake yin dariya, tace, “Ai abinda shima yayan ya hango kenan, bara kiji, inba ni nai masa maganaba dama bazai mikiba, sam yaron nan bashi da yarda, yanzunma dan ya gannine ya yarda ya zauna miki cinya�?.
“Abu-Turab!�? Zainab ta kira sunansa.
Juyowa yay yana kallonta, tare da amsa mata.
“Kasan wacece wannan?�?. Tai maganar tana nuna masa Gwaggo.
Kallon Gwaggo Abu-Turab yayi, sai kuma ya girgiza kai ya bata amsa da larabci.
Zainab tace, “A'a da hausa nakeso�?.
Shiru yay kamar bazai sake maganaba.
Sai kuma cayay, “Aunty Zee!�?
Tace, “Na'am�?.
“Inane nan mukazo?�?
“Abu-Turab nan shine gidansu Abbu da Ummie da ni, kuma kuma shine gidanku, nanne ƙasarmu, kaga wannan daka zauna mata a cinya, itace maman Abbu, ɗayar maman Abbunma tana nan waje itama (Ayyah)�?.
Shiru Abu-Turab yay yana kallon Gwaggo dake murmushi jin Abu-Turab na surutu ashe raɗam, sai ya maida kallonsa ga Zainab ɗin.
“Aunty Zee!, shi Abbu dama yanada Ummie har biyu? Mukuma miyasa tamu Ummie ɗin ɗayace?�?.
Babu shiri Gwaggo ta saka dariya ita da Zainab.
Zainab tace, “Kuma ai Umminku biyu, ba ganiba, gakuma Ummie, kaga biyu kenan aiko?�?.
Kansa ya ɗaga mata cikin gamsuwa, sai cayay “Aunty zee miyasa su su Ummien Abbu basuje Dhahran ba sun zauna dashi suna kaishi makaranta, suna masa wanka, suna kaishi yawo?�?.
Dariya sosai Zainab da Gwaggo keyi, Saiga Sadiyama dake fama da tsohon ciki ta shigo, ta zauna tana tambayarsu miya basu dariya haka?.
Gaya mata Zainab tayi, Sadiya itama tai dariya tana miƙama Abu-Turab hannu yazo, amma sai yaƙi yama maƙale Gwaggo.
Yana lafe jikin Gwaggo yace, “Aunty Zee ita kuma wannan Ummien waye?�?.
Zainab tace, “Itama Ummienka ce�?.
Shiru yayi yana kallon Sadiya, a ransa kuma dai yanajin kamar abin yayi yawa, kenan Ummin tasa tamafi biyu.
Kafin yay wata tambayar Abu-Talib sarkin hidima ya shigo, ganin Abu-Turab a cinyar Gwaggo shima sai yaje ya ɗane saboda kishi.
Abu-Turab ya shiga turesa akan sai ya tashi, nanko faɗa ya kaure.
Wannan abu ya saka Gwaggo dariya sosai da Sadiya, Zainab tace ai kaɗanma kenan indai su Abu-Talib ne, hayaniyarsu ta saka Ahmad daya fito alwala leƙa ɗakin, dan yasan faɗan da suka sabane sukeyi.
Koda ya ɗaga labulen yaga a jikin Gwaggonsa suke wannan bidigeren sai ya daka musu tsawa, “Wane kalar rainine wannan zakuzo jikinta kuna faɗa? Abu-Talib ba aikoka nai ka kiranin Aunty Zee tazo taci abinci ba?�?.
Yanda duk suka nutsu sai suka bama Gwaggo tausayi, ashe Ahmad ɗin na nan bai canjaba ko akan ƴaƴansa, hannunsu ta kama ta maida a cinyarta ta zaunar da duk sun miƙe suna neman wajen ɓuya, tace, “Babu ruwanka kai dai, cjikinka ko nawa?�?.
Ahmad yay murmushi da faɗin, “Nakine Gwaggo, amma ai saisu zauna lafiya ba suyita tsallen banzaba, shifa wannanma aikosa nayi amma yama manta�?.
Sadiya tace, “To yaya ai gara su more abinsu, cinyar da basu taɓa hawaba cefa, ina Haysam?�?.
“Wannan ai shi sai a hankali, yana can maƙale Mudanseer, da Ayyah kawai ya yarda sai Mudan ɗin, gadai wanda ya sake da mutane nan uban hidima�?. Ya nuna Abu-Talib.
Dariya sukai har Gwaggo, Ahmad ya saki labulen yana faɗin bara yaje salla ya dawo.
Duk yanda su Ahmad sukaso samun sakewa su gaisa da iyayensu hakan ya gagara, sai dare bayan tafiyar ƙannensa dasu Yaya Maryam sannan suka ɗan samu nutsuwar zama gaisuwa da iyayensu da kakarsu Iya, akayi hirar yaushe gamo har kusan ƙarfe ɗaya, sai da su Baba sukace suje su kwanta hakanan sannan, dan Abu-Turab ma shi tuni yayi barci, su Haysam ne dai ido biyu.
Umm-Ruman ɗakin Amminta ta tafi tai kwanciyarta, Haysam kam da Abu-Talib ɗakin Ayyah, Abu-Turab da Zainab kuma ɗakin Gwaggo, Ahmad kuwa ya kwana shi kaɗai a ɗakinsu na sashen Ayyah.
★★★★
Washe garima dai haka suka tashi da ƴan sannu da zuwa, kowa sai sha'awarsu yake da ƴan yaransu masu kama da larabawan ƙasar Morocco, su basuyi fariba, amma jin daɗi ya saka fatarsu gogewa tana kuma ƙyalli da wani cika idanu.
Abinda kuma ya sake birgesu da yaran duk abinda aka basu ci sukeyi, da wahala a basu abinci suce basa cinsa, duk da wani abun ma basu sanshiba, amma haka zasu amsa, sai dai idan basaso zasuci kaɗan nefa suce sun ƙoshi.
Tsaf Ahmad ya lura basa cin abinci sosai, kuma bakomai bane sai rashin sabo da cimar nanɗin, amma yay biris dasu a cewarsa da haka zasu saba da cin ai.
Itama dai Umm-Ruman bata taɓa cewa komaiba, dan ita takantama takeyi.
Zainab data fahimci komaice take ɗaukarsu a sace taje wajen Yaya Mudan ko Abu tace a saya musu wani abun ko biscuits ne haka.
Kwanansu Uku anan gidan suna gaisawa da ƴan uwa da abokan arziƙi, dan kullum cikin zuwa akeyi, abokan Ahmad sai kawo matansu sukeyi yimusu sannu da zuwa, su Sufyan duk an zama manyan mutane, dan shima yana aikinsa yanzu gashi yayi ƙiba abinsa, yaransa biyu shima yanzun.
Babane yace yakamata su koma gidansu hakanan, dan ya kula ananɗin kamar a takure suke, musamman ma Rumana da kowa ya fahimci laulayin ciki takeyi, banda uban gayyar da saida yaji Ayyah ta faɗa sannan hankalinsa yakai.
Yaji daɗi, amma sai antayama Rumana harara yake akan wai bata faɗa masaba, itako tai biris dashi.
Ita batasan da zancen gidaba, duk da dai taga an gyara gidansu tsaf, kowane sashe yasha gyara tamkar ba gidanba, an rushe sorayen ƙofar gida guda biyu anyi guda ɗaya da shaguna a waje da aka zuba kayan saidawa a dukansu, dan ƙofar gidan nasu ya zama wata ƴar ƙaramar kasuwa maiban sha'awa. Cikin gidan kuma dukda ba gini aka canja masaba yasha gyara sosai daya canja fasali saboda dabarun masu gini daya samu.
Da yamma bayan Mudan ya dawo daga kasuwa ya kwashesu a motarsa har zuwa anguwar da Ahmad yay gini wanda ko a labari bai taɓa sanarma Rumana ba, dukda ahima dai a hoto kawai yake ganin gidan,