Showing 144001 words to 147000 words out of 165545 words
tsinci kanta a halin da yafi wannan ma, yaron nan yashiga ƙuncin rayuwa a dalilin butulci, hakama iyayensa, amma suka danne zukatansu basu raba zuminci damuba, sanadin Ahmad kika dawo gidannan Gaje, a wannan gaɓar kuma dolene ki barshi, bari na har abada, dan haka kije gida na sakeki, na katse sauran igiyar data rage a tsakaninmu dama ƙwara ɗayace.........�?
Cikin hanzari baba Hamza ya katse baba Yusha'u da faɗin, “Haba Yusha'u, wannan wane irin maganace? Miyasa zaka saketa? Koma dai miye ya rigada ya faru, ya kamata kuma mu ɗaukesa matsayin jarabawar da babu hannun da ya isa gogeta a duniya, sam banji daɗin wannan hukuncin nakaba, bankuma yi zato ko tsammanin zaka yankesa ba........�?
Baba Iliyasu yace, “Yaya wannan hukunci yayi dai-dai wlhy, lokaci yayi da zamu dawo cikin hankalinmu, kaine babban yayanmu, wanda muke kallo tamkar uba, tayaya zamu cigaba da kallo a koda yaushe ana cuta maka kaida zuri'arka?, tun daga zamanin ƙuruciya har wannan ranar da muke yau iyalanka haƙuri kawai suke a gidannan, babu kalar haɗin masifa da ba'ai musuba, shikenan kuma dan ALLAH yasa kun kasance masu kawaici sai a maidaku juji? Wlhy bama gaje ba, kowacce ƴar iskar mata yanzu a gidanan inhar bata dai-daita sahuntaba mu zamu daidaita matashi, dan munsan gaje tanada mabiya masu koyi da munanan halayenta a gidannan.......�?
Nanma dai babane ya sake katse baba iliyasu, dan (Kowa yasan baba iliyasu da matarsa yake shima).
A mamakin kowa sai akaga mama gaje ta miƙe bata cema kowa uffanba ta shiga ɗaki, mintuna baifi gomaba ta fito sanye da hijjab ta fice daga gidan nanma bata tankama kowaba.
Da kallo duk suka bita, dan zukatansu sun fara basu ƙwaƙwalwarta kamar ta fara samun matsala.
Babane yace Mudan ya bita yaga wane hali take ciki, koda Mudan ya biyota sai yaga ta tari napep tana faɗa masa ya kaita anguwar su inna mari.
Gida Mudan ya koma ya sanar musu, hakan ya saka baba Yusha'u faɗin, “Dama kune kuke ɗaukarta mai matsala, amma ni nasan wacece gaje, tajecan ta ƙarata, nidai na yanda ƙwallon mangwaro na kuma huta da ƙuda�?.
Shiru kowa yayi, sai iyace tai gyaran murya, dan haka kowa ya maida hankalinsa gareta.
Nasiha ta shiga musu, tare da nuna musu muhimmancin zumunci da sakamakon mai wargazashi, takuma sakasu suka ƙara neman gafarar juna, taima su Ayyah nasiha akan su ƙara haƙuri da kowa su cigaba da ɗaukar girman da ALLAH ya ɗora musu, insha ALLAHU zasu cigaba da zama masu ribane har abadan.
_________________________
A saudiyya ma dai abubuwa sunyi sauƙi, sai dai abinda zuciya ta gaza mantawa, dan a tsakaninnan ba ƙaramar tsanar Samina Ahmad ke ƙara jiba a ransa sosai.
Ko gida ya tuna sai kaga ɓacin rai ya mamaye fuskarsa, abu kaɗan zai kama faɗa a kansa, ranar tsautsayi na bin Haysam Rumana ta ajiyema Ahmad ɗin tea zaisha da daddare wajen tsalle-tsallen yara na wasa ya ɓarar dashi, aiko Ahmad ya kama faɗa hardasu zane Haysam yayi.
Agaban Rumana komai ya faru, amma sai ta ɗauke kanta tankarma batasan sunaiba, sai Zainab ce keta kuka tana roƙon Ahmad yayi haƙuri, daga ƙarshema Rumana sai tabar masu falon kawai.
Ranar Haysam yaci kuka yaronan abin tausayi, daga ƙarshe yay barcin dole.
Tun daga lokacin ya koma tsoron Ahmad ɗin, ko sallamarsa yaji zakiga ya gudu ya ɓuya koda a bayan Rumana ne ko Zainab.
Sai kuma abun ya fara damun Ahmad ɗin, ranar ya dawo daga makaranta da wuri ya iske Rumana kwance bata da lafiya, duk da dai taƙi sanar masa, dan takai sati uku tana fama amma ganin yanayin da yake ciki na saurin fushi a wannan tsakanin saita danne tai gum da bakinta.
Yau ɗinma koda ya fahimci bata da lafiyar sai ta fuske abinta.
Shine ya kasa haƙuri ya tambayeta da cewar, “Ruman lafiya kuwa?�?.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tana cewa, “Babu komai�?.
Duk yanda yaso jin damuwarta taƙi faɗa masa, tama haɗe fuska taƙi sake masa kamar yanda ta saba.
Numfashi ya sauke kawai ya shiga bayi yayi wanka, harya fito bata motsa daga kwancen da takeba a gado, ya zira jallabiya fara yana mai satar kallonta, “Bara na ɗakko Sadauki a makaranta�?.
“Uhum�? kawai tace masa ta ɗauke kanta.
Ya kalleta da ƙyau yanajin mamaki a ransa, amma ganin taƙi kallonsa sai ya fita kawai.
Koda Ahmad yaje makarantar su Haysam ɗaukarsa Haysam sai yaƙi yarda dashi, anyi lallashin duniya yaronnan yace shi sai dai Ummien sa ya keso.
Badan malaman sun san Ahmad ba, kuma ga tsananin kamar da Haysam keyi da shi da sai suce kodai dama ba mahaifinsa bane?.
Lallashi da wayo irin wanda akema yara babu wanda ba'aima Haysam ba amma yaƙi kallon ko Ahmad ɗin.
Wannan abu yay masifar sosama Ahmad rai, har ya gano kuskuren daya tafka ga iyalan nasa da basu da laifin komai akan damuwarsa.
Daga ƙarshe dole sai ɗaukar Haysam Ahmad yayi yaron na kuka tamkar za'a yankashi, sauƙinsama makarantar kusa da gida take, bawani uban nisa bane mai yawa tsakaninsu.
Har sukaje gida Haysam na turje-turje da kuka.
Umm-Ruman na bayi tana amai suka shigo, ta kuskure bakinta ta fito jikinta duk babu ƙwari, ga fuskartama ta nuna alamun a wahale take.
Ahmad ya sauke Haysam yana kallonta, itako ta ɗauke kanta ta haye gado ta sake kwanciya tana jan bargo.
Haysam kuwa da Ahmad ya sauke da gudu yaje ya maƙalƙaleta yana ɓoyewa cikin bargon data lulluɓa.
Jikin Ahmad sai ya sake yin sanyi, ya zauna a bakin gadon yana mai zuba musu ido ranshi na ƙuna.
Har washe gari Ahmad na tare da wannan damuwa, dan da safenma Haysam ƙin yarda yay ya kaisa makaranta, gashi Rumana na kwance babu lafiya sosai, ko breakfast ma sai Zainab ce ta haɗa musu saboda tana ƙoƙarin koyama yarinyar duk abinda ya dace.
Dole sai Zainab ce ta ɗauki Haysam ɗin, Ahmad na biye dasu a baya har majarantar, daga can itama ta wuce shikuma ya dawo gida..............✍�?
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
8/
...............Zama yay a bakin gadon yana mai kai hannu ya yaye bargon da Rumana ke ciki, duk tana jinsa, amma rashin ƙwarin jiki da take fama dashi saboda yawan amai ya hanata koda kallonsa.
Hawowa yay gadon ya kwanta bayanta tare da mannata a jikinsa, ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido saboda zafin da jikinta ya ɗauka.
Itama ajiyar zuciyar ta sauke amma ko motsawa batayi ba.
Murya ƙasa-ƙasa yace, “Haba Gwal ɗina, yanzu wannan rayuwar da kika zaɓa mana kina ganin ta dace kenan? Ace kina fama da ciwo amma kinƙi yarda muje asibiti?�?.
Murmushi ƙaɗan Rumana tayi jin furucin yayan nata, batace dashi komaiba itadai.
Shima tashi yay zaune ya yaye bargon gaba ɗaya, sannan ya ɗagota jikinsa yana faɗin, “Please muje namiki wanka, kuma banason musu�?.
Bata musa masanba kuwa, dan tana buƙatar wankan, rashin jin ƙwarin jikine ya hanata tashi, da taimakonsa tai wanka da ruwa mai ɗumi sosai dataji ƙwarin jikinta kaɗan, koda suka fitoma shine ya taimaka mata ta shafa mai ta saka doguwar riga.
Shima shiryawar yayi ya ɗakko kayan karin da Zainab ta haɗa musu ya kawo ɗakin, amma sai Rumana tace bazata iya ciba ta ƙoshi, da ƙyar ya takura mata tasha shayi babu madara, aiko tana gamawa sai amai.
Da gudu ta tashi zuwa bayi shima ya bita, ta bashi matuƙar tausayi, sai kuma ya fara zargi a ransa kodai cikine da Gwal ɗin tashi?.
Wani irin ɗoki ya ziyarci zuciyarsa, dan haka suna fitowa cayay mata asibiti zasuje, duk yanda take masa magiyar ya barta, bai sauraretaba ya saka mata gyalen jallabiyar dake jikinta, dole ta yarda suka tafi kuwa.
_______________________________
Rayuwar jail da Samina ta tsinci kanta a ciki rayuwace da sam bata da daɗi, dan ALLAH ya haɗata zamane da wasu mugaye dake azabtar da rayuwarta.
Cikin ƙanƙanin lokaci komanta ya canja, tai wani irin baƙi saboda man bilicin da fuskarta bata samu, gashi tayi gida-gida tamkar ta ƙone, ga ƙuraje.
Yayinda zuciya take azabtuwa ta tarin ƙaunar Ahmad da baisan tanayiba, tunda take a rayuwarta bata taɓa jin son Ahmad mai masifar zafi irin a wannan tsakaninba, ji take idan bata rayu da shiba tamkar zata iya rasa ranta, kullum cikin tunaninsa take da roƙon ya dawo gareta dan ALLAH.
Samina Ahmad baya jin wannan kirayen naki sam, sai dai haƙuri kinji😢🤒.
Tana ambaton kalmar data sani gameda Sanin Ma'aruff fiye da sau dubu a rana, tare da ɗunbin jin zafin mahaifiyarta da kakarta da tafi tsana fiye da kowa yanzun a duniya, dan a ganinta kakarta inna mari ce silar komai, sai ƙawayen banza mugaye irinsu Nafy, tare da son zuciya da ruɗi na neman wayewa da son duniyar da baida amfani, domin ita dai gashi bai mata amfaninba.
_______________________________
Su Ahmad suna isa asibiti a gwajin farko aka gano cikin da ke jikin Rumana ɗan watanni biyu, wanda Ahmad yake hasashen zuwan su Rumana Saudiyya babu jimawa ta sameshi.
Yayi murna sosai da farin ciki, inda harya kasa haƙuri sai da ya kira Yaya Maryam ya gwargwaɗa mata.
Itama kuma Rumana lokacin tanata barci saboda Ruwan da aka saka mata.
Awarsu kusan shida a asibitin sannan aka sallamesu, lokacin da ruwan da aka sakama Rumana ya ƙare, yanda taga fuskar Ahmad ɗin a washe ya bata mamaki.
Duk da ita ta daɗe da sanin ciki gareta, tunda taga wata ya shige batai jini ba tasan abinda Ahmad ɗin ke fata ya samu, yanda ya koma mafaɗacin ƙarfi da yajine yasa ta danne abunta a rai taƙi sanar masa.
Murmushi ya sake sakar mata yana lumshe idanu, ya jawota ya saka jikinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, kafin ya ɗago fuskarta yay mata sumba kusan huɗu a goshi da kumatunta.
Turesa ta ɗanyi tana faɗin, “Yaya wai mike faruwa hakane?�?.
“Kina nufin bakisan mike faruwa bane? Wlhy nasan kin san da abin farin cikinnan kika ɓoyemin Babie R ɗina�?.
“Ni bansan komaiba�? Rumana ta faɗa tana ɗauke kanta gefe�?.
Hannu yasa ya maido da fuskar tata inda take, yace, “Gwal ɗina ke ɗinnan ko, shikenan dai bara sai munje gida kawai�?.
Shiru tai bata iya cewa komaiba, suka fito zuwa gida saboda an basu sallama, takumaji daɗin jikinta sosai yanzu babu laifi, sai da suka biya ta makarantar su Haysam suka ɗaukesa, yau ɗinma dai ƙin yarda yayi da Ahmad, sai da yaga Ummien sane saiya gudu ya maƙalƙaleta.
Rumana tai murmushi tana riƙe hannunsa da faɗin, “Oh Sadaukin Abbunsa kana lafiya?�?.
Yaron ya faɗa jikinta yana dariyar farin cikin ganinta, koda Ahmad ya miƙa masa hannu sai ya noƙe kafaɗa alamar bazaijeba.
Ahmad yay guntuntun murmushi kawai.
Har suka isa gida Haysam nata bama Rumana labarin abinda take masa tambaya a kai cikin rashin ƙwarewar maganarsa, dan yanzun yanda yake magana da larabci yafi masa sauƙi akan hausar, danma suna ƙoƙarin masa dan basa buƙatar ya manta da yarensa, to dama dai Ahmad ɗinne maijin larabcin sosai a gidan. Sai itama Zainab da yanzu Alhmdllh ta fara ji saboda makaranta, Rumana kam sai jefi-jefi irin na islamiyya da wanda take tsinta annan.
A gida duk yanda Ahmad yaso sakewa da Haysam kamar da can baya sam yaƙi, zai fara kiran ƴan uwa ya baza musu tana da ciki ta fara roƙonshi akan dan ALLAH karyay hakan, badan yasoba dole ya haƙura yabi yanda takeso tunda yasan dai Yaya Maryam ta riga da taji ai.
Cikin hikima kuma ya cigaba da jan Haysam a jiki, da masa wasa tamkar da, sai a hankali kuma yaron ya koma sakewa da shi tamkar da can baya, shaƙuwa ma ta sake shiga tsakaninsu tunda yanata ƙara wayo.
Haka Umm-Ruman ta cigaba da rainon cikinta dake ɗan wahal da ita, dan wannan karon da Amai yazo mata, sai dai tanata jurewa dan kar Ahmad yace bazai nema mata makaranta ba sai ta haihu.
Shiko da yaga kamar da sauƙi yanzu sai ya cigaba da cuku-cukun makarantar tata da taimakon Gaddafi, dan matar Gaddafin ma jin ɓangaren islamic Rumana keson faɗaɗa karatunta, sai itama taji sha'awar komawa karatun, duk da kuwa tayi karatu har matakin masters, to a ganinta hakan bai zama ya wadatarba dan islam shine babban tushen da zaka karanta kai alfahari da shi a duniya da lahirarka, boko kuwa aikin alkairin da zakai ta dalilin karantarsane zai amfanar da kai a duniya da lahira.
Komai tare akai musu, Gaddafi ya bada gudunmawa sosai saboda yafi Ahmad ƙarfi sosai.
Randa Ahmad yazo mata da bayanin komai, tare da takardunta sun kammala, jikinsa ta faɗa tana kukan daɗi, bata taɓa zato ko tsamanin irin waɗannan nasarorinba a rayuwarta, amma gashi a dalilin yima iyaye biyayya tama wuce inda kowa yake zato, dalilin haƙurin da tai da Ahmad a farkon aurensu ya jawo mata alkairin da hasashen zuciya bai taɓa kaiwa nanba.
Ahmad dake shafa bayanta yay murmushi yana magana a hankali cikin kunnenta.
“Gwal ɗina tawace ni kaɗai, hakama farin cikinta nawane ni kaɗai, kin cancanci nasarar data kere haka a rayu Umm-Ruman, duk wanda yay haƙuru da jarabawa da ƙyaƙyƙyawar zuciya badan jiran sakamako ba to lallai sai ya kasance mai tarin nasara a nan gidan duniya ko a lahira, karkaga ka wahala iya wahala a rayuwa baka samu nasarar sakamako irin na labarin novels ba ka ɗauka shikenan kai ka rasa, ɗan uwa/ƴar uwa! Kun manta akwai wata sabuwar rayuwar da tafi ta gidan duniya komai? Labarin littattafai misaline kawai wa rayuwa ake nunawa, Iyakar daɗewar ɗan adam a duniya shekaru ɗari ne kacal, amma ka tuna tun zamanin annabawa ake mutuwa, saika shekara talatin kacal a duniya ka mutu kaje kai shekara dubunnai a barzahu kafin a tashi kiyama, mi kake tunani a iya zaman barzahu kawai idan har baka aikata alkari ba a ƙanƙanuwar rayuwarka ta duniya😭, miyasa haƙuri da juriyar jarawar shekarun da bazasu taɓa haura ɗari ba, su gagareka jurewa? Miyasa daɗin da bai taɓa tsallake shekara ɗari na a duniyarka zai ruɗeka ka manta da dubbunan shekarun dake gabanka na barzahu kawai?, miyasa daɗin dake ƙalilan na duniya zai ruɗeka ka manta da ranar hisabi ranar da bata da kwatankwaci ko misali😭?, ranar rarrabe gaskiya, ranar tonon silili, ranar da uwa ke gudun ɗanta, ranar da ɗa ke gudun iyayensa, ranar da kanka kawai ka sani, ranar buɗe ɓoyyayun sirrika😭 (Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un) ƴan uwana! Ƴan uwana! Mi muke tunani haka da zurfine? Mi muke buri haka da yawane? Mi muke fatan samu haka da yawane? Mi muke ƙoƙarin mallaka haka da yawa ne? Mi yake canjamu haka da yawane? Mi yake ruɗarmu haka da yawa ne? Mi muke taƙama dashi haka da yawa ne? Da mi muka dogara haka da yawa ne? Suwa muke tunanin ko zaton sun tsaya mana haka da yawa ne? Ina mukabar imaninmu tafiya haka da yawa ne? Ina muka bar zukatanmu haka da yawa ne?😭😭.
“🙏🏻😭Ya rabbi ka gafarta mana badan halinmu ba�?.
Umm-Ruman ta sake ƙanƙame Ahmad tana zirar da hawaye, jikinta na sake yin sanyi game da komai ma, shi kansa da yake maganar hawayen yakeyi......
“Abbu! Kuka kakeji?�?.
Sukaji maganar Haysam a kansu a bazata.
Saurin sakin Rumana Ahmad yayi, ya goge hawayensa cikin dabara kafin ya duƙa gaban Haysam dan ya daidaita tsahonsa da shi, ya dafa kafaɗun Haysam ɗin yana murmushi.
“A'a Sadauki na, ba kuka nakeji ba, abune ya faɗamin a ido sai Ummineka take ciremin fa�?.
Haysam yay shiru kamar ya yarda, sai kuma ya sake jehoma Ahmad tambaya,
“To Abbu itama ai naga ruwa na fita a idonta?�?.