Showing 33001 words to 36000 words out of 165545 words

Chapter 12 - Gudu Da Waiwaye Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

362

ɗauke da ruwan leda a filet.
Koda ta ajiye a gabantsa sai ya tsirama ruwan ido kawai ba tare da ya ɗaukaba.
Hakan ya saka Rumana tsayawa tana kallonsa itama.
“Babu ruwane a gidan sai wannan?�?. Ya faɗa yana nuna filet ɗin.
“Na tambayeta ne shine ta bani wannan wai na rijiyar baida daɗi sosai suma wannan suke sha.
Filet ɗin ya tura gabanta, da alamun ɓacin rai a fuskarsa kaɗan yace, “Bani wancan haka nan�?.
Tamkar Umm-Rumana zata fasa kuka haka taji, yanzu mata tai musu abin alkairi kuma sai yace ta maida? To mi zata ce mata ita kuwa?.
“Zaki ɗauka ne? ko sai kin gama tunanin?�?.
Kafin ya rufe baki ta sungumi filet ɗin ta fice cikin sassarfa..............✍�?






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻R NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(12)*



............Jiki a sanyaye ta koma ƙofar ɗakin maman Amatullah.
Maman Amatullah dake zaune tana ɗura zoɓo a gorori na saidawa ta amsawa Rumana sallama tana faɗin “shigo mana Amarya�?.
Kunya duk ta lulluɓe Umm-Rumana, ta ajiye filet ɗin ruwan tana magana cikin in ina “Dan ALLAH kiyi haƙuri, wai ya fi son na rijiyan�?.
Murmushi maman Ama tayi, tace, “Amarya karki damu, haka maza suke, abinda suke buƙata kawai suke so, bara na ɗiba miki wannan yafi ɗan sanyi to�?.
Rumana dai batace komaiba, ta amsa ruwan tana mata godiya ta fice.
Inda ta barsa nan ta iske sa yana danna waya, ta ajiye kofin ruwan a gabansa “Ga shi�?.
Bai ce komaiba ya ajiye wayar.

Tana cin abincin da aka sakata dole tana satar kallonsa yanda yake shan magani kamar zaiyi kuka, sai yayi kamar zai sha sai ya fasa yana matse ido, idan kuma ya jefa a baki da ƙyar yake haɗiyewa kamar zaiyi amai.
Ba sabon abu bane a wajenta tunda tasan baya son magani, ya ɓata lokaci sosai kafin ya gama shan maganin da bai wuce kwayoyi shida ba.
Ficewa yay, mintuna kaɗan sai gashi ya shigo, botiki ya ɗauka ya fita tare da ƙaramin banbunsu.
Hakan yasa Rumana miƙewa itama ta shiga tattare kwankan da suka gama, ta ɗakko wani filet ɗin ta juye kazar jiya ta ɗora a tiren da zainab ta kawo abinci ta ajiyesu gefe.
Mamaki ya bata ganin yana ɗibar ruwa, da alama dai gugar ya fiddo dan ga ƙugiya nan a gefe ya ajiye.
Kwanikan ta ajiye gefe ta koma ɗakin, tana ƙoƙarin shiga ta tsinkayo muryarsa yana faɗin, “Ki kwashe kwanikan nan shima ki fiddosa�?.
“To�? kawai ta iya cemasa.
Yanzu ita ina zata saka waɗannan kwankan haka? Duk da basu da yawa ɗakin babu wani fili mai yawa daya rage, kuma dai bata ce zata jerasu a ƙasa ba ai.
Haka dai ta gama fiddasu ta ɗauki banbun takai masa, sai da ta ɗauraye shi sannan ta ajiye.
Ya ɗauki wanda ya cika da ruwan ya kai ɗakin, itako sai kallonsa take, dan banbun yanacin kusan boket huɗu.
Ruwan ta ɗiba a ƙaramar roba ta koma gefe tana wanke kwanikan, shi kuma ya ɗauki banbun data ajiye ya maidashi ƙofar ɗakinsu ya ajiye, idan ya cika botiki sai yaje ya juye.
Hakan da Rumana ta ganine ya sata miƙewa tabar wanke-wanken, idan ya cika botikin sai taje ta juye, a haka har suka cika banbun da botikan uku, biyu na roba ɗaya na ƙarfe.
Ƙarasa wanke-wanke tazo tanai, shikuma ya ɗauki ruwan botikin ƙarfen ya nufi bayi.
A lokacin kuma Maman Ama... Ta fito riƙe da Amatullah tana kuka.
Rumana tai murmushi tana kallonsu da faɗin, “A'a Amatullah yaya dai?�?.
“Rigima kawai mara dalili, ɗan zoɓon dana rage na ƙasan botiki ta zubarmin a ɗaki, shine kuma bazan gogeba sai na bar mata tai wanka a ciki�?.
Rumana tace, “Lallai hajiyar ɓarna kenan, ina Yayana shi? Ban ganshiba tunda na tashi?�?.
“Wannan ai tun jiya bama ya gidan, da ƙanwata tazo jiya da yamma ya maƙale mata sai da ta tafi dashi�?.
“ALLAH sarki, to ALLAH ya dawo dashi lafiya�?.
Rumana ta faɗa tana kama Amatullah data rarrafo wajenta.
Ɗaukarta tayi, ta zauna a bakin rijiyar tana mata wasa, ahaka Ahmad yazo ya wucesu.
Ƙin shiga ɗakin Amatullah tayi, har sai da ya leƙo, kamar ance ta ɗago sai suka haɗa ido, “Zonan�? ya faɗa kawai yana sakin labulen.
Miƙewa tai ɗauke da Amatullah ta nufi ɗakin.
Tsaye ta iskeshi yana taje sumarsa a gaban mirror, tace, “Gani Yaya�?.
Bai tankaba sai da ya gama, ya ajiye kum ɗin yana faɗin, “Bara naje can gida baba na kirana, naga babu abin girki ko?�?.
Tai jimm saboda bata gane kan tambayarba.
Katse mata tunani yay da cewar, “Risho nake nufi ko abin gawayi�?.
“Eh babu, amma inaga zasu kawo yau sukace�?.
“Okey�? kawai ya faɗa yana ƙoƙarin ɗaura agogo a hannunsa, mikuma ya tuna sai taji ya ja siririn tsaki tare da kuncesa ya buɗe jakar daya ɗauki kaya ya jefashi ciki, ya zaro wani ya saka, kumatun Amatullah dake miƙa masa hannu tanason ya ɗauketa yaɗan shafa ya wucesu batare da yace komaiba.
Rumana tai ajiyar zuya bayan ya fice tana ɗan girgiza kai, aranta tana tunanin ko yaya wannan zama nasu zai kasance kenan oho?.
Fitowa tai tsakar gida tanama Amatullah wasa, inda maman Ahmad ke ɗan mata hira daga kicin ɗinsu tana girkin rana.
Ita dai Rumana murmushin ta yafi hirar yawa, dan dama can ita bamai yawan magana bace, ta kuma kula Mama Amatullah akwai surutu.
A haka su Fa'iza sukazo suka iskesu, sosai Rumana taji daɗin ganinsu.
Suka shiga ɗaki sai shaƙiyanci suke mata, harda tambayarta wai yaya jiyan? Dan sunga Yah Ahmad a gida yanata ƙyallin angwanci.
Duka takai musu, suka kauce suna dariya, haka sukaita tsokanarta, kazar kuwa da suka gani sai da ta ɗiba musu, suka kuwa ci suna faɗin, “Tunda ke tsoro ya hanaki kici muko ci mukayi, Rumana wai dan ALLAH da wuya kamar yanda ake faɗa?�?.
Rumana ta kalli Salima mai maganar tana faɗin, “Minene?�?.
Gado Salima ta nuna mata da yin magana ƙasa-ƙasa kamar mai munafunci.
Tashi Rumana tayi tsaye, “Oh ni ALLAH ya shiryeku, ni dai babu ruwana wlhy, kuje ku tambayo Yah Ahmad ɗin mana�?.
“Kutumelecy amma baki da man kai Rumana yasin�? cewar Fa'iza.
Salima tace, “A'a so take ya maidamu niƙaƙƙiyar gyada ta ƙuli-ƙuli alkur'an, kinga kuwa yanzu da muka haɗu dashi a gida sai wani cin magani yakeyi, niko a raina har gulmarsa nayi, nace waishi Yah Ahmad yamayi auren bazai canjaba ne?�?.
Dariya Fa'iza da Rumana suka sanya, Salima ma mai maganar ta tayasu tana sake cewa “Wlhy na zata yau zan ganshi fuska a washe, Rumana ko dai baki bada kai bane?�?.
“Wai Salima yaushe kika koma hakane? To ALLAH ya gyara lamarinki da wuri, kema dai na kula auren kikeso�?.
Fa'iza tai saurin faɗin, “Mi takeci na baka na zuba, Wlhy Malam yace muma mu kawo mazan aure, wai muna gama jarabawa aure za'ai mana, abinda Yaya Samina tayi ya tada hankalin kowa, bazasu sake yarda ƴaƴansu suyi zurfi a karatuba sai dai idan mijinka naso ya kaika da kanshi�?.
Cikin marairaice murya Rumana tace, “Kuma godema ALLAH kuda gashi zaku ƙarasa, ni kam nasan ai nayi kenan�?.
“Karkice haka wlhy, tunda Yah Ahmad nason karatu zai barki ki ƙarasa, ALLAH dai yasa kar bebin mu yay shigar sauri kawai�?.
Hararta Umm-Rumana tayi.
Suka sanya mata dariya.
Daga nan suka koma hirar Samina, tare da iskance-iskancen data tsuro dasu a gidan a safiyar yau.
Rumana tace, “ALLAH ya ƙyauta to, ALLAH ya shiryeta�?.
Amin dai, su Fa'iza suka faɗa a tare.

Su Fa'iza na gidan har Sadiya da Na'ima ƙanwar Rumana suka kawo abincin rana da ƴan tarkacen kwanika da aka ƙara saima Umm-Rumana, harda ƙaramin risho da abin gawayi, sai Abu dake biye dasu da ƙatuwar jakkar Ahmad ta kaya da tarkacensa.
Sannu Rumana tai musu, suma suka zauna aka ɓalle hira, Abu nata zuba musu shirme suna kwasar dariya, yaran anguwa kuma nata shigowa jefi-jefi ganin ɗakin amarya, harma da mata maƙwafta ƴan gutsiri tsoma, dan yanda auren ya kasance duk ya shiga kunnensu.


_________________________


Ahmad kuwa koda ya fita dauriya kawai yakeyi, dan bayajin ƙarfin jikinsa sam, ga zuciyarsa har yanzu a cunkushe take, kansa kuma bai daina masa ciwo ba.
A majalisar abokansa ya fara yada zango, ya zauna suka gaisa yana sake musu godiya, sukuma suna tambayarsa jikinsa da amarya.
Yaja kusan minti talatin a wajensu kafin ya miƙe ya ƙarasa gidansu, sashen su Malam ya fara shiga suka gaisa, Malam nata saka masa albarka, hakama tsoffin da aka bari ƴan shema su huɗu da Iya, yaɗan daɗe anan ma, ya fito yana murmushin ƙarfin hali na tsokanarsa da sukeyi irin dai wasan jika da kaka.
Sashen Baba Ilyasu ya shiga, ya gaida matansa sannan ya fito zuwa Sashen su Rumana.
A tsakar gida ya iske Ammi da Mama gaje, kowa na hidimarsa, ya risina ya gaidasu tamkar yanda ya saba, Ammi ce kawai ta amsa masa cikin jin nauyinsa da batayi da, Mama gaje kuwa ɗaki ta shige bata amsashiba.
Bai damuba ya miƙe ya fito abinsa.
Ya shiga sashensu, ƴan biki duk sun kama gabansu, sai ƙanwar gwaggo kawai data rage bata wuceba inna Asma'u.
Da Ayyah ya fara cin karo a tsakar gida suna ƙoƙarin kwance zare a ƙafar ɗaya daga agwaginsa ita da Mudan.
Ya ƙarasa gabansu yana faɗin, “Ayyah miya sameta ne?�?.
“Wlhy ɗan albarka zarene ya sarƙe ƙafarta, gashi nama lura kamar ƙafar tata ciwo take tun jiya wajen taron nan, to ALLAH baisa nasamu kamata ba suka fice sai yanzu abun ya faɗomin arai, shine nashiga nemanta sai kuma na ganta jikin kejin kajincan a takure kamar wadda aka ɗaure, ashe zarene ya dabai baye ƙafar�?.
“To, bai dai ji mata ciwo ba ko?�?.
“Eh bai jiba, amma Yaya ina ganin gara a saidasu kawai, kwanan nan naji ana maganar agwagi suna fama da murgwi, na gidan malam kalla sai mutuwa suke suma�?. Madan dake maganar ya faɗa idonsa akan Ahmad.
Ahmad yace, “To Mudan saika cigita mai sayen muga idan zasu ɗanyi daraja, amma abar guda biyu, dan nagama wata fara mai yarfin baƙi kamar ƙwai takeyi�?.
Ayyah tace, “Ai naga kamarma fa ta fara ƙyanƙyasa da safenan indai ƴar budurwar nance...�?
Kafin Ahmad ya bada amsa Inna Asma'u ta fito daga ɗakin Gwaggo riƙe da kayan wankin Gwaggon.
“A'a, ango ɗan gidan Ayyah ne a gidan? Jiki yayi sauƙi kenan?�?.
Maida hankali gareta Ahmad yayi, ya taka zuwa inda take yana risinawa ya gaisheta, ta amsa cike da kulawa tana tambayarsa jikinsa.
Ya amsa da cewar da sauƙi.
“To Alhmdllh, ai haka muke son ji, Ina ɗiyar tamu amaryar ƙamshi?�?.
Kansa ya kuma sunkuyarwa ya amsa da cewar, “Tana lafiya itama�?.
Daga haka ya miƙe ya shiga ɗakin Gwaggo.
Tana zaune Zainab durƙushe gabanta tana cire mata abu a haƙori, sai yarfa hannu take tana kukan shagwaɓa na autanci.
Zama yay yana kallonsu, Gwaggo da sallamarsa kawai ta amsa ta bige hannun Zainab dake riƙe nata, “Idan bazaki tsaya ba tashi kiban waje, ji iskanci saikace ina cire miki rai�?.
“ALLAH Gwaggo da Zafi fa�? Zainab tai magana tana share hawaye.
“To jeki kicire da kanki mana�?.
“Yi haƙuri to zan tsaya ALLAH kuwa�? Zainab ta bama Gwaggo amsa.
Ahmad dake kallonsu baice komaiba ya lumshe idanu yana cewa “Ina kwana?�?.
Amsawa Gwaggo tayi kamar yanda ta saba masa, sai dai ta tambayi yaya jikinsa da Rumana?.
Yaji daɗi sosai, ya amsa mata murya a raunane.
Ita dai sharesa tayi, duk da kuwa ɗunbin tausayinsa da ga shi har Rumanar nacin ranta.
Shiru babu wanda ya sake tankama wani, har Gwaggo ta gama cirema Zainab haƙorin makka data sa ya maƙale yaƙi fita, tashi yay ya fito da ga ɗakin yaje ɗakin Ayyah suka gaisa itama.
Sai jero masa tambayoyi take akan jikinsa, yay murmushi saboda ganin yanda damuwa ke kwance a fuskarta, kwanciya yay a gadonta dan wani sabon zazzaɓi yakeji.
Ayyah dake kallonsa ta ɗora hannunta saman goshinsa tana faɗin, “Ɗan albarka wani zazzaɓinne fa? Anya kasha magungunanka?�?.
A hankali yace, “Nasha Ayyah, bani bargo sanyi nakeji�?.
Babu musu ta ɗakko Bargo ta rufa masa, ahaka barci yay awon gaba dashi.

Sai da aka kira sallar zuhur Ayyah ta tashesa dan yayi salla, yay alwala ya fito shi da Mudanseer, a soron gidan sukaci karo da Samina taci kwalliya zata fita, kallo ɗaya yaymata ya ɗauke idonsa, hakan yasa taja siririn tsaki.
Kasa jurewa Mudan yayi yay saurin kallonta yana cewa, “K da ubanwa kike?�?.
Baki ta taɓe tana tauna cingam yay ƙara ƙas-ƙas tai fari da idanu, “Da wanda ya tsargu man....�?
Bata kai ƙarsheba ya sauke mata mari, zai ƙara na biyu Ahmad daya juyo ya kallesu ya dakatar dashi da faɗin, “Kai wuce muje mana�?.
Samina kuwa sai ta fashe da kuka dafe da kunci, da gudu ta juya cikin gida tana kwalama mama gaje kira.

Ahmad sun dawo salla suka iske marin da Mudan yayma Samina ya zama Hayaniya a gidan, dan kuwa mama gaje hannun Samina ta kamo har sashen su Ahmad akan bazata yarda ba, wai Ahmad yasa Mudan ya daki Samina.
Gwaggo uffan bata ceba, sai Inna Asma'u ce ta tanka, sai ko Ayyah data idar da salla itama ta fito ta taya inna Asma'u, nanko abu ya zama hayaniya Mama gaje nata daddatsa magana wa jama'ar gidan, har Malam da Iya bata bariba, Ammin Rumana kam ai tafi kowa shan Zagi da su Ayyah.
Ahmad ya raɓa ta gefensu ya shige ɗakin Ayyah ya sake kwanciyarsa, ko kallon ɗaya a cikinsu baiyiba.
Hakan da yayi ba ƙaramin ciwo yayma mama Gaje da Samina ba, dan sunso ya tanka su hau kansa.
Mudanseer kam cayay inhar Samina bata bar sashenba wlhy dukan mutuwa zai lakaɗa mata, abinda ya ƙara rura hayaniyar kenan, Gashi su baba basa nan, sai da Iya ta shigo tai magana su Ayyah sukai shiru, Mama Gage kam ai kamar tunzurata akayi, taita zuba tsiya har sai da ta gaji tai shiru dan kanta............✍�?






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(13)*



..............Koda Ayyah ta shigo ɗaki nasiha tai tayima Ahmad akan wannan sabon lamari da ya shigo musu cikin gida.
Ahmad dake jin zazzaɓi yace, “Karki damu Ayyah, ni wlhy abunsu bai damuna,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login