Showing 114001 words to 117000 words out of 165545 words

Chapter 39 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

379

faɗa mata akan taje shikuma ya samo mota su tafi asibiti.
Amma sai Iya ta tsaidashi, a tare suka koma sashen nasu, lokacin sosai Rumana ma ta gama galabaita, dan har wani ruwa ya fashe mata, sai kiran sunan Yah Ahmad takeyi da Ammin ta.
Gabanta ya duƙa ya riƙe hannunta shima muryarsa na rawa yake faɗin, “Kinganni nan kusa dake Gwal ɗina, kiyi haƙuri yanzu zan samo mota muje asibiti kinji ko�?.
Cikin kuka rurus take ɗaga masa kai alamar to.
Iya ta korashi waje dan ta kula haihuwace gadan-gadan ta tahoma Rumana.
Koda Ahmad ya fito jingina yay da bango ya lumshe idanu, ji yake kamar ya taya Babie R ɗinsa kuka, dan sosai kukanta ke sukarsa, gani yake laifinsa ne, da bai kusanceta ba ƙila hakan da bai faru ba, shikuma kasa jurewa yay, dan a jigace yake da son jinta a jikinsa.
Dai-dai nan su Ayyah suka shigo gidan, duk sai da gabansu ya faɗi ganinsa a wajen, dan kukan da Rumana keyi idan ba matsowa kai kusaba ba wai zaka jita bane, zuwa yanzu ma ta bar kukan sai nishi da Iya ke cewa tayi.

Kafinma su Ayyah su sami damar tambayarsa suka jiyo nishin Rumana, hakanne ya tabbatar musu haihuwace, jin iya ce a ciki sai Ayyah ta shiga danta taimaka mata, Gwaggo kuma ta fara yunƙurin ɗora ruwan wanka bayan ta shiga ɗakin baba ta ɗakko wasu sassaƙen magunguna.
Kaf gidan babu wanda yasan hidimar da ake sai iya su, ko Abu da yake baida man kai daya shigo cin abinci bai fahimta ba, ya ga dai Ahmad sai kai kawo yake a tsakar wajen cikin damuwa, da yake ba wasa yake da suba sai bai iya ya tambayesa ko lafiya ba?.
Cikin amincin ALLAH mai rahma mai jinƙai ALLAH ya sauki Umm-Ruman lafiya bayan baƙar wahalar data gama sha, duk da a hakanma su Iya sunce haihuwar tazo mata da sauƙi, ballema tana da dauriya, dan bata irin ihun nan kamar ɗiyan maguzawa.
Tunda Ahmad yaji kukan jinjiri ya sauke wani nannauyan numfashi da har Gwaggo sai da ta jiyosa ta kallesa, duk da itama ta sauke ajiyar zuciya, tausayi ya bata daga shi har Umm-Ruman ɗin dake filin daga.
Ayyah ta fito ta ɗauki abu ta koma, tana cema Ahmad ya samu waje ya zauna tunda an sauka lafiya ai.
Nanma ya sake samun nutsuwa, sai bin gwaggo da kallo yake yaga ko zaiga yanda zata nuna, sai dai bai fahimci komaiba daga fuskarta, ta dai ɗauka buta tayi alwala ta shige ɗaki abinta.
Kansa ya duƙar ƙasa yanata cigaba da jeroma ubangiji godiya da kirari akan wannan ƙyauta da yay masa.

A haka su Fa'iza suka shigo gidan suka iskesa, sannu duk sukai masa, a mamakinsu sai sukaga fuskarsa washe da fara'a, su dai ɗakinsu suka shiga dansu ajiye littatafan hannunsu da hijjabai.
Sadiya tace, “Oh ni waye yayma katifarnan haka? Zainab halan kece?�?.
Zainab sarkin tsiwa tace, “Kai Yaya Sadiya, ALLAH zai sakamin dan wlhy bani baceba�?.
Duka Sadiya ta kai mata, ita kuma ta fita da gudu zuwa ɗakin Gwaggo dan takai ƙara.
Gwaggo dake ƙoƙarin fitowa sukaci karo da Zainab, tace, “K kuma lafiya?�?.
“Gwaggo ba yaya Sadiya bace, wai dan mun dawo munga an hargitsa katifa shine wai tace nice, kuma wlhy ni bani bace nama rigasu tafiya makaranta......�?
Kafin Gwaggo tace wani abu Sadiya ta fito daga ɗakin tana faɗin, “Nifa Gwaggo daga na tambayeta ne, maimakon tace ba ita bace shine harda wani cewa ALLAH zai saka mata na mata sharri ma kenan?, bakigafa yanda akaima katifarba kaca-kaca kamar wani ya hau yay danbe�?.
Fa'iza tace, “ƙilama aljanune wlhy Gwaggo, ni dai yau ban kwana a ɗakin nan�?.
Ahmad duk yana zaune yana saurarensu, amma ko kai bai ɗago ya kallesu ba, balle ya nuna yasan wanda yayi.
Gwaggo da batace uffanba ta nufi ɗakin dan ta gani, dai-dai nan kukan ɗan jariri ya kuma cika sashen.
A take su Fa'iza duk suka fiddo idanu waje alamun mamaki, har haɗa baki suke wajen ambaton, “gwaggo Rumana ta haihu ne?�?.
Da hannu tai musu nuni da suyi shiru, aiko sai kowacce tai ɓam da bakinta amma tsagwaron murna ya mamayesu, suka kama tsalle tare da afkawa ɗakin suka haye katifar da suke cewa sunajin tsoro, kota kan Gwaggo dake ƙarema katifar kallo basu biba.
Itama sai tai fitowarta bata tanka musuba.

Cikin awa biyu Gwaggo da Ayyah suka kammala kimtsa komai, sannan kusan sha ɗaya na dare, Ayya ce taje cikin dubara ta sanar ma Ammi dan ba'ason faɗin haihuwar sai safiya idan ALLAH ya kaimu.
Addu'a kawai Ammi tayi amma bata zoba.
Ayyah ta kama hannun Ahmad suka shiga ɗakin ya tsaya daga ƙofar ɗaki, jaririn dake nannaɗe cikin zani ta ɗakko masa, dukda da akwai ɗan ƙarni-ƙarni jikinsa, dan zaitun kawai aka shafa masa hakan bai hana Ahmad amsarshiba jikinsa sai tsuma yake, lokacin da idonsa ya sauka akan yaron kuwa sai suka ciko da ƙwalla, ya ɗora bakinsa akan goshin yaron ya sumbata yana murmushi.
Ayyah ma dake murmushi tana kallonsa tace, “Ɗan albarka nayi miji gashi nan tubar kalla masha ALLAH�?.
Murmushi yayma Ayyah sai dai bai iya cewa komaiba, jiyake kamar ya maida yaron cikin jikinsa, ya kai dubansa ga Rumana dake kwance a kan gado ta juya musu baya wani wahalallen barci yay awon gaba da ita, Iya ko data sake kimtse-kimtse, dan so take ta ɗaurayema yaron jiki ko yayane, Rumana dai anɗan gargasa matane kafin safiya.
Murya a sanyaye yace, “Ayyah Gwal ɗin fa?�?.
Ayyah tace, “Wane kuma Gwal ɗan albarka?�?.
Fahimtar suɓutar bakin da yayne ya sakashi miƙa mata yaron ya fita da sauri yana dariya.
Iya da duk take saurarensu tace, “Ɗan jakar uba, a gaban uwar takama Gwal zaka ce? Ashe bamu kaɗai akema rashin kunyar ba, ni dana gama wahalar amsar maka haihuwar wannan raguwar matar taka baka fara tambayata ba sai ita�?.
Shi dai bai bata amsaba yama fice daga gidan cikin tsagwaron farin ciki da yarasa a ina zaije ya juyesa ko zaiji sassauci.

Ayyah da sai lokacin ta fahimci inda zancensa ya dosa itama tai dariya tana girgiza kai.
Sai da Iya ta kammala komai tsaf ta fice sanan Ayyah taje har ɗaki ta kamo Gwaggo dan dole tazo taga baby.
Lokacin kusan sha biyu ma.
Gwaggo ta ɗaukesa tai masa addu'a tana mai kallonsa tamkar sanda ta haifi Ahmad, Rumana dai tanata barcinta batasan wainar da ake toyawa ba.
Gwaggo na fita su fa'iza suka shigo, sai santin ɗan yaron suke, sukam, ai sai da Gwaggo ta korasu suje su kwanta sannan.

Ahmad ma da wannan tsagwaron farin ciki ya isa gida, har zai kwanta ya tuna akwai najasa a jikinsa, dole yaje yay wanka tare da ɗauro alwala, saima ya kasa kwanciyar kuma ya hau nafilfilin miƙama UBANGIJI godiya.
A wannan dare haka wannan ahali suka kwana cikin tsagwaron farin ciki mara misaltuwa.


★★★★★★

Asubar fari Ayyah ta fito baba ya taimaka mata suka haɗa wutar ɗora ruwan wanka, lokacin da ake ƙoƙarin shiga massalaci ai harya tafaso cikin amincin UBANGIJI.
Iya na idar da salla nan tayo, ita taima Rumana cikakken wanka mai gamsar da jikin duk wata maijego data samesa, Ayyah kuma taima jinjiri, Fa'iza ta kimtsa ɗakin Ayyah aka kunna turaren wuta ɗaki ya ɗauki ƙamshin jego.
An naɗe yaro a kayan sanyin da aka sakama Ahmad lokacin yana jinjiri shima ruwan ganye da ratsin fari, (kunsan mutan da akwai ɓoyo da bama abu muhimmanci, dama Ayyah tai alƙawarin inhar ALLAH ya kaita da rai, duk randa Ahmad yay aure ya haihu kayan da za'a fara sakama ɗansa ko ƴarsa kenan) to gashi ALLAH ya cika mata burinta kuwa, da yake kuma kayan saƙace mai inganci da tsari.
Shiko sai barcinsa yake yaji ɗumi.
Kafin gari ya gama haske har gwaggo ta kammala damun kunu da yaji kayan ƙamshi, ga kuma shayi shima yaji kayan ƙamshin.
Mudan ya shigo gaishesu yay gamo da wannan farin ciki, dan shi bai shigo gidanba a jiya yanata dinkin wasu anguna kusan ma kwana yay, da yake kuma ba wani ɗaga murya sukeba sai baisan mi ake cikiba, ko fitar Yah Ahmad bai ganiba, ya daiga shigowarsa bayan sallar isha'i.
Gaba ɗaya farinciki ya gama rufesa, ya ƙwaƙume jinjiri tamkar zai maidasa ciki, koda baba ya shigo a lokacin dan shima sai yanzune zai gansa da ƙyar Mudan ya bashi, ita dai Rumana kanta na a ƙasa ko Mudan ɗin ta kasa amsawa santinsa balle kuma ga baba ya shigo.
Ta dai gaidashi, ya tambayeta yaya jikinta? Ta amsa da ƙyar.
Jariri daketa barci yaji daɗin wanka yasha addu'oi wajen baba, Mudan ko ya fice nemi kayan shayi da Ayyah ta faɗa masa.
Babu daɗewa ya dawo harda soyayyen ƙwai.
Sai a lokacin kuma Iya ta dage ta callara ghuɗa domin tabbatarma kowa dai anyi haihuwa.
Ba ƙaramin faɗuwar gaba wannan ghuɗa ta saka mama gaje ba, itace farkon isowa sashen su Ahmad kafin sauran matan gidan.
Sai dai yanda suka iske mai jego tsaf ya tabbar musu da haihuwar bata yanzu bace, nanfa aka shiga taya juna murna da tsokanar jariri kasancewarsa jika a wajensu.
Mama gaje dai ta ciki na ciki, dan duk a rikice tace tana ƙoƙarin danne wane kawai.
Gida dai ya kacame da murna, duk da farar safiyar nan yaran gidan haka sukaita rige-rigen bin gidajen yayunsu dan sukai musu labari.

Sanda Ahmad ya iso gidan kuwa, duk yanda yaso shiga ɗakin Ayyah su gaisa da Rumana hakan gagararsa yay, dole ya haƙura bayan yaɗan gaggaisa da matan gidan sukai masa barka da addu'a wa jariri dole ya haƙura ya koma ƙofar gida wajen abokansa da suma suka kacame masa da murna, bakinsa ya kasa rufuwa kuwa sai murmushi yake saki.

Mama gaje kam ɗaki ta koma tamkar wata zararriya, sai ƙoƙarin kiran Number Samina take yaƙi tafiya, sai tsaki take tana faman zagaye ɗakinta da waya a hannu, wani irin zafi na azalzalar zuciyarta🥴...........✍�?




_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_37_*


*_MATAR AUDU😜🥱_*



.........Lokacin da mama gaje ke a wannan ruɗani na neman number Samina ido rufe tana can suna tafka bala'i da Ma'aruff.
Dan gaba ɗaya a kwanakin nan dama sai a hankula, asirin da ke a jikinsa ya bar jikinsa, hakan yasa sam Samina ta kasa gane kansa a wannan lokutan.
A daren jiya kuma bayan sun gama rigima akan fitar da zaiyi ta dare ta tareshi akan baizai fitaba ya shashsheƙa mata maruka ya fice abinsa, zama tai taci kukanta gwargwadon iko ta haƙura dan kanta, sai kusan ƙarfe ɗaya ya dawo gidan, tana ɗakinta ta kasa barci har lokacin, amma sai bata fitoba dan duk zatonta shi kaɗaine yauma ya dawo a bigensa kamar yanda ya saba.
Sai dai bata saniba tare yake da karuwarsa, kuma sabuwar ƙawarta Basira, wadda suke kira (Basy), suka shige ɗakinsa kuma suka kulle kansu, ranar a nan Basy ta kwana.

Da safe Samina ta fito haɗa breakfast taci karo dasu a kicin babu mai suturar arziƙi tsakanin shi da karuwar tasa, wai yunwa takeji shine ya rakota ta haɗa shayi.
Neman zubewa Samina tayi, ta dafe bango da sauri tana ƙoƙarin maido hankalinta jikinta, dai-dai Ma'aruff da karuwarsa sun juyi zasu fita daga kicin ɗin, shi ɗauke da tiren da suka soya ƙwai da shayi a kofuna biyu.
Gabanta yay wata mummunar faɗuwa saboda ganinma wacece karuwar Ma'aruff ɗin, ko kunyar ALLAH baiji balle fargabar inda ya shigo wanda alamomi sun tabbatar mata a gidanma Basy ta kwana da mijinta, suna maƙale da juna lamarin zattakaici.
Zuciya kuwa ta kwashi Samina ta tare hanyar da za subi tana huci,
“Wannan la'ananniyar kuma daga ina bunsuru?�?.
Ma'aruff ya miƙama Basy tiren hannunsa yana kallon Samina, yace, “Bunsuru?�?.
Cike da tsiwa tace, “Ashe ka jini, guntun iskancin naka ya kai har ka ɗakko karuwa ka kawo mani cikin gidan aurena ku kwana saboda kai baƙin jahiline babu ilimin arabi a kank.....�?
Mari daya ɗauketa da shine ya hanata kai ƙarshen maganarta, ta faɗa jikin drawer kicin dafe da kunci, amma ta daure batai kuka ba, ci gaba tai da zaginsa daga shi har karuwar tasa.
Yako yunƙuro zai sake kai mata duka ta kauce, sai damar shaƙo wuyar budurwar ALLAH ya bata, nanfa kokawa ta ɓarke a tsakaninsu, shi sai ƙoƙarin ƙwaƙule hanun Samina yake daga wuyan basy yana faɗin, “K wai wace irin mahaikaciyace, ki saketa karki min kisan kai a gida!!!�?
Ko saurarensa Samina batayi, ta shaƙe Basy sosai sai kakari take idanunta duk sun firfito saboda tsagwaron matsa da taji.
Da ƙyar Ma'aruff ya yakice Samina daga jikin Basy, wadda tuni numfashinta ya rabu da gangar jikinta ta suma.
Dukan Saminar ya shiga yi tana ramawa itama, duk abinda ya tare mata gaba ɗauka take ta kwaɗa masa, a haka har suka fito falo, da ƙyar ta ƙwaci kanta ta afka ɗaki ta kulle tana danƙarama iyayensa zagi shima yana danƙarama nata🤦🏻‍♀😢.
Kan Basy ya koma yana jijjigata, sai dai yaga ashe ma ta suma, da farkoma ɗaukarsa kota mutu ne, sai da ya zuba mata ruwan sanyi ta kawo nannauyan numfashi.
Kuka ta sanya masa akan wlhy bazata yardaba, dama ya kawota gidansa ne dan Samina taci zarafinta, to wlhy saita ɗauki mataki bazata bar Samina tasha a banza ba.
Duk yanda yaso ta sauraresa sam taƙi, ta shiga ɗakinsa ta tattara kayanta, yana ƙoƙarin riƙeta tana tureshi da faɗin karya sake taɓata.
Yanaji yana gani ta fice daga gidan, ya zube a kan kujera yana dafe kansa ga raunikan da duk Samina tai masa, sun fasa abubuwa da dama na kwalliya da akaima falon, da ace yau zai iya sai ya saki Samina saki uku, to amma idan har ya saketa bai rama wannan abun da tai masa yau ba to lallai baici riba ba ma ashe, sanan shi ba namiji bane, dolene ya tabbatar mata shiɗin da gaske yamafi bunsuru kamar yanda ta ambata.

Samina na kwance ne tanata rusar kuka mai ciwo, tunda ta auri ma'aruff bata taɓa zaman kwana uku dashi ba cikin kwanciyar hankali, idan ta toshe wannan ƙofa sai ya buɗe waccan, sam farin cikin da taima kanta fata a gidansa gaba ɗaya ta kasa samunsa, wace iriyar rayuwace wannan?.


“To Samina, ni dai bily bansan wa kike tambayaba, fans ko kune?🤷🏻‍♀�?.


___________________________________

Duk yanda Ahmad yaso samun ganin Umm-Ruman hakan ya gagara, dan mutanema sake shigowa suke, jinjirinma sai da abokansa sukazone aka kawo musu shi soro sukai masa addu'a, sannan ya gansa a duk safiyar yau.
Yaje maida yaron ne cikin gida yayma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login