Showing 123001 words to 126000 words out of 165545 words
tsala, sai tunaninta ya fara bata ƙilama Ma'aruff ɗin yanacan make cikin giya baizo gidanba.
Lallai tunanin Samina yazo da ruɗani a gareta, ya kuma karanta mata ba dai-daiba, dan kuwa dai yau ango Ma'aruff ko lemon bai damu da shaba balle akai ga giya, yana manne da amaryarsa da sukasha soyayyarsu, duk da dai daga ƙarshe abin yazo masa da ruɗani, dan kuwa dai amarya a fafake take ba budurwa bace, wani ya ɗana.
Ance wanzami baya son jarfa, hakan yasaka hankalin Ma'aruff tashi matuƙa, ya hauta da bala'i ta taka masa birki nan take, dan ta tabbatar masa bazata ɗauki haukarsa ba, harda tambayarsa wai shi dama budurcinta ne matsalarsa?.
Wannan tambaya ta ƙonama Ma'aruff rai, sai dai ya gaza cewa uffan saboda wani shegen tsoron Mufida yaji ya mamayesa.
“Aiki ga mai ƙareka”😂⛹♀
___________________________________
Su Umm-Ruman masu jego kam an kammala wanka, tayi dumurmur da ita kamar ka sace ta ka gudu, hakama Haysam abin sha'awa, ga ƙyawun yaro da yay gado uwa da uba nata fitowa, dama iyayen kamarsu ɗaya, hakan yasa bama a iya banbance dawa yake kama a cikinsu, wasuma sukance ya ɗara iyayen ƙyau.
Ita kanta Rumana takan zauna taita kallonsa idan babu kowa kusa, a ranta tana ƙiyasta yanzufa wannan mallakinsune ita da Yayanta.
Hakan na saka zuciyarta farin ciki sosai, shi kansa Ahmad idan ya kira labarinsa mafi yawa nakan Haysam, wataran Rumana har nuna kishinta take a fili, shiko yayta mata dariya, hotunan Haysam kam ai kullum sai an masa an tura masa, idan ita batayiba ma Mudan zaiyi ko Abu da aka sayi waya shima ya shigo gari da ƴar mai shan jininsa😂.
Umm-Ruman ta fara ƙoƙarin zagaya dangi ziyara, wanda da farko da Ahmad yaso kawo tirjiya Ayyah ta taka masa birki akan dolema yasama ransa haƙuri tunda haka al'adar take, sannan tunda Rumana tai aure ina yake barinta zuwa? Tanada dangin mahaifiya a gari suma kuma ai suna buƙatarta, ga dangin gwaggo suma ya kamata ta ringa shiga.
Dole yay shiru yabi umarni kam, aiko saiga su Rumana har shema ita dasu fa'iza, kwannansu huɗu suka dawo da tarin alkairi, dan ƴan Shema sunji daɗin wannan ziyara sosai.
Cikin ƴaƴan ƴan uwa kuwa wani ya maƙalema Fa'iza, kuma da gaske yake babu ƙarya, itama dai Fa'izan ta amsa, dan yay mata, sai dai fargabarta batason zama Shema kamar yanda ta sanarma su Rumana.
Sun bata shawarar addu'a kawai da neman zaɓin ALLAH, dan yafi kowa sanin abinda ya tsara.
Da zaman wankan Rumana, da ziyarce-ziyarcenta kusan watanni biyu da wasu ƴan kwanaki da tafiyar Ahmad.
Dan haka ya fara shirin zuwa gida, sai dai a wannan karon yasha banban da zuwan baya, dan kuwa zaizone domin ɗauke matarsa da ɗansa su koma kusa dashi kamar yanda iyayensu sukai masa alƙawari.
Ranar juma'a kwatsam babu zato sai gashi, kowa yayi murnar ganinsa kuwa, musamman yara da sukasan zasuci tsaraba kamar yanda ya saba kawo musu.
Ita dai Rumana duk wannan bikin murnar dawowar Ahmad da ake tana sashensu tanaji amma bata zoba, yaga dai Haysam dake goye a bayan Zainab yana barci.
Bayan yasha ruwa ya miƙe kamar yanda ya saba domin gaida matan gidan dasu iya.
Sashensu Iya ya fara shiga, ya gaisa da kakanninsa daketa tsokanarsa da cewar angon zumuɗi.
Shi dai dariya kawai yakeyi, dan kuwa dai sun gama ranfosa.
Koda ya fito sai ya shiga Sashen baba iliyasu, nanma ya gaisa da matansa sannan ya nufi sashen su Umm-Ruman, dan tunda bai gantaba asashensu yasan tana nan.
Sai dai anan ɗinma bai gantanba harya gama gaisawa da Ammi, ita mama gaje ma bata gidan.
Duk kuma Rumana na jinsu, dan tana ɗakin baba tana masa shara, hakan yasa taita leƙen Ahmad ta window ba tare daya saniba.
Shima dai haka kawai zuciyarsa da idanunsa suka karkata ga ɗakin baban, sai yakeji kamar akwai abunsa mai muhimmanci a cikin ɗakin.
Yana fita kuwa Ammi ta ƙwalamata kira.
Fitowa Rumana tai da sharar data kwashe tana amsawa.
“Ammi gani�?
“Na ganki ai, k bakiji mijinki ya dawo bane?�?.
Shiru Rumana tai bata iya cewa komaiba, ta dai duƙar da kai ƙasa, itama Ammin bata sake ce mata komaiba tama ɗauke kanta daga gareta baki ɗaya.
Sai da ta kammala abinda takeyi sannan ta nufi sashen su Ahmad ɗin a kunyace, dan Ammi sai antaya mata harara takeyi.
Tunda tai sallama Ahmad dake zaune riƙe da Haysam daya tashi barci ya zuba mata idanu, itako taƙi kallon sashensa.
Ayyah tace, “Ɗiyata aida yanzu zanje biko, dan ko abinci na hana mijinki nikam sai kinzo�?.
Murmushi Rumana tayi, aɗan in ina tace, “Shara naima Baba Ayyah�?.
Ɗauke kai Ahmad yay daga kallonta ya maida ga Haysam, ji yake kamar ya haɗiye ɗan yaronsa, a ƙasan ransa kuwa yana tuno yanda yaji akan ɗakin baba, ashe kuwa tana ciki.
Duk wannan hidima da akeyi Gwaggo na ɗakinta, tunda suka gaisa da Ahmad tai shigewarta ɗakinta.
Umm-Rumana ta taka inda yake, kujerar dake gefensa kaɗan taja ta zauna, “Sannu da zuwa Yaya, ina yini?�?.
“Sai yanzu aka san dani?�?.
Yay maganar yana wasa da hannun Haysam.
Ita dai tunda tasan tayi laifi sai tace yayi haƙuri kawai, ta miƙe ta amso abincin da Ayyah ke kiranta ta ɗauka masa takai ɗaki.
Sai da ta shiga da kusan mintuna uku sannan ya shiga ɗauke da ɗansa.
Tana ƙoƙarin zuba masa ya shigo, hakan yasa bata fasaba bakuma ta kallesu ba shida ɗan nasa.
Shiko ya kasa ɗauke idonsa a kanta, dan ƙyawun data ƙara da ƴar ƙibar datai mata ƙyau sunyi mugun tsole masa idanu.
Gabansa ta tura komai sannan ta ɗago ta kallesa, irin kallon da yake binta da shi na ƙurulla ya sakata jin kunya, tai murmushi tana ɗauke nata idon, “Yaya wai kallon fa?�?.
Ajiyar zuciya ya sauke kaɗan yana janye idonsa da salon lumshewa.
Bai iya cewa komaiba, sai cokali daya ɗauka zai fara cin abincin.
Katsesa tai da faɗin, “Kawoshi to yanda zakaji daɗin cin abincin�?.
Bai musaba ya buɗe hannayensa alamar ta ɗauki Haysam ɗin dake kan cinyarsa, sai faman watsal-watsal yake da ƙafafu na lafiya da ALLAH ya bashi.
Tasowa tai ta duƙo domin ɗaukarsa, hakan ya basu kusanci sosai ita dashi, dan har suna iya jin saukar numfashin juna, kowa na shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin ɗan uwansa, gashi yanda wuyan rigar yake daɗan girma ya samawa idon Ahmad abinci.
Ita dai tsigar jikinta na tashi ta ɗauki Haysam a kasalance ta matsa baya.
Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke ya fara cin abincinsa.
Kamar jira Haysam keyi ta ɗaukesa ya fara ƙananun kuka, banza tai masa, a ranta tana fadin, “Kujimin yaro da neman dalili?�?.
Ahmad ya ɗago ido ya kalleta da mamaki, ga yaro na kuka amma tayi biris, kafin yay magana Ayyah dake waje tace, “Waishi wannan alhajin baza'aji da shi bane Rumana? Kema kinsan yunwa yakeji tunda barci ya tashi dama�?.
Rumana tace, “Ayyah rigimace fa kawai, gashi nan zan bashi ruwa�?.
Ayyah tace, “Ruwan ƙaniya, ki bashi nono kafin nazo kanki�?.
Rumana ta dingure kan Haysam sannan taja hijjab ta saka wai batason Ahmad ya ganta, a haka ta fara Shayar dashi, shiko yaro kamar yasan za'aima ubansa buƙulu yaƙi amsa saboda zufar dole da aka ƙirƙirar masa.
Cikin haushi ta cire hijjab ɗin tana faɗin, “Kai wai ba a sirri da kai dan maigarin garinku?�?.
Murmushi kawai Ahmad yayi yana ɗauke idonsa daga kallonsu.
“Yaga za'a cuci masa Abbansa a hanashi ganin halalinsa ba dole yay boreba�? Ahmad yay maganar ba tare da ya kalli Rumana ba.
Baki ta kumbura, amma bata tankaba, sai harar Haysam takeyi kamar yasan tanayi😝.
Shidai Ahmad ya samu tv, yanacin abincinsa yana kallo.
Rumana dai kasa jure wannan kallo tai, ta samu da Haysam yaɗan sha ta ciresa tana gyara rigarta, dai-dai lokacin Mudan ya shigo ɗakin bayan yayi sallama sun amsa Ahmad ya bashi izinin shigowa.
“Ashe da gaske yaran nan suke kaiɗinne dai?�?.
Murmushi Ahmad dake Kallon Mudan yayi, yana ƙaunar ƙanin nasa sosai, hakama Rumana dake ƙoƙarin miƙewa ta basu waje.
Mudan ya amshi Haysam daga hannunta yana gaishe da Yayansa, ita kuma ta fice a binta.
Bata sake shiyowa ɗakinba. suko sunata hira abinsu, sai da aka kira sallar magriba Ahmad yabar gidan zuwa can gidansu, dan tun shigowarsa su Fa'iza suka tafi gyarawa.
Maman Amatullah kawai ya iske a tsakar gida tana shara, sai maman Aysha data shigo suke ƴar gulmarsu, kuma kamar an saita sunayi da Rumana ne akan wai taƙi dawowa.
Sai su Ahmad dake wasan ruwa a bakin rijiya shi da Amatullah.
A bazata sukaji sallamar Ahmad, wanda sarai yaji kalmar maman Aysha ta ƙarshe saboda bata magana a hankali ita dama.
Duk sai suka daburce wajen gaishesa da masa sannu da zuwa, shi dai ya amsa kawai ba tare da ko kallonsu yayi ba, Mudan yasa makulli ya buɗe masa ƙofar suka shiga.
Ko zama Mudan baiyiba ya fito yabar Ahmad.
A zuciyar Ahmad godiya yakema UBANGIJI da ya tsame matarsa ga wannan muguwar al'adar, shi sam bata birgesa tun ma yana yaro, sai kuma ALLAH ya soshi Ayyah da Gwaggo babu ruwansu da irin wannan tsogume-tsogumen ma.
Ya fito wanka yana alwala Kausar ta shigo itama, ashe gidan sunan ƙawarta taje, gaisawa sukai tana binsa da kallo.
Shi dai da baisan tanaiba ma tuni ya miƙe ya saka butar ɗaki ya fice abinsa.
Aiko kamar jira take ta nufi kicin inda maman Ama ke girki.
“Maman Ahmad wannan matar kuwa zata dawo? Ƙiri da muzu ta maida miji gwauron ƙarfi da yaji�?.
Maman Ama ta fito tana taɓe baki, “Wlhy maman Siyama yanzu muma muka gam ni da maman Aysha, yanzu dai ai zamusha kallo, tunda ta gama wanka ga kuma miji ya dawo maji ma gani�?.
Baki Kausar ta taɓe tana ƙoƙarin sauke Siyama dake goye a baya ta tashi barci, taja kujera ta zauna alamar koma ɗakin bazata shigaba balle tunanin yin salla.
Nanko suka sake buɗe babin gulmar Rumana da batasan sunaiba.
___________________________________
Ɓangaren Samina sam abubuwa babu sauƙi, komai sake rikice mata yakeyi, dan yanzu idan har kikaga Ma'aruff a sashenta to tabbas Mufida bata gida ne kokuma sunyi faɗa, ko yazo mata a buge ta korosa, dan tace bazai taɓa zama mata a sashe yan warin giya ba, bai dametaba yaje yay ta sha shiya sani, amma babu maganar raɓarta.
Tofa shine sai kiga ya taho wajen wadda ya raina Samina, ita kuma da bakinta bai iya mutuwa saboda azabar tsiwa da yace kule zatace cas, kafin kace mi sunyi sama, yako bubbugeta babu abinda yasha kansa.
Ya saka mai gadi ya hana kowa zuwa wajenta saboda zugar Mufida, ashe lokacin bikima shine yasa aka hana ƙawayenta shigowa gidan, sai da ta kira Nafy tana mata tsogumi shine ta sanar da ita komai daya faru, ran Samina ya ɓaci suka haura sama da Ma'aruff, ranarma sunci uban faɗa a gidan Mufida nata kwasar dariya.
Dolene duk wanda yasan Samina ya ganta a tsakanin nan ya tausaya mata, tayi figi-figi da ita kamar wadda aka ƙwato daga bakin kura, gashi saboda man bilicin ɗin data daina shafawa saboda ƙarewar nata ƙuraje sun mata futu-futu da fuska, nan yayi baƙi nan yayi ja, fuskar tai wata iri kamar wadda ta tashi daga jiyyar ƙuna.
Duk ɓarin kuɗin da yake mata da yanzu ya daina, sai abinda mufida tace akeyi a gidan.
Da kuka na maganin damuwa da tuni Samina yayi mata, sunan Ahmad kuwa ai babu fashi a rana saita ambata sama da sau goma, abu kaɗan Ma'aruff yay mata saitace da Yaa Ahmad ne da ba hakaba.
Ga rashin mutuncin dangi miji, sosai surukarta ke nuna fifiko tsakaninta da Mufida.
__________________________________
A randa Ahmad yazo a ranar yayma iyayensa tuni akan maganar abinda ya kawosa nason tafiya da iyalansa, dan yace kwana uku zaiyi kacal ma su juya.
Babu wanda yay musu a cikinsu, tunda dama kowa yasan da zancen, dan haka shiri kawai suka somayi.
Sai kuma Rumana duk ta shiga damuwa, ta roƙesa dan ALLAH su tafi da Zainab tunda ta gama firamare ɗinta, idan sukaje can sai a sata sakandire.
Da farko dai yay shiru kamar bazai amince ba, amma da yaga tana kuka sai yace zai tun tuɓi su baba idan sun amince, idan sunce a'a tofa sai dai tayi haƙuri, tunda da dai ga Haysam nan ya ishe ɗauke kewa.
Ita dai tata addu'ar ALLAH yasa a dace, da dare ya samu baba da maganar bayan ya fara sanarma Ayyah dama.
Baba yaso tirjewa, hakama gwaggo, amma da Ayyah ta saka baki sai suka amince, koda suka sanarma malam da iya fatan alkairi sukayi, iya tace dama tanada niyyar magana akan abama su Rumana wata a yaran gidan.
Ana gobe zasu tafi Rumana taje can gidansu, su mama Ama na soro zaune suna hira da makwafta, mamakin ganinta ya kamasu, dan a zatonsu kota dawone, har wata maman Salim na faɗin, “Maman Haysam masu jego na dawowar dare ke ta rana kike?�?
Murmushi tayi amma bata bata amsaba sai da ta zauna, suka amshi Haysam dake bayan ƙanwarta khadija suna yaba ƙyawun da yaron ya ƙara.
Sai da ta gaisa da kowa kafin tace, “Ba dawowa naiba, munzo muku sallamane dan da sassafe zamu wuce�?.
Cikin mamaki duk suk kalleta, maman Ama ta ɗora da tambayar “Yo ina kuma zakuje amarya?�?.
Kafin Rumana ta bada amsa khadija ta amshe da faɗin, “Porthercout zasu tafi ita da yayanmu�?.
Kallon kallo aka koma. Kausar tace, “Yawon shaƙatawa za'a kenan Amarya?�?.
Nanma Khadija dai ta bata amsa da faɗin, “A'a zasu koma can dai da zama sai dai suzo mana yawo�?.
Tsitt soron yayi, sai maman Aysha ce cikin yaƙe ta katse shirun, “A to lallai su marya gara wasai, kice guduwa za'ai kudu a barmu, su Haysam ashe ƴan kudanci za'a koma�?.
A yanda take maganar kawai ya isa tabbatarma da mutum bada daɗin rai takeyiba.
Su kuma sauran sai famar yaƙe sukeyi, ita dai Rumana miƙewa tai ta nufi ɗakinta, shigarta babu jimawa sai ga Ahmad shima ya shigo.
Ya wuto su maman Ama Haysam na wajensu.
Rumana ta amsa masa sallama tana cigaba da abinda takeyi, shima amsawa yay yana zama a bakin gadon idonsa a kanta, daure zuciyarsa kawai yake harsu tafi ba tare daya nema ruwan dazai kashe ƙishinsa daga gareta ba.
Itama ta lura da hakan, shiyyasa taketa addu'a da fatan harsu wuce kar yace yana buƙatarta, dan ita dai bazata sake maimaita abin kunyar da sukai a ranar da naƙudar Haysam ta dole tazo mataba.
Tana kimtse-kimtsenta yana binta da kallo, hakan yasa ta ƙwalama khadija kira, sarai Ahmad ya fahimci dalilin kiran khadijan, hakan yasa ya cije baki a ransa yana faɗin duk wayon amarya dai sai ansha manta, kuma zaki gane baki da wayo yarinya.