Showing 129001 words to 132000 words out of 165545 words
Ɓangaren Samina kuwa sai da su Ma'aruff sukai watanni biyar cif sannan suka dawo, saiko ga Mufida ta dawo da fatan surukarsu, dan ta dawone tana laulayin ciki, hakan ya tada hankalin Samina, musamman yanda kowa ke nuna ƙaunar wannan ciki hatta da shi kansa Ma'aruff ɗin.
Har takai ta kasa haƙuri sai da tai masa magana, aiko suka hau sama dashi, harda faɗin wai baƙinciki Samina ke masa saboda taga ya samu ƙaruwa, to sai dai ta mutu kuwa, duk baƙin cikinta shi dai ya rigada yayi mata rata, idan kuma tai masa hauka yanzu zata nufi gidansu da jan kati.
A harzuƙe tace, “Saime idan ka sakenin, wlhy ni murnama zanyi na rabu da ƙaddararern auren mashayi mazinaci�?.
Sai da yay mata wata dariya mai ƙularwa sannan ya haɗe rai, yace, “Aiko tunda kika nema saki da kanki bazan sakekinba, shashasha kawai sauran titi�?.
Samina ta kwashe da dariya itama duk da maganarsa ta doketa, tace, “Nida kai ɗinne dai duka sauran titin, kuma hukunci ɗaya ALLAH zai mana, garama ni na tuba.....�?
Bai ƙarasa jin abinda zata faɗaba ya fice.
Samina ta fashe da kukan takaici tare ɗunbin nadama da kaico na abinda Ma'aruff ke jifanta dashi a kullum na kiranta sauran titi..........✍�?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_42_*
.............Su Umm-Ruman nada watanni na bakwai a port wani abin farin ciki da cigaba ya sake riskarsu, dan kuwa dai karatun da Ahmad keta ƙoƙarin komawa ya samu gurbin yinsa a ƙasar Saudi-arebia.
Cikin tsantsar farin ciki ya iso gidan, lokacin Rumana na kicin tana girkin dare, Zainab na Assignment ɗin makaranta a falo, sai Haysam da suketa rigima saboda rarrafe da yake yanason hanata abinda take, idan ta janye buks ɗinta sai ya haye mata saman wuya yana ƴar ƙara ta wasa da akasan yara dashi.
Rumana na jiyosu daga kicin ita dai.
Zainab ta amsama yayan nata sallamarsa tana masa sannu da zuwa.
Amsa wa yay da fara'ar data bata mamaki sosai, sallamar Ahmad ɗin ta saka Haysam dake riƙe da kayan wasansa da Zainab ta bashi dan ya barta shima rarrafawa da hanzarinsa ya nufesa, kasancewarsu basu da yawa a gidan, kuma ba wani waje ake fita da shiba yasa duk yasan ƴan gidansu, ko Zainab ta dawo makaranta haka yake mata, gashi da wayo masha ALLAH, bazaka taɓa ɗauka watanninsa taraba kenan, har tafiya yaɗan fara gwadawa, sai dai tsoro kan hanashi miƙewa shi kaɗai sai ya dafa kujera ko bango.
Ahmad ya ajiye takardun hannunsa ya ɗaukesa yana murmushi, “Oh my king yoyoyo�?. Yay maganar da sumbatar kuncin yaron, zama yay a kujera Haysam na jikinsa, ya kalli Zainab yana faɗin, “Ina auntyn taki?�?.
Zainab dake ƙoƙarin miƙewa tace, “Yaya tana kicin, bara na kirata�?.
Wasa ya cigaba da yima Haysam, Zainab kuma ta nufi kicin kiran Rumana sai ma sukaci karo a hanya, dan dama Rumanan na jiyosu, kawai tana dai mamakin miya maidosa gida da wuri haka?.
Cike da shauƙi Ahmad ke kallonta, inba an faɗa makaba bazaka taɓa ɗauka itace ta haifi Haysam ba, musamman ma yanzu da Port ɗin ta kama jikinta, ta sake kyau dayin dumur-dumur abinta alamun samuwar kwanciyar hankali mai inganci.
Hannunsa ta taɓa, hakan yasashi kawo numfashi a hankali.
Ta ɗanyi murmushi tana faɗin, “Wannan kallonfa Zumana?�?.
Sashin da Zainab take yakai dubansa, duk da dai yasan da wahala ace tana nan dan inhar yana falon bata zama sai indan sune suka kirata.
Umm-Ruman ma inda ya kalla tabi da kallo, sai kuma ta maido idonta kansa, dai-dai shima ya juyo idanunsu suka shige cikin na juna.
Cikin tare numfashinta yace, “Gwal ɗina kodai na sake yin ajiya ne?�?.
Babu shiri ta waro idanu waje da faɗin, “Ajiya kuma Yaya? A ina?�?.
Sai da ya shanye ruwan data miƙa masa sannan ya bata amsa yana nuna Haysam dake wasa da kwalliyar gaban rigarsa.
“Ƙanuwar Haysam mana�?.
“Yaya rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mataba, yaron da ko shekara baiyiba�?.
Murmushi yayi yana shafa kan Haysam, yace, “Matsoraciya kawai, baki tambayeni na dawo da wuri ba?�?.
“Wlhy da wannan mamakin na fito My boss, sai ka mantar dani da wannan ƙyaƙyƙyawar fuskar taka�?.
“Kin rainani wlhy�? ya faɗa cikin faɗaɗa murmushin fuskarsa har haƙoransa na bayyana.
Itama murmushin tayi, kafin ta sake magana ya miƙa mata takardun gefensa.
Amsa tayi cike da ɗunbin mamaki, shikuma ya tsura mata idanu yaga yaya zatai.
Cikin tsagwaron mamaki ta ɗago tana kallonsa bayan kammala duba takardun guda uku, “Yaya dan ALLAH yimin ƙarin bayani, ban fahimci komaiba bayan sunan Saudia kuma da naka�?.
Kunnenta yaja har saida ta riƙe hannunsa tana ƴar ƙara sannan ya saki yana dungure mata kai, “Ashe a banza aka cima su baba kuɗin tara�?.
“Ba komai ai sun yafe�? Rumana ta faɗa tana dariya.
Shima dariyar yayi yana amsar takardun daga hannunta.
“Kinsan takardun minene?�?.
“Abinda nake jiran ji kenan Zumana�?.
Sai da ya sauke Haysam dake ƙoƙarin sauka daga jikinsa ƙasa sannan ya cigaba da faɗin, “Na makaranta nane, ammafa a ƙasar Saudi-Arebia�?.
Sosai Umm-Ruman ta waro manyan idanunta waje, “Yaya wasa ko gaske dan ALLAH?�?.
Hannunsa ya miƙa mata ta kama, yay mata nuni daya taso, babu musu kuwa ta taso ɗin ya ɗorata bisa cinyarsa, cikin magana a hankali kamar mai gudin a jisu yace, “Indai haihuwar Haysam bata zama wasaba haka shima wannan ba wasa bane Babie R�?.
Rungumesa Ruman tayi cikin murna tana dariya, hakan ya saka Zainab fitowa dan taga dariyar mi suke haka?.
Da sauri ta nema komawa baya amma sai Ahmad ya kirata, dole ta dawo kanta a ƙasa saboda a yanda suke, ya miƙa mata hannu itama alamar tazo, har lokacin kuma Rumana na jikinsa ya hanata tashi.
“Kinsa mi Auntynki kema murna?�?.
Kanta ta girgiza har sannan ta kasa kallonsu.
Sanar mata yayi itama, babu shiri Zainab ta faɗa jikinsu tana ihun murna itama, hakan ya saka Haysam fashewa da kuka saboda tsoratan da yayi.
Sakinsu Ahmad yayi suka maida hankalinsu gareshi, ganin yanda ya raɓe jikin kujera kamar wani marayane ya basu dariya.
Aiko suka shiga masa dariya, Zainab ta ɗakkosa itama tanayi.
Ahmad ya amshesa yana faɗin, “Sorry Abbanmu, kayi fushi kai ba'a faɗa makaba ko?, to tuba muke Sadaukina�?.
Zainab da Rumana dai dariya sukeyi har sannan, Rumana ta kalli Zainab tana faɗin, “Zainab haɗo masa abincinsa inagama yunwa yakeji�?.
Da to ta amsa ta nufi kicin, Rumana kuma ta nufi ɗakin barcinsu domin haɗama Ahmad ruwan wanka.
Bayan ta kammala haɗawa ta leƙo ta faɗa masa ga ruwa.
Amsa mata yay yana miƙama Zainab data fito Haysam.
Koda Ahmad ya shigo ɗakin Umm-Ruman saita sake rungumesa, alamar dai har sannan tana cikin farin cikin, ta haɗe bakinsu waje ɗaya, su oga Amadi dama kaɗan ake jira, koda Rumana taso janye bakinta sai yaƙi, ya kuma ƙanƙameta cikin sauke numfashi yake faɗin, “Yarinya ai kuma baki isaba, kin kawo kanki ai�?.
Za tai magana ya kuma maidawa, dole tai shiru ta koma amsar saƙwanninsa masu tsayawa a rai.
Daga ƙarshe dai tare sukai wankan🤫.
★★★★★★
Sati ɗaya da samun wannan takarda Ahmad ya tafi gida, wannan karon Rumana ta saka ran zaije dasu, amma sai yace saboda makarantar Zainab, dole ta amshi uzirinsa ta haƙura ya tafi ya barsu da kewa.
Ya zoma ahalinsa da farinciki mai yawa, yayinda maƙiya abin ya zafesu a zuciya, dan mama gaje yini tai haɗiyar zuciya, gashi ta kira Number Samina a rufe, da yamma kuma tace zataje gidan inna mari baba ya hanata.
Washe garin zuwan Ahmad aka sanya ranar su Fa'iza, dama akan hakan ne baba ya kirasa, sai kuma ga dalilin zuwan nasa akan tafiya karatunsa.
Wata ɗaya aka saka kacal, saboda Ahmad ne zaiyi komai, gashi kuma watan gobe idan ALLAH ya kaimu zai wuce idan yakai tsakkiya, nanda kwanaki 45 kenan kacal.
Bai bar kano ba saida ya tabbatar ya rage kaso mafi yawa na abubuwan buƙatar hidimar bikin ƙannen nasa guda biyu, kwanansa shida ya dawo akan sai biki kuma, zai ringa turoma Mudan kuɗi a hankali ana cigaba da rage hidimomi.
Ya tafi iyayensa na sanya masa albarka, tare da tsarabar da aka shiryama su Rumana.
Kasancewar tasan yau zai dawo da wuri tai gyaran gidan komai yay ƙal, dama ta wanko kanta a wani saloon dake nan kusa dasu, Haysam ma an masa aski daya ƙara fiddo ƙyawunsa, dan shima akwai suma ya gada uwa da uba.
Zainab dama tayi kitso kwanaki biyu da suka wuce saboda makaranta.
Alala tai masa mai daɗi, dan tasan shine abinda yafi so a rayuwarsa sai kuma tuwo, tai kwalliyarta cikin shadda siket da riga, inda shima Haysam akai masa gayunsa, zainab kam bata dawo makarantaba, dan lokacin ƙarfe sha biyu da kusan rabi.
Saboda tafiyar yamma yayo jiya sai gasu sun iso da wuri, a gajiye ya shigo gidan saboda zaman mota.
Yay sallama shiru babu amsa, sai idanunsa daya sauke akan Haysam dake barci a falo, yay murmushi yana ƙarasowa ga yaron, gaban kujerar ya durƙusa tare da ranƙwafawa ya sumbaci kumatunsa da goshinsa, yayinda hancinsa ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da yaron keyi.
Umm-Ruman dake bayansa tsaye bai saniba tai murmushi, sai da ya miƙe ta matso jikinsa ta rungumeshi ta baya tana ɗora kanta a bayansa, a tare duk suka sauke ajiyar zuciya, Ahmad ya ɗora hannunsa akan nata data zagaye cikinsa yana firzo iskar bakinsa, zagayo da ita yay gabansa yana ƙarema kwalliyar tata kallo.
“Gwal ɗina kinsan kuwa ke sarauniyace ko a cikin matanma?�? yay maganar yana ɗora goshinsa akan nata.
Murmushi tayi tare da dora laɓɓanta akan nashi ta sumbata kaɗan ba tare da tace komaiba.
Yana ƙoƙarin maida laɓɓansa akan nata zainab ta shigo da sallama, dukansu baya sukaja kowa yabar jikin ɗan uwansa.
Zainab dama bata lura da yanda sukeba tahau ɗokin ganin yayanta ya dawo, sannu da zuwa tai masa kafin ta ƙaraso ta duƙa tana gaisheshi da tambayarsa jama'ar gida.
Fuskarsa da ɗan murmushi ya amsa mata yana zama cikin kujera, ya tambayeta karatu tace Alhmdllh, saƙon gaishe-gaishen da duk aka aiko mata ya shiga lissafa mata, dai-dai nan Rumana ta dawo ɗauke da ruwa a kofi.
Gefensa ta zauna kaɗan ta tsiyaya masa ta bashi.
Amsa yay yana wani narke mata fuska cike da salo, ita dai ta kauda kanta tana murmushi, saima ta tashi zuwa ɗaki domin haɗa masa ruwa, harta gama ta dawo suna wajen shi da Zainab, Haysam dai bai tashiba yanata barci.
Kusan mintuna uku sannan ya miƙe zuwa ɗaki, Zainab ma ta nufi ɗakinta tana faɗin bara tazo taci abinci yunwa takeji, Rumana tai dariya cikin tsokana take bata amsa da, “Ai yau keda ɗanki banyi girki da kuba, iya yaya kawai zaici abincin gidannan�?.
Zainab taja birki cikin shagwaɓa take fadin, “Mi mukayi aunty?�?.
“Ku kuka sani, idan ya tashi ki tambayesa tsiyar da yaymin yau a gidannan, bugu yaci kafin nai masa wanka yay barcinnan�?.
Saurin dawowa Zainab tayi, ta duƙa gaban Haysam tana tattaɓashi da faɗin, “Kai aunty Rumana, dan ALLAH da gaske bugunsa kikayi?�?.
“Oh kin ɗauka wasa nake kenan?�?. Rumana ta faɗa tana shigewa ɗaki.
Zainab kamar zatai kuka taketa shafa kan Haysam dake barci lokaci-lokaci yana sauke ajiyar zuciya, yayinda haushin auntyn tata ya kamata.
Tana fiddoma Ahmad kayan da zaisa idan ya fito sai gashi ya fito ɗaure da tawul, ta baya ya rungumeta dukda laimar ruwan dake jikinsa, Rumana ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, “Wayyo Yaya jikinka sanyi�?.
“Da gaske?�? yay maganar yana shinshinar wuyanta tare da goga mata gashin ƙasunbarsa dake jiƙe da ruwa.
Tuni tsigar jikinta tahau tashi, babu shiri ta juyo tana fuskantarsa, ta ɗora hannayenta a wuyansa suna mai kallon juna ido cikin ido, kowanne fuska ɗauke da murmushi, Ahmad daya ɗan ranƙwafo saboda finta tsaho da yayi ya sumbaci kuncinta,
“Malama ƙarasamin�? ya faɗa yana juya idanu.
Rumana da bata fahimcesa ba tace, “Mizan ƙarasa?........�?
“Kiss ɗina na ɗazu mana�? yay maganar cikin tare mata numfashi.
Dariyar data sake narkar dashi tai tana ƙoƙarin zille masa, yay azamar turata jikinsa gaba ɗaya yana dariya, “Baki da man kai Babie R, karma ki ɗauka zan yafe sai kinyi, dan ɗazun naji kamar na make Zee ɗincan datazo ta katse min jin daɗi�?.
Sosai yanzunkam Rumana ke dariya, tace, “Autar Gwaggon zaka bige? Aiko da an cika tara�?.
“To ai ita ɗince tazo min a lokacin da bai daceba�?.
Rumana ta zame jikinta tana cigaba da masa dariya, “Nidai ka shirya kazo ga abinci karya huce ma, kasa a ranka daga goman dare har safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu duk nakane lokacin�?.
“Uhyim wayo ko Gwal? Shikenan na amsa, ALLAH yasa na jefa ƙwallona a raga to�?.
“Nikam wannan fata da kakemin Yaya ka bari, sai Haysam ya cika shekara huɗu�?.
“Humm haba yarinya wasan yara kenan, insha ALLAH nanda shekara huɗun kin yaye min babie gal ɗina mai kama dake�?.
Fita Rumana tai dan ta kula idan ta biyesa zasu kwana a wajenne.
Tare sukai zaman cin abincin su uku, har suka gama Haysam bai tashi ba, Ahmad ya shige ɗaki ya kwanta danya ɗan huta.
Bai samu ganawa da Haysam ba kuwa sai da ya tashi, cikin ɗoki da kewar juna ya rungume yaronsa yana mai jin farin cikin ganinsa cikin ƙoshin lafiya.
Shima yaron da ALLAH ya bama wayo tamkar ba ɗan fariba sai maƙalƙale Abbunsa yake
___________________________________
A ɓangaren Samina abubuwa sunyi tsamari sosai, dan kuwa kullum cikin takalarta fitina Mufida take, tun bata biye mata saboda cikin jikinta harta shiga tanka mata, kuma koda itace da gaskiya idan Ma'aruff yazo sai ya goya da bayan Mufidan.
Akwai randa sukai wani faɗa shari'a har gidansu Ma'aruff ɗin, amma ƙiri da musu mamansu Ma'aruff ta goyama Mufida baya duk da Samina ce da gaskiya.
Abinnan ya ƙonama Samina rai harta tafi gida, koda taje ta sanarma Mama gaje sai taita lallaɓata akan ta koma, dan yanzu idan maƙiyansu sukaji dariya zasuyi musu, tayi haƙuri watarana sai labari,